Showing 1 words to 3000 words out of 14985 words

Chapter 1 - FARAR HAIHUWA Book 1 Chapter A Writing by Batul Mamman.pdf

04 Jun 2025

540

FARAR HAIHUWA💰1

Bismillahir Rahmanir Rahim



Kai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin halin
da kanwarta take ciki. Inna Uwale dake zaune a kan tabarma ta daga hannu sama idanunta duk
sun ciko da hawaye tace Ya Allah ka bani farin jika ko wanne iri ne. Ya Allah fari kyakkyawa
kamar ni. Zulai aminiyarta tace amin amin Uwale ai ranar sai munyi sadaka. Tani dake kai kawo
da sauran matan da 'yan uwansu ke cikin dakin haihuwar suka zuba mata ido. Ta kuwa cigaba
da adduar farin jika kamar yadda ta saba. Cikin kunar rai Tani tace amma Uwale baki da
mutumci ko kadan. Kanwar tawa tana ciki rai a hannun Allah kina wani fatan a haifa miki farin
jika. Farin jikan yaci.....bullowar mal Yakubu yasa tayi shiru ta share hawayen bakin cikin da ke
shirin sauko mata. Ita kuwa Inna Uwale tace ashe baki da kunya Tani? Ban girmi uwarki
Baraatu ba? Ita dai Tani shiru tayi don tana gani mutumcin Mal Yakubu mijin kanwarta. Yayi
gumi sharkaf saboda tafiyar da yayi zuwa asibitin a kafa bayan dan Tani din ya bishi gona ya
sanar dashi halin da ake ciki. Ramlah da Sadi suna ganinsa suka mike suna murna suka tsaya
a gabansa. Daukar Sadi yayi itama Ramlah tasa kuka sai an dauketa. Tana kukan bata sani ba
ta taka kafar Inna Uwale. Wata kara ta saki kafin ta hankade ta ta fadi kasa. Matsa can gun yar
uwarki, shegiya baka mummuna. Mal Yakubu yace haba inna a nan din ma. Tani ta dauke ta
tana goge mata bakinta da yasha kasa. Yarinya sai kuka take. Yo ba kaine duk ka cuceni ba
dan nan. Mata aka sami abin kallo jin yadda Uwale ta bude murya. Ta cigaba dube ni nan ga
fari ga kyau haka Allah Yayi ni tun kuruciya don ma girma yazo. Ta daga siririyar kafarta ta hagu
wadda shan inna ya shanye tace da wannan Allah Ya ragewa aya zakinta duk kyan dire na ban
sami mijin arziki ba sai ubanka. Allah dai Ya jikansa. Babu irin adduar da banyi ba da cikin ka
don ka fini sanin baki ne. Allah Ya taimake ni na haifo ka fari tas ga kyau. Sai hawaye shar suka
sauko mata ya durkusa kasa don Allah Inna kiyi shiru. Sauran matan dake wurin suna ta kallo
an sami labarin kaiwa gida yau. Yaron nan da yake mai bakin kashi ne ya rasa wadda zai aura
sai yar maiduguri. Wallahi kunga wannan yayar tata ta nuna Tani har ta fita haske. Kalarta fa
kamar dauda yadda dai kuka ga 'ya'yan nan. Ba yadda banyi ba har da kwanciya a asibiti duk
don a fasa auren yaki jin maganata. Ga haihuwar balai duk shekara. Yanzu wannan cakurkurar,
ta nuna Ramlah zaayiwa kani na biyu. To ni mijina ba arziki har ya mutu shima dan babu. Ni
kuwa kafin na mutu sai naje makka da kudin jika ko na mijin jika. Haka kawai yadda nake da
kyan nan bazan bar baya bakikkirin ba. Mal Yakubu ya share hawayen idanunsa. Inda sabo ya
saba da halin innarsa amma irin wannan a cikin mutane ta gama zubar masa da mutumci.

