Showing 6001 words to 9000 words out of 13265 words
Chapter 3 - Barauniya Amarya by sadnaf and Mrs fawwaz-1-1.txt
wanan halin naki bazaki taba iya dainawa ba koda kuwa kinada naki kud'in dan kinriga kin saba, d'auke d'auke gashi kin janyo wa kanki abun kunya kinje kinyiwa kanwar sirikinki sata, " katseta Kausar tayi tace " zandaina insha Allahu dan Allah kibani shawara yazanyi inkaucewa had'uwa da hajiyanan" shiru Jameela tayi tana tunanin tace "ki kwantar da hankalinki ba kince mai makeup ta taho ba, indai tazo wani irin makeup zakice ta miki tacanja miki kamani kinsan in akayi makeup din kamanin ma canjawa yake, dabaru zamu sata tayi ki canza kamani yanda Hajiyar bazata ganeki ba", wani irin ajiyar zuciya Kausar tayi tace kai amma naji dad'in shawararki, katseta Jameela tayi taringa mata fad'a data gyara halinta, zuwan Khalid da mai makeup ne ya katse mata shawarar da take bata, Kausar data fita Khalid dagewa yayi sai yakaita chemist tace mishi tasha magani, cemata yayi kud'i yabiya da tsad'a ayi mata makeup yanaso anjima inya ganta kar ya ganeta dahaka sukayi sallama, suka shiga cikin gida ita da
Mai makeup din.
Cikin awa d'aya da rabi Kausar ta canja kamani SADNAF TA KALLI MRS FAWAZZ tace "makeup shegen abune kinga yanda Kausar ta canja kamani" "ni muni ma naga tayi" Mrs Fawazz tace tana daga wuya dan taga Kausar sosai, "tashi murigasu zuwa wajen dinner muga ko Hajiya Zulaihat tazo, intaga Kausar B'??R??UNIY??R ??M??RY?? zata ganeta kuwa, Sadnaf tace tana yin gaba, mrs Fawazz da gudu tabi Sadnaf tana "kijirani mana sai zuba sauri" kike.
DINNER
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B'??RUNIY??R
??M??RY??
????♀
Na
S??DN??F
*&*
ʍʀs ʄaաաaʐ??
*®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
35-40
Mai makeup ta tak'ark'are sosai ta yi ma Kausar makeup Wanda idan ba farin sani kayi mata ba ba zaka tab'a gane ta ba,tayi kyau iya kyau,Jamila sai yaba kyau da tayi take yi.
Kausar ta ce mai makeup ta D'an basu waje zasu gana da jamilan
Bayan fitar ta Kausar ta dubi jamila ta ce "ya kika gani?" Murmushi Jamila tayi tace "wallahi ba k'aramin kyau kika yi ba Amaryar khaleed".
"Ke nifa tambayar ki nake ba za dai a gane ni ba ko?" Jamila ta ce "gaskiya ko ni ba Dan a gaba na aka yi ba da wallahi ba zan yi saurin gane ki ba ,ballantana ita da ta ganki sau d'aya".
Murmushi Kausar tayi had'e da wata ajiyar zuciya mai nuna alamun ta samu relief , suna cikin Wannan maganar sai ga call d'in ango ya shigo yake cewa sun iso fa,ta ce to suna zuwa.
Kausar ta dubi jamila ta ce "angwaye fa sun k'araso", jamila ta ce "Tou bara a yiwa k'awayen mu magana sai su fara fita".
Sai da kowa ya gama fita tukunna mai makeup ta D'an k'ara gyara ma Kausar face d'in ta sannan jamila ta rik'o tail d'in gown d'in Amarya suka fito, "subhanallah" shine abinda khaleed ke fad'i domin kyaun da ya ga Kausar tayi ba'a magana,
wedding gown ce a jikin ta,sai ta saka net d'in kanta ta rufe face d'in ta,da yake net rub'i biyu ne sai ba a ganin fuskar sosai. Khaleed fitowa yayi daga mota ya zo inda take, kama hannun ta yayi suka k'araso ya bud'e mata mota ta shiga ita kuma Jamila ta shiga gaba suka d'au hanya.
