Showing 9001 words to 12000 words out of 14985 words

Chapter 4 - FARAR HAIHUWA Book 1 Chapter A Writing by Batul Mamman.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

2028

yarinyar fa. Kalli wayar hannunta abinda take saurin boyewa
kenan kada na gani. Uwale tayi murmushi zancen banza ai kudin dashi na na bata ta siya
dashi. Hanan tace Allah Baba ita ta bani.bari saurin rantsuwa ni tsakanina daku shawara ce. Iya
abinda zanyi miki nayi na tarbiya. Allah Ya shirya.
Ficewa yayi rai a bace ya tafi dakin yaran wurin Dije da Zaliha. Baba sannu da zuwa...yauwa
Zulaihatu. Taba min yayarki nasan bata ji shigowata ba. Tsinkin tsintsiya Zaliha ta sawa
Dijengala a kafa ta mike a firgice. Wayyo Allah...muryarta duk ta cika gidan. Tana ganin babanta
ta matsa kusa dashi. Baba kaga Zaliha ko...zan zane ta fa. Guje guje suka rinka yi a tsakar
gidan yana dariya. Yaran nan biyu kadai ne suke wanke masa bacin ransa da damuwa. Sune
kuma Uwale bata so don abin mamaki duk farin Sabuwa haka ta haifo Zaliha baka har tafi Dije
duhu. Shiyasa uwale bata shiga sabgarsu kamar babu su a gida.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:12 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰15

Ranka ya dade ga takardun filayen guda uku aka samu a wuri daya. Alh Sulaiman Hassan ya
kalli sakatarensa Modibbo nagode dan fillo. Zanyi magana da managers din sauran kamfanin
sai muyi finalising project din. Modibbo yace hakan yayi ranka ya dade amma akwai sako daga
wurin Hajiya fa. Murmushi yayi alamun yasan sakon Hajiyar yace nasan cewa tayi ka tabbatar
yau na tashi da wuri ko? Shima Modibbo murmushin yayi ni dai umarni nake bi kuma lokaci ya
riga yayi. Wai ni waye ke biyanka ne ni ko ita? Ai Alhaji da kai da kaya duk mallakar wuya ne. To
naji ya fada tare da mikewa.

A hankali yake tuki don yau drebansa bai zo ba matarsa ta haihu. Karatun Al-Quran yake ji
kira'ar Sheik Khaleel Husary yana bi cikin nutsuwa har ya isa gidansa a unguwar bompai ta
cikin garin kano.

A falo ya tarar da ita ta gama hade rai alamun tana fushi dashi. Mata ne biyu zaune tare da ita.
ko da ya gaisheta da kyar ta amsa masa shima yasan yayi laifi bai matsa mata ba yayi hanyar
bene tace cikin fushi Sulaiman ina zaka je kuma? Umma zan canja kaya ne na dawo. To kayi
sauri yaran kawata ne suka zo gaisheni shine nace su jira kazo ku gaisa. To kawai yace a ransa
kuwa harda dariya...umma kenan ta zama matchmaker karfi da yaji ita a dole sai yayi aure a
wannan shekarar. Shima kullum yana adduar samun ta gari yasan kuma Allah mai jin rokon
bayinSa ne.

Wanka yayi yasa kananan kaya ya sauko. Yana zama Umma ta mike to bari na duba abinda
ake dafawa. Yasan so take ta basu wuri ya ce to kawai. Tana tashi dayar wadda take ta yi masa
kirikiri da ido tace Yayanmu ni sunana Ainau wannan kuma kanwata ce Bilkisu. Ko kallonsu
baiyi ba don basu yi kama da masu kunya ba ya zaro kudi a aljihunsa ya mika musu ga kudin
mota nice meeting you. Sai anjima muje nasa dreban Umma ya kaiku gida. Ainau ta bata rai ai
Hajiya tace mu jira zaka kaimu da kanka idan ka dawo saboda kaga gidan. Ashe ma doluwa ce
yarinyar ya fada a ransa. Kinga naji ciwo a hannun bari a kaiku. Bani number dinki zan kiraki
musamman. Kanwar tace nifa? Itama karbar tata yayi yana so suyi su fita kafin Umma ta dawo.
Sai da yaga fitar motar daga gate din gidan ya dawo ya zauna. Muryar ummansa yaji tace
Sulaiman ina su Ainaun suke. Ai sun tafi wai sauri suke yi...amma yaron nan baka da kirki. Wai
so kake na mutu banga jika na ba shekarunka talatin da shida fa...jin ta fara shakar hanci yasan
kukan blackmail ne ya tashi. Kiyi hakuri Ummana na sami mata ina jira mu gama daidaitawa ne.
Ta washe baki hakoran makkanta suka bayyana. Da gaske Sulaiman? Da gaske Umma..to ai
da kayi magana da wuri bazan kira yaran nan ba, dama nima duk basu yi min ba. Yadda tayi
maganar yasa shi dariya sosai.