Goron bakinta ta furzar tace wallahi indai ta haifi fari ko fara nayi alqawarin yi mata wankan jego
da hannuna. Ga mutane suna min shaida. Ni ban tsani Munari ba harkar bakar fata ahalin tsiya
da talauci ne bana so. Tana gama magana wata nurse ta fito tace ina wadanda suka kawo
Maimunatu Ado? Mal Yakubu yayi saurin matsowa gaba. Inna uwale ma ta cangalo kafa tace
Nas fada min me aka samu. Fari ne? Ko kallonta nurse din bata yi ba tace masa ta sauka lafiya
za'a fito da ita zuwa dakin hutu. Uwale tace tana zaro manyan idanunta ke yar nan karki min

rashin kunya, ya ina tambayarki me aka samu zaki min banza. Ki fada min gaskiya fari ne ko
baki? Don wadan can yaran ko irin farin nan na jarirai wallahi baa haifesu dashi ba. Nurse ta
kalli mal Yakubu tace masa namiji ne tayi gaba abinta.

Zulai kawar uwale ta kama hanci ta rangada guda. Uwale ta kuwa make ta, to uwar kinibibi ai
baki ga kalar dan ba zaki cika mana kunne.




Batul Mamman💖
[8/22, 2:50 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰3



Mal Yakubu ya fito da dan kudi daga aljihunsa ya nuna mata. Kinga na ajiye saboda siyan rago
amma tunda haka Allah Ya qaddara mana sai ki fada min abinda kike so na saya miki. Tasan
duk don ya kwantar mata da hankali ne saboda abinda inna Uwale tayi mata. Tace haba baban
Ramlah ka bari muje gida mana. Ya girgiza kai kinsan Allah maimunatu bana son Yaya Salihu
yaji zancen nan. Kinga lokacin haihuwar Sadi da inna ta hana a yanka masa rago cewa yayi na
sake ki ba dole bane auren. Maimunatu bazan iya rayuwa da wata mace ba bayan ki. Don
girman Allah kada ki bari a raba mu. Murmushi tayi bata manta yadda ya rinka rokon yayanta ba
har saida iyaye suka shiga maganar. Tace ni da kai Malam Yakubu mutu ka raba. Dariya yayi
sosai sannan ya fita neman taxi da zata kai su gida.

A tsakar gida Inna uwale da zulai suka zauna tana ta bambami tun a hanya. Ni munari zata
cuta? Ni uwale wallahi sai anyi min farar haihuwa a gidan nan. Sai naga jika mai kyau da
daukar hankali zulai, sai jikana mace ko namiji yayi kudi. Ni banda abin namiji ma ina tsiya ina
bakar fata. Munari fa banda hakora ni ban taba ganin wani abu mai haske a jikinta ba. Zulai dai
sai bada baki take don tana samu a wurin aminiyar tata. Bayan sunci abinci Uwale tace ke ni a
ina zaki samo min farar mace bazawara mai 'ya'ya ne.? Zulai ta ware ido farar bazawara mai
'ya'ya fa kika ce uwale. Eh saboda su hadu da dannan su haifi farare. Ko wacce iri ce indai fara
ce ina so. Don ma duka yaranki sunyi aure ne ai da ko Sabuwa ya aura dama ita naso masa
tuntuni. Zulai tace to zan duba Uwale gashi kinga Sabuwan ma suna ta fada da mijin gashi
haihuwarta biyu. Dan karen kwadayi gare da zulai duk talaucin gidan Uwale sun fita arziki nesa
ba kusa ba ga rashin abinci. Uwale tace ki barta a gidanta a samo wata saboda idan an kashe
auren sai tayi idda fa. Ni kuwa so nake nan da sati biyu ma amarya ta tare. Zulai tace to bari na
tafi kinsan da zafi zafi ake dukan karfe.

