Showing 12001 words to 14985 words out of 14985 words

Chapter 5 - FARAR HAIHUWA Book 1 Chapter A Writing by Batul Mamman.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

2030

kama. Yana jin yadda Dijengala take tsalle da ihu.
Mal Yakubu ne ya iso soron da yar fitila. Shima bai kula da su Sulaiman ba don ya zata sun tafi.
Dije dena ihu nine...tana ganinsa tayi saurin matsawa kusa dashi tana magana da karfi, baba
aljanu ne suke son bude min ido, dansu suka turo min shegu. Kul kike zagi dije...shima baba
zuciyarsa ta kusa bugawa daya ji ance daddy mu tafi. Sai a hankali ya gane Alh Sulaiman ne da
dansa.




Batul Mamman💖

[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰21



Da kyar ya iya tsayar da dariyarsa yace Mal 'yar nan taka tana da abin dariya. Ai nima na
tsorata don nayi tunanin kun tafi. Ammar ya nuna takalminsa ne ya kwance na tsaya daure
masa sai aka dauke wutar kuma ina tunanin wayata tana mota. Sake sallama suka yi kafin
Sulaiman ya gama fita yaji mal yakubu yana tambayarta ina zata.. wallahi baba yunwa ce kuma
zaliha bata kawo abincin ba, dama wainar fulawa zan siyo ta ashirin. Dariya yayi haba Dije
wainar ashirin ai sai da kiyi kuskurar baki da ita. Me kace baba? Banji ba. Muje na baki nawa
abincin kici a daki kada sabuwa ta gani. Daddy mu tafi mana wari nan. Sai a lokacin sulaiman
ya dawo hankalinsa yaja hannun Ammar suka fita bakin layin inda yayi parking motarsa.
****************
Ashir ya rasa abinda ke masa dadi. Tun washegarin zuwansa banki zuciyarsa ke masa radadi
ya rasa dalili. Ji yake kamar ya koma bankin ya nemi yarinyar da ta yi masa magana amma shi
ko fuskarta ma bazai iya tunawa ba don bai kalleta da kyau ba. Wata biyu ya rage bikinsa
amma yan kwanakin nan baya son ko jin sunan matar da zai aura. Dama dai auren baya
gabansa don shine na uku ma. ba ya dadewa da mata suke rabuwa, hakan na damun yan
uwansa shiyasa wannan karon babansa ya yanke shawarar hada shi da yar kaninsa da mijinta
ya rasu shekaru shida da suka wuce, wato sakina mahaifiyar Ammar. Gidansu Ashir suna da
rufin asiri dai dai gwarwado. Lokacin da ya fara aikin kwangila ga aikin office shine kudi suka
zauna masa sosai. Kasa nutsuwa yayi karshe ya yanke shawarar zuwa bankin a daren bayan
yayi magriba a kofar gidansu.

Hanan na sauka daga adaidaita sahu suka hada ido da mutumin da take ta nema. Gabansa ne
ya fadi yana ganinta. Banda kyawunta wani yanayi ya shiga mai wutar fassara. Idan bai auri
yarinyar nan ba rayuwarsa tana cikin matsala. Har wani gumi ke keto masa. Karasawa yayi inda
take ba tare da yayi mata magana ba ya mikawa dan sahu dubu daya yace mata zo mu karasa
bakin motata. Ba musu ta bishi...lallai aikin Babba yayi kyau.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰22



Bude mata yayi ta zauna a seat din gaba. Shima yana zama yace me ya fito dake a daren nan?
Ta rausayar da kai tana kare masa kallo, ga kyau ga kudi.ready made kenan..kai ya kamata
nayiwa wannan tambayar. Hmm ina jin abinda ya fito dani ne ya fito dake. Me kenan ta
tambayeshi ciki da jindadi. Yana kallonta yace tunaninki mana. Duk kin hanani sakat...ina

tunanin kema hakan take a wurinki. Ni fa kudi nazo dauka ba wurinka nazo ba. To fitar min daga
mota indai hakane. Tsoron kada garin jan aji ta rasa shi yasa tayi saurin cewa wasa nake maka.
Nima ka hanani nutsuwa tun ranar da muka hadu. Yaji dadin amsarta...ni sunana Ashir Sani. Ina
aiki a NNPC sannan ina harkar kwangila sosai. A takaice dai i am a very busy man. Ina ruwanta
da yawan aikinsa indai akwai kudi. Ta fada masa nata sunan daga nan hira suka rinka yi kamar
sun dade da juna. Ganin tara ta wuce yace muje na kaiki gida.

