Showing 9001 words to 12000 words out of 16112 words

Chapter 4 - YAN TIRIRRISHI! Complete BY NAINARH KD.pdf

25 May 2025

1445

Jack dake tsaye a wurin ya kafa masa
haƙoransa irin na zombie a wuya wani irin masifafen zafi da raɗaɗi ya sa Daniel Jack ya
durƙushe ƙasa duk da haka idanunsa na kan Sadiq da tun da Daniel Jack ya yi gefe da shi ya
ɗan faɗi sai ya tsaya ganin ikon Allah cikin tashin hankali.


Cikin wani irin dauriya na jin raɗaɗi Daniel ya furta.


“Ka gudu Abokina ka ceci kanka sannan ka yi ƙoƙari ka dawo cikin hayyacinka ka dakatar da
ɓarnar da kuke shirin yaɗa wa Innocent people da yawa za su rasa rayukansu”

Shiru ya yi sakamakon ƙasusuwan jikinsa da suka fara wani irin ƙara idanunsa suna rinewa
zuwa sifar na zombie take kuma jikinsa ya fara wani irin malkwashewa shi kuma yana fitar da
ƙara da kuma gurnani.

Cikin kiɗima Sadiq ya tashi yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin da Daniel yake sai dai take wannan
Zombie ɗin ya fara ƙoƙarin kai masa farmaki hakan ya sa suka shiga ƴar tsere yayin da dabara
Sadiq yake tattara abubuwan sa masu amfani yana sakawa cikin wata backpack sannan ya
rataya a wuyansa zuwa lokacin shi ma Daniel ya gama zama zombie da wani irin masifar gudu
Sadiq ya baro Room ɗin tare da datse ƙofar sai dai tun kafin ya yi nisa wannan Zombie ɗin da
kuma Daniel shima da ya zama Zombie suka ɓalla ƙofar suka fito ma'aikatan wurin da basu san
abin da yake faruwa ba suka fara guje-guje sai dai duk wanda Zombie's suka samu cizo suke yi
zuwa wani lokaci shima kuma ya zama zombie hakan ya sa cikin ƙanƙanin lokaci ƙasa da
awanni ashirin da huɗu Kasuwar Zamani ko kuma a ce New World ta zama labari domin duk
jama'ar ciki sun koma zombie sai waɗan da Allah ya ba wa damar ƙubuta ƙauyuka da garuruwa
dake makwabtaka da kasuwar ma tuni Zombie's sun kai musu farmaki.
WANNAN KE NAN!
CI GABAN LABARI.
More comments more more and more na posting da zaku ke samu.!

♡‘YAN TIRIRRISHI♡

...©NainarhKDnkd's

https://chat.whatsapp.com/ICXo7IragdJBkz13G5ex9G

P.8,9

Baya suka ja da sauri ganin yadda yake tunkaro su yana wani irin gurnani, alama Habib yake yi
musu da suyi su bar gidan ya musu nuni da hanyar fita sai dai tsoro da tashin hankali ya sa
suka kasa fahimtar abin da yake nufi dan sun kasa ma motsi, da gudu ɗaya daga cikin matan
gidan ta nufa wata hanya daban bana fita ba tana kurma ihu ai kuwa shima Zombie'n ya mara
ma ta baya kafin ta ankara ya cakumota sun fara ciniya yayin da ya sama nasarar cizonta a ciki
ya farka wurin ya zaro ƴan hanjinta ya kai musu wawusa, wannan tashin hankalin ya sa Iya
Sahu sumewa Haleema da ita ma takeji dama sumar tayi da ya fiye ma ta ta yi saurin tarota
ganin zata faɗi tana kiran sunanta shi kuwa Habib hannun Rabi'ah ya damƙa bai sake bi ta kan
kowa ba ya nufa waje da ita ganin haka ya sa duk suka mara masa baya cikin tashin hankali
amma banda Uwani da ta tsaya ƙiƙam ta kasa gaba bare baya.

“Me kike jirane Uwani kizo muje ko kuwa so kike kema ki mutu?”

