Showing 12001 words to 15000 words out of 16112 words
dai fa ce Sadiq S
Sulaiman senior ɗin su ne ita da Rabi'ah tun suna secondary school kuma first love ɗin Rabi'ah
kafin daga baya suyi break-up dalilin halayensu da suka sha banban kuma tun daga secondary
school basu ƙara haɗu da shi face to face ba, ita dai Haleema ta kan ji labari sama-sama a kan
sa ita kam dama Rabi'ah ko son jin sunansa batayi.
“Jesus na shiga uku na ni Mary Mum ki taimakeni wannan abu ya cijeni shikenan nima zan
zama kamar su zan koma zombie yeh yeh yo!”
Ihun da Mary ta kurma tare da faɗin hakan shi ya mayar da hankalinsu gareta sai lokacin suka
lura ashe ma waya takeyi ko kafin, wata cikinsu ta ce wani abu nan ta shiga labarta ma wacce
take waya ɗin da ita abin da yake faruwa nan suka fahimci Mahafiyarta ce da yake tsaban ruɗe
wa a handsfree ta saka kiran shi ya sa raɗau su Haleema suka ji abin da maman nata ke cewa.
Cikin kuka Maman ta ce.
“Jesus, kina jina ko Mary ki kashe kanki kawai dan ba zan so jin kin koma zombie ba hankalina
zai fi kwanciya idan a ce kashe kanki kikayi tun kafin ki koma zombie...”
Ganin yadda Mary ta yi tsitt da alama tana tunani a kan abin da mahaifiyar nata ta ce ne da
kuma yadda take kallon bindigar dake hannun Sadiq ya sa cikin zaro ido da tashin hankali
Haleema ta shiga girgiza ma ta kai tana yi ma ta alama da hannu a kan kar ta yi hakan sannan
ta buɗe baki da ƙyar ta ce.
“Dan Allah Mary ki saurareni kar kiyi haka har yanzu fa baki koma Zombie'n ba ki jira mu
gannn....”
Jinin da ya tallatsa ya wanke ma ta fuska shi ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi
domin kuwa Mary ko saurarenta batayi ba sai ma girgiza ma ta kai da ta yi tana hawaye sannan
cikin shammata ta ƙari sa tare da wafce bindigar hannun Sadiq ko kafin su yi wani yunƙuri tuni
ta saita bindigar saitin kanta sannan ta matsa kunamar take harsashi ya fasa kanta da hakan ya
sa jini tallatsa ya wanke fuskar Haleema.
Wani irin zaro ido Haleema ta yi cikin tsananin tashin hankali kafin kuma ta fara ganin komai na
Duniyar ya fara sauya ma ta wani irin jiri dake barazanar zubar da ita ya sa ba shiri ta zube a
saman gwiwowinta tana mai fashewa da wani irin kuka da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta
ganin wannan tashin hankalin da take ganin ƙawayen nata sun shiga ne duk a sanadin ta domin
da bata matsa musu a kan sai sun zo har nan an yi Tirirrishi ba a ganin ta da duk haka bata faru
ba da bata rasa mutane biyu cikin ƙawayen nata ba tsoron ta bai wuce a kan nan gaba kuma su
waye kuma har nawa za'a rasa ba shi ya sa ta kasa jurewa zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi
takeyi ma ta kuka take yi da dukkan ƙarfinta gaba ɗaya sun yi shiru duk jikinsu ya yi sanyi daga
masu hawaye sai masu sheshsheƙa an rasa mai lallashinta har da sai da ta yi iyayinta sannan
Rabi'ah da Suhaima suka ƙari sa suna ɗan lallashinta ganin zata iya samun matsala idan ta ci
gaba da kukan.
“Rabi'ah, Suhaima bazan iya jurewa ba duk ta sanadina suka rasa ransu yanzu an rasa Mutum
biyu nan gaba fa idan kuma na sake rasaku ya zan yi da rayuwata?!”
Haleema ta faɗa cikin kuka.
“Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu babu abin da zai sake faruwa.”
