Showing 6001 words to 9000 words out of 16112 words

Chapter 3 - YAN TIRIRRISHI! Complete BY NAINARH KD.pdf

25 May 2025

1448

ɗin Soja ne”


Maganar da ta yi ya sa Ƴar Gwal zaro ido tare da kwanciya ba shiri tana rufe ko'ina na jikinta
sannan ta duba Rabi'ah ta ce.

“Sai da safe!”

Maganarta da kuma reaction ɗinta ba ƙaramin dariya ya bawa Rabi'ah ba.


Hakan ya sa ta dara tana ɗan girgiza kai dama su biyu suka rage basu kwanta ba hakan ya sa
ita ma ta yi kwanciyarta.



WASHEGARI!


Kasancewar da wuri motocin guda biyu da suka lalace musu a jiya suka ƙari so kuma da yake
duk wani abu da za su amfani da shi yana ciki shi ya sa sai da suka jira ƙari sowar Motocin suka
kawo musu kayan sannan zuwa sha ɗaya na safe suka fara aiki ka'indana'in abinci suka girka
kala-kala lafiyayyu na gani na faɗa gidan sai ƙamshi ke tashi da yake ɓangare guda a ka basu
kuma anan suka kwana jiya wato ɓangaren Uwani Matar Kawu Iliya da yake baya nan ita kuma
Uwani taga ƴan birni da gayunsa ga turanci ita kuma a Duniya abun da yake burgeta shi ne ta
ganta gata ga ƴan birni ko ɗan gayu musamman a ce yana turanci shi ya sa jiki na rawa ta basu
ɓangarenta suyi abin da suke so ita sai a Ɗakin Iya Sahu ta kwana da yake ma bata taɓa
haihuwa ba dan ko shekara basu yi da aure ba dan ma Kawu Iliya ɗin ba mazauni ba ne kuma
shi ne kaɗai namiji cikin ƴaƴan Iya Sahu dama yaranta uku kacal mahaifiyar Haleema ita ce
Babba sai kuma Mahaifiyar Miemie sannan sai Auta Iliya dukkansu a Abuja suke Aure sai dai
duk yadda Mahaifiyar Haleema taso shawo kanta a kan ta koma Abuja wurinsu ƙi ta yi shima
kuma Iliya da yake ba wani damunsa zama a birnin ya yi ba shi ya sa duk da a can ya taso
hannun Mahaifiyar Haleema amma sai ya yo gudowarsa ya yi aure anan ƙauye duk da ba haka
Mahafiyar Haleema ta so ba.



Wani irin ƙamshin suyan kaji ne da ya cika gaba ɗaya gidan ya sa ba shiri Uwani dake tsakar
gida suna fira da ɗaya daga cikin surukan Abokiyar zaman Iya Sahu ba shiri ta tashi tare da
nufar ɓangaren nata garin sauri har tana kusan tuntuɓe sai dai cak! Taja tunga lokacin da ta
karya kwana ta ƙari sa ɓangaren ganin yadda suka wani baje suna cin abinci a nutse yayin da
wasu ke suyar nama.

“Yawwa ga wannan ki miƙa wa Iya Sahu ta bawa kowa da kowa sai ki dawo ki shiga da wannan
Ɗakin Aunty Uwani ki a je wanda zamu wuce ma su Mommy da shi ne ai haka kika ce ake yi
ko?”


Suhaima da Haleema ta bar ma ta ragamar komai ta ƙare maganar tana duban Ƴar Gwal dake

siɗe hannu dan kammala cin Jallof ɗin Spaghetti da ta yi ke nan washe baki ta yi dama kuma ita
ce take faɗa musu duk abin da a ke yi domin Dukansu har Haleeman ba wacce ta san ya ake
wani Tirirrishi sunan ma sai a bakin Iya Sahu Haleema taji shi ne tun da ta kira su da shi ita
kuma Rabi'ah ta kama, Haleema duk da ta kasance wayayyiya kuma wacce ta yi ilimi mai zufi
amma tana son yin abubuwa na al'adar Malam bahaushe muddun bai saɓawa addini ba shi ya
sa sai da tasan yadda ta yi a ka zo yin wannan Tirirrishi ita hana su zama a gidanta da
Mahaifiyar Miemie ta yi ma daɗi ya yi ma ta dan dama tafiso suyi a ƙauyen kuma anan ɗin sun fi
sakin jiki duk da tafiyar mai nisa sukayi.