Gidan Sabuwa ta nufa ta tarar da ita da mijin suna fada saboda babu abinci a gidan ga yaranta
suna jin yunwa. Zulai ta zakalkale kamar ba suruka ba yana ta basu hakuri suna zaginsa.
Karshe zulai tace kaga Inuwa ka sakar min 'yata yanzu wallahi ko in hadaka da 'yan sanda.
Yaro mara kunya haka ko yau ka saketa zata sami mijin aure. Ai farar mace kadara ce. Idan

kaki kuma wallahi sharri zan kulla maka wanda zaisa ka raina kanka. Yace haba Gwaggo
meyayi zafi haka? Ni bazan saketa ba. Sabuwa tace Gwaggo ban fa gaji da auren ba kawai don
babu abinci sai kice ya sake ni. Ta zumburo baki. Zulai ta make bakin banza zan miki gata kina
min fitsara. Zulai ta ja hannunta suka shiga daki ta fada mata hadin da take son yi. Kinga idan
kika haifi farin da uwale ke jarabar so wallahi sai yadda muka yi da ita. Kina kallo dai yadda kike
wahala nan ga fararen 'ya'yan shegen mijinki baya gani. Sabuwa ta bata rai Gwaggo nifa ina
son sa gaskiya. zulai ta saki wata ashariya Sabuwa zan miki rashin mutumci fa. Bar ganin ni na
haifeki bani da kyau a harkar samu. Ki tada balli a daren yau ya sallameki kawai.


Batul Mamman💖
[8/22, 2:51 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰2



Da dafa bango Munari ta fito daga dakin nurse na biye da ita da jaririn. Tani ta gyara goyonta ta
mika hannu zata karbi dan Uwale tayi saurin shigewa gabanta tace bani nan. Ni na haifi
ubansa. Tana bude zani ta kwala ihu ta mikawa zulai dan ta kai goshinta kasa tayi sujjada. Allah
nagode maka...ta kalli surukarta munari kin kwaci kanki wallahi. Ke dai Allah Yayi miki albarka.
Da kanta ta rike Munari suka karasa dakin aka bata gado. Tani da mijinta suna ta yi mata
sannu. Inna uwale ta sake karbar dan tana ta washe baki tace jamaa kunga abin arziki ko.
Yarinya mai son gamawa da duniya lafiya kenan. Ashe tumatir da su mangwaron dana rinka
siya miki yau kinga ranarsu ko. Ashe banyi asarar kudina ba. Zulai ai na fada miki duk miyar
kadi ko harkar daddawa sai da na hanata gashi kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu. Kiri kiri ta
hana kowa daukarsa saboda tsabar murna. Zaninta taji zai kwance ta mikawa Zulai dan ba don
taso ba tana magana. Ai sunan babana zaa saka maka yaro. Nima a nan na gado farin da kyau
har kaima ka dandala. Zulai ta dan jujjuya yaron a firgice Uwale tace ya haka ne? So kike ya
fadi? Zulai tace a'a fa Uwale gani nayi kamar baya motsi. Kinga fa ko kuka baiyi ba. Allah tsine
mai karya ta fada tare da karbe dan. Ai kuwa abinda zulai ta fada gaskiya ne. Uwale ta juya shi
shiru ba motsi. Yaro ga shi fari kato ga kyau amma bai zo da rai ba. Da cangala kafar uwale ta
fita kiran nurse kuzo ku daba min dannan na shiga uku na ni Hadiza ina zan sa kaina. Nurse
tazo tace a'a maimunatu baki fada musu yaron bashi da rai bane? Hawaye ne ya sauko mata
tace yanzu zan fada. Tani ta zauna gefen gadon ta rungumeta. Yi hakuri Munari Allah Yasa mai
ceton mu ne Ya yi masa rahma. Mal Yakubu ya ajiye Sadi ya karbe yaron daga hannun Uwale
ya kare masa kallo sannan ya rufe shi sosai da zanin. Uwale cikin kuka tace yanzu mai kyan ne
ya mutu? To wallahi kasa a ranka Yakubu kamar kayi aure ka gama. Kan uba ni zaki yiwa haka
munari? Ki haifi bakake digirgir farin kuma ya koma. Yar purse dinta ta dauka tace Zulai zo mu
tafi gida. Daga bakin kofa tace tsakanin na dake munari Allah Ya isa, muguwa mai bakar aniya.

