Showing 3001 words to 6000 words out of 14985 words

Chapter 2 - FARAR HAIHUWA Book 1 Chapter A Writing by Batul Mamman.pdf

04 Jun 2025

541

ta faman nema miki yarinyar da Yakubu zai aura jiya da daddare sai ga
Sabuwa. Uwale tace fara gaya min zancen yarinyar kafin muyi zancen sabuwan. Zulai ta sha
kunu Uwale baki da kara fa. Aurenta fa ya mutu. Ajiye ludayin tayi eyye kika ce me? Nace
aurenta ya mutu. Ashe wata biyar kenan da mijin ua saketa bata fada ba ta zauna gidan tana
son ya mayar da ita gashi har iddah ta kare. Jiya yayi mata korar kare. Sai wasu hawayen ke
zubuwa daga idon Zulai ganin kudaje na bin kokon furar tasan sarai uwale na gani zata zubar
da ita gaba daya. Uwale tace to ai ki bar binciken haka tunda har ta gama iddah kuma na tuna
duk yaranta farare ne. Ki bar komai a hannuna ranar asabar zata tare a gidan wannan alqawari
ne. Zulai sai murna , uwale tace ga fura ki sha. Kafin ta rufe baki Zulai ta janye kokon ta kafa
kai. Mayunwaciya Uwale ta fada a sarari.

Tana zuwa gida ta sanar da Sabuwa yadda suka yi. Ni dai na fada musu kin gama iddah idan
ba haka nayi ba kinsan uwale da rashin hakuri kamar zawo sai ta bashi wata. Sabuwa ta hadiyi
yawo da kyar tace Gwaggo ina jin ciki gareni fa wata kusan biyu. Muhuci zulai ta kwala mata a
ka. Baki da aiki sai ciki ne duk yunwar gidan inuwa. To bari kiji. Ranar asabar zaa daura
aurenku sai kiyi shiru da bakinki. Idan kika haihu sai muce bakwaini[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:02 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰6



Sabuwa ta ware idanu kai Gwaggo ai kinga auren babu iddah ma ba kyau ko? Zulai ta banza
rufe min baki. Inji uban wa aka ce ba kyau. Aure kan aure ne ba kyau kuma dai ba shi zakiyi ba
tunda ya sake ki. To cikin fa? Shi ciki ai ba matsala kinsan Uwale babu abinda ba zatayi ba
akan farin jika. To nasan tana da gonaki biyu na gadonta kinga ko ita muka samu mun huta.
Sabuwa dai bata gamsu ba tace Gwaggo zunubin fa. Ai dan zai zama shege...kul kika kira shi
shege da ubansa fa. Ina fata bai san da cikin ba? Eh bai sani ba. Zunubin kuma zamuyi ta
cewa astangafirillah sai kiga Allah Ya yafe. Sabuwa tace Astagfirullah dai Gwaggo. To naji
yanzu dai kin amince ko. Na amince Gwaggo. Sukq zauna suka kulla duk yadda zasuyi a gidan
Uwale idan aure ya yiwu. Saar su daya kauyen da Sabuwa ke aure daban da nasu saboda
haka da wuya yaji labarin auren.

Shirye shirye ya kankama na bikin Sabuwa da Mal Yakubu. Uwale da Zulai le kidansu da
rawarsu don shi angon ko a ransa. Kullum yana rarrashin Munari ta kara hakuri idan ya sami
kudi zai raba musu gida da Inna Uwale. Ana saura kwana biyu Yaya Salihu yazo garin
Danmarka gaida iyayensa shi da matarsa Ruma. Tani na jin labarinsa ta tafi gidan ta zayyana
masa halin da Munari ke ciki. Fada ya rinka yi iyakar karfinsa Inno tana bashi hakuri. Inna Ladi
tace ni bazaka burge ni ba sai kaje gidan kayiwa uwarsa barazana yadda zata yi shayin
takurawa 'yata. Kamar jira yake ya tafi gidan cikin fushi. A bakin kofa ya gamu da Mal Yakubu
ya fara zazzaga masifa. Mal Yakubu duk ya tsorata yana ta bashi hakuri. Har gidan ya shiga
sukayi ta da Uwale yace ke Maimuna dauko mayafinki ya kama hannun yaran..birni zamu tafi
kai kuma ka biyoni da takardarta. Mal Yakubu dai harda kuka itama Munari tana yi. Da kyar
Yaya Salihu ya aminci ya barta amma ya dauke Sadi dashi zan tafi. Mal Yakubu yace wallahi na