Ƴar Gwal da ta ɗan dakata ta faɗa tana duban Uwani, a hankali Uwani ta ɗa go ta duba Ƴar
Gwal sai kuma kawai ta fashe da kuka tare da zaman ƴan bori a ƙasa, takaici ya sa Ƴar Gwal
taji kamar ta shaƙeta, ji ta yi kamar ta tafi ta barta, sai kuma ta ƙari sa wurin Uwanin da gudu
tare da damƙo hannunta Uwani ta miƙe tsaye tana share majina da hawaye sun yi taku ɗaya
biyu a na ukun sai ji Ƴar Gwal ta yi Uwani ta maƙale taƙi ci gaba da tafiya.

Kallon yanzu kuma mene ne abin da kike nufi Ƴar Gwal ta yi ma Uwani sai kuwa Uwani buɗar
bakinta sai cewa ta yi.
“Wayyo Allah Abincina! Abincin ‘ƳAN TIRIRRISHI”

Slowly Ƴar Gwal juya gaba ɗayanta tana bin ta da wani irin kallo na takaici sai dai kafin ta kai ga
furta komai Uwani ta juya da gudu ta nufa ɓangaren ta da gudun da ta yi ne kuma ya dawo da
hankalin wannan zombie ɗin kanta daidai kuma lokacin Ƴar Gwal ta mara ma ta baya da yake
ta saitin zombie ɗin ne sam bata lura da yadda hankalinsa ya dawo kansu ba.

“Na rantse da Allah idan baki fito ba zan tafi wato ke ana gari ba lafiya ke kuma ta abinci kike.”

Ƴar Gwal da ta tsaya a tsakiyar ɓangaren Uwani ta faɗa hakan cikin ƙosawa daidai lokacin
kuma Uwani ta fito kinkime da kuloli har biyu ta buɗe baki zata yi magana idanunta suka yi
kyakkyawan ganin da ya sa ba shiri kula ɗaya dake hannunta ta suɓuce ta yi ƙasa ita kuma ta
saki baki so take ta kwala ihu ko a kawo ma ta agaji amma ta kasa bare har ta ankarar da Ƴar
Gwal abin da ta gani, ganin yadda Uwanin ta yi ne ta kuma kafe gefe guda da kallo ya sa Ƴar
Gwal juyawa domin ganin abin da Uwanin ke kalla da ya sa ta kafe wuri guda kamar wata
Status.

Ai kuwa idanunta suka yi ma ta karo da wannan zombie da yake tunkaro ta cikin wani irin tafiya
yana jan ƙafa sakamakon hannun bokitin ƙarfe da ya maƙale masa a ƙafan tashin hankali da
ruɗani ya sa Ƴar Gwal ta rasa abin yi sai kawai ta rimtse idanunta da ƙarfi ganin yadda ya wani
tunkaro ta yana buɗe bakinsa dake malalar jini ga fuskar nan tasa gunin ban tsoro da tashin
hankali.

Shiru ta yi tana jiran mai afkuwa tana jiran taji an damƙi wuyanta ana yagan naman amma jin
shiru ba abin da ya faru ya sa slowly ta fara buɗe idanunta sai kuwa ta ware su kan Habib dake
kokawa da Zombie da sauri ta ƙara ware idanunta cike da mamaki a zuciyarta ta ce. “Shi
wannan ko tsoron wannan mugun abu ya cije sa shima ya zama irinsa baya yi?”
Cikin Sa'a Habib ya sama nasarar tura Zombie'n cikin wani ɗaki dake ɓangaren da ba komai
sannan ya maza ya rufo ƙofar, dubansu ya yi yana sauke haki.

“Ku tafi..”


Ai tun kafin ya rufe baki Uwani ta yi gaba ko ta kan kularta guda ɗaya da ta faɗi bata bi ba, ita
kuwa Ƴar Gwal tsaban neman magana sai da ta ƙari sa ta ɗauki kular abincin da Uwani ta ƴar
sannan ta bi bayanta sai da Habib ya tabbatar da sun yi nisa sannan ya mara musu baya.

Da yake lokacin da suka fita har sun shiga mota Rabi'ah ta ankara da Ƴar Gwal bata fito ba shi

ne ta roƙi Habib da ya dawo ya taho da su shi ne ya dawo.