Modibbo da abokinsa Mal Yakubu suna zaune kofar wani gida da su mal yakubu ke aikin
ginawa yace mutumina Alhajin kamfaninmu ya sayi wasu filaye manya guda uku. Ban dai san
abinda zai gina a wurin ba amma naga so yake ayi ginin da wuri. Zanyi masa magana akan ka
ka samu shiga cikin masu yin aikin. Nagode Modibbo Allah Ya bar zumunci. Wallahi kudin

karatun yaran nan da ciwon Dije sune suke damuna. Kada ka damu in sha Allah zaka sami
wani abin yanzu don Alh Sulaiman akwai kirki. Haka suka zauna suna ta hira har laasar tayi
suka tafi gida tare.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰16




Hannu yaji ya sakalo masa wuya ta baya. Daddy oyoyo...tashi yayi ya daga Ammar sama yana
ta dariya. Umma ta fito ni kun cika min gida da ihu abinda kuka iya kenan. Dariya suka sake yi
mata Ammar yace Daddy dazu mamana tazo kafin ka dawo daga office. Umma ya kalla tace
Ammar je ka daki ka dauko wa daddy tsarabar da tayi maka. Yana fita tace zuwa tayi ta sanar
dani ta sami mijin aure. Ai gara tayi auren ta dade shekara shida ai ba kwana shida bane.
Sulaiman yace Umma Allah Yasa dai ba fushi kike dani ba akan rashin aurenta. Gyara zama
tayi ko kadan duk uzurin da ka bani na karba. Idan ka kai mata Ammar ranar jumaa sai kaji ko
waye mutumin.

Alh Sulaiman Hassan shine da na biyu a wurin Haj Bintu. mahaifinsa babban dan kasuwa ne
kuma yana da kamfanin yin kafet har uku a kasar. Shekarar Sulaiman ashirin da daya baban
nasa ya rasu bayan yasha jinya yayansa Yusuf ya cigaba da kula da kamfanin baban. A lokacin
da yake masters dinsa a fannin aikin banki , Yusuf ya rasu sakamakon hatsarin mota da yayi.
Ya bar matarsa sakina da ciki wata biyar. Bayan ta haihu ne Umma tayi ta kokarin hadasu da
Sulaiman yaki yarda a cewarsa bazai dena kallonta a matsayin matar wansa ba. Shekaru shida
kenan sai yanzu ta sami wani zata aura.

Saboda matsin layin daga can baya Sulaiman yayi parking motarsa shi da Modibbo suka taka
da kafa zuwa kofar gidan Mal Yakubu. Kwata ce a kofar gidan dole suka shiga daga dan zauren
waje inda Uwale ke kiwon tumaki. Banda wari da zarni babu abinda ke tashi a wurin. Sulaiman
ya gimtse fuska. Modibbo sarai ya gane warin ke damunsa yace yallabai kayi hakuri shiyasa
nace ka zauna a mota na kira shi.
Ba komai Allah Yasa ya fito yanzu dai.

Wata kyakkyawar yarinya ce ta fito fara tas harda dan karin mai. Cikin yanga take tafiya. Gaba
daya hankalin Alh Sulaiman ya koma kanta. Baba yace yana zuwa ta fada ba tare da tayi musu
sallama ko gaishe su ba. Ciki ta koma tana taunar cingam.