bar maka shi don girman Allah kada ka rabani da matata. Yaya Salihu yace mata zan kaiwa
Ruma kinji ko munari sai ta hada shi da Ali su shiga makaranta idan sun dan kara girma.
Godiya tayi masa ya kawo kudi ya bata. A waje ya sake jaddadawa Mal Yakubu ya kular masa
da kanwa sannan idan anyi auren zai sa ido a kansa. Daidai da rana daya yaji zance mara dadi
zai dauki mataki.

Ranar lahadi da karfe biyun rana bayan an idar da sallar azahar aka daura auren Mal Yakubu
da Sabuwa. Dakinsa aka saka amarya ya zama bashi da daki a gidan sai na wadda take da
girki. Da daurin gindin uwale Sabuwa ta goge da yiwa Munari wulakanci a gidan. Kullum hakuri
take saboda yadda mijinta ke iyakar kokarinsa wurin kyautata mata. Watan Sabuwa biyu a
gidan ta fara bayyana cikinta kamar yadda suka yi da Zulai. Uwale kamar ta lashe ta don so.
Kullum Zulai tana gidan abinci safe ,rana da dare duk an mata kwano. Habaici iri iri Munari take
sha idan suka hade kansu karkashin bishiya da yamma. Kirikiri Uwale ta hana Sabuwa girki
kullum Munari keyi idan dare yayi kuma ta tubure tace sai Mal Yakubu ya shigo dakinta ranar
girkinta.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:02 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰7




Haka rayuwa ta kasance a gidan Mal Yakubu yau fari gobe tsumma a wajen Munari. Ba don
soyayyar da suke ma juna ita da mijinta ba da tuni ta bar gidan.

Sabuwa na kwance a kofar dakinta da daurin kirji tana shan rake Uwale ta fito daga bandaki
tace kai sabuwa ki raba kanki da zaki fa saboda nakuda. Kinji ki Inna kamar wata sabon shiga?
Haihuwa ta uku har sai kin karanta min yadda zanyi? Ta yatsina fuska ke fa daya kawai kika yi
ta tsaya miki cak. Munari daga cikin dakinta tace Allah Ya kara ta cigaba da yiwa yarta Ramlah
kitso. Uwale har wani tsoron sabuwa take ta ajiye butar hannunta tace to Allah Ya baki hakuri
uwar biyu. Wannan ciki naki badai girma ba. Gaban Sabuwa ya fadi ita bata taba ciki mai
girman wannan ba ma gashi a karyar da tayi baifi wata bakwai ba. Bata sake tankawa Uwale ba
don kada a ja maganar ta cigaba da shan rakenta.

Bayan sati uku wata rana Uwale da zulai sun fita unguwa tun safe nakuda ta kama Sabuwa. A
muguntar Uwale kulle gidan tayi ta waje wai kada munari ta fita saboda taji Mal Yakubu yana
cewa ta dawo da wuri tasan sarai unguwa zata. Da munari ta shirya ta shirya yarta zasu fita taji
kofar a garkame. Ta gaji da ja ta dawo daki rai a bace. Dama gidan kanwar Inno zata je ziyara.
Tana ajiye gyalenta taji kamar ana kiranta daga dakin Sabuwa. Shiru tayi ta tabbatar sannan ta
fito cikin sauri. A kwance ta ga Sabuwa tana nishi da kyar duk ta hada gumi duk da sanyin gari.
Munari jika na rawa don itama bata saba ba tace Sabuwa kinga Inna ta kullemu ta waje kuma