Cikin motar Habib da Rabi'ah ke zaune gaban motar Ƴar Gwal da Uwani suka shige yayin da
shi kuma ya shiga mazaunin driver sauran Motocin guda biyu kuma na ‘ƳAN TIRIRRISHI shi su
Haleema suka shiga Allah ya taimake su Direbobin suna nan.

Da wani irin gudun tsiya suka ja motocin domin barin ƙauyen sai dai kuma me? Babu hanya
domin rabi da rabi na mutanen ƙauyen sun zama Zombie's kuma wurare da dama wuta ke
kamawa a ƙauyen shi ya sa gaba ɗaya hanya ta toshe sun kasa samun hanya ga kuma yadda
Zombie's ɗin suke ta uban kai ma musu farmaki da yake motar Habib ne a gaba shi ya sa ya
kusa yabi da su ta cikin daji cikin tsula gudu sauran motocin na take masa baya.

*Abuja, Nigeria.*

Tun waye war garin yau ta lura da ita sam bata cikin nutsuwarta kuma da an tambaye ta sai ta
ce ba komai shi ya sa ta bari sai da suka bar cikin mutane kasancewar gidan maƙil yake da ƴan
biki sakamakon yau ɗaura aure, bayan an ɗaura auren Wuraren uku na yamma ta sameta a
bedroom ta zauna shiru da alama ta yi nisa ne a Duniyar tunani.

“Mama! Mama”

Ta kira sunanta sai dai shiru hakan ya sa ta ɗan taɓe ta tana ci gaba da kiran sunanta firgita ta
yi sai kuma ta dubeta tana ƴar dariya ta ce.

“Ah Hafsa kece? Yaushe kika shigo ban sani ba?”

Bata ce mata komai ba sai da ta zauna gefen gadon suna fuskantar juna sannan ta dubeta cikin
kulawa ta ce.

“Mama ba tun yau ba tun jiya nake lura kamar wani abu yana damunki kamar kina cikin damuna
amma da an tambaye ki sai ki ce babu komai bayan kuma da komai ɗin ko dai abin da
Mommyn Miemie ta yi ma Aunty Haleema da ƙawayenta ne ya sa kike damun kanki har haka?”

Girgiza kai Mama ta yi sannan ta ce.

“Da wannan dan wannan amma a sanin halin Zuwaira (Mahafiyar Miemie) da nayi zata aikata
fiye da hakan shi ya sa ban damu ba ko kaɗan duk da abin da ta yi ya yi min zafi sosai saboda
ita ɗin ƴar uwata ce ɗaya kwallin kwal da nake da amma ta biye son zuciya.”


Cike da takaici Hafsa ta girgiza kai ta ce.

“Ai Mama indai Mommy Zuwaira ce zata yi abin da ya fi haka ba gashi ba saboda tsaban rashin
ta ido bayan tayi ma su Haleema wannan tsiyar kuma har da wani iya haɗa su da ƴarta, dama
fa baƙin ciki kawai take yi saboda Haleema zata aura wanda ya fi mijin da ƴar ta take Aure
komai na rayuwa kama daga kuɗi nasaba da kuma kyawawan halaye....”
“To ai shikenan ai ta yi ma kanta ni yanzu abin da yake ɗa ga min hankali wannan doguwar
tafiya da su Haleema suka yi zuwa ƙauye tun da suka tafi hankali na ba'a kwance yake ba sam
wani irin faɗuwar gaba nake ji dana rasa dalili gashi tun safe nake gwada kiran layin Haleema
amma bata shiga.”

Mama ta katse Hafsa da faɗin hakan cikin yanayi na damuwa.


♡‘YAN TIRIRRISHI♡

...©NainarhKDnkd's

https://chat.whatsapp.com/ICXo7IragdJBkz13G5ex9G

P.10,11.

“Karki damu in sha Allahu ma babu abin da yake faruwa sai Alkhairi kin manta can ɗin ana iya
samun matsalar network ne?”