Karɓan kulolin ta yi bayan ta bawa Suhaima amsa sannan ta tafi ta kai da ta dawo ta tarar da
Rabi'ah tana raba halin dan ba'a ce da kowa take ba sai dai in ta yi wani abun kawai Suhaima
ko Miemie da ta fi sakawa ido su yi murmushi dan ta dena basu haushi sai dariya dan sun lura
ita haka take.

Wani abincin mai yawan gaske Suhaima ta sake bawa Ƴar Gwal ta ce a kaima Uwani ai kuwa
farin ciki da murna kamar me a wurin Uwani musamman ganin uban naman dake ciki kuma duk
da wurin kala huɗu suka yi abincin amma sai da suka ɗiba ma ta a ko wanne kaɗan ta ɗiba ta
adana sauran tana faɗin sai Mijinta Iliya ya dawo da yake sun yi waya ya sanar da ita yana
hanya, ita Uwani bawai nama ne bata taɓa ci ba a'a tsaban ɗoki ne kawai da yadda ƴan gayu
da komai nasu yake burgeta shi ya sa ma yanzu jiki na rawa take cin abincin na ‘YAN
TIRIRRISHI saboda sun kasance ƴan gayu.



Zuwa bayan wani lokaci ma tuni sun fara shiga wanka suna shirye-shiryen ɗaukar hanyar
komawa Abuja da yake da Iya Sahu da kuma Uwani har da Ƴar Gwal za'a je shi ya sa
dukkansu shiri suke ba kama hannun yaro musamman ma Uwani da Ƴar Gwal da suka fi kowa
zaƙuwa da ƙosawa wani abun ma idan suka yi sai dai su Haleema suka yi ta dariya cikin nishaɗi
suke gabatar da komai har zuwa wani lokaci da suka ji garin ya ɗauki wani irin hayaniya kamar
me can kuma iface-ifacen mutane ya biyo baya kafin wasu mintuna sai ga Habib ya shigo a
wani irin jigace cikin sa'a kuwa ya hango Rabi'ah da duk sun gama shirya wa sai dai suna tsaye
ne cirko-cirko cikin rashin abin yi domin wannan hayaniya da iface-ifacen bana lafiya ba su sun
ma yi tunanin ko ƴan fashi ne.


“Rabi'ah taho mu bar Garin nan da sauri babu lafiya...”

“Wai mene ne yake faruwa Uhum Uncle Habib ko dai Ƴan fashi ne?”


Rabi'ah ta tambaya a ruɗe tana ƙoƙarin kwace hannunta da ya riƙe ƙam. Su kam sauran jin ta
ambaci ƴan fashi duk da suma haka suke zargi amma hankalinsu ba ƙaramin ƙara tashi ya yi

ba.

“Ba lokacin da zan yi miki bayani ba ne yanzu kizo muje kawai kuma kwara ma a ce ƴan fashi
ne suka kawo farmaki bisa abin da yake faruwa....”


Maganar Habib ya maƙale a fatar bakinsa lokacin wasu suka shigo gidan a guje su biyu ne sai
kuma wani halitta da suka rasa gane kansa da ya buga wani uban tsalle ya cafki wuyar ɗaya
daga cikin mazan da suka shigo a guje ya danne shi a ƙasa yana wani hargagi lokaci guda
kuma yana ta ƙoƙarin cizonsa duk yadda mutumin ya so kare kansa lamarin ya cutara sai da
wannan abu ya cije shi a wuya kuma a take ya fito da naman wurin da hakan ya ƙara jefasu
cikin tashin hankali har da masu yunƙurin amai domin lamarin ba kyan gani.

“M..m.. mene ne wannan Uncle...?”