saboda zurfin soro babu mai jinmu kiyi hakuri na dubaki. Cikin masifa tace kiji dadin kasheni
ko...ki fita ki nemo taimako Munari don idan na mutu sai nayi miki fatalwa. Babu irin bugun da
Munari batayi ba babu wanda yazo kashe reza ta samo a daki ta dawo kan sabuwa. Tace kiyi
hakuri inajin bakwaini zaki haifa don kai ya fito. Da taimakon Allah Munari tana ta yi mata addua
ta samu Sabuwa ta haihu. Yarinya ce santaleliya fara tas irin wadda Uwale take so. Munari ta
yanke cibi ta taimaka mahaifa ta fito. Kai Sabuwa wannan 'ya da takai wata tara ban san irin
girman da zata yi ba. Ruwan wanka ta dora ta wanke jaririya ta kaiwa sabuwa ruwan wanka.
Sai bayan laasar Uwale da zulai suka dawo. Tun daga tsakar gida uwale ke yiwa Munari dariyar
keta ta hanata fita. Munari ko a jikinta tace Inna kinyi kawa fa. Ko kulata bata yi ba harda tsaki
zata wuce tace Inna nace kinyi kawa fa Sabuwa ta haihu. Zulai ta yi dakin cikin sauri Uwale
tana binta tana cangala kafa. Allah Kasa fara ce, Allah Kasa fara ce. Haka take fada har ta
shiga dakin. Baby ta dauka ta rungume. Yarinyar akwai kyau ga hasken da Uwale ke buri. Zulai
ta rike yarta. Sabuwa bakwaini kika haifa? Me ya faru haka? Waya karbi haihuwar? Sabuwa
tace nakuda ce ta kamani gashi kun kulle gidan. Munari ce tayi komai, Uwale ta rungume yar ta
fita. Munari ta gani tana kwasar tuwo ta dan saki fuska nagode fa Munari sannu da kokari. Zulai
da ta gama zige yarta a cikin daki ta fito da sauri wace godiya zakiyi mata uwale? Ashe kina fita
ta kama Sabuwa da kokawa shine haihuwar tazo ba shiri. Ai don kada a kamata da laifin kisa ta
karbi haihuwar. Uwale ta bata rai muguwa azzaluma da mai kyan zaki kashe min. To ta Allah ba
taki ba baka mai bakar aniya. Tuwon ma bazata ci ba kada kisa guba. Kwashe abinki ki bace
min da gani. Hawaye ne ya saukowa Munari ta je har kofar dakin ta leka Sabuwa na kwance a
kan gado. Cike da takaici tace Sabuwa abinda zaki saka min dashi kenan ko? Allah na gani
kuma baya bacci. Zulai tayi tsaki muguwa kinga farar haihuwa kina bakin ciki.

Mal Yakubu dai yayi farinciki daidai gwargwado yace to Inna sai asa mata sunanki ko. Tunda
kan Ramlah kika ce kada asa sunanki. Uwale tace yo haka kurum zaka sawa wancan
mummunar abar sunana? Ya jawo abarsa ya rungume suk yaransa yafi sonta. Inna tace itama
wannan bazaka sa mata sunana ba saboda kyanta. Akwai sunan gayu dana taba ji wallahi wata
rana dana je gidan Harira jikanta ya kunna talabijin. Sabuwa tace ni fa Inna kada ki bata wa
yata suna. Inna tace ni dai Hannan naji an fada ai ko yayi dadi ko? Sabuwa ta bata fuska
Hannan kamar marowaciya Hanan ake cewa. Na yarda Malam a saka mata. Mal Yakubu yace
to Allah Ya raya ya dauki Ramlah ya tashi yayi waje.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Hanan. Uwale sa guda ta bayar aka yanka cikin shanunta
uku. Anyi bushasha ranar suna kamar haihuwar fari. Yan uwan Sabuwa suna ta zuba habaici ga
Munari. Ga 'ya mai goshin arziki an haifa. Haka dai akayi ta taro Munari da nata yan uwan suna
daga cikin daki. Yayar sabuwa na suyar nama ta bawa duka yaransu aka tsallake Ramlah. Ta
rinka binsu da kallo har Uwale ta kula tayi tsaki ai idan baki bata ba Hanne yarinyar nan kamar
mayya sai tasa ki kone da mai. Cillo mata kashi ta gwaigwaya. Hanne ta dauko wani guntun
qashi ta jefawa Ramlah. Qashin bai zame ko ina ba sai bakin rijiya Ramlah ta bishi da dan
gudunta. Tana zuwa bakin rijiyar takalminta daya ya zame daga kafarta santsi ya kwasheta sai
cikin rij[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:03 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰9