Cewar Hafsa ta faɗa hakan ne ba dan komai ba sai dan kwantar ma da Mahafiyar nata hankali
duk da ita ma tana cikin damuwa domin tun bayan ɗaura auren ango da kansa ya kirata yana yi
ma ta ƙorafin tun safe da suka yi waya da Haleema bai sake samun layinta ba shi ya sa
hankalinsa ya kasa kwanciya, lokacin da yake faɗa ma ta haka ba ƙaramin tashin hankali ta
shiga ba sai dai ta daure tare da faɗa masa ya kwantar da hankali ba wani abu wata ƙila
matsalar network ne da haka ta rabu da shi sai dai ganin an kawo i yanzu ba wani labari ita ma
hankalinta ya tashi sosai musamman da ya kasance ba'a samun layin kowa hatta shi ma Uncle
Iliya da bayan ɗaura aure ya kama hanyar komawa ƙauyen, daurewa kawai ta yi ta hanyar ci
gaba da kwantar ma da Mama hankali da tausasan kalamai na kuma tabbatar ma ta sa in sha
Allah ba abin da yake faruwa da haka ta samu ta bar bedroom ɗin.
*****
Tafiya suka yi mai ɗan nisa kafin motar Habib ta maƙale wuri ɗaya duk yadda ya so ta ci gaba
tafiya abu ya cutura gashi cikin daji suke kuma yamma ta fara sako kai a dole duk suka fito
daga motocin ganin nasa ya tsaya yayin da ya je yana duba matsalar dake damun motar su
kuma suna tsay-tsaye cirko-cirko cikin rashin madafa Iya Sahu lokaci-lokaci take share hawaye
da an tambayeta sai taƙi kula kowa can kuma sai cewa ta yi.
“Allah Sarki Tasalla (Abokiyar zamanta) ko wani hali take ciki yanzu ita da surukanta oho.”

Sai suka ga Iya Sahu ta saka kuka har da wani sheshsheƙa.
Duk shiru suka yi dan sun ma rasa abin faɗa sai Haleema ce ta sama zarafin faɗin.
“Kiyi haƙuri Iya Sahu in sha Allahu ba abin da ya samesu kamar yadda muka gudu suma za su
sama wurin ɓuya...”
“Wani na yi haƙuri ƴar nan kina dai gani a gabanmu wancan mugun halittar Zommie ko me
kukace sunanshi ya cije ɗaya daga cikin surukan Tasalla, shikenan ita ma nasan zuwa yanzu ta
zama kamar sa ni dai ba zan gaji da faɗin Allah ya kwashewa waɗan da suka ƙirƙiro wannan
masifa albarka ba shikenan ƙarshen duniya tazo.”
Iya sahu ta sake fashewa da kuka bayan ta kai nan a zarcenta abin nata ya basu dariya da
kuma tausayi haka dai Haleema ta ci gaba da rarrashi.

“Yanzu ya zamuyi ke nan ba zai yiwu mu ci gaba da tsayawa anan na tsawon lokaci ba saboda
Akwai matukar haɗari yin hakan gashi kuma dare na kawo kai motar taka kuma taƙi yi...”

“Haba Muhsin wani irin magana kake haka au wai kai da a tunaninka ci gaba da tsayawa
zamuyi a nan wallahi ba zata saɓu ba idan kaga zaka iya Allah ba mai rabo Sa'a ni dai kaga
tafiya ta kawai ina ji ina gani ba zan bari na kashe kaina a banza ba.”

Ɗayan Drivern ya katse ɗayan da ya fara magana yana maganar bai ma sake bi ta kan wanda
ya kira da Muhsin ɗin ba ya shige mota yaja da gudu ya bar dajin ya ƙara gaba duk irin kiran da
Muhsin ɗin da su Haleema suke kwala masa yaƙi tsayawa ai kuwa ko dena hangosa basu yi ba
kamar ance Mary ta duba gefenta kwatsam taga Zombie's har guda uku suna tahowa ɗaya ma
babu hannnaye da ƙafa ɗaya a tare da shi amma tsaban bala'i haka yake jan ƙafa ɗayan domin
ƙari sawa gare su ya sama naman bil'adama kuma ba komai ba ne ya nusar da su da mutane a
wurin sai ƙarar motar da Drivern ya ja da kuma ihun kiransa da suke yi.

