Showing 21001 words to 24000 words out of 30638 words
juna batare da
wani yace da wani qala ba,
Shikuwa Yarimah Hamdan zuba Mata ido yayi cike da tausayawa zuwa yanzun tausayi take
basa gashi tafiya ta sameshi ta gaggawa dole zai tafi yabarta anan kafin ya dawo, da wannan
tunanin ya kwanta a kusa da ita ya gyarata bacci ya daukesu washegari ya rigata tashi yayi
sallah sannan ya tasheta itama tayi ya matso gabanta ya tsugunna yace “zanje India mahaifina
yanason ganina cikin gaggawa nasan Kiran akanki ne ki kula da kanki Harmdan Amana
nabarmiki kanki babana ya kasance sarkine a yanki Dhafur kuma bil'adam ne kamarke Kuma
abokine wa kakanki kada kiyi yunqurin guduwa zakisha wahala still akwai cikina a jikinki ki
kulamin da kanki idan wani Abu ya faru wlh zan gigita duniyarki"
Tunda ya fara mgnr har ya gama batace masa kanzil ba ya sunkuyo yass harshensa ya lashi
hawayenta yace “kuka Kuma meye na kukan nine fah ba wani ba ki daina banaso Ina rayuwa
daidai dakene Harmdan ki kulamin da kanki da babynmu" yana fadin haka ya dafa cikinta kawai
saita nemeshi ta rasa ta firgita ainun don har miqewa tayi kafin ta saita nutsuwarta ta miqe ta
canza kayanta ta fito parlourn ta zauna tare da buga uban tagumi.
Ji tayi an janye hannunta ta dago da sauri ganin Safwan ne yasata saurin fadawa jikinsa ta
rushe da kuka tana shafa bayansa tace “baiyi maka komai ba Safwan ka gudu don Allah ka
gudu ya tafi bayanan..." Rufe Mata baki yayi yana girgiza Kai yace “meye amfanin guduwata
bayan ke bakida ikon guduwa Harmdan ni kaina ya gama kullewa na kasa gane komai game da
alaqarku da wannan bawan Allan iyakar sanina babu yanda zaayi Tarayyar nan ta yuwu
tsakanin mutum da aljan Harmdan kiyiwa Allah ki fitar dani zullumi zuciyata tana cikin
mawuyacin hali fah"
Sake shigewa tayi jikinsa tanaci gaba da kukanta tana shafa kansa tace “bansan komai ba sai
abinda nake yawan gani a mafarkina sai Kuma abinda mariqiyata ta sanar dani kafin rasuwarta
Safwan rayuwata tana cikin garari wlh anan din matsera na samu Kuma nan da sauqin rayuwa
fiye da hannun dana fito da Kuma wanda zan iya fadawa idan nabarshi safwan akwai rudani
cikin rayuwata akwai matsaloli da asalinsu bani na haifarwa da kaina suba bansan ta Ina suka
samu har suke bibiyata ba...."
Kukan da yakecinta ne yasata katse bayanin nata inda shikuma ya dagata cak ya nufi dakinta
da ita ya kwantar da ita yana qoqarin kwanciya kusa da ita tayi saurin miqewa tare da cewa
“kada ka fara Safwan nayi gurbatar da idan ka sake wani abu ya shiga tsakanina dakai zaka iya
rasa rayuwarka Ni ba mutum bace kamar yanda kake tunani...." Wata zabura Safwan yayi yayi baya da sauri ta sake fashewa da kuka tace “nasan haka zata
faru shiyasa duk Wanda ya tambayeni wani abu game dani nake qin sanar dashi ya zanyi haka
son zuciya ya zabamin Safwan tabbas babu qaddara a cikin kuncin rayuwata duk da nakasance
musulma Amma ban yarda da qaddara ba a wannan bigiren inada burin daukar fansa akan duk
Wanda yayi sanadin jefa rayuwata cikin hatsarin nan banida da power da qarfi kamar na sauran
wadanda suka kasance cakude irina Kuma ni basu barni a jinsi daya kamarka ba meye yasa
iyayena suka haifeni suka wofintar dani da rayuwata?"
A dan tsorace ya matsa gabanta ya sanya hannu ya dagota tare da daukar tissue ya fara share
Mata hawayenta yace “kibar kukan nan haka kiyimin bayani Harmdan nayi Miki alqawarin zan
kasance tare dake a kowanne yanayi dadi ko akasin haka"
Sake shigewa tayi jikinsa tace “kada kayi alqawarin da bazaka iya cikawa ba Safwan dole ka
barni saboda kasancewarka dani kamar qirge cikin wa'adin kwanakinka" kallonta yayi ta dago
itama ta kalleshi tare da miqewa tace.