Sai da cikin Munari yayi wata shida Uwale da sabuwa suka san dashi. Gaba daya Sabuwa
hankalinta a tashe yake tana tsoron kada Munari ta sake haihuwa hankalin Mal Yakubu ya
koma kan abinda ta haifa. Yanzu ma kamar yasan Hanan ba yarsa bace baya bi ta kan ta sai
Inna Uwale ta dame shi. Ita kuwa kullum tana rike da ita a tsakar gida ko dakinta tana mata
waka. Hannan farar jikar Uwale. Zaki auri mai kudi mai mota,zaki kaini makka da madina.

Duk wahalar da Munari ke sha saboda cikinta yakai watan haihuwa Uwale bata daga mata kafa
akan girki ba irin yadda aka yiwa Sabuwa gata. Ganin aka Mal Yakubu ya siyo risho har biyu
yasa a kitchen din. Uwale bata san dashi ba sai da ta fito da goyon Hanan tana ta cangala yar
kafarta. Eyye me zan gani haka? Fito fiti kinibabbe ta kirawo Mal Yakubu daga daki. Wato don
munafurci shine zaka wani siyo risho saboda matarka ta dena wahala ko? To ban yarda ba. Ni
nafi son abincin da aka dafa da itace. Yafi dadi da inganci. Sabuwa tace a'a fa inna waye baya
son sauki ni gaskiya nafi son rishon. To...to ai shikenan saboda kada fatarki tayi duhu a bakin
murhu ba. Ta harari Munari kunyi sa'a uwar mai kyau tana son rishon ba don haka ba da kunga
tsiya wallahi. Kamar kullum shi dai Mal Yakubu sai aikin bada hakuri.

Tun dare Munari ke fama da ciwon baya kadan kadan tana daurewa. Zuwa asuba abin ya
ta'azzara gashi ba girkinta bane. Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar dakinta. Dakin Inna uwale
ta nufa tana tafiya da kyar. Tana ta kwankwasawa Uwale na jin muryarta ta sake gyara
kwanciya....aikin banza haihuwa ta hudu ai zaki iya da kanki. Haka ta koma kofar dakin
Sabuwa tana bugu. Mal Yakubu ne ya fito ya kamata zuwa dakinta yace Sabuwa ta tashi Inna
su kula da ita sannan ya fita zuwa gidan makocinsa mai akori kura ya taimaka masa su tafi
asibiti. Yana dawowa daga bakin kofa ya jiyo kukan jariri. Da gudu ya karasa ya ganta kwance
kan tabarma ita kadai da baby a gabanta. Duk ya rude yace bari na kira Inna...hannu ta daga
masa barshi kawai Malam ga reza can dauko ka yanke cibiyar.

Su kadai suka yi abinsu su Inna ko leqe. Ya fita ya bawa makocinsa hakuri ya dawo ya buga
kofar daki cikin fushi. sabuwa ki fito kafin na shigo dakin nan don wallahi na shigo jikinki zaiyi
tsami. Ta fito tana mika...yanzu don wulakanci ince ki tashi inna ku taimakawa Maimunatu sai ku
barta ita kadai? Inna ta fito dan nan ni kake cewa munyi maka wulakanci? To mungode Baba
sai ka fadi me kake so muyi yanzu. Inna ni ba haka nake nufi ba amma ai ko sannu ayi mata.
Sannu maigida to me aka samu? Mace ce ya fada ya kasa boye murnarsa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:05 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰8

Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko cirko an
rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru. Uwale tace ni dai ba ruwana ,fa bani bace.
Munari tace wai meye ne? Me kuke leqe a rijiyar? Wata makociyarsu ce tayi karfin halin fada
mata...Ramlah ce ta fada.
Wata kururuwa Munari tayi cikin zafin nama ta nufi rijiyar ana rirriketa. Tani tace cikin rudewa
garin yaya ta fada? Wata yar cin shinkafar sunan tace qashi ne Hanne ta jefa mata bakin rijiya
shine ta bishi ta fada. Mal Yakubu aka fita kira a majalisarsu. Munari tun tana kuka da sauti har
muryarta ta dashe....wayyo Allah kawai take cewa. Abin tausayi ta zama.
Mal Yakubu ya shigo yana tambayar me ya faru ake nemansa. Munari ta mike ta rije wuyan
rigarsa. Baban Ramlah idan na rasa 'yata bazan zauna a gidan nan ba. Yi hakuri ki fada min
abinda ya faru. Wani yaro yana cin nama yace 'yarta ce ta fada rijiya. Mal Yakubu yace
Ramlah? Babbar riga ya tube zai shiga shima aka rike shi. Uwale ta soma kuka don Allah dan
nan kada ka shiga kaima ka mutu. Suna haka Sabi mai hakar rijiya ya shigo da wasu maza.
Igiya mai kauri aka daura masa ya shiga. Duk sakan a wurin su Munari tamkar shekara suke
jinsa. Kamar wata zautacciya haka ta koma. Sai bayan kusan minyi goma ya fara jan igiyar.
Cikin sauri aka jawo shi da Ramlah a kafadarsa. Mal Yakubu ya karbe ta ya kwantar akan
tabarka. Cikinta ya danna ruwa y rinka fita ta bakinta da hanci. Munari ko wurin bata je ba tana
zaune inda wasu mata suka riketa ta share hawaye Allah Ya jikanki Ramlah kawai take fada.

Duk yayi iya yinsa ya tabbatar yarsa ta rasu. Cikin kuka ya bude hannun da yaga ta damke
sosai. Qashin data dauka ne ashe ba rabonta bane. Wace 'yar....din ce ta jefa kashin bakin
rijiya? Jin kowa yayi tsit ya sake kunduma zagi cikin tsawa. Aka samu wata ta nuna Hanne.
Kanta yayi kamar zaki cikin fushi wani abokinsa ya rike shi. A tsorace tace Uwale ce tace min
mayya ce na jefa mata qashi shine tautsayi yasa na jefa bakin rijiya. Suna wannan fadan
Munari ta dauke gawar yarta ta kai daki ta fara shirin yi mata sutura. Taron suna ya koma na
mutuwa ita dai Uwale tayi tsit don yau dan nata ya bata tsoro. Yana matukar son Ramlah sosai.
Bayan an tafi kaita ne Munari tana zaune gaban iyayenta da suka zo ta fara jan numfashi da
kyar. Mal Yakubu aka kira ya zo ya fitar da ita a rude. Ya kalli innarsa cikin bacin rai. Idan itama
ta mutu yau zan saki Sabuwa kuma ta tafi da yarta bana so. Asibiti suka nufa inda likita ya
tabbatar jininta yayi mugun hawa kuma tana dauke da ciki na wata daya. Duk da bakin cikin
dake damunsa Mal Yakubu yayi matukar murna. Ta taga yake leken matarsa saboda ance a
barta ta huta sosai. Yana adduar ta sami lafiya.

Bayan kwana takwas da rasuwar Ramlah Inna Ladi tazo gidan da sauran yaransu mata hada
kayan Munari. Mal Yakubu yana ta bada hakuri yana zubar da hawaye. Inna Ladi tace kaga ka
bari mu tafi ta laluma kafin yayanta ya zo kaima tunda baka ganshi ba kasan baya gari ne. Kiyi
hakuri inna ya zan saki Maimuna a wannan lokacin ga rashin 'ya ga kuma rabo a tare da ita.
Inna Ladi ta kalle ta Munari da gaske ne? Kanta ta sunkuyar kasa sai hawaye. Yi shiru kinji
kada ciwonki ya tashi. Ta dubi Uwale dake zaune tana yiwa Hannan rawa Sabuwa tana bacci a
daki. Yakubu kasan kashe min jika akayi da gangan muka hakura yanzu haka zata zauna cikin

bakin cikin rayuwa a gidanka? Kiyi hakuri inna babu fa wani yanayi mai dorewa. Zan kula da ita
muddin raina bazan bari wani ya wulakanta ta ba,yana magana yana kallon Inna Uwale. Ta
dago kai nasan dani kake dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login