Suna fita Tani tace gaskiya baban Ramlah abinda Inna tayiwa Munari bata kyauta ba. Wannan
wane irin rashin imani ne. Mace ta rasa danta a rinka binta da bakaken maganganu. Wallahi sai
na fadawa Yaya Salihu ai ba daga sama ta fado ba tana da dangi. Munari tace Yaya Tani kiyi
hakuri don Allah. Ya zaki bani hakuri bayan ke aka batawa Munari... mal Yakubu ya rinka bata

hakuri. Yaya Salihu mutumin kirki ne amma akan yan uwansa bashi da kyau duk da kasancewar
ba uwa daya suke ba amma iyayensu na zaman lafiya. Jafaru ta kira danta mai kimanin
shekaru takwas. Yana shigowa yace Umma Munari sannu. Ta dan murmushi yauwa dan
albarka. Tani ta goya masa Sadi ta rike hannun Ramlah. Bari mu tafi munari yaran nan basu ci
abinci ba na taho dasu. Mal Yakubu ya kara bata hakuri. Yanzu zamu taho muma zan nemo dan
tasi ne saboda jikinta.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:00 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰4



Sabuwa duk abin duniya ya isheta saboda yadda Zulai ta rinka yi mata fada. Tana kwance kan
katifarta zuciyarta tana mata saka da warwara. Inuwa ne ya shigo dakin ya nemi kwanciya kusa
da ita. Wani tsami ne ya daki hancinta ta mike cikin fada. Don wulakanci banda rashin abinci a
gidanka kullum sai ka kwanta min kana wari? Don Allah ni ka tashi jiki sai tsami kamar kayi
wanka da kwata. Ya tashi ya kai mata duka ta rike hannun sannan ta kwada masa wani
kwantareren takalmi a ka. Cikin karaji ya biyota waje suna ta fada sai ta tuna hudubar zulai. Nan
da nan ta fara zaginsa tana cewa ya saketa sanin cewa yana da saurin fushi. In sake ki ko
Sabuwa? Ni kike cewa na sake ki ko? Ta eh in dai ka haifu cikin uwa da uba. Ransa ya kara
baci har kin manta sakin da nayi miki kwanaki Zulai ta rinka hadani da Allah na mayar dake ko?
Ai da kenan Inuwa yanzu kuwa na gaji bazan zauna yunwa ta kashe min 'ya'ya ba. Yayi dariya
makota duk sun saba jinsu kije Sabuwa na sake ki saki daya amma wannan karon kada kuzo
biko don wata zan nema. Kuma ki tafi ke kadai don a nan kika sami yaran ba dasu kika zo ba.
Ita kalmar sakin kawai taji tasa kuka wallahi inuwa wasa nake don girman Allah ka mayar dani
kafin kowa ma yaji. A zuciyarta fatan ta daya ya mayar da ita. Ina zata idan ta bar gidansa?
Gwaggonta da kyar take ciyar da kanta gashi sauran yayyenta duk sunyi aure. Me ya kaita ma
yarda da shawarar gwaggo. A wurin girki ta kwana washegari yayo fatali da ita da kayanta.

Cikin kuka ta karasa gida. Gwaggo Zulai na ganinta da kaya da kumburarriyar fuska ta tashi
cikin sauri. Ya sake ki ko Sabuwa? Ai dadina dake jin magana. Sabuwa ta turo baki ta zauna
kan tabarma yanzu Gwaggo baki damu da dukan dana sha ba sai saki ko. To ya sakeni amma
wallahi idan baki yi min tanadi mai kyau ba sai na jawo miki magana a unguwar nan. Zulai ta
rike baki lallai yar nan baki da kunya. To ki kwantar da hankalinki Yakubu zan tabbatar kin aura.

Tani duk ta zayyanawa iyayen su abinda Uwale tayi wa Munari. Babar su Tani Inno tace to ai
inda sabo ta saba sai tayi hakuri. Shi kuma yaron Allah Ya jikan shi. Inna Ladi kishiyarta babar
su Salihu tace Allah Ya shiryeki Jummai. A fada miki abinda tayiwa auta shine zaki wani tabe
baki. Allah Ya jikan Malam amma da yana nan bazai lamunci wannan abin ba. Bari Yayan ku ya
dawo daga birni Tani da kanshi zashi gidan. Inno tace haba Yaya don Allah kada ma ya sani.