Cewar Suhaima cikin lallashi. Ita kuwa Rabi'ah shiru ta yi kamar ba zata ce komai ba sai kuma
ta furta.
“Nasan da niyya koma su waye waɗan da suka ƙirƙira wannan bala'i suka yi kuma in sha Allahu
ta silar hakan ƙarshensu zai zo domin Allah yana sane da dukkan azzalumai bare kuma marasa
imani har haka da za su ƙirƙira Zombie Domin ƙarar da al'umma. In sha Allahu ƙarshen su gaba
ɗaya ba zai yi kyau ba azzalumai kawai.”
Gaba ɗaya amsawa suka yi da Ameen kowa da irin mugun fatan da yake yi musu amma banda
Sadiq da yake ji jikinsa bai taɓa yin sanyi ba bai kuma ji danasani ba gaba ɗaya sai yanzu yake
jin ya matuƙar tsanar kansa.
Ya sauke ajiyar zuciya yana kau da kai.
Bayan wasu mintoci.
Tafiya suka ci gaba a cikin dajin babu mai cewa kowa komai domin har Sadiq zai bi nasan
hanyar daban amma sai suka ce ya bisu su tafi tare ganin irin taimakon da ya yi musu.
Tsayawa suka yi lokacin da suka ƙari sa gaban wani irin makeken gida ginin zamani da ƙaton
gate a gabansa cikin mamaki Iya Sahu ta riƙe haɓa ta ce.
“Ikon Allah ke nan dai wannan shi ne gidan da muke jin labarinsa...”
“Wani gida ke nan Iya kuma mene ne gidan ya yi wani irin labari kuke ji a kansa?”
Rabi'ah da gidan ya gama tafiya da imaninta ta faɗa tana duban Iya Sahu sai dai tun kafin iya
Sahu ta ce wani abu Ƴar Gwal ta ce.
“Cewa a ke da Fatalwu a gidan kuma GIDAN IKO ma a ke ce masa dama Wallahi ina so naga
gidan gashi yau ina tsaye ƙofar gidan.”
“Ke Ƴar nan raba kanki ai Bama wai ba domin an tabbatar wannan gida Fatalwu Bama ɗaya ko
biyu a ciki ba banda hakan mai zai saka a zo ƙaton daji kamar wannan a gina sankacecen gida
irin haka sannan a barshi a ƙi tarewa.”
Iya sahu ta katse Ƴar Gwal tana ƙara ƙare ma gidan kallo.
Gaba ɗaya kallon gidan suke suna jin yadda wani shauƙi na son shiga ciki ya ɗauke su gaba
ɗaya burinsu bai wuce su shiga ciki ba.
Taɓe baki Rabi'ah ta yi.
“Ai wallahi ba Fatalwa ba in ma rufanai ne a gidan sai dai su ganni su kyale a to ban da ƙarya
irin na mutane ji gida tsaftsaf da shi kuma ginin zamani amma a ce wani Fatalwu ne a ciki nabi
Fatalwun da gudu dan ubansu.”
Dariya ta bawa kowa da maganarta duk da halin da suke ciki na jimami.
Iya sahu da ta fara yarda da maganar Rabi'ah ta ce.
“Eh to kuma fa haka ne ji ye min dai ƴar nan ba wani Fatalwu kawai so a ke a tsorata mutane
dama shi ya sa a ka daɗe ana yaɗa jita-jita wai Fatalwu ne a gidan.”
Ta faɗa tana kama ƙaton gate ɗin gidan take wuya taji ta ƙara matsuwa da su shiga ciki.
“Dare ya yi kuma babu Wurin kwana ina ga mu shiga ciki kawai da addu'a in sha Allahu ba
wasu Fatalwu in ya so da safiya tayi mu ci gaba da tafiyarmu.”
Cewar Muhsin yana jira yaji ta bakinsu.
Gaba ɗaya sun yi na'am da shawararsa hakan ya sa duk suka nufa hanyar shiga gidan
gadan-gadan tsaban ƙosawa da zumuɗi ma ko addu'ar basu yi ba shima kansa mai maganar a
yi addu'ar ba yi ya yi ba su ka sa hannu a tare suka buɗe ƙaton gate ɗin suka kuwa ci Sa'a a
buɗe yake ba kuwa da tunanin komai ba suka antaya ciki....