Rabi'ah ta faɗa idanunta suna rufe wa alamar dai suma za ta yi. Hankali tashe Habib ya juya
yana jijjigata tare da kiran sunanta sai dai ko motsi bata yi kuma a daidai wannan lokaci wannan
halittar ya miƙe tsaye tare da nufar Habib da gudun gaske domin aiwatar da ƙudirin ruhinsa a
kan sa wato da ya ci namansa domin a wannan taƙin da yake wata iriyar balaƴa'iyar yunwa ce
ke damunsa da yake ji in ba naman bil'adama yaci ba to fa babu zaman lafiya kamar kuma ba
naman mutumin da ya ciza bane a bakinsa bai gama ci ba...
Rashin comments kan iya sa na dakata da posting gaba ɗaya.
NainarhKDnkd's
07067953066

♡‘YAN TIRIRRISHI♡

P. 5,6,7

...©NainarhKDnkd's

“Zo...zo..zombie?!”
Wata daga cikin ƙawayen Haleema ɗin mai suna Mary ta faɗa a rikice.
Daidai lokacin ita kuma Ƴar Gwal da taga yadda wannan abu ya tunkaro Habib ta ware murya
tare da faɗin.
“Ka kula gashi nan ya tunkaro ka!”
Su kuwa sauran jama'ar wurin jin abin da Mary ta ce ne ya sa waɗan da suka gane abin da take
nufi cikin tsananin ruɗe wa har suna haɗa baki wurin faɗin.
“Zom... Me?!”
Tuni wasu sun fara guduwa ɗakuna suna ɓuya dan wannan bala'in da suke gani ido biyu sun yi
zaton wata ƙila mafarki ne zuwa anjima za su farka duk dai ba sun gana fahimtar abin da yake
faruwa ba ne.

Da wani irin mugun sauri Habib ya juya lokacin da yaji abin da Ƴar Gwal ta ce sai dai cikin
rashin sa'a juyawar da zai yi hakan ya yi daidai da kai masa farmaki da abin ya yi cikin jarunta
ya yi saurin tarewa sai dai da yake shammatarsa abin ya yi kuma wani mugun ƙarfi na ban
mamaki ne ya sa shi rinjayar Habib suka faɗi a tare yana ci gaba da ƙoƙarin ya kai ma Habib
farmaki burinsa kawai ya cije shi kuma duk yadda Habib ya yi ƙoƙari wurin ganin ya cececi
kansa abu ya cutura Zombie'n yana daf da kai masa cizo ke nan sai kwaf! Suka ji ƙarar buga
abu mai ƙarfi da a ka yi a kan Zombie'n da yake da mugun ƙarfi a ka buga nan take kuwa kan
nasa ya fashe jini ya fara wani malala da sauri Habib ya mirgina da Zombie'n gefe sannan ya
miƙe yana sauke haki tare da mayar da dubansa kan Ƴar Gwal dake riƙe da ƙaton gatarin da ta
buga a kan Zombie'n har ya fasa kansa jikinta babu inda baya rawa sai zare ido takeyi sai kuma
lokaci ɗaya ta yi wurgi da gatarin tare da kurma ihu taja gefe tana sauke haki idanunta a kan
Zombie'n da ko motsi bayayi.

“Uncle Habib wai mene ne wannan kamar abin nan da nake gani a Film ne yake faruwa ido biyo
yau a gabana na shiga uku na, Dan Allah kucemin mafarki nake ba zahiri bane duka abin da na
gani”

Rabi'ah ta faɗa tana rumtse ido cikin tashin hankali.


“Tabbas wannan abu Zombie ne kuma ba shi kaɗai ba ne domin zuwa yanzu kusan rabi ko na
ma ce fiye da rabi na mutanen garin nan sun koma Zombie's ni kaina mamakin wannan
cukurkuɗaɗen al'amarin nake.”


Habib ya bata amsa yana mai dubansu gaba ɗaya.


“Amma kuma daga ina wannan masifa ta fara kuma a Nigeriya, Nigeriya ma yankin Arewa a ce
an wayi gari ana zama Zombie's bayan Duniya ta tabbatar da tsabagen lafiya da baƙaƙen fata
suka fi fararen fata irin wannan abu bai taɓa faruwa da baƙaƙen fata ba sai dai a jishi a yankin
farare amma mene ne sila yau an wayi gari yankin baƙaƙe suna komawa Zombie's kuma dole
akwai wata a ƙasa.”



