Showing 1 words to 3000 words out of 16112 words
♡YAN TIRIRRISHI
(_~Ajalin Kaza!!!~_)
*"When fate calls, will you answer?"*
Story And Written By;
Khadeejarth Sabi'u Yahyah
Nainarh KD, As you know me.
The Writer of;
1. SARAUNIYAR KYAU
2. ANEESERH (THE INNOCENT GIRL)
3. TSANTSAR SO
4. KIN CUCENI
5. RANAR BIYAN BUƘATA
6. BA TABBAS
7. CAPTAIN AYUSHERH
8. ‘YAN TIRIRRISHI!
_A new blockbuster novel from the Nainarh KD the perfect pen, the story with the full of;_
# Love # Horror # Barkwanci
# Funny # Against The Perfect Exceptional Love!!
Free Book..From the beginning to the conclusion...
Dedicated to Maman Afrah..(Allah ya biya miki buƙatun ki na Alkhairi My ta musamman.
Copy is not allowed.¡!
Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!
_Assalamu Alaikum Jama'a barkanmu da sake kasancewa gaba ɗaya cikin wannan sabon
tafiya mai cike da abin mamaki mai taken, ‘YAN TIRIRRISHI._
_Godiya ga Allah SWT da ya bani aron lokaci ya kuma bani ikon kammala littatafaina a baya,
sannan ya nufe ni da fara wannan duka cikin iko da amincewarsa._
_‘YAN TIRIRRISHI labari ne mai ɗauke da sabon salo da kuma abubuwa da dama cikinsa yana
kuma tafe da sinƙi-sinƙin Barkwanci faɗakarwa nishaɗantarwa da kuma uwa uba jan hankali
musamman ga wasu matan da kishi yake rufe musu ido su aikata mummunar ta'asa ba tare da
tunani a kan me kaje ya dawo ba. Allah ya sa mu amfana da abin da labarin ke tafe da shi.
Allahumma Ameen._
Perfectly Pen's ️
Meet the amazing stories from the perfect writer's, Perfectly Pen's....
1. ‘YAN TIRIRRISHI
By Nainarh KD
2. SHIRYAYYIYAR KADDARA
By Queen Kainart
3. BAƘIN SHAFI
By OumYasmeen.
Official THRILLER...
https://chat.whatsapp.com/ICXo7IragdJBkz13G5ex9G
Title: ♡‘YAN TIRIRRISHI!♡
Author: NainarhKD
...Life as a Monster or Die as Human...❤️
Genre: Horror, Action, Comedy, Dystopian, Zombie Apocalypse
Tagline: "Survival comes at a deadly cost"
Description:
In a world overrun by the undead, humanity teeters on the brink of extinction.
______
Wani irin kuka Miemie ta fashe da shi lokaci guda kuma suna ƙanƙame juna ita da ‘Yar Gwal da
ita ma hankalinta yake a mugun tashe ganin wannan tashin hankali da tun da uwarta ta haifeta
bata taɓa gani ba.
“Innalillahi wayyo Allah na shiga uku ya tashi jama'a tashi ya yi fa!”
Rabi'ah ta faɗa a matuƙar ruɗe idanu warwaje take duban wannan mutumin da ya fara motsi
jikinsa yana wani irin makwashewa ƙasusuwansa suna bada wani sauti lokaci guda fuskarsa ya
koma wani irin abin tsoro ga saitin wurin da a ka cizesan ya yi wani mugun rami yana fitar da
wani wawwaran jini.
“Shima fa Zombie'n ya zama wayyo Allah!”
Haleema ta sake faɗa cikin tsananin tashin hankali tana ƙamewa wuri guda ta ma kasa motsi
bare tunanin gudun ceton rai.
Wani irin hautsinewa ƴaƴan cikin ‘Yar Gwal suka yi ganin mummunar halittar da Mutumin ya
koma da kuma jin abin da Haleema ta faɗa rashin abin yi da kuma tashin hankali ya sa ta ɗafale
bayan Miemie ba tare da ta sani ba tana sakin wani marayan kuka....