♡YAN TIRIRRISHI!♡
P.12,13.
Shigarsu gidan keda wuya ƙaton Gate ɗin ya mayar da kansa ya rufe gam, zuwa lokacin da
suka shige kuwa ginin gidan ne gaba ɗaya ya fara sauyawa kamar al'mara daga yadda yake
gini na zamani mai kyau da burgewa lokaci ƙanƙani ya rikiɗe ya koma tsohon gini irin na
zamanin da can yadda kasan ya yi Shekaru sama da ɗari ba'a taɓa shiga ba haka ya koma... Abuja, Nigeria
Cikin matsanancin tashin hankali take tun lokacin da ta sama labarin abin da yake faruwa na
cutar da ta yaɗu mutane suna cizon junansu suna komawa Zombie's gashi a inda Yarinyar ta
ɗaya tilo wato Rabi'ah ta tafi nan ne wannan masifar da suka tsinci kansu ciki ya samo asali ga
ƙaninta Habib shima da ta tura dan ya saka ma ta ido a kan Rabi'ah'n tun samun wannan
mummunar labari take faman kiran shi amma amsa ɗaya ne layin sam baya shiga shi ya sa
gaba ɗaya ta ruɗe duk ta fita hayyacinta, ba tare da ɓata lokaci ba kuwa ta yi amfani da ƙarfin
ikon da take da matsayin ta na General na Sojoji wurin saka doka mai tsauri a kan ganin
wannan cuta da mutane ke zama zombie bata shigo Abuja ba gefe guda kuma ta ware sojojin
na musamman suna shawagi a yankunan da wannan al'amari ya rufta da su da kuma saka ido
domin ceto waɗan da wannan cuta bata ritsa da su ba gefe guda gagarumin zama na gaggawa
da gwamnati ta shirya a kan wannan al'amari ta tafi a inda suka tattauna a kan yadda za'a ɓullo
wa lamarin duk da abin akwai ɗaure kai domin har zuwa lokacin basu san ta ya a ka yi wannan
abu ya samo asali ba....
Ɓangaren Mahaifiyar Amarya Haleema kuwa kusan zaucewa za'a ce Mama da Hafsa dama
sauran ƴan uwa suka yi lokacin da suka sama labarin abin da yake faruwa bare kuma shi kansa
ango da ya fita hayyacinsa ƙarin tashin hankalin kuma shi ne da ko'a waya basu sama Haleema
ba bare susan halin da take ciki.
Ɓangaren su Haleema kuwa lokacin da suka shige cikin gidan wani irin ƙayataccen haɗaɗɗen
palo na ban mamaki suka tarar wanda ya basu mamaki dan da farko sai da suka ɗan tsorata
ganin haɗu war palon duk da dai ba'a cikin hayyacinsu suke ba sakamakon abin da yake
faruwa.
“Ni Ƴasu ina ne nan muka kawo kanmu kuma an ya bamuyi kuskuren shigowa gidan nan ba
kuwa?”
Iya Sahu ta faɗa tana riƙe haɓa.
“Haba dai ji gida har gida ai ba wani abu kar ma ki tsoratar damu bari ma ki gani na ga kamar
kitchen ne a can bana duba ko'a sama abin da taɓa wa dan cikina har wani kiran chiroma yake”
Zieey ta bawa Iya Sahu amsa tana shigewa kitchen dake gefe, yayin da Rabi'ah da bata kai ga
zama ba kamar sauran saima ƙare ma palon kallo da take yi a nazarce ta ce.
“Bara na duba ko zan ga Toilet.”
Ta faɗa tana yin gaba, yayin da duk sauran suka zazzauna suna hutawa da kuma tunanin abin
da za su tarar nan gaba dan hankalinsu ba wai ya kwanta ba ne ba, shi kuwa Habib fita daga
palon ya yi yana danna waya dan yaga Akwai network so yake ya samu ya keɓe ya kira
mahaifiyar Rabi'ah Wato General ya sanar da ita suna cikin ƙoshin lafiya.