Alh Sulaiman na fitowa daga layin gidansu Hanan ya hangota cikin motar wani. Ina taje a daren
nan ya tambayi kansa. Motar na kara matsowa yaga kamar yasan mai tukin amma ya kasa tuna
ko waye. Bai kawo komai a ransa ba ya tafi gida.

Cikin sati biyu soyayya ta kullu sosai tsakanin Ashir da Hanan. Ta sanar da uwale da sabuwa
komai game dashi. Tuni ta sace zukatansu bare da suka ga irin hidimar da yake mata. Mal
Yakubu dai ya nuna rashin amincewarsa. A cewarsa bazasu mayar dashi karamin mutum ba.
Ya riga ya amsawa Alh Sulaiman har yace zai turo iyayensa don baya son a dauki lokaci. Uwale
tace to dan nema mai toshe kofar arziki. Shi Sulaimanun nawa ya taba bata tunda yazo. Inna ki
dena koyawa yarinyar nan son kudi, zuwansa uku fa kullum ba ta gida. Yau idan ta dawo sai
naci mutumcinta. Shegen yawo kamar kaza. Uwale ta sha kunu bana son irin haka fa, ka manta
tana karatu ne? Ni dai na gama magana yarinya Ashiru zata aura. Jiya da ya shigo dubu goma
ya bani. Ni Uwale da dubu goma tawa ta kaina. Ka sallami wannan abokin ginin naka don
bazan bashi jikata ba.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰23



Abokin gini kuma Inna? Ni da na fada miki gini zanyi masa yana da kamfani. Sabuwa da tun
farko bata yi magana ba tace haba Malam wai kai a dole sai ka nuna baka son yarinyar nan ne?
Ya arziki na binmu kana sa kafa kana shurewa. Babu wanda ya isa yayi mata dole. Wanda take
so zata aura. Idan kuma dole ne sai ks bashi Dijengala ai itama mace ce. Inna Uwale ta tuntsire
da dariya...wa yaga barahaza. Ba yadda ya iya dole ya kyalesu idan suka hade masa kai don
baya iya musu da Inna Uwale. A zuciyarsa ya gama yanke shawarar sanar da Modibbo ya
bawa Alh Sulaiman hakuri. Dama can ba sa'an auren yarsa bane shima don yaga kamar auren
zai hanata yawo ne.

Alh Sulaiman yana mamakin yadda duk lokacin da yaje baya samun Hanan kullum sai ace
masa bata nan, gashi Umma duk ta kwallafa rai. Shi kanshi yana son ya kara ganin kyakkyawar
fuskar Hanan din. Yarinyar akwai class. Yana dawowa daga office ya shirya ya tafi gidansu da

yamma. kila don saboda zuwan dare yake shiyasa baya samunta. Yau tararta zaiyi kafin ta fita.
Yana tuki Dijengala ta fado masa a rai. Shi kadai yayi murmushi Allah Yasa itama na sameta...a
ransa har ya gama shawarar idan yau auri hanan zai ce ta taho da kanwar tata.

