Showing 30001 words to 30638 words out of 30638 words

Chapter 11 - ZAMAN! PERIOD BOOK BY OUM HAIRAN .pdf

01 Jul 2025

3441

sauke
numfashi.

Dagota yayi ya saqalota da Hannunsa mara lfy ya dora habarsa saman kanta yaja fasali yace
“inasonki Harmdan" rungumeshi ya qarayi tana sauke ajiyar zuciya suka shiga dakin nata itadai
Rukky tafiya tayi saboda ta lura qawar tata tayi nisa sun jima suna kallon juna kafin yayi Mata
murmushi yace “mom tanaso tayi taron biki Amma na hanata yanzu haka da ita muke suna tare
da Mal na Allah a soron baqi tace yau a gidanki zaki kwana"



Zaro ido tayi shima ya zaro sukayi dariya a tare yace “nasha wahala Amma na dace masoyin
gsky shine bakajin komai don ka sadaukar da komai akansa" sunkuyar da kanta tayi ya sakeyin
murmushi yana Shirin yin mgn Suka shigo da sauri Harmdan tayi qasa da kanta sukayi dariya
tare Mom ta kamo hannunta tace “dole kyaji kunyata Mana kin sacemin da shekaru kusan biyu
Koda yake ya riga ya wucce yanzu sabuwar rayuwa zamu tunkara sai a yawaita Istigfari




Kuka ta saka ta shige jikin Mom Mom ta rinqa lallashinta hardai tayi shiru suka miqe suka tafi ko
a gdansu Safwan bangare guda aka ware Mata ita da mijinta saboda Mal na Allah yace kada a
nisantata da mutane Junnul ashiq nacine dasu idan aka kebanceta zai it's dawowa ya gallebesu
haka kuwa akayi ko da sukaje Mom Hana akaita bangarenta tayi Saida tayi sati biyu a
bangarenta tana gyarasu su uku Kubra da Bushira sai Hamdan gyara mara algus Safwan kuwa
yana jinyar hanunsa cikin sati biyun yaji sauqi sosai idan yaga dugu dugu saiya zagayo gurin
matar tasa Amma Babu fuska dole haka yake hqr ranar juma'a aka fara bikin Rukky itace
babbar qawarta bikin Yaya uku Alh Barau yakeyi Bushira Kubrah da Safwan komai iri daya yayi
mawa Harmdan da yayansa Kuma ya hada Mata lefe kamar yanda aka kawowa yayansa ranar
kamu da yamma saiga dangin mahaifinta daga gana har yanzu ba musulmi bane Amma sun
waye sosai suka qullo kudade masu kauri suka bawa Mom akan ayi Mata kayan daki
musamman qanwar mahaifinta Mom taso taqi karba Amma suka dage haka ta karba tabasu
masauki akayi biki dasu ranar lahadi akakai amare gidajensu kowacce aka barota da halinta
wannan dare anyi kwanan soyayya Safwan ba daga qafa kwana biyu baqi suka gama watsewa
gidan ya rage daga mom sai Harmdan Mom tana ganin wani salo na rashin kunya gurin
Safwan, wata biyu da tariyar ta fara rashin lfy gwajin farko aka gano cikine wayyoh murna gurin
Safwan da iyayensa har Dad a zuwa dubata.




Watanni sukayita tafiya tana rainon cikinta lkcn haihuwa ta sullubo yaranta biyu duka mata
akasha suna yara sukaci sunansu Fadima da Zainab watansu hudu ta fara fuskantar yanayi
kafin ta ankara anyi Mata barna suna zuwa asibiti akace sabon cikine wata daya ta nuna bataso
Mom ta rinqayi Mata nasiha harda ta hqr hakanan shima ta haifeshi namiji Mukhtar shima
shekararsa days tayi masa qani a shekara uku dai sukayi yara hudu Allah kenan me kyauta da

qari wahalar da tasha a haihuwar Mahmood ne yasa Mom nema Mata tazarar gargajiya sukaci
gaba da rayuwarsu da yaransu hudu gwanin sha'awa,
Rukky kuwa itama Allah ya tarfawa garinta nono abokin Safwan Jabir shine ya aureta Suma
suna zamansu lfy cikin so da qaunar juna soyayya me qarfi tana gudana tsakanin masoyan inda
rayuwa taketa albarka komai ya wucce kamar komai Bai faruba.



_Alhmdllh Nan na kawo qarshen wannan lbr daya wahalar dani 🤕 dafatan zakuyimin afuwa na
jina Shiru da kuka rinqayi insha Allah bazan sake daukan lbrn da zai bani Kashi haka ba🤣_
_Sai Allah ya hadamu a *_BATURE_* _idan naga dama Kuma na kirashi da *_AURENA
DASHI_* *_(Ahlil kitab)_*



_Ke muku fatan alkhairi_



*_Ummuh Hairan_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login