________
“Sannunku da ƙoƙari kuzo mu ƙari sa ciki.”
Cewar Haleema tana murmushi. Rabi'ah da ta juya baya tana ƙare ma garin kallo da gaba ɗaya
bai fi ta ƙirga yawan gine-ginen ciki ba acewarta ta juyo tana ya mutsa fuska tare da buɗe baki
zatayi magana daidai lokacin kuma ‘Yar Gwal ta fito daga cikin gidansu a guje hannunta riƙe da
kwalla mai ɗauke da manja Iya Sahu ta biyota ita kuma ‘Yar Gwal da batasan da Mutum
gabanta ba gadan-gadan ta nufo saitin da Rabi'ah da juyowarta ke nan take ai kuwa tun kafin
Rabi'ah ta yi wani yunƙuri tuni aikin gama ya gama domin daga kwallar mai ɗauke da manjan
har Manjan dake cike sama suka yi gaba ɗaya sannan da suka tashi yowa ƙasa basuyi masauki
a ko'ina ba sai saman fuskar Rabi'ah Manjan gaba ɗaya ya wanke ma ta fuska sannan ya
wanke farin Hijjabin jikinta yayin da sai da kwallar ta bugi goshin Rabi'ah sannan ta faɗi ƙasa,
Rabi'ah bata gama tantance abin da ke wakana a duniyarta ba ita ma ‘Yar Gwal da Marmara ne
ta taka ya sa ta yi wannan aika-aika ta faɗa jikin Rabi'ah ita ma ta sama nata rabon na manja
sai gaba ɗayansu suka yi ƙasa ji kake tim! Sun faɗi , Rabi'ah ta saki ƙarar azaba tana dafe
kwankwaso.
____
“Wayyo Allah Mommy! Kizo ki taimakeni tsoro nake ji wannan wacce irin masifa ce mutane da
an cije su sai dai su koma Zombie's gari ya koma tamkar maƙabarta!”
Cikin wani irin matsanancin kuka Miemie take wannan maganar hawaye nayi ma ta zarya kamar
ba gobe.
Kallonta Rabi'ah ta yi wannan karon bataji haushinta ba ko kaɗan sai ma tausayi da ta bata
hakan ya sa ta ɗan rungumota tana lallashi.
____
♡♡♡♡
Tafiya suka yi mai nisa daga wuraren da suke duk domin taya ƙawarsu murnar aurenta shi ya
sa suka yarda suka yi kasadar biyota wannan wuri da sunan su ɗin ‘YAN TIRIRRISHI ne sai dai
kwatsam ba tare da sanin dalili ko mafara ba sun tsinci kansu cikin wata iriyar duniya mai cike
da abin tsoro yayin da wata mummunar cuta ta yaɗu ba wai cuta ba ce da a ke samu ta
numfashi ko iska ko wani abu makarancin haka wannan daban ne wasu irin halitta ne na
matattu mutane da suke komawa ZOMBIE da sun cije Mutum cikin lokaci ƙanƙani komai nashi
yake sauyawa shima ya koma ZOMBIE. Ta ya kuke tunanin za su iya kuɓuta daga wannan
masifa? Wai ma mene ne mafarar wannan masifar ne?
Ku biyo alƙalamin NainarhKD domin warware zare da a bawa.
When a mysterious virus turns people into ravenous zombies, the few remaining survivors must
confront an unthinkable choice:
Become a monster to survive, or die as a human.
Follow the journey of a small group of survivors as they navigate the treacherous landscape of a
zombie-infested world, confronting the darkness within themselves and the true horror of their
new reality.
Questions for discussion:
1. Would you rather die as a human or become a zombie to survive?
2. How far would you go to protect your loved ones in a zombie apocalypse?
3. What does it mean to be human in a world gone mad?
Recommended for:
- Fans of zombie fiction and horror
- Those who enjoy dystopian and apocalyptic stories
- Readers looking for a thrilling and thought-provoking page-turner find out ƳAN TIRIRRISHI!