Mal yakubu ya fito ya gaishe da Alh Sulaiman sannan ya gabatar da kansa. Alh Sulaiman yayi
masa bayanin wurin da filayen suke ya kuma bukaci yazo kamfani ya same shi washegari.

Ihun da suka ji yasa su yin shiru Dijengala ta fito da gudu tana kuka. Murya can sama tace
Baba kaga Mama ta hanani wanka yau ma wai zan karar da ruwa. Kaji yadda nake tsami
kuwa...matsawa tayi gabansa tana daga masa hannuwanta har gashin hammata Alh Sulaiman
yana gani. Kuma fa jinin wata na yazo tun jiya . Subhanallahi Dije sauke hannun mana ya kama
hannunta zai koma cin gidan da ita. Tirjewa tayi Baba dukana fa zata yi kuma kullum Yaya
Hanan tana yi da Zaliha. Duk kunya ta kamashi ya daga murya don taji abinda yake fada...muje
nace zan mata magana. Burinsa kawai su koma cikin gida. Sai lokacin taga mutane tsaye...lahh
baba modibbo sannu da zuwa. Sai ta rike baki au...duk kunji abinda na fada ko? Wayyo kunya
ta dafe kai tare da komawa cikin gida. Alh Sulaiman kuwa dariya ce ta kwace masa ganin
yadda Dije take baragada a gabansu. Sai dai fa akwai wari dan kare.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰17



Wani murmushin ya sake yi shi kadai Umma ta jefe shi da pillow din kujera kai ni dariyar me
kake yi kamar kwancen hauka....wata dariyar ya sake yi sannan ya bata labarin Dijengala
kurma. Itama dariyar tayi maimakon ka taimaka mata shine kake dariya. Ni mubar wannan
zancen dai ya sunan yarinyar da kayi min zancenta ne? Ga mamakinsa sai yaji yace Hanan.
Daren ranar tunaninta ya rinka yi. Tana da kyau mai daukar hankali gashi da gani tana da tsafta
ba kamar Dijengala ba. Wani murmushin ya sake yi da ya tuno yadda take magana. Daga nan
har yayi bacci tunaninsa yana kan Dije yana dariya.

Ranar litinin duk ya kagu modibbo ya iso. Yana zuwa kuwa tambayarsa tayi ko anyiwa Hanan
miji. Modibbo yadan yi turus...Hanan dai yar abokinsa ce amma ko kadan bata da hali. Ranka
ya dade ba ayi mata miji ba a iya sanina. To ka sanar da mahaifinta idan ya amince zan nemi
aurenta. Modibbo ya nuna farincikinsa a fili amma ba don yadda Dije ta tashi ba sai shirme da
shiririta ga lalurar kurumta da ita zai so Alhajin ya nema.
*******************
Rana duk ta dami Hanan a kofar banki inda take jiran kawarta. Wata mota take ta kallo, ba
karamin kyau tayi mata ba...duk mai motar nan ko ba'a fada ba mai kudi ne kuma mai kyau.
Tayi dan tsaki ita kyau ma bai dameta ba indai akwai kudi. Tana zaune a wurin wani matashi ya
fito ya bude motar. Gaba daya ya tafi da hankaliñta ta bishi da ido. Kana ganinsa kaga kudi don
yawan shige shigenta tana gane mai kudi tana gane yaron mai kudi. Wannan matashin kam
shine da kudin. Tashi tayi ta kade skirt dinta tayi saurin zuwa gaban motar inda yake shirin rufe
kofa tace Alhaji kwana biyu. Ya dan dago kai a dakile yace ya kin sanni ne? Tayi baya yi hakuri

sai naga kamar wani da na sani ne. Sai kashe murya take tana magana ciki ciki. Ya bata rai
bashi bane to...matsa na rufe kofar. Kafin ta gama matsawa ya bugeta da kofar ya figi motarsa.
Kafin ya bace ta gama haddace numbar motarsa.






