Showing 15001 words to 16112 words out of 16112 words

Chapter 6 - YAN TIRIRRISHI! Complete BY NAINARH KD.pdf

25 May 2025

1453

tarwatsewar gilashi da gidan yake yi ya dakata haka ma waɗan nan
muryoyin kafin kuma wata kakkaurar murya ta karaɗe dukkanin palon tana kuma amsa amo a
gidan dama dajin baki ɗaya.


“Tabbas kun kawo kanku gidan mutuwa inda ba'a shiga a fita haƙiƙa kun yi kuskuren kawo
kanku cikin Masarautar mu wato Gidan iko sai mun ga bayan kowannenku kamar yadda muka
ga bayan wannan la'anannen.”


Muryar marar daɗi da ta karaɗe palon ta ƙare maganar ana yi musu nuni kuma da gawar Sadiq
da ke gebe duk da basu san ta inda mai maganar yake ba ko kafin kuma suyi wani yunƙuri sai
ga bidiyo ya bayyana a tsakiyar Palon saman iska bidiyo ne na Sadiq da Daniel Jack lokacin da
suke arguing a kan abin da Sadiq ɗin ya yi na haɗa kai da turawa har zuwa lokacin da wannan
Zombie'n ya fasa gilashin ya kuma kai ma Daniel Jack farmaki da zuwa lokacin da Sadiq ya
gudu a wurin.

Basu gama shan mamaki da ganin wannan bidiyon ba sai kuma ya yanke a ka ƙara wani shi
kuma Suhaima ce tare da Sadiq a bidiyon suna waya ne a kan bikinsu da ya kusa domin an
saka musu rana daga haka kuma bidiyon ya yanke wannan murya mara daɗi ta ci gaba da
faɗin.
“Saboda haka ya cancanci ya mutu shi ya sa muka kashe shi mutuwa mafi ƙasƙanci...”


“Baku da ikon aikata hakan dan kawai ya aikata abin da ya aikata sai kuma a ka ce ku kashe
shi hukuma ita ce zata yanke masa hukunci kafin yaje ya tarar dana Ubangiji baku ba aljanu
kuma idan ma haka ne mun yarda shi mai laifi ne shi ya sa kuka kashe shi amma mu kuma fa
laifin miye mukayi muku da kukeson kashe mu....”

Wani irin dunƙulallen iska ne ya ɗauke Rabi'ah dake maganar ya yi sama da ita kafin kuma a ka
saukota ƙasa a ka yasar a tsakiyar Palon ta saki ƙara na azaba tana dafe bayanta da hakan ya
zama sila na ganin cizon dake hannunta da suka yi cikin zaro ido da tashin hankali ɗaya daga
cikin ƴan matan ta ce.
“Cizon miye a hannunki Rabi'ah kar dai kice kema Zombie'n ne ya cije ki?”


Budurwar ta faɗa cike da tsoro tana ja da baya, da sauri Rabi'ah ta rufe Wurin cizon idanunta a
ƙasa ta ce.

“kuyi haƙuri nima ban lura ba sai...”


“me kike nufi da muyi hakuri iyyye so kike kamar yadda a ka cijeki zaki zama zombie muma mu
bari ki cije mu ko me.”

Kawu Iliya ya faɗa a hasale, cikin tsananin damuwa Rabi'ah ta basu labarin ainihin Yadda akai
har aka cijetan kuma bada niyya ta ɓoye musu ba sai dai tun kafin ta rufe baki Muryar aljanar
nan ta katseta da faɗin.


“kema kuma kin zama maci amana saboda haka sai mun hallaka ki domin alƙawarine mukayi
duk wani maci amana ba zamu kyaleshi ba har sai mun ga bayanshi domin muma amanar mu a
ka ci a ka rufe mu a wannan kurkukun gidan tsawon shekaru masu yawa saboda haka duk wani
maci amana ko kuma wanda ya kawo kansa wurin mu ba zamu taɓa barinsa da rai ba...”