Wani uban ihu ta kwala tana ja da baya cike da tsoro jikinta babu inda baya rawa take suma
sauran suka ankara da abin da ta gani sai dai ruɗani da tashin hankalin da ta shiga ya sa ta
kasa tashi daga faɗi ƙasa da ta yi lokacin da ta kurma ihu ai kuwa wani irin super ɗaya daga
cikin Zombie'n ya yi tare da kai ma ta wani mummunar cizo a kunne yayin da ɗayan yake wani
gurnani yana jan ƙafarsa ɗaya ɗayan kuma shima ɗaya daga cikin ƳAN TIRIRRISHI'n ya kaima
farmaki take kuwa ya cije ta duk yadda Mary ta so kwace kanta abu ya cutura har sai da
wannan zombie ya ɗayo naman kunnenta tsaban cizo take ta shiga kurma ihun azaba cike da
jin raɗaɗi.


“Wayyo Allah Mommy! Kizo ki taimakeni tsoro nake ji wannan wacce irin masifa ce mutane da
an cije su sai dai su koma Zombie's gari ya koma tamkar maƙabarta!”

Cikin wani irin matsanancin kuka Miemie take wannan maganar hawaye nayi ma ta zarya kamar
ba gobe.

Kallonta Rabi'ah ta yi wannan karon bataji haushinta ba ko kaɗan sai ma tausayi da ta bata
hakan ya sa ta ɗan rungumota tana lallashi.


Ganin yadda gadan-gadan Zombie'n da ya cije Mary ya tashi ya nufe su ne yana wani irin
gurnani kuma da masifan gudu ya sa suma duk juya suka juya suka fara gudun ceton rai
Haleema riƙe da Iya Sahu yayin da Suhaima ta taimakawa Mary ta tashi tsaye haka ma Zieey ta
nufa wurin ɗayan budurwar domin taimaka ma ta su gudu sai dai ganin yadda ta fara wani irin
gurnani ƙasusuwanta suna bada wani irin sauti jikinta yana makwalkwashewa idanunta sun
sauya kala lokaci guda kuma fuskarta ta koma abin tsoro sak irin na zombie shi ne dalilin da ya
sa Zieey ta tsaya cak cikin matsanancin faɗuwar gaba ta fara ja da baya ganin yadda a wani
karkace kuma ta kwance budurwar da ta koma zombie take tunkaro ta kafin kuma ta wani irin
miƙe wa tare da daka tsalle ta cakumo Zieey da niyyar kai ma ta cizo ihun da Zieey ta kurma da
kuma ƙarar da ya ninka wanda Zieey ta yi wanda wannan zombie ɗin da ya ciza Mary da kuma
mai shirin cizon Zieey suka saki lokaci guda ne ya dakatar da kowa daga gudun da suka fara
jinin da ya tallatsa ya wanke fuskar Zieey sakamakon harbin Zombie'n da a ka yi a ka shi ne ya
sa Zieey kusan suma cikin dauriya ta cillar da Zombie'n da ta ɗafale ma ta tana wani irin zaro
ido kafin lokaci guda su gaba ɗaya suka ɗaga kai domin ganin mahalukin da ya yi ma waɗan
Zombie's harbi irin na kwarewa a kai da lokaci guda suka mutu sai kuwa suka yi karo da shi
tsaye sanye da t-shirt da wanda sai backpack da ya goya hannunsa riƙe da bindigar da ya yi
amfani da ita gefensa kuma wani Matashi ne shima tsaye sai dai da gani kasan a tsorace yake
lokaci guda kusan mutane huɗun nan wato Iya Sahu da Haleema da ma Uwani da Ƴar Gwal
suka haɗa baki wurin faɗin.

“Kawu Iliya.”


Yayin da a daidai lokacin zuciyar Rabi'ah dana Suhaima ta yi mummunar bugu na ganin
Matashin da ya yi harbin can ƙasan maƙoshi Rabi'ah ta furta.

“Sadiq S Sulaiman?!”

Ita kam Suhaima sai cewa ta yi a fili.

“Abbakar Sadiq?”

A tare daga shi har Matashin dake gefansa da su Iya Sahu suka kira da Iliya suka kalle
mutanen wurin sai dai an rasa mai magana sai kallon kallo kawai da a ke yi ita Haleema ma sai
da taji Suhaima ta ce Abbakar Sadiq sannan ta gane shi ba kowa ba ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login