Gaba ɗaya duban Suhaima da take maganar cike da al'ajabi suka yi Habib ya ce.
“Daga jin kalamanki koda ke ba likita ba ce to tabbas kin san wani abu a kan fannin lafiya sai
dai yanzu ba lokacin wannan ba ne bamu da isasshen lokaci barin garin nan zamuyi tun kafin
gaba ɗaya mutanen ciki su koma Zombie's....”


Maganar Habib ta katse ne lokacin suka ga wannan Mutumin na farko da a ka ciza ya yi wani

motsi lokaci guda kuma jikinsa yana wani irin ƙara da makwalkwashewa da alama shima
Zombie'n zai zama.


“Ku jajja baya.”


Habib ya faɗa yana duban Mutumin.

“Jesus Christ, yeh yyeh jama'a kuna gani shi ma Zombie'n zai zama!”


Mary ta faɗa da gurɓatacciyar hausarta tana nuna Mutumin cike da tsoro.

Wani irin kuka Miemie ta fashe da shi lokaci guda kuma suna ƙanƙame juna ita da ‘Yar Gwal da
ita ma hankalinta yake a mugun tashe ganin wannan tashin hankali da tun da uwarta ta haifeta
bata taɓa gani ba.

“Innalillahi wayyo Allah na shiga uku na ya tashi jama'a tashi ya yi fa!”

Rabi'ah ta faɗa a matuƙar ruɗe idanu warwaje take duban wannan mutumin da ya fara motsi
jikinsa yana wani irin malkwashewa ƙasusuwansa suna bada wani sauti lokaci guda fuskarsa ya
koma wani irin abin tsoro ga saitin wurin da a ka cizesan ya yi wani mugun rami yana fitar da
wani wawwaran jini.
“Shima fa Zombie'n ya zama wayyo Allah!”

Haleema ta sake faɗa cikin tsananin tashin hankali tana ƙamewa wuri guda ta ma kasa motsi
bare tunanin gudun ceton rai.


Wani irin hautsinewa ƴaƴan cikin ‘Yar Gwal suka yi ganin mummunar halittar da Mutumin ya
koma da kuma jin abin da Haleema ta faɗa rashin abin yi da kuma tashin hankali ya sa ta ɗafale
bayan Miemie ba tare da ta sani ba tana sakin wani marayan kuka.

_______

24HRS Back....
Awanni ashirin da huɗu baya.


*Scientific Research Lab*

Wani irin gini ne mai tsayi da girma da kuma tsari kana gani kasan turawa ne suka tsara abin su
kuma daga yadda suka yi ginin zaka fahimci cewa Lab ne wato wurin bincike kuma na kimiyya
duba da sunan da a ka saka ma sa.

Daga cikinsa ma yafi wajen kyau wuri ne iri-iri ɓangare-ɓangare ko wanne ma'aikata ne na
kiwon lafiya masu bincike cikin uniform suna gudanar da aikinsu cikin kwarewa daga can gini na
ƙarshe kuwa cikin Lab ɗin wani irin ɗaki ne mai girman gaske da ya haɗa abubuwa da dama na
bincike daga can gefe guda wani Matashi ne bak'ar fata wankan tarwatsa dogo, da ba zai haure
shekaru talatin da biyu ba yana tsaye sanye da Lab coat sai Goggles irin wannan Glasses ɗin
da masu bincike suke sakawa a idanunsa sai kuma face mask dake fuskarsa ya juya baya
hannunsa dake cikin Gloves riƙe da Lab notebook yana rubutu a hankali a ciki gaba ɗaya
hankalinsa ya tattara ne ya mayar a kan wani gilashi mai girman gaske dake gabansa a tsaye
gilashin yake ciki kuwa wani mutum ne kwance a ciki idanunsa a rufe, baya motsi tamkar babu
rai a tare da shi ga kuma wani ruwa mai haɗe da sinadari dake a cikin gilashin ruwan mai launin
shuɗi-shuɗi.