Lokacin da ya kira layin nata kiran farko ta ɗa ga cikin tashin hankali take tambayarsa halin da
suke ciki dan saboda tsananin ruɗe wa ma kuka ta saka ta kasa nutsuwa ta saurari abin da zai
ce ma ta sai da ƙyar ya samu ta nutsu shi kuma sai da ya kwantar ma ta da hankali sosai
sannan ya faɗa ma ta Dukkanin abin da yake faruwa da halin da suke ciki kuma daga ƙarshe ya
tura ma ta location na wurin da suke acewarta kar ma ya yarda suyi kuskuren fita daga gidan
domin sojoji zata turo a helicopter domin taimaka musu zuwa Abuja'n domin an saka tsoro sosai
yadda masu cutar ma'ana Zombie's ɗin ba za su iya shiga Abuja ba dama sauran States ɗin da
abin bai shafa ba kuma likitoci kwararru suna iya kar bakin ƙoƙarinsu dan ganin an samo
maganin wannan cuta.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa lokacin da ya sauke wayar sannan ya juya da
nufin komawa ciki sai dai cak ya ɗan ja tunga cike da mamaki yake kallonta tsaye gabansa tana
sakar masa murmushi, ɓoyayyiyar ajiyar ya sauke dan kuwa ta bashi tsoro saboda bai taɓa
zaton da mutum a bayansa.
“W-wani abu kike nema?”
Ya tambaya yana ɗan kallonta ganin ta zuba masa ido shiru ta yi masa saima ci gaba da
kallonsa da take kamar ma bataji abin da ya ce ba har sai da ya sake magana sannan ta yi
firgigit tana dubansa baki washe ta ce.
“A-ah d-dama fa abinci na kawo maka.”
Cike da mamaki ya dubeta da kular da take miƙo masa sai ma kuma ya nuna kansa cikin nuna
zallar mamaki ya ce.
“Abinci, ni kuma?”
“Eh mana nasan kana jin yunwa shi ya sa na kawo maka karɓa.”
Ƴar Gwal ta yi maganar tana sake miƙa masa. Tana kuma tuna yadda tayima Uwani wayau ba
tare da ta sani ba ta ɗauke abincin ta fito.
Rabi'ah...
Da sauri ta mayar da ƙofar toilet ɗin ta rufe lokacin da ta shiga ciki tana sauke ajiyar zuciya sai
da ta tabbatar da ta sama nutsuwa sannan ta buɗe idanunta dake lumshe tana zaro hannunta
da ta ɓoye a baya kamar wani ya ce zai gani ta yaye dogon hannun rigar jikinta a take sawun
cizo da haƙuri ta bayyana, ajiyar zuciya ta sauke tana tuna lokacin da ta sama wannan cizo, a
lokacin bayan ta saka Habib ya koma domin ceton Ƴar Gwal ita kuma sai ta fito daga motar ta
tsaya tsaye tana jiran dawowarsa cikin shammmata kuwa Zombie'n da sam bata lura da shi ba
ya kai ma ta hari sai dai ta yi saurin an kara sai dai duk yadda taso ta tare kanta abu ya cutura
har sai da ya sama nasarar cizonta sai dai sam bata lura ba har sai da wurin ya fara yi ma ta
zafi lokacin da suke kan hanyar ƙari sowa wannan gida sai dai tana mamakin duk tsawon
wannan daɗewan da ita ba zama Zombie'n ba bayan kuma ba'a haure minti guda da zarar
Zombie'n ya cije ka kai ma zaka zama kamar shi, ƙura ma kanta ido ta yi ta madubin toilet ɗin
kafin ta fashe da wani irin kuka dan bata da abin yi sama da hakan sai da ta yi ma'ishi sannan
ta wanke fuskarta tana ci gaba da kallon kanta a madubin a take kuma tass! Kakeji Madubin ya
tarwatse da hakan ya sa ta ja baya cike da mamaki da kuma ruɗani dan ita dai tasan bata taɓa
ba kuma bata ga komai ya taɓa ba amma kuma madubin ya fashe da kanshi ko kafin ta yi wani
yunƙuri wani irin ƙara marar daɗin saurare ya karaɗe gaba ɗaya gidan da hakan ya sa ta yi
saurin toshe kunnenta gudun kar ƙarar ya yi ma ta illa sai kuma ta fito daga kitchen ɗin a guje ta
ƙari sa palon ta tarar da wani tashin hankalin gaba ɗayansu ta gani tsay-tsaye cikin
matsanancin tashin hankali sun yi ma tsakiyar palon zobe da alama wani abin na tashin hankali
suke gani.
