Showing 6001 words to 9000 words out of 14985 words

Chapter 3 - FARAR HAIHUWA Book 1 Chapter A Writing by Batul Mamman.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

2029

nan ka cigaba da zargina don kawai yarka ta mutu. Ba ga wata
Allah Ya baka ba? Girgiza kai yayi ya cigaba da bawa su Inna hakuri.
Tun daga lokacin babu me shiga harkar Munari a gidan saboda yadda iyayenta suka sa musu
ido. Sai habaici daga gefe. Mijinta kuma yana nuna mata so da kulawa sosai suna ta rainon
cikinta cikin sirri. Wata rana suna cin abinci tace ni kuwa Mal meyasa baka so su inna su san
ina da ciki? Munari kenan ai ba murna zasu yi ba. Karshenta a rinka yin abinda zaa bata miki rai
har ciwonki ya tashi. Ko kin manta Yaya Salihu yace duk ranar da jininki ya hau ko zanyi kukan
jini sai na sakeki. Dariya tayi masa aikuwa gobe zanyi masa aike. Au tsokanata ma kike ko?
Zan rama ne... yanzu dai kiyi ta sa hijab da zaman daki so nake kawai Inna taji haihuwa. Allah
ba don darajar ta haifeni ba da tuni nasa an daure....hannu tasa ta rufe masa baki. Haba Mal?
Ka manta Allah Yace kada mu fadi kalma mara dadi game da iyayenmu? Kada ka manta
kwananta ne ya kare mu kuma hakurinmu shine ladanmu. Hakane Munari nima yau na dana.
Allah Yayi miki albarka Ya saukeki lafiya. Amin M[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:06 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰10



Inna uwale ta tabe baki sai mace ta takarkare ta haihu amma karshe kaga bakin jariri. Allah Ya
raya dauko min abin na gani a nan bana son doguwar tafiya saboda kafa. Ba musu ya je ya
dauko mata 'yar da kansa ya kawota. Ba yabo ba fallasa itama dai bakar ce amma ba sosai ba
gata kyakkyawa kamarsu daya da mal Yakubu. Inna tana kallonta ta mika masa gata nan bari
naje nayi sallah. Ita kuwa Sabuwa ko kallon yar bata yi ba ta juya zata koma daki. Dawo nan ya
daka mata tsawa. Wuce kije ki dora mata ruwan wanka. Inna uwale tace ka ma isa...ita da take
da jaririya. Dama ai gasa ce tasa munarin haihuwa yanzu. Girgiza kai yayi cike da takaici yaje
ya dora ruwan da kansa.

Daga ranar 'yan uwan munari ke yi mata komai. Ana saura kwana biyu suna tace Mal wane
suna zaka saka mata ne? Haba munari ai shawara zamuyi dake. Ta sunkuyar da kanta kasa
nasan wanda ya mutu baya dawowa amma inda hali a saka mata Ramlah. Murmushinsa ya
fadada dama haka naso ina dai tsoron yi miki fami ne. Allah Ya raya mana ita. Tace amin.
Uwale dake bakin kofar dakin ita da Zulai wanda dama gulma suka zo ji ta shigo tana matsar
kwalla. Yanzu dan nan ko kara bazaka min ba kasa sunana sai zabin matarka. Inna ke fa kika
ce ba kya so tun a haihuwar marigayiya. Akan Hanan ma kika sake cewa bakya so kika zaba
mata wanan sunan. Ta dan fito da ido ni dan nan? Abin harda sharri? To ba damuwa ka saka
mata sunan da kake so. Tana juyawa zata fita Munari tace haba Inna kiyi hakuri sunanki za'a
saka mata. Ba haka inna uwale taso ba, so tayi Munari ta ce bata son sunan sai ta hadasu fada
da Yakubu. Tsaki tayi ta fice Zulai na rufa mata baya. Duk da abin baiyiwa munari dadi ba sai ta
nuna wa Mal Yakubu jindadinta sosai.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Khadija. wata yar uwar baban Mal yakubu ce tazo ta