Yau ma can baya ta ajiye motarsa. Sabuwar benz ce da masu kudi ke yayi ya shigo lokon a
kafa. Farin yadi ne a jikinsa mai bula bula. Wandon da shafi amma babu a rigar, ana ganin farar
vest din dake ciki. Takalminsa da hula duk ruwan toka ne. Yayi kyau sai kamshi ke tashi duk
inda ya wuce. Bai ankara ba yazo daidai kwatar kofar gidan Mal Yakubu yaji an kwala ihu sai
ruwan kwata ya gani ya fallatso masa ko ta ina a jikin kayansa harda gefen fuskarsa. Ransa ya
gama baci sosai saboda shi mutum ne mai matukar kyankyami. Dijengala ya gani kafarta daya
a cikin kwatar babu ko mayafi a jikinta tana kuka. Ganinsa a tsaye yasa kukan ya karu ta soma
bashi hakuri da karfi. Don Allah kayi hakuri ban sani ba. Inna ce ta biyoni da bulalar doki. Kafin
yayi magana wata dattijuwa ta fito daga gidan da ke kusa dana su Dije. Daga murya tayi yadda
Digen zata ji...me ya faru Digengala? Ta sake wani sabon kukan sannan ta fita daga kwatar ta
karasa wurin matar. Gwaggo, Inna ce tace yau bazanci abinci ba sai na debo ruwa bokiti goma.
Kuma fa na debo shida amma yunwa nake ji. Tace na sa baba yaki siyo ruwa saboda sun
hanani na wanka jiya daya fita. Gwaggo taja hannunta kiyi hakuri kinji yar albarka shigo kici
abinci kiyi wankan. Ta kalli Sulaiman wanda ya zuba musu ido. Alhaji shigo kaima kuma kayi
hakuri.

Ya kalli tsohuwar ba damuwa? Haba yaro ni da 'ya'yana biyar ne a gidan nan babu mace ko
daya sai matar babban. Kazo ka dan gyara jikinka. Suna shiga daga bakin kofa ya tsaya aka
bashi buta ya dauraye kafarsa yana ta dage hanci. Kadan ya rage burinsa ya koma gida kawai.
Yana ta kallon yadda Dije ke cin abinci da sauri da sauri. Yace don Allah ina da tambaya
gwaggo. Ina jinka ta amsa. Wai ita yarinyar nan wace ce ita? Kamar jira take ta bashi labarin
duk abinda ta sani game da Dijengala da wahalar da Sabuwa da uwale ke bata. Sosai ya
tausaya mata bata da wata damuwa sai ya cikinta. Yayi godiya zai fita Gwaggo tana yiwa Dije
waka. Dijengala ta maigari, ba auren talaka ba. Yana bakin kofa suka ji ance sai auren musaki
ba, kurma irinta.

Inna Uwale ce ta hau kan wata katuwar bambu ta ruwa da aka kifa daga gidanta. Sabuwa ta
riketa ta tsaya don kar ta fada ta leko ta katangar da ta hada gidanta dana gwaggo. Sulaiman
har dan tsorata yayi sai kuma ya tsaya yana jin tijara irinta Uwale. Dije tuni ta tashi daya kan
kwanon tuwon ta koma bayan gwaggo ta buya. Zaki shigo gidan ki same ni ne 'yar banzar
yarinya, waye bawanki da zai debo ruwan. Gwaggo tace Ke dai Uwale kinji kunya wallahi...idan
zaki shekara kina nunawa yarinyar nan tsana bazaki taba canjawa kanki suna a matsayin
kakarta ba. Kuma wallahi idan kika sake min leqe da wannan shanyayyar kafar taki sai na tsire
miki idanu. Cikin fushi tace ni kike fadawa haka...wallahi zan hadaki da hukuma su shiga
tsakaninmu. Makotaka ai ba hauka bane duk kin samin ido inji uwale. Gwaggo tace anji kunya
dai ace danki ma hakuri yake da halinki, duk kin bata masa gida da tashin hankali. Kin rabashi
da matarsa da yake so kin hada shi da wannan makirar. Shewa uwale tayi kamar ba tsohuwa
ba. Ai na isa ne.

Sabuwa ce taji cizon cinnaka a kafa ta saki Uwale ji kake timmm ta fado tana ihu. Gwaggo tace
Allah Ya kara kadan ma kika gani.

Shi dai Sulaiman tunda yaji maganganun wanda basu san ma yana kofar soron ba sai tausayin
Dijengala mai cin tuwo ya kam[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰24




Yana isa gida Ammar ya tare shi a bakin kofa...hmmm daddy wari. Umma dake zaune tana
yanke farce tace daga ina haka. Itama ta kama hanci kai me ya sami kayanka. Ina zuwa umma
bari na gyara jikina.