Khaleed yasa hannu ya bude net din ya ga yanda face din ta sha ado kamar doll baby, kasa d'auke idon shi daga kanta yayi, kallonta kawai yake yana k'ara godewa Allah da ya bashi wannan zankad'ed'iyar matar.
( kyaun D'an maciji)
Ya ce "my preety gaskiya ba k'aramin kyau kika yi ba, kin ci sunan sarauniya kyau, ke ni idan ma akwai abinda ya fi sarauniya kece, yau dai family na zasu ga matar khaleed, dama kowa ya samun ido ana son aga wadda zan aura",
Ita dai Kausar murmushin yak'e kawai take yi,amma har yanzu hankalin ta ya kasa kwanciya, a haka har suka isa wajen dinner d'in.
Jamila ce ta fita ta sanar cewa ga Amarya da Ango nan sun k'araso, don haka aka tattaro yaran da zasuyi flower girls, suka zo,sun D'an jima a wajen kafin aka jera yaran a gaba biyu kuma a baya suna rik'e da tail d'in rigar Amarya, gaskiya abin ya burge kowa a wajen suna tafe ana watsa ma Kausar da Ango flowers ,taku suke d'as- d'as dasu gwanin ban sha'awa, ai kuwa masu camera suka hau aikin su.
A haka har suka isa inda aka tanadar musu, zaman su da 10 minutes jigajigan iyayen ango Wanda suke ji dashi shima yake ji dazu suka taho wajen, a lokacin. E khaleed yake rada ma Kausar " ga Anty zulaihat din nan da nake gaya miki ta taho" ji tayi zuciyata fa fara lugude kamar zata fara k'irjinta ta fito waje.
Su Hajiya zulaihat suna karasiwa wajen ta ce yau dai zanga Amaryar khaleed dama jiya ta boye fuska ta hana ni ganinta amma yau duk abin ta siya na ganta". Jin haka ya sa Kausar jikin ta ya fara rawa kamar ana kada mata mazari, Anty Zulaihat ta sa hannu ta yaye net d'in da ya rufe ma Kausar fuska, suna hada ido Hajiya zulaihat ta ja da baya tana kallon Kausar din
Ganin haka yasa khaleed fara washe baki yace "Anty na ya kika ga Amaryar,ko duk kyaun ta ne ya sa kika rud'e haka?" Ta ce " hahh aa ba wai haka bane kawai dai ta min kama ne da wata shegiyar yarinya da tayi min sata, matsoraciya, Amarya ce fa amma ta ke sata,Amma ba ita bace wannan, Ai gaskiya Amarya tayi ka iya zab'e"
A nan Anty Zulaiha take Labartawa khaleed yanda suka yi da B'??RUNIY??R ??M??RY??
Jikin Kausar ya dinga rawa gumi ya dinga keto mata,khaleed kula yayi da yanda jikin Kausar ke rawa ya matsa yamata magana yace beauty me ya faru dake naga jikin ki narawa?
Tace ba komai kawai ni ban saba da shiga jama'a haka ba duk a takura nake
Yace Mata calm down my preety Ai ba wani Abu bane
Jamila ta lura da yanda gaba d'aya Kausar ta rikice don haka sai ta zo take mata magana a kunne tace ta nutsu mana kada a gano ki mana.
Lokacin da Hajiya zulaihat zata tafi ta zo sai ta sake zuwa ta kalli Kausar ta ce "Amarya baki da k'anwa ko wata 'Yar uwa mai suna Fatima?"
Kausar mak'e muryarta tayi don kart a gane ta tace "a'a"
Khaleed ya ce "kai Antyna lallai ba k'aramin haushin satar nan kika ji ba"
Ta ce "Ai kai kam Dole ne inji haushi mana zoben gold d'ina da mijina ya siya min tsinanniyar yarinyar nan ta sace ,Ai wallahi duk inda na had'u da yarinyar nan sai na tozarta ta na wulak'anta ta".