(The Zombie Apocalypse) Special journey of life to survive, good plot, love, and Chaos....
مسب* الله نمحرلا *ميحرلا
...01
Ragwajab kakeji lokacin da Motar ta tsaya cak ta bada wannan sauti. A hankali ƴan matan
suka fara saukowa daga Motar suna ya mutsa fuska kowacce da abin da ya dameta aƙalla za
su kai su goma sha ɗaya.
Cikin ƙosawa Rabi'ah ta ce. “wai driver mun ƙari so garin ne da naga an tsaya ko ya ya?”
Ta ƙare maganar lokacin da ita ma ta sakko daga motar tana miƙa na gajiya, bata jira driver ya
bata amsa ba ta kalla Haleema dake jingine da motar tana faman latsa waya ta ce. “Haleema
wai me ke faruwa ne ya naga an sauke mu anan kuma ban ga alamun gidaje ba sai
bishiyoyi....”
“karki damu ai mun kusa ƙari sawa, Suhaima ce ta nemi a tsaya wai fitsari takeji.”
Cewar Budurwar da Rabi'ah ta kira da Haleema tana yi ma ta nuni da wurin da Suhaima tabi.
Shiru Rabi'ah ta yi jin wacce a ka ambata, sai ta taɓe baki tare da jingina da motar tana ɗan
kallon dajin har idonta ya sauka a kan ta, dariya ta ɗan yi sannan a fili ta ce.
“wai ke, ko dai dole kika ma waccan Yarinyarne a kan sai ta biyo mu?”
Ta faɗa tana taɓo Haleema tare da yi ma ta nuni da Wurin da Budurwar ta ware take zaune a
takure sai lokacin Haleema ta lura ta ita dan a tunaninta bata fito daga Motar ba ma, girgiza kai
Haleema ta yi. “bana son sa ido fa Rabi'ah yanzu mene ne ruwanki da ita?”
Rabi'ah tana ƴar dariya ta ce. “babu fa amma gani nayi sai kace wacce a ka yi ma dole a kan
sai ta biyo mu...”
“ke dai kika sani.”
Cewar Haleema tana ci gaba da ƙoƙarin kiran lambar da take yi tun ɗazu sai dai saboda
yanayin wurin da suke babu network ya sa kiran bata shiga.
Rabi'ah kuwa nutsuwa ta yi tana ƙirga yawan ƴan matan dariya na cinta faɗi take. “lallai kam
gamu ‘YAN TIRIRRISHI mun faso gari wajen rai Goma lallai abin nayi ne...”
“ba goma ba ne mu goma sha ɗaya ne baki lura ba.”
Haleema ta katseta da faɗin hakan. “ai ke Amarya ce shi ya sa ban ƙirga dake ba.”
Rabi'ah ta faɗa tana gyara tsayuwarta jikin motar sakamakon hango Suhaima da ta yi ta tunkaro
wurin.
“Ƴan Mata a koma mota muyi mu ƙari sa please.”
Haleema da ta hango Suhaima ita ma ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa ta shiga Motar sai kuma ta
tsaya tana kallon Rabi'ah da ta yi bake-bake jikin Motar daidai lokacin kuma Suhaima ta ƙari so
wurin ba tare da ta kula kowa ba ta nufa hanyar shiga Motar sai dai Rabi'ah ta kare hanyar ba
damar shiga. “Malama bani hanya na wuce”
Suhaima ta faɗa ba tare da dubi Rabi'ah ba dan ta lura tun lokacin da suka baro Kaduna
Yarinyar neman ta da faɗa take yi ita kuma ba zata biye ma ta ba domin a halin yanzu bata cikin
hayyacinta sakamakon abin da ta gani ji take ma kamar ta fasa zuwa wannan ƙauyen da zasu
je domin TIRIRRISHI sai dai idan ta tuna wacece Haleema a wurinta sai taji ba zata iya watsa
ma ta ƙasa a ido ba gwara ta jira tun da zuwa gobe za su yi abin da ya kai su ana ɗaura Aure
za su koma Kaduna.