Bayan yayi wanka doguwar riga yasa ya sauko kasa. Yana zama ya fara yiwa Umma hirar
dijengala. Yadda yake bayanin cike da nishadi kamar ba shi aka watsawa kwata ba. Umma tace
wai ni Sulaiman kanwar kake so ne ko yayar? Murmushi yayi Umma yar nake so mana. Ita
wannan Dijen zanso ki ganta. To ai yadda kake fada kamar babar hanan din ke takura mata. Ba
don yar ka fara nema ba ai da sai ince ka nemi Dijen don naga tafi burgeka. Ahh haba umma
kurma ce fa. Ta rike baki to sai me Sulaiman? Kurma ba mutum bace? Ni nafi son irin auren nan
da zai kasance taimako ga wani.

Tun da Umma tayi masa magana sai kawai hankalinsa ya rabu biyu. Tabbas sau biyu yana tarar
da rigima da Dije akan ruwan wanka. Kana ganinta kuma sam babu gyara. Yasan a kalla zata
kai shekaru ashirin. Da wannan tunanin ya jira litinin tazo. A office ya sake yiwa modibbo
tambayoyi akan Hanan. Wannan karon gaskiya ya gaya masa game da halayyarta. Kuma a
yadda babansu ya fada min jiya wai kakar ta zata kaima aikin gini kake yi shiyasa suke son a
bawa wani. Mal Yakubu har kunyar ka yake ji saboda yadda take ficewa daga gidan kafin kazo.
Hmm wato sun dauka talaka ne shi yake fada a ransa. To idan ba damuwa modibbo ka sanar
dashi zanzo gidansa zuwa karshen sati akwai maganar da zamuyi. Modibbo fata ya rinka yi Alh
Sulaiman ya nemi auren Dije.

Alh Sani ya kalli dansa Ashir..yanzu da gaske ka fasa auren sakina? Ashir me kake son mayar
dani ne. Haj Lami tace kaga duk wancan auren kai kake zaba masa kila shiyasa baya karko
wannan karon don Allah kada kayi masa dole. Ai dama da saninki yake wannan wulakancin.
Yanzu meye aibun Sakina? Haj tace bazawara ce fa. Ga budurwa ya samu son kowa. Har
hotonta nagani. Alh Sani yace shi ma ai bazawarin ne...bazan tilasta masa aurenta ba kada ya
bata mana zumunci amma wallahi Ashir idan ka kara sakin mace zan maka ba dadi. Shashasha
wanda bai san mutumcin kansa ba. Shi dai Ashir ko tak bai ce ba ya tashi ya tafi gidansa. Me
zaiyi da wata Sakina ana zaune kalau. Yadda son Hanan ke ci masa zuciya baya fatan a wuce
wata daya bata zama matarsa ba.

Yau Alh Sulaiman da abokinsa ya tafi gidan Mal Yakubu bayan sun yanke shawara shi da

Ummansa. Umar yace yanzu Sulaiman har lokon nan ka zo neman aure? Wannan yarinya ta
ciri tuta. Yayi dariya sai ma ka ganta mutumina. Ai na iya zabe.

Goruba take ci a kofar gidan Gwaggo ita da kawarta. Kawar ce ta fara hango su Sulaiman tace
ke Dijengala kinga wasu yan gayu can. Dije na ganin Sulaiman ta gane shi. Al'Quran shine
mutumin dana watsawa kwata. Tashi mu gudu dan sanda ya dauko min. Na shiga uku.

Da gudunta ta tafi zata shiga gida ta kira babanta ya basu hakuri don taga kamar kayan jikin
abokinsa na yan sanda ne. Bakaken kaya ne shirt da wando ne. A kokarin gudun ne dan
katakon daya raba kwatar gidansu ya rufta da ita ta sake yi masa kwalliya da kwata. Rasa bakin
magana yayi don takaici yana tunanin fasa abinda ya kawo shi. Ita kuwa Dijengala ta gama
tsurewa don tsoro ta bare baki tana kuka, muryarta a sama.





Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰26



Gwaggo ta dauko tabaryarta tayo hanyar soro. Tana ganinsu tace au Alhaji kaine...kaji shirmen
Dijengala ko. Wallahi duk na zata da gaske take. Kallon jikinsa tayi...ba dai yau ma kwatar kuka
fada ba? Murmushi yayi yace bata kula bane ta fada ciki.

Daga ciki suka jiyo Dije tana cewa ba dai sun tafi da Gwaggo ba. Na shiga uku me zan fadawa
'ya'yanta. Shigowarsu ta gani ta saki baki na tuba don Allah ku yi hakuri kaga ni bana ma ji
sosai kaina bazai yi kudi ba. Gwaggo tace rufa min baki sarkin surutu.dauko musu ruwa a buta.
Kema ki je ki gyara jikinki.
Bayan sun kammala gwaggo tace kai kuma kullum kuka hadu da Dije sai tayi maka wanka da
kwata. Ba komai Gwaggo dama mahaifinta nake son gani. Bari naje nayi masa magana da
kaina to, kasan halin yarinyar nan ina iya turata taki dawowa.

A wulakance su Uwale suka gaisa da gwaggo tace wurin Mal nazo. Sabuwa tace bacci yake yi.
Mal yakubu ya fito suka gaisa. Tace dama kayi bako ne shine babu dan aike nazo yi masa
sallama da kai. Uwale tace haka dai aka iya gulma da sa ido. Gwaggo bata kula ba suka fito
waje...mal yakubu bakon yana gidana fa. Yace sunansa Alh Sulaiman. Mal yace subhanallah
wallahi har kunyarsa nake ji. Ya sanar da ita yadda suka akan maganar Hanan. Gwaggo tace to
Allah Ya kyauta muje sai kayi musu bayani.

Umar ne ya gabatarwa mal Yakubu bukatarsu game da Dijengala. Sulaiman yace baba kada

kaga kamar ina maka yawo da hankali. Naga kamar Hanan din tana da wani ne shiyasa.
Tamkar an mishi albishir da kujerar makka yace da gaske kake Alhaji? Kai zaka auri Dijengala.
Sulaiman yace in har ka amince. Na fara sanar da kai ne don neman izini kafin na turo maka
iyayena. Farincikinsa baya misaltuwa yayi godiya sosai. Umar ya bashi dubu ashirin yace baba
ga wannan mungode.

Suna tafiya Mal ya dauki kudin ya bawa gwaggo ajiya dama ya saba shawara da ita. Yace
yanzu zan sami nutsuwar amsawa wanda yazo neman auren hanan. Dama saboda na riga na
amsa tun farko ne. Gwaggo tace ai gara tayi auren saboda Uwale kara bata ta take yi. Haka
suka yi ta yan shawarwarinsu sanan ya kira Dije ta fito daga daki suka koma gida.
Ashir ya dage sai shirye shirye yake. Anyiwa gidansa sabon fenti an gyara ko ina. Dama ya
kusa gama hada lefen Sakina saboda haka abinda ya rage ba yawa. Ya dai kashe kudi sosai
don duk abinda Hanan tace ta zauna. A dan lokacin da suka hadu ya siya mata sabuwar waya
ga kudi daya ke kashe mata.
Mal Yakubu ya sanar da uwale zaije gida ya sanar da kawunsa da nata yan uwan za'a zo
neman auren Hanan dana Dije. Uwale da Sabuwa sam basu damu ba da jin Dije ta sami miji
tunda Mal Yakubu yace wannan abokin ginin nasa ne zai aureta. Shima yana sane yaki fada
don gudun kada su toshewa yar tasa hanyar arziki. Ita uwale harda cewa kyan da dama ya gaji
ubansa, tunda ita mace ce gara ta auri mai aiki irin na ubanta.

Tunaninsa bai wuce ina ma Munari tana nan. Ina ma zata ga auren yarsu. Babu ranar da baya
tuna su ita da Sadi. Amma gashi Inna uwale ta gargade shi ko sau daya yabi hanyar gidan su
munari bata yafe masa ba.
Haka yaje kauyensu ya sanar da yan uwansa zancen auren ya dawo a ranar.




Batul Mamman💖
Copied By

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login