Batul Mamman💖
[8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰18



Kawarta Hajara ce ta fito jaka cike da kudi. Sorry Hanan na barki jira ko? Gaskiya da mita zan
miki amma na fasa. Wani kamu nayi mai kauri. Hajara tace haba a yana ina? Hanan ta fada
mata yadda suka yi. Amma zancen gaskiya kawata yayi min akwai kudi. Ji nayi kamar kudin
jikinsa yana kirana. Shegiya uwar son kudi nasan wannan mai cangala kafar zaki kaiwa. Allah
sarki innata tafi kowa kaunata. Ni ba wannan ba Hajara ki rakani gidan Babba mana. Akan
mutumin nan sai anyi aiki.

Dayake halinsu yazo daya shiyasa kullum a makaranta tare suke. Hajara da Hanan suka wuce
gidan Babba wani malamin tsibbu. Don yanzu bin malamai harda yan mata. Allah Ya kara shirya
mu. Bayan dukkan bayani Babba yace Hanan kin san sunansa? A'a amma ga numbar motarsa,
ka taba yi min aiki akan wannan wawan malamin da numbar waya ai. Ba damuwa Hanan ga
wanan turaren ki saka kan garwashi sai ki rubuta numbar motar a takaddu goma ki rinka
dorawa akan wutar har su cinye duka. Sai ki lazumci zuwa wurin da kuka hadu na kwana goma.
Idan baki ganshi ba to motar ba tasa bace. Godiya tayi sosai tace idan ciniki ya fada zaka
ganni.

Bayan kwana uku Modibbo ya sanar da Mal Yakubu bukatar Alh Sulaiman. Murnarsa bazata
misaltu ba ya sanar da Uwale. Burinshi dama tayi aure ya gaji da sintirin da samari ke yi masa a
kofar gida. Sabuwa ma tayi murna har ta sanar da babarta Zulai. Cikin dare ta bawa mijinta
shawarar ya aurar da Dijengala. Banda abinki Sabuwa ina Dije take da saurayi. Tayi wani
murmushin keta...wani kurma ne dan uwan Zainab makociyarmu. Tace a kauyensu yake Kura.
Hade rai yayi dakata malama ni 'yata bata gama kurmancewa ba kinji ko. Ki rike abinki rabonta
na tafe. Kuma dama ina son yi miki magana Allah ranar da kika sake hanata ruwan wanka zaku
yini a gidan nan ba ruwa. Yar hirar tuni ta watse ya juya yayi kwanciyarsa.

Gari na wayewa cike da zumudi Uwale ta sanar da Hanan zancen Sulaiman. Ta wani harareta
jiya tasha uban hayaki akan wani yau a kawo mata zancen wani Alh Sulaiman. Kinga Inna ki
bar maganar nan ina da wani. Haba Hannan mutumin nan fa kudi gareshi sosai. Mafarkina a
kanki ne zai tabbata. Hanan ta wuce zata shiga wanka. Kinga Inna ki bar maganar nan ku bashi

Dijengala ko Zaliha. Auzubillah uwale ta fada tana tofar da yawu. Dije ai ai musaki irinta. Yarinya
ga baki ga muni.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰19



Hanan tayi sati daya tana zuwa bankin da suka je da Hajara tun safe har sai sun tashi amma
mai motar bai dawo ba. Rai a bace ta koma gida duk ta kusa gama kashe kudin hannunta a
hawa motar zuwa banki.

Dakinsu ta shiga zata cire kayanta tayi wanka Dije ta shigo tana waka da karfi. Hakan ya kara
batawa Hanan rai ke rufa min baki banza kawai. Ta fice tana tsaki. Babanta ta gani a kofar
kitchen yana magana da Sabuwa...yauwa zo hanan dama zancenki muke yi. Ta turo baki gaba
ta karasa gabansa ta tsaya. Nasan an fada miki maganar Alh Sulaiman ko. Wanda kuke aikin
gini dashi baba? Eh ya amsa mata. A zuci tace tabdi magini zan aura? Allah Ya kiyaye, itama
Mama tsautsayi ya kawota gidan nan. Mal yakubu yace dama tafiya ce ta kamashi amma ya
dawo zai zo yau da daddare inji modibbo. Uhmm tace ta wuce bandaki. Wallahi bazai sameta a
gida ba ma. Me zatayi da talaka.