A wani irin hargitse a ka turo ƙofar wurin wani Matashin Bature da a Shekaru za su daidai da
baƙin fatar dake ciki, Baturen ya bayyana yana mai sauke huci cikin ɓacin rai yake duban
wanda yake cikin da ya juyo yana bin sa da kallon lafiya? Sai dai tun kafin ya ce wani abu, rai a
ɓace Baturen ya fara faɗin.
“Why Sadiq me ya sa ka zaɓi wannan hanyar? me ya sa tun fari baka faɗa min gaskiya ba kayi
amfani dani da Lab ɗina ka haɗa kai da wasu mutane can badan kuna shirin yaɗa ɓarna ku
cutar da mutane?”

Tun da ya fara Maganar cikin harshen turanci wanda ya kira da Sadiq ɗin ne ya wani harɗe
hannu a ƙirji bayan ya a je Lab notebook dake hannunsa idanunsa kafe a kansa bai katse shi
ba har sai da yaga ya yi shiru dan kansa sannan ya saki wani malalacin murmushi da ya bawa
abokin nasa Bature mamaki.

“Daniel Jack ke nan wa ya faɗa maka wannan Sadiq ɗin dake gabanka shi ne abokinka da ka
sani shekaru masu kauri a baya? To wannan wani Sadiq ne sabo da ba abin da ya saka a gaba
sai neman Duniya kuma ina dab da samu sannan da kake maganar wasu mutane can daban ai
sun ɗin Turawa ne kamar ka saboda haka ka ma dena kiransu da wasu mutane can daban dan
duk halin ku ɗaya ban da haka mai zai saka duk kuɗaɗenka ka baro ƙasar ka kazo nan ka buɗe
wannan Research Lab ɗin?”


“Saboda ina son na taimakawa al'ummar Duniya da baiwar da nake shi a ɓangaren”

Daniel Jack ya katse shi da faɗin hakan a fusace sannan ya ci gaba.


“kuma da kake maganar su waɗan da ka haɗa kai da su kuke shirin aikata wannan ɗanyan aiki
sun kasance Turawa ai ba duka ne aka taru a ka zama ɗaya ba domin ni Bature ne amma son
zuciya da neman Duniya ba zai taɓa rufe min ido nayi wannan aika-aikar ba bare kuma kai daka
kasance musulmi kuma a ƙasarka da danginka suke a ke ƙoƙarin wannan yaɗa ɓarna karfa ka
manta zombie kuke shirin farmakar ƙasarka da shi, wai kuwa ka manta haɗarin da wannan abu
yake da shi ne? Ba fa ƙasarka ba hatta Duniya ba zata tsira ba da abin da kuke shirin yi saboda
haka ina roƙonka for the sake of our true friendship ka dakata da wannan abu da kake shirin yi.”

Wata ƴar iskar dariyar ƙeta da Sadiq ya saki ita ce ta sa Daniel Jack ya yi shiru jikinsa ya yi
sanyi yana yi ma Sadiq ɗin wani irin duba cikin sanyin jiki bai taɓa tunanin kuɗi za su canza
abokin nasa ba musamman da ya san shi da halaye nagartattu ga kuma addinin da yake ciki da
a har kullum sha'awa yake bashi kuma shi ma yana da burin wata rana ya kasance cikin jama'a
na wannan addini.

“A kan kuɗi kake komai ba? Me ya sa tun farko baka sameni ka sanar dani ko dala biliyan nawa
kake buƙata ba amma ka zaɓi bin wannan gurɓatacciyar hanya?”

Daniel Jack ya kasa ci gaba da maganar ganin wannan gilashin da mutumin ke ciki ya fara
tsagewa yayin da Mutumin ya buɗe idanunsa gaba ɗaya halittar jikinsa ya gama komawa irin na
zombie sak ko kafin Sadiq ya ankara Mutumin da ya koma zombie ya fara ƙoƙarin ganin ya fasa
gilashin duk kuwa da mugun ƙarfin da yake da shi.

Cikin wani irin ruɗe wa hankali a tashe Daniel Jack ya cillar da Airpad ɗin hannunsa sannan ya
ƙari sa wurin da mugun sauri ya janye Sadiq daidai lokacin kuma wannan zombie ɗin ya sama
nasarar fasa gilashin aikuwa cafka ɗaya ya yi ma Daniel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login