“M-me nene yake faruwa anan?”
Ta tambaya a ɗan rikice tana ƙoƙarin ƙari sawa wurin da mugun sauri Haleema ta ƙari sa tare
da tararta cikin wani irin yanayi take faɗin.
“ba wani abu fa ba sai kin gani ba.”
Kallon rashin yarda Rabi'ah tayima Haleema kafin ta mayar da akalan kallon nata a kan
Suhaima da idanunta ya yi jajur ga kuma hawaye da yake faman zirya faman fuskarta kamar an
buɗe famfo.
Slowly Rabi'ah ta mayar da idanunta a ƙasa wurin da suke kalla lokacin da ta ƙari sa wurin,
wani irin bugawa na tsananin tashin hankali zuciyarta ta yi tana wani irin tsinkewa tare da zillo
yadda kasan zata fito waje lokacin da idanunta suka sauka a kan Sadiq dake kwance baya
numfashi alamar babu rai a tare da shi ga jini dake fita daga kanshi yana malale wurin, wani irin
juwa ne da ya kwashe ta da har ya kusa kaita ƙasa tana ci gaba da kallon gawar Sadiq ɗin cikin
wani irin tashin hankali kafin cikin wata ruɗaɗiyar murya da kuma sarƙewar muryar lokaci guda
ta furta.
“M-m-me ne ne yake faruwa anan garin ya ya hakan ta kasance.”
Ta faɗa tana kallon su da jajayen idanunta Habib da ya ƙari sa wurin da niyyar taimaka ma ta ta
miƙe ne ya furta.
“Ƙarar faɗowarsa daga saman bene kawai mukaji all of a sudden ba tare da sanin dalili ko
mafarar hakan ba....”
“Muyi gaggawar barin gidan nan domin ina iya jiyo alamun muggan halittun da suke ciki kuma
da alama sune suka yi silar da ya faɗo har ya mutu tabbas mun yi kuskuren shigowa gidan
nan...”
Iya Sahu ta faɗa cike da tabbatar da kalamanta ta hanyar nuna tashin hankali ɓaro-ɓaro saman
fuskarta.
Cike da tashin hankali duk suke kallonta jin abin da ta faɗa ta kuwa sake tabbatar musu da
kalamanta ta hanyar ɗa ga musu kai alamar tabbatar wa.
Cikin wani irin tashin hankali kowanensu ya nufa ƙofar palon domin fita daga gidan ko sa tsira
da rayuwarsu duk da suna da tabbacin idan suka fitan ma ba wai sun tsira bane wani tashin
hankalin ne yake can yake jiransu wato Zombie's.
Sai dai kwatsam suna ƙari sawa wurin ƙofar ko kafin su sama nasarar fita da ƙarfin tsiya ƙofar
ya mayar da kanta ta rufe lokaci guda kuma gidan gaba ɗaya ya fara wani irin girgiza yayin da
wasu kalan muryoyi suka karaɗe ko'ina na gidan cikin muryoyi marasa daɗin ji ake wasu
gwalan-gwalan da sam basa iya fahimtar abin da ake faɗa ban da zaro ido da ƙanƙame juna
cikin tashin hankali ba abin da suke yi gaba ɗaya tsaban tashin hankali sun ma kasa addu'a
zuwa can juyawa da ƙarar