Khaleed ya ce "gaskiya bata kyauta ba dole kiji haushi".
Bayan an tashi ne a mota khaleed ke bawa Kausar labarin B'??R??u??NIY??R ??M??RY??, sai yake ce mata "Ai wallahi preety na na tsani sata bana shiri Sam da mai sata, don duk Wanda yake sata babu abinda ba zai iya aikatawa ba,ita kam waccan Amarya mijinta ya shiga uku, Ace matarka taje saloon tayi sata Ai wallahi abin kunya ne, yanzu da an kaita station d'in da wane ido zata kalli Angon ta gaya masa sata tayi ana shagalin bikinsu? Kai Allah ya sawwak'e,ba gwarama ta tambaye shi ba idan bata da kudi nE? Amma ace mace da sata? Ai gaskiya girma ta fad'i"
Kausar dai shuru tayi ta kasa cewa komai,don gani take kamar ya gane itace shi yasa yake mata hannun ka mai sanda.
Can dai khaleed yaji sai zuba yake amma Kausar tayi shiru ya dube ta yace my pretty ya dai? Ko jikin ne? Kai kawai ta d'aga mishi alamar "E" Amma bata yi magana ba don ita kadai ta San halin da take ciki.
Shi kuwa jin tace jikin ne yasa shi ya tausaya mata, sai sannu yake faman jera mata tana amshewa.
Sai da suka biya suya spot ya siya musu Chips da kaza sai exotic manya guda biyu sannan suka wuce gida.
Jamila kuwa tunda khaleed ya fara labarin b'arauniyar Amarya take dariya a ciki din ta San mutuniyar tata tana cikin wani hali,bata sake shan dariya ba sai da Kausar tace bata da lafiya da sannun da khaleed yake ta jera mata.
Lokacin da suka shiga gida Kausar gown d'inta ta cire ta shige toilet ta sauke gudawar da ta ke matsinta, Ai kuwa jameela ta sake kwashewa da wata dariyar tace "gobe ma kya kuma"
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 40-45
Kausar tana fitowa daga band'aki ta zube akan gado tana hamdala,tab'e baki Jameela tayi tace "dan Allah mai amfanin haka kinji dai abinda mijinki yace ya tsani mace mai sata, dan Allah Kausar ki gyara halinki da yau wanan matar ta ganeki dawane ido zaka kalli Khalid da danginsa,sata bashida amfani,yanzu kinga ma idan asirinki bai tonu yanzu ba zai Tonu nan gaba dan hajiya Zulaihat d'inan dole wataran ta ganki ba makeup ki kuma dubi alwashin data sha na tozartaki dan Satan da kikayi mata ya mata ciwo," ajiyar zuciya Kausar tayi tace Jameela ki tayani da addua bansan ya akayi na tsinci kaina acikin irin wanan mumunar d'abiar ba,amma insha Allahu na daina,yanzu basukan mutane danaci nake tunanin yanda zan biya kinga yanzu bashin wajen dubu dari uku da sittin ake bina,bansan ya zanyi ba,hajiya SA'A Dana karbi kuloli agurinta kawai dubu Dari da ashirin kud'inta agurina gashi bata wasa da kud'i gobe na mata alkawari bansan daga ina zan fara ba," tsaki Jameela tayi tace "tun farko Kausar ke kika janyo wa kanki ki ajiye kanki a inda Allah ya ajiyeki mana gashi kinzo kin d'orawa kanki bashin mutane,nidai shawarar dazan baki Allah cikin mutunci da mutunta wa duk wayanda kika k'arbi kayansa ki mayar mishi kice bakida kud'i da dai ki kara sata Kausar kinga nabaki shawara tin wuri ki tsira da mutuncinki karkiyi abinda mutuncinki zai zube a idon mijinki da mutane," kiran daya shigo wayar Kausar ne ya katse musu maganar dasuke,d'aukar wayar tayi ta gwallo ido tana kallon Jameela "ki d'aga mana kika tsaya kina kallona," "hajiya SA'A danake miki zancenta yanzu ita ke kirana wlh batada hakuri akan kud'i" Kausar tace tana daga wayar,bayan mintina uku ta kashe wayar tace " kinji ba wai bazata k'arbi kulolin ba sun d'ade awajena kud'inta kawai takeso goben nan yanzu jameela ya zanyi" ajiyar Zuciya Jameela tayi tace "ki tambayi Al ameen yabaki da dai kiyi sata Kausar ko rabine inya baki sai ki r'oketa ta daga miki k'afa ahankali zaki cika mata sauran" "to shikenan Jameela zan gwada tambayarsa Allah yasa nasamu" Ameen Jameela tace tana cire rigar jikinta.
Kausar tunanin yanda zata samu kud'i taringayi,Wanda kuma take ganin bai kamata ta tambayi Khalid kud'i ba sabida intana da tausayi yakamata ta tausaya mishi sabida bak'aramin kud'i ya kashe a bikinan ba,dan lura ma dayayi basuda karfi sosai shiyasa ya saki bakin aljihu dai dai da abincin da zasuyi a gidansu shi ya siya musu,ahaka ta kwana tana tunanin mafita har bacci b'arawo ya saceta.
Washegari k'arfe 11:30 duban mutane suka shaida d'aurin auren Kausar da Khalid akan sadaki dubu hamsin, Khalid sai washe baki yake cikin gidan yashiga da abokanansa suka sha hotuna da amarya Kausar data gaji da k'yau dan wanan Karin ba make up aka mata ba simple make up tayi ,takuma yi masifar k'yau Khalid kasa d'auke idonsa yayi akanta ji yake kamar ya rungumeta a cikin taron mutane,Allah Allah yaringayi yamma tayi akai mishi amaryarsa,bayan sunsha hotuna sitting room d'in gidan suka nufa da abokanansa dan anan aka ajiye musu abinci, amarya Kausar kuwa d'aurewa take tana dariya dan Hajiya SA'A tun da sassafe take damunta da waya akan kud'inta hakan shi ya jefata acikin zullumi da tunani,yakumbo kanwar hajjo ita tazo taja hanunta daga tsakiyar k'awayenta tace mata yayan mahaifinta na kiranta kasancewar shine walliyinta,suna isa wajensa ta durkusa akasa duka y'ayy'enta na wajen da Hajjon ita kanta,rafar dubu dari biyar biyar ya danka mata yace mata ga sadakinta ahannunta hakkinta ne tayi yanda taga dama dashi, yayi mata nasiha da add'uar zaman lafiya tskaninta da Khalid ya tashi dan yatafi,godiya tayi mishi,zuciyarta fall murna dan tasan yanzu ta samu kud'in dazata rage bashin Hajiya SA'A tasan indai tabata wanan dubu hamsin d'in zata d'aga mata K'afa,kawun nata nabarin d'akin da y'ayy'enta Hajjo ta d'auke kud'in daga cinyarta tace mata ataru rufawa juna asiri tasan cewar taci bashin mutane agarin yimata kayan d'aki sabida haka dashi zata rage bashin dake kanta,k'irga dubu goma tayi tabata tace ga shi ta rik'e ahanunta tunda kud'in hakkinta ne, Kausar gabad'aya ji tayi tarasa mai ke mata d'adi dan abinda tasa rai dashi gashi hajjo ta k'wace tahadata da dubu goma,a zuciye ta mik'awa hajjo dubu goman tace suhada su biya bashin dashi,tuni kuwa hajjo ta amshe ta sa mata albarka,mik'ewa Kausar tayi tabar d'akin rai a bace ta nufi d'akinsu Jameela ce ta tambayeta da mai yafaru taga ranta abace, labarta mata tayi,takuma d'auki wayarta ta nunawa Jameela taga yawan miss call d'in da hajiya SA'A tayi mata,akarshe ta fashe da kuka wai batasan yazatayi ba,rarrashinta Jameela tayi tace ta kwatanta mata gidan Hajiya SA'A taje ta bata hakuri ta d'aga musu k'afa,da wanan maganar hankalin Kausar ya kwanta,haka kuwa akayi Jameela taje tasamu Hajiya SA'A tabata hakurin ta d'agawa Kausar k'afa fir tak'iya tace tabasu nan da gobe Idan ba akawo mata kud'inta ba hukuma ce zata rabasu da Kausar dan wata d'aya kenan data kwasar mata kaya,babu irin ban baki da Jameela batayi mata ba tak'i ahaka suka rabu,tadawo ta gayawa Kausar yanda sukeyi da ita,atakaice abinda ya ragewa Kausar walwala kenan aranar har aka kaita gidanta tana tunanin yanda zata samu kud'i.
Khalid kuwa bayan abokanansa sun rakoshi sun siyi baki,sun musu addu'oi tashi yayi dan ya rakasu,wani abokinshi banbangida yaja shi gefe ya d'auko wani Leda yabashi yace masa kud'ine dubu dari uku da hamsin ya ajiye mishi jibi zai k'arba, dan yau babu banki ne da a banki yayi niyyar sawa bayaso kuma ya tafi da kud'in gida,karba Khalid yayi sukayi sallama yanufi cikin gida,da murmushi ya shiga d'akin yana "amaryata takaina ya zauna agefenta ya ajiye ledar akan gadon, yabud'e mayafin data rufe fuska dashi, tayi sauri ta runtse idanta Dan haka kawai takejin kunyar Khalid, wani irin runguma yamata kamar zai maidata ciki,sai daya jagwalgwalata ya cikata,yace ta tashi suje suyi alwala suyiwa Allah godiya mik'ewa yayi yad'auki ledar yabude ya fito da kud'in ciki ya duba Dan K'arba kawai yayi bai duba ba,Kausar ware idonta tayi sosai tana kallon rafar dubu dubu guda uku da rafar dari Biyar guda d'aya dake hanun Khalid, a drawer ya ajiye kud'in ya juyo tayi sauri ta kau da kanta hanunta ya rik'e suka nufi band'aki,Kausar kuwa tuni zuciyarta yafara raya mata abubuwa,ahaka sukayi sallah zuciyarta da hankalinta na wajen kud'in da Khalid ya ajiye acikin drawern,ahaka suka rayya daren tana tunanin kud'in.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????♀
N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Page 45-50
Khalid dasafe shi yataya Kausar yan gyare gyare,aka kawo musu breakfast daga gidan Hajiya Zulaihat,Kausar kuwa tun asuba da Khalid yashiga wanka taringa attempting din d'aukar dubu hamsin nakai sai wata zuciyar ta hanata haka ta hakura tana tunanin yanda zatayi,bayan sun gama breakfast suna zaune a Palo suna hira,kiran Hajiya SA'A yashigo wayar Kausar gabanta ne yayi wani irin fad'uwa atake murmushin datakeyi ya kau,Khalid kuwa dayayi noticing changes d' inta once,wayar hanunta ya k'arba dan yaga wake kiranta,ganin Hajiya SA'A a rubuce ne yasa ya kalli Kausar yace " wacece Hajiya SA'A"? Kausar da take da saurin kuka tuni hawaye ya ciko a idonta,hankalin Khalid ya tashi,Kausar da tayi niyyar boye mishi amma ganin batada mafita ne yasa tace bari ta gwada fad'a masa da dai ta d'aukar masa kud'i tunda su biyu ne agidan inta d'auke mishi dole zai San itace,cikin sanyin murya tace mishi bashin Hajiya SA'A taci dubu hamsin shine take damunta,shiru Khalid yayi yana tunanin can