“ƙarya kuke yi domin baku isa ku cutar damu ba domin kuwa mun riƙe Allah kuma mun fi ƙarfin
ku kuma babu abin da kuka isa kuyi wa Rabi'ah tun da ba ha'intar mu ta yi ba. Kuma sannan
da'a ce zata zama Zombie da tuntuni ta zama saboda haka tun da ta kawo wannan lokaci ba ta
zama ba hakan na nufin ita ɗin TA DABAN ce ba zata taɓa zama Zombie'n ba..”

Muryar Iya Sahu cike da rashin tsoro ta katse su da faɗin hakan cikin hargowa, sannan ta dube
mutanen wurin cikin kwarin gwiwa ta ci gaba da faɗin.

“kada ku bari wannan aljanar ta yi nasara a kan mu mu yita addu'a har Allah ya bamu ikon fita
daga gidan...”


Cike da kwarin gwiwa duk suka amsa ma ta kafin su fara addu'a daga sun gama wata suke
kama wata da fari dariyar shaƙiyanci aljanar ta sheƙe da shi amma zuwa wani lokaci da suka ci
gaba da Addu'o'in ba saurarawa sai ta fara roƙonsu a kan su tsaya saboda suna ƙonata suna
kuma cutar ma ta da yara da Masarautar ta amma su ka ƙi saurararta sun kusa awa guda suna
karon ba gajiyawa duk da lokacin dare da ya yi sosai ga kuma gajiya da yunwa a tare da su
amma haka suka daure suna ci gaba da karanto Addu'o'in ai kuwa kamar al'mara suka ga an yi
jifa da su sai gasu sun bayyana a tsakiyar gidan cikin tsananin farin ciki ba kuma tare da sun
dena karatun ba suka tashi a tare har da riƙe hannu suka ƙari sa wurin Gate ɗin nan ma suka yi
masa ƙawanya wasu suna bubbugawa wasu suna ci gaba da karatun gaba ɗaya sun fita
hayyacinsu zuwa lokacin da yake suma aljanun ƴan taurin kai ne sai suka fara tsoratar da su
amma duk da hakan suka daure suna ci gaba da karatun idanunsu a rufe saboda kar ma suga
abin tsoron da a ke nuna musu, sun ɗan ɗauki lokaci mai tsawo a hakan kafin kamar a mafarki
sukaji ƙofar ta buɗe a tare kuma cikin wani irin yanayi suka buɗe idanunsu suna masu takawa
wurin fita daga gidan ai kuwa sukayi kiciɓis da wasu daga cikin sojojin da General ta aiko sun
ƙari so da jimawa sunata shawagi a wurin suna nemansu da basu gansu ba har sun fara shirin
komawa cikin helicoptern nasu subar wurin sai kuwa cikin ikon Allah sai gasu Rabi'ah sun sama
nasarar fitowa daga gidan iko lokacin da suka ga helicoptern dake sama har uku da kuma
sojojin sai suka sauke ajiyar zuciya domin sun fahimci wahala ce ta ƙare musu za'a taimaka
musu a fili suka haɗa baki wurin faɗin “ALHAMDULLILAH”

_____
MA SHA ALLAH

KUMA ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH ALA KULLI HALIN....


Anan na kawo ƙarshen wannan taƙaitaccen labari nawa mai taken ƳAN TIRIRRISHI ina fata
mun ƙaru da abubuwan dake ciki Allah ta'ala ya sa mu dace a gurguje dai mu haɗu a littafina da
zai fara zuwar muku cikin satin nan da yardar mai duka mai taken BA RIBA, (there is no other
choice ) ku jira fitowarsa kawai domin littafin na daban ne ko daga jin sunan ma ba sai an

faɗa ba.


NainarhKDnkd's ✍️
07067953066
Or
08081129487
Tue,May, 20. 2025.
Thank you Again...❤️

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login