Yanzu sai kiji yana cewa a sako masa kanwarsa. Inna Ladi tace to tashi muje gidan. Inno tace ni
ba zani ba Yaya rigima ce bana so. Inna Ladi ta sabi mayafi suka fita ita da Tani bayan ta ajiye
yaran wurin Inno.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:00 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰5



A tsakar gida suka tarar da Munari tana iza wuta ga hayaki saboda yanayin damina icen duk ya
jike. Inna Ladi tayi saurin zuwa wurin ta karba. Da kyar Munari ta iya durkusawa ta gaisheta.
Inna Ladi tace haba mike...ina kike Uwale fito Allah Ya tona asirin ki. Yanzu yar ta haihu jiya,
haihuwar ma mai ciwo tunda ba dan amma don tsabar wulakanci da kanta zata dora ruwan
wanka da wannan icen haka? Uwale ta cangalo kafa daga daki ta fito. Idan kun damu da ita sai
ku dora mata. Inna ladi tace tafiya muka yi jaje gidan kanin babanta garin kwari shiyasa tani
bata same mu a gida ba . Dama tace jiyan ma ita ta dora ruwan. Haba Uwale rashin imanin naki
har ya kai nan. Uwale tayi wani juyi ita ga mai kyau...ta tafa hannuwa yafi nan Ladi. Ki
tambayeta abinda tayi min. Dan farin ne fa ya mutu sai wadan can gawayin kullum su nake gani
a gidan nan. Sannan ace bazanyi fada ba. Inna Ladi tace Munari dauko gyalenki wallahi na gaji
da wannan diban albarka. Idan yayanki ya dawo sai ayita ra kare. Tana gama magana Mal
Yakubu ya shigo da dan guntun ragonsa kafi zuru. Jin abinda ake fada ya karasa gaban
matarsa. Munari don Allah kada ki tafi. Inna Ladi ki rufa min asiri kada ku raba ni da ita. Hawaye
ne taf a cikin idonsa Uwale na gani tace kwarankwatsa ka bari hawayen nan suka fito gaban
surukarka sai na daga maka nono. Da kaji anyi zancen saki sai kuka kamar ka auri hurul...hurul
me ma? .oho matan aljannah dai nake. To ka zabi daya ko ka sake tan ko kuma nan da sati
biyu ka auri duk wadda na zaba maka. Da hanzari yace zanyi auren inna. Ya koma kallon
Munari koma daki in dafa miki ruwan kinji. Kinga rago can na siyo zan gasa miki. Sosai Inna
Ladi taji tausayinsa amma sai ta dake ni dai tafiya zanyi da ita mun gaji. Uwale tayi tsaki aikin
banza kin saki baki kishiyar uwa zata kashe miki aure kin zata sonki take. Makirci ne kawai irin
namu na mata. Munari sai a lokacin tayi magana.. Inna ki dena fadin abinda kika ga dama kan
Innarmu don akanta wallahi zan....zaki me??? Kaji ko dan nan matarka zata zageni. Inna Ladi
tace Tani dora ruwan wankan ko sake kallon Uwale bata yi ba taja hannun Munari suka koma
daki.

Bayan kwana hudu da haihuwar munari Uwale na zaune karkashin bishiya tana shan fura Zulai
ta shigo. Tana ganin furar yawunta ya tsinke. Ita kuwa uwale bata san tana yi ba kuma bata yi
mata tayi ba. Can ta lura da kallon da Ramlah ke yi mata. Ta ja tsaki shegiya mayya duk ta kafa
min ido zo ki karba. Yarinya ta taso daga wurin wasanta tazo gaban uwale. Dan yatsa ta tsoma
cikin furar ta dangwala mata a harshe. Ramlah ta lashe tas ta koma wasa. Zulai dai abin duniya
ya isheta sai ta fara tunanin abubuwan tausayi da suka sameta kamar rashin abinci da rashin

tayin fura daga kawarta. Nan da nan sai ga hawaye Uwale ta tande baki tace lafiya zulai. Uhmm
ina fa lafiya Uwale. Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login