“Shekaru 50 da suka wucce anyi wani ZAMAN! da qila baizo muku nan ba ya tsaya ne a yankin
Africa ta kudu zuwa Ghana da Burkinafaso abubuwa sun lalace sunyi tsananin da jama'ar
wannan yankuna suka shiga halin ni ƴasu da ƙaƙanikayi ba komaine ya janyo musu shiga
wannan ƙangi ba sai son duniya da son tar dukiya wanda hakan yajasu ga faɗawa tarkon
tsaface tsaface da sihirce sihirce.
Idan ana maganar tsafi da sihiri to duniyar shaiɗanun aljanu tana gaba gaba wajen ƙulluwar
komai da jefa duniyar bil'adam cikin garari, tabbas hakance ta faru da yankin su mahaifina
wanda suka kasance masu ɗabi'ar bautar tsafi wani ƙaramin yanki ne a ƙasar Ghana da ake
kira FUTHAR mahaifina wands ya kasance ɗane a gurin sarkin wannan alƙarya ta Futhar me
suna Haisam ya kasance mutum me tsananin son mulki da dukiya hakan tasa yayi nisa sosai
wajen wannan muguwar É—abi'a tasu ta tsafi inda bayajin komai don ya kashe mutum akan biyan
buƙatarsa.
Hakance tayi masa jagora ya zama gagara badau uban matsafa wanda ba yankin Futhar ba
hatta masarautar dake jagorancin ƙasarsu baki daya tana tsoronshi tana shakkar shiga
sharafinsa inda dangantaka tsakaninsa da mahaifinsa tayi tsami domin kullum kujerar tsohonsa
yake hari shikuma ya kasance shine É—a na biyar a wannan masarauta bayan haka ma shi ba
É—an mata bane É—an baiwane.......
*Ummuh Hairan*
[12/25/2020, 6:44 PM] Real Oum Hairan: *_ZAMAN!_*
*Period*
*_09013718241_*
*Ummuh Hairan*
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
*27-28*
Hakanne tabawa mahaifina dama ya fantsama neman sa'ar tsafi babu dare babu Rana a
burinsa na saiya mulki wannan gari nasu, kullum lkc qure masa yake Kuma kullum qara buri
yake.
Wata Rana da ta kasance ranar sa'arsa Kuma ranar rashin sa'arsa yana kwance a dakinsa
yanata saqawa da warwarewa kawai sai yaji dirar Abu kamar faduwar dutse a bisansa ya
tsorata ainun Amma dake namijin gaskene sai ya dake yaci gaba da bin inda Motsin yake da
kallo har zuwa wani lkc da wani duhu ya mamaye dakin baqin duhu na gaban a kwatanta
Wanda ya haddasawa Yarimah Haisam laluben makunne fitilar aci balbal din dakin kafin ya ida
Kai hannunsa sai yaga dakin yayi haske ya sauke ajiyar zuciya yana Mai duban abinda yake
qoqarin kawo mass wargi cikin daularsa mamaki ne ya cikashi ganin wani gajeran aljani baqin
qirin ya gurfana gabansa.
Rusunawa yayi cikin alamun girmamawa yace “tuba nake yakai wannan gagarerren bani adama
haqiqa Kira ya isheni daga shugaba Hundar inda ya umarceni da nayi gaggawa wajen zuwa na
daukoka daga wannan duniya na kawoka duniyarmu ta shaidanun aljanu inda anan ne zaka
samu cikar burinka na zama sarkin wannan hatsabibiyar masarauta ta Futhar" Jin wannan kyakkyawan albishir yasa mahaifina baiyi wata wata ba a wannan yammaci yabi
aljani Iya'ul sunyi tafiya me tsayi cikin duhun dare Wai a hakama don an daure musu tsayin
dajin ne sannan suka isa wata babbar daula dake kusa da qasar China inda aka shigar da
mahaifina ya gurfana gaban shugaban hatsabiban matsafan duniya wato Hundar, Koda ganin
Haisam sai Hundar ya kece da dariya ya miqe yana tafa hannu yana cewa.
Barkaaa barkaaa barka da zuwa yakai wannan zaqaqurin dan sarki tabbas haqa yana gaf da
cimma ruwa matuqar kayi biyayya ga umarnin mu ta Kaine zaka zauna a wannan tsafatacciyar
karaga ta masarautarku wacce kowa yake haqonta kayi sani a yanda akayi yarjejeniya da
dodon tsafin masarautarku shine Kai bazakayi sarauta ba saboda kaidin ba dan Mata bane dan
baiwa ne ba iyakai kadai ba a cikin yayan matan ma guda daya aka ware akeso yayi sarautar
matuqar bashi ba babu me zama a wannan kujerar ya tashi da ransa saboda haka ka tsaya kaji
sharadi na Kuma dolene kabi idan ba haka ba ni