karbi jaririyar wanzami yazo za'a cire mata beli. Uwale ta gama lura da yadda munari ke
matukar kaunar jaririyarta sai ta fita wurin wanzamin tare da waziriyarta zulai. Basu dade da fita
ba aka jiyo sautin kukan Khadija da katuwar murya kamar zata shide. Mata an sami abinyi suka
yo soro da gudu. Tani ce kan gaba tana zuwa ta tarar uwale ta kwaye gefen fuskarta wanzan
yana kallon kalangunta ya fara zanawa jaririya a gefen fuskarta na dama. Fizgota Tani tayi ta
koma cikin gidan da sauri. Munari ta karbeta zata bata nono amma taki karba sai wani irin kuka
take. Har dakin Uwale ta biyosu. Amma Tani baki da ta ido. Yanzu nace ayiwa yarinya kalangu
zanen fulani irin nawa shine zaki dauketa. Munari tana hawaye tace yanzu Inna duk gidan nan
wa aka taba yiwa zane a fuska shine zaki ce ayi mata. Au kema rashin kunyar zaki min? Bani
ita a karasa mun barshi a zaune. Munari tasa zani ta goya yarta tana ta kuka. Wallahi Inna idan
kinga anyi wa yarinyar nan zane a fuskarta to mutuwa nayi. Ya kike so nayi da raina ne?
Matsalar yau daban ta gobe daban. Allah bari Mal ya dawo idan mutuwar aurena ce tazo sai dai
na tafi da yata. Zanen nan fa Allah Ya tsinewa maiyi da wanda akeyiwa. Kuka wiwi Uwale tasa
ita a dole anyi mata rashin kunya. Nufinki Allah Ya tsine min ko? To yau zanga wanda dan nan
zai zaba cikin mu biyu.

Daga gefe wasu mata suka ce gidan uwale duk taron suna sai anyi dirama. Ai munari ta
kyautawa kanta yau.






Batul Mamman💖
[8/22, 3:09 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰11



Wasa wasa har magariba ta gabato ana ta mayar da zance a gidan Mal Yakubu. Shi dai tun a
kofar gida da labari ya riske shi komawa yayi ya kira wan babansa Baba Hadi.

A tsakar gidan ya tarar dasu gaba daya da sauran mata 'yan jin kwakwaf. Baba Hadi na
shigowa yace duk su fice su bar gidan. Sum sum suka rinka fita daya bayan daya. Ba dai haka
aka so ba don sun so jin yadda zata kaya aji dadin ba da labari. Suna fita Inna Uwale cikin kuka
take labarta masa abinda ya faru. Baba Hadi yace ba matsala ke Munari bani yar . Ba musu ta
mika masa jaririyar bayanta. Yace to Yakubu karbo yayarta ya nuna Hanan dake hannun
Sabuwa. Bari na sa Yau ya kira wanzamin duk sai ayi musu. Shima Sadi idan suka zo gari sai a
karbo shi a yi masa. Uwale ta wurgo kafa cikin sauri bangane ba Yaya Hadi wai harda Hannan
za'ayi wa? Eh ya amsa a takaice. Dukkansu ba jikokinki bane? Tayi tsuru tsuru da ido...anya ayi
harda ita? Sabuwa ta ce Al-Quran ba za ayi mata ba. Mal bani 'yata. Baba hadi yace au ita
wannan da baki isa da uwarta ba shine zaki ce kada ayi mata, amma ita munari ko kadan baki
damu da lamarinta ba? To wallahi ki fita idona Uwale. Akan yadda kike takurawa matar yaron

nan zan nuna miki ni ba marigayi bane. Shine yake jure halinki na tsiya. Kai ta sunkuyar kasa
bata ce uffan ba. Ya mikawa munari yarta. Ki kara hakuri kinji Maimunatu. Allah Ya raya muku
yaranku. Tana ta godiya ya fita Mal ya raka shi.

Tun daga lokacin uwale ta kara kunnawa Munari karan tsana. Duk lokacin da Mal Yakubu ya fita
sai wulakanci kala kala. A can birni kuwa Yaya Salihu yasa Sadi a makaranta tare da yaransa.
Lokacin da Ummita ta shiga wata na ashirin da haihuwa Munari tayi shirin yayeta. Wata rana
tana kwasar tuwo Ummita tana ta zillo a bayanta. Tace haba mamana so kike na kona hannu
ne? Uwale wadda tuni zulai ta bata shawarar yadda zata kori munari daga gidanta ta daga waje
ni kuwa munari kin fiye kinibibi yaushe ta zama mamanki. Na zata sunan uwarki Baraatu.
Munari tayi murmushi Inna ai kema uwata ce. To indai haka ne daga yau tunda dai nike da iko
da kowa a gidan nan yarinyar nan zaa rinka kiranta Dijengala. Ni na tsani suna Ummita dinnan.
Gara dai a kirata dijengala a gargajiyance. Munari tace to ba komai inna ai yadda kike so haka
zaayi. Ba haka inna uwale taso ji don fada tazo takala. Sabuwa ta fito daga dakinta tace inna
kinji da yadda ta amsa miki kuwa? Ai gatse tayi miki. Allah Ya kyauta uwar miji ace bata isa da
surukarta ba. Ni kina ji ai sanda ta sawa tawa yar suna. Wannan ma idan na haife ita zata sa
suna.

Munari dai bata kula ba don tasan neman rigimar tasu ne ya tashi. Da Uwale taga haka zama
tayi a wurin sai da mal yakubu taji sallamarsa tasa kuka. Karya da gaskiya ta rinka hada masa
Sabuwa na mara mata baya. Ganin ko kadan bai yarda ba tace kai na gaji so nake indai ba tare
na haife ku ba ka saketa ta koma gidan ubanta. Munari ta soma hawaye tana bata hakuri. Ta
tabe baki kyayi kya gama. Yau abincinki ya kare a gidan nan. Idan baka saketa ba yanzu a
gabana ba wallahi sai na tsine maka albarka. Haba inna ya kike so nayi ne? Babu abinda kike
nema da bana miki. Don Allah kiyi hakuri. Itama kukan tasa masa idan baka saketa ba Allah
Yakubu zan maka mugun baki. Naki jinin bakar matar nan. Ka saketa yanzu.

Munari tace mal idan kana son gamawa da duniya lafiya kabi umarnin Inna. Yana kuka tanayi
yace na sakeki saki daya. Wani kukan ne ya zo mata da karfi ta shiga daki dauko mayafi. Inna
don ta kara kuntata mata tace kwanto goyon ai ba dashi kika zo ba. Dama yar ta isa yaye.
Munari ta kalli mal yakubu yace Inna don Allah. .hannu ta daga Allah Ya tsi....da sauri munari ta
kwanto yar da take matukar so ta bashi ta fita daga gidan cikin kuka.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:10 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰13



Da gudu ta karasa don yau akan wannan yar Mal yakubu yana iya karairaya ta. Tana dagota
wani irin tari ta rinka yi har uwale ta jiyo su ta fito. To 'yar nema zaki fara sanaar tarin ne....kai
lafiya sabuwa me ya faru? Wallahi Inna bansani ba. A cikin robar wanka na ganta. Na shiga uku

na yau a gidan nan. Ba kuka zakiyi ba dauko gyalenki mu kaita kemis. Kila ruwa ta shaqa. Su
'ya'yan munari kamar kifaye kowa ya tashi mutuwa sai ya tsumbula ruwa.

Basu tarar da mai kemis ba dole suka wuce asibiti. A nan Mal Yakubu ya hadu dasu bayan dan
aiken su inna ya riske shi. Likita yace gaskiya Mal akwai ganganci a tare daku. Yarinyar nan ba
karamin kamu sanyi yayi mata ba tun kafin yau. Sannan idan ta tashi za'a sake yi mata wasu
gwaje gwajen amma gaskiya a yadda na fahimta kunnuwanta sun tabu. Da kyar zata ji kamar
da. Shi kam mal yakubu sarkin hawaye har ya fara. Sabuwa taci fada don ma inna ta tsaya
mata ne. Karshe yace idan ta sake bari wani abu ya sami yarsa sakinta zaiyi ya hadata da
hukuma.

Labarin abinda ya sami Dijengala ya sami su Inno. Hanawa sukayi a sanar da munari son kada
tace zata taho tunda ta fara karatu a wata makarantar addini. Inna Ladi da ce taje gidan ta
bukaci a basu ita tunda basa sonta. Bayan doguwar muhawara tace su jira shammaci daga
kotu. Wannan kalami nata na karshe ne yasa Zulai ta bawa Uwale shawarar suje wurin wani
malami a dauke musu hankali daga kan Dije. Anya ayi haka Zulai? Nifa gaskiya bana son inyi
shirka. Haba Uwale malami ne fa ba boka ba. Ai irin malaman nan ba bokaye bane, suna da
ilimin islama gashi idan kika je zaki ga littattafai da carbi kala kala. Sannan idan kika bari aka
shiga kotu daurin shekaru zasu yi miki duk da tsufanki da yar kafarki. Tuni Uwale ta tsorata .A
haka ta ja raayin Uwale suka je wurin malamin. Bukatarsu biyu ce. Mal Yakubu yaso Sabuwa ya
hakura da abinda ya faru sannan Munari da 'yan uwanta a dauke musu hankali daga kan Dije
da zancen zuwa kotun nan. Ya kasance munari ta manta ma da yar tata gaba daya.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰12



Cikin kuka ta shiga gidansu da sallama. Inna Ladi ta ajiye butar hannunta ta taro ta. Me ya faru
Munari? Ta shafa bayanta taji ba goyo. Ina 'yar? Ba dai ta mutu ba. Munari ta kasa magana sai
kuka. Inno tace wai ba magana ake miki ba. Inna ya sakeni, inna uwale tace idan bai sakeni ba
zata tsine masa. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ita kuwa Uwale tana son gamawa da duniya
lafiya? Ina ruwanta da zaman ku inji Inna Ladi. Inno dama bata saka baki a lamarin gidan yarta
saboda kara amma yau bakinciki ya isheta. An sako mata 'ya da magaribar fari. Tace ina goyon.
Munari ta sake fashewa da kuka tace ba dashi nazo ba. Inno tace Alhandulillahi in anyi duniya
don Manzon Allah SAW kin bar gidan Yakubu har abada. Saurin dago kai tayi haba Inno wallahi
ba da son ranshi bane. Na dai fada miki...munari ba fa sadakarki aka bani ba. Haihuwarki nayi
kamar kowanne da. Kyautace Allah Ya bani to nayi hakurin da zanyi Allah Ya yanke miki
wahala. Inna Ladi tace hakane amma kada muyi saurin yanke hukunci.

Sallama suka ji daga waje. Inna Ladi ta amsa don ta gane mai muryar tare da yi masa izinin
shigowa. Yana shiga gidan ya zube a kasa yana basu hakuri. Inno tace ai ni so nake ka cike
mata sakin gabadaya. Inno kiyi hakuri don girman Allah. Zan kama mata gida sai na mayar da
ita can. Kaga tun ina ganin mutumci da kimarka ka bar gidan nan kafin ayi abun kunya. Yadda
Uwale ta karbi Ummita to zan aikawa Yayansu ya dawo maka da danka. A'a inno na bar masa
ki dena maganar nan don Allah. Ya kalli Inna ladi ki bata hakuri, ko kula shi bata yi ba taja
hannun munari tana tirjewa cikin dakinta. Haka ya gaji da zama ya koma gida.

Washegari kafin azahar Inna Ladi ta aika Tani tazo da mai binta Shafa suka raka Munari birni
gidan Salihu bisa umarnin iyayensu.

Haka Dijengala inji kakarta uwale ta tashi cikin kuncin rayuwa da wahala. Mahaifinta ne kadai
gatanta. Tana da shekara biyu Sabuwa ta kara haihuwa. Dama ba wata kulawa Digengala ke
samu ba hatta wanka sai babanta ya matsa ake yi mata. Watarana ya fita da sassafe Sabuwa
ta kai ruwa bandaki a katuwar roba ta kira Hanan da Dijengala tayi musu wanka. Tana gamawa
yarta tace muje in shafa miki mai tukunna. Dije wadda aka yiwa tsirara sai rawar dari take
saboda sanyi tace Mama nima wanka. Wani mari Sabuwa ta gaura mata ta dauki yarta suka
fita. Dije tana kuka ta taka sabulu ta zame ta fada cikin robar ruwan. Sai da sabuwa ta gama
shirya Hanan bayan kusan minti goma ta dawo ta tarar da Dijengala ta kusa shidewa a robar
ruwa.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰14




BAYAN SHEKARA 17

Cikin daga murya irin na wadanda basa ji sosai tace Inna ina kwana? Uwale ta sha kunu matsa
can ni kada ki tofe ni da yawo kinzo kina min ihu a ka. Dijengala tace naam? Alamun bata ji
abinda kakarta ta fada ba. Tsaki Uwale tayi tare da daga hannu lafiya nace. Murmushi tayi
wanda yake kara mata kyau tace au banji ba ne. Dama ai ba jin kike ba. Ta sake daga hannu
tashi ki bani wuri. To..to..to ta mike ta koma dakin su ita da Hanan da kanwarsu Zaliha.

Wata yaloluwar katifa ta nufa ta kwanta. A hankali idanunta suka ciko da hawaye. Ita meyasa
bata da Umma? Ina dangin ummanta suke? Hawayen ne suka gangaro sai tari ya sarke ta.
Zaliha ce ta ganta bayan ta dawo daga makaranta. Yaya Dije sannu ta dafe mata kirji. don idan

ta fara tarin numfashinta har neman daukewa yake. Rashin kudi sosai yasa Babanta ke yawo
da ita gidan masu maganin gargajiya, wasu suce sanyi wasu suce asma. Zaliha ta dago kan
dije ta bata ruwa bayan tarin ya lafa. Ta daga murya Yaya Dije kuka kika yi ko? Tayi saurin
girgiza kai tari ne Zaliha. Allah Yasa da gaske kike, bari naje na dauko mana abinci nasan
yunwa kike ji ma.

Haka dokar Sabuwa ta koma abincin Hanan daban, Zaliha da Dije tare ake hada musu. Tunda
Dije ta gama secondary school wadda ba wani abin kirki ta iya ba saboda rashin kunne kullum
sai ta jira Zaliha ta dawo zasu ci. A cewar sabuwa kada dije ta cinye abincin. Babansu bai taba
sanin wannan dokar ba don har yanzu yana so da kula da lamuran yarsa. Shekararsu goma
sha biyar da baro kauyensu suka koma birni da zama. Takurawar iyayen Munari kan sai an
basu Dije yasa Uwale sayar da filayenta harda gidansu ta matsa masa sai sun tashi indai ba so
yake ya kulleta a gidan yari ba. Tayi mamakin yadda aikin malam bai kama su ba sai dai kuma
bata kara jin duriyar Munari ba tunda tasa Yakubu ya saketa. Aikin gini da noma yake yi a haka
yake ciyar da iyalinsa yake saka su a makarantar gwamnati. Tun tafiyarsu wadda basu yiwa
kowa sallama ba iyayen Munari suka sanar da ita duk abinda ya faru. Tayi kuka sosai saboda
tana matukar son 'yarta kuma ta kara tsanar Yakubu akan guduwa da yayi da ita. Allah Yasa ma
Sadi yana wurinta.

Hanan ta fara karatu a polytechnique ta garin kano tana ji da kyau da gayu. Duk gidansu babu
wanda take so kamar kakarta Uwale saboda yadda take shagwabata tana kuranta kyaunta. Duk
yar yaudarar samarin da take da izinin kakarta take yi. Tana kwance kan gadon uwale tana
chatting Mal Yakubu ya shigo dakin. Wani wuntsulowa tayi da sauri zat gudu. Hannunta ya rike
ya dawo da ita dakin munafuka ina zuwa. Ya zaka kirata munafuka dan nan ka kiyayeni fa akan
Hannan wallahi. Inna kina bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login