Haj Bintu tana ta kallon yadda Sulaiman ke shirin fita daga dawowarsa ko abinci bai ci ba. Ina
zaka ne don nasan wannan shigar bata zaman gida bace. Hular hannunsa ya gyara Umma
gidansu Hanan zani amma da Ammar zan tafi saboda zan kaishi aski. Wato ka dawo zaka nuna
min ban iya kular maka da danka ba ko? Yana dariya ya bata hakuri. To ina tsarabarta ko haka
zaka tafi? Mata fa sai da ihsani. Zan biya na siyo wani abun a hanya. Hannun Ammar ya kama
suka tafi yana ta yi masa hira.

Hanan ta rasa yadda zata yi ta fice daga gidansu tunda babanta yaki fita tun safe. In ba rashin
aikin yi ba kakkarfan mutum kamarsa ya zauna a gida wuni guda....tayi tsaki. Zaliha tace lafiya.
Hararar ta tayi ban sani ba ta bata amsa tare da fita daga dakin. Mal Yakubu na fita zuwa
masallaci sallar magriba ta fice ba tare da sanin kowa ba.
Alh Sulaiman yana dosar gidan ya fara jin warin kwatar kofar gidan. Shifa harkar warin nan
baya kaunarta. Ya rasa dan aike gashi bashi da numbar wayar kowa a gidan.Ammar ya tura ciki
ya sanar da zuwansa. Yaro ya shiga kai tsaye dakin da ya hango haske ya nufa. Uwale ce da
Sabuwa suke kallo yace salamu alaikum wai daddy na yace ya zo. Sabuwa ta kalli dan
kyakkyawan yaron kai kuma daga ina wa ya turo ka? Mal Yakubu ya shigo yace dan Alh
Sulaiman ne mai son Hanan. Kirata Sabuwa yana jirantaa soro.

Batul Mamman💖
[8/22, 3:15 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰20




Sau uku ta kira taji shiru. A zaune ta tarar da Dije tana gyangyadi kafin Zaliha ta dauko musu
tuwo. Shureta tayi da kafa ke kurma tashi...a firgice ta tashi tace mama me ya faru? Ta dungure
mata kai tare da rage murya ubanki ne ya faru. Dije ta bata fuska tana nuna kirjinta ubana?
Ubana?? Sai hawaye...ke yi min shiru munafuka ana magana sai kiyi ta kallon bakin mutane
ina Hanan? Dije tace ta fita tun dazu. Kai yarinyar nan zata ja min masifa ta koma daki ta fadaw
Mal yakubu.

Ransa yayi matukar baci gashi yar wayar tasa ma ba kudi bare ya kirata. Uwale tace yarinyar
nan neman tona min asiri take ga wayata kirata. A kashe suka ji wayar. Bari na fada masa
kawai ,ita kuma yau tamu ce ni da ita.

Jin Zaliha bata dawo daga dauko musu tuwo ba Dijengala ta duba kitchen bata ganta ba ga
yunwa yana cinta. Ita kuwa Zaliha cikinta ne ya kada ta tafi bandaki. Wata tsohuwar naira
ashirin ta dauko a kasan akwatinta ta saci jiki zata je siyan wainar fulawa a gidan Zainab
makociyarsu. Tana saka kafarta a soron aka dauke wuta, saboda duhu hannunta take mikawa
kamar makauniya tana neman hanyar fita, wani mulmulallen abu mai dan gashi gashi taji ta
shafa ta tabbatar ba kan daya daga tumakin Sabuwa bane. Ammar data tabawa kai ihu ya
saka. Daddy kamani naji an taba min kai. Sulaiman yace ina zuwa Ammar wayata nake nema.
Dije sake taba kan tayi don ta tabbatar da abinda ta taba, gashi tana jin kamar maganganu
amma ta kasa gane me ake fada. Ihu tasa iya karfinta wayyo Allah baba nayi gamo. Sulaiman
tuni ya gano muryar yar kazamar yarinyar nan yace ke rufa mana baki yana neman hannun
Ammar su fita. Ta soma kuka Al'Quran naira ashirin ce a hannuna waina fulawa zan siyo a
gidan Zainab yunwa nake ji. Gashi don Allah kada ku mayar dani kaza ko doya. Ba shiri
sulaiman ya soma dariya...hannun dansa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login