“Rabi'ah bakijin ta ce ki bata hanya ta wuce ne?”
Haleema ta faɗa tana duban Rabi'ah.
“e naji sai dai jira nake ta maimaita dan banma ɗauka tana magana ba.”
Rabi'ah ta faɗa tana matsawa gefe dan dama cewa ta yi koda bala'i sai ta saka wannan ƴar iya
yin ta yi magana kuma ta sakatan saboda haka burinta ya cika.
Suhaima bata ƙara cewa komai ba ta shiga Motar sauran ƴan matan ma duk suka shiga har da
Amarya Haleema sannan driver ya ja Motar suka ɗauki hanyar ƙari sawa garin da suka nufa.
“ke dallah Malama kin ishemu da wannan koke-koken sai kace saceki zamuyi haba ko kuwa
wani ne ya yi miki dole a kan sai kin biyomu wato ke ga kwaɗayayyiyar nama ko shi ne kin biyo
ƴan tirirrishi saboda kici daɗi sai kace ba gidanku muka fara zuwa ba domin muyi tirirrishin a can
amma kyatumarki ta yi mana ɗibar albarka har da haɗa mu da kare daga ƙarshe ma zani a
hannu na samu na baro gidan naku ina sauke haki waiku masu gidan Gate kar a lalata muku....”
Rabi'ah ke wannan sababi babu ƙaƙƙautawa dama takaicin da mahaifiyar Yarinyar ta gumsa
musu bai saketa ba gata ita kuma yanzu tazo ta wani ishesu da kukan banza.
Ɗiff Budurwar ta yi ta dakata da kukan duk da ba girme ma ta Rabi'ah ta yi ba hasali ma sai dai
su zo sa'anni sai dai kasancewar Rabi'ah ɗin tana da ɗan girman jiki shi ya sa za'a ɗauka ta
girme ma ta ne sosai.
“haba mana Rabi'ah Please ki barta taji da abin da takeji mana.”
Haleema ta faɗa cikin sanyin murya sannan ta kalla budurwar tare da faɗin. “sorry Please
Miemie Rabi'ah ɗin ce sai a hankali.”
“a'a fa Haleema ki dena tare ma ta ai gwara Rabi'ahn ta cicci ma ta kina gani dai har da ita cikin
masu yi mana kallon banza lokacin da muka je gidansu.”
Cewar wata daga cikin ƴan Matan mai suna Zieey.
“ya isa dai Dan Allah a bar maganar!.”
Haleema ta faɗa da son maganar ta ƙare a hakan dan har wani ciwon kai surutun nasu ya fara
saka ma ta duk da dai gefe guda ita ma bataji daɗin abin da mahaifiyar Miemie ɗin ta yi musu
ba sai dai ba yadda zatayi tun da Ƙanwar mahaifiyarta ce.
“ah maganar fa ba zata ƙare ba tsakani da Allah fa kina gani fa har yanzu ciwon da naji garin
gudun ceton rai bai dena raɗaɗi ba fisabilillah ki auna mana ki gani.”
Cewar Rabi'ah tana yi ma ta nuni da ciwon da taji a gwiwa garin gudun ceton rai lokacin da
Mahaifiyar Miemie ta sakar musu kare.
Haleema zatayi magana Suhaima da bata saka musu baki a firan ba ta riga ta da faɗin.
“amma ai koma mene ne ya faru bai kamata ki huce haushi a kan ita Miemie ɗin ba tun da ba
ita ce ta sakar muku karen ba”
“Oops! Su jaɓa an sako baki bara muyi gummm...”
Rabi'ah ta yi saurin katse Suhaima da faɗin hakan tana wani juyo ma ta ƙeya. Takaici ya cika
Suhaima tana shirin magana Haleema ta riga da. “dan Allah kiyi haƙuri Suhaima ke kuma
Rabi'ah mene ne haka Please ki bari mana ai gaskiya ta faɗa.”
Duk shiru suka yi ma ta ba wacce ta kulata Haleema ta girgiza kai don ta rasa me ya sa sam
babu ga maciji Tsakanin Rabi'ah da Suhaima duk da kasancewar yau ne suka fara haɗu wa ita
Rabi'ah da ɗan banzan Surutu ga faɗi ba'a tambaye ki kuma sannan bata barin kota kwana
yayin da Suhaima ta kasance miskila lamba ɗaya kuma bata shiga harkar kowa, shi ya sa
Rabi'ah takeyi ma ta kallon mai shegen jijjida kai ga kuma iya yi dan kawai ta kasance ƴar
minista. Dukkansu su biyun ƙawayen Haleema ne na makaranta ita Rabi'ah Secondary School
suka yi tare da Haleema yayin da ita kuma Suhaima sun haɗu ne a koleji, kuma dukkanninsu
suna mutunci sosai da Haleema shi ya sa a halin yanzu da lokacin bikinta ya yi suka zo ma ta
sai dai sam babu jituwa a tsakaninsu hakan kuma baya yi ma Haleema daɗi dan batason ta
kare ɗaya, ɗayan kuma taji haushi dan dukkansu tana ji da su a cikin ƙawayen nata.
*
“Ma sha Allah Alhamdullilah Allah ya yi mun ƙari so Wagga gari domin muyi tirirrishi kuma mu
‘YAN TIRIRRISHI nan gani nan bari kuma komai baƙin cikin Mutum dole mu ragargaji kaji!!!”
Rabi'ah ta ƙare maganar tana durowa daga Motar domin Motar nasu da suka taho cikinta irin
wannan Motar ce ta ɗibar shanu to a cikinta suka taho.
Su dai sauran ƴan Matan ma dariya Rabi'ah ta basu dan sun fahimci habaici take yi ma Miemie.
Yayin da Haleema ta girgiza kai kurum tasan halin Rabi'ah zatayi ma abin da ya fi hakan.
“Sannunku da ƙoƙari kuzo mu ƙari sa ciki.”
Cewar Haleema tana murmushi. Rabi'ah da ta juya baya tana ƙare ma garin kallo da gaba ɗaya
bai fi ta ƙirga yawan gine-ginen ciki ba acewarta ta juyo tana ya mutsa fuska tare da buɗe baki
zatayi magana daidai lokacin kuma ‘Yar Gwal ta fito daga cikin gidansu a guje hannunta riƙe da
kwalla mai ɗauke da manja Iya Sahu ta biyota ita kuma ‘Yar Gwal da batasan da Mutum
gabanta ba gadan-gadan ta nufo saitin da Rabi'ah da juyowarta ke nan take ai kuwa tun kafin
Rabi'ah ta yi wani yunƙuri tuni aikin gama ya gama domin daga kwallar mai ɗauke da manjan
har Manjan dake cike sama suka yi gaba ɗaya sannan da suka tashi yowa ƙasa basuyi masauki
a ko'ina ba sai saman fuskar Rabi'ah Manjan gaba ɗaya ya wanke ma ta fuska sannan ya
wanke farin Hijjabin jikinta yayin da sai da kwallar ta bugi goshin Rabi'ah sannan ta faɗi ƙasa,
Rabi'ah bata gama tantance abin da ke wakana a duniyarta ba ita ma ‘Yar Gwal da Marmara ne
ta taka ya sa ta yi wannan aika-aika ta faɗa jikin Rabi'ah ita ma ta sama nata rabon na manja
sai gaba ɗayansu suka yi ƙasa ji kake tim! Sun faɗi , Rabi'ah ta saki ƙarar azaba tana dafe
kwankwaso.
Yayin da su Haleema dake tsaye gefe daga masu salati sai masu ɓoye dariya domin yadda
al'amarin ya wakana ba ƙaramin daurewa Mutum zai yi ba wurin ɓoye dariya. Ita kanta Miemie
sai da ta dara musamman da ta kalla fuskar Rabi'ah da ta samu ta miƙe tsaye da ƙyar tana
faman kiran sunan Allah dan a tunaninta ma da aljanu ta yi gamo suka yi ma ta wannan
aika-aika ga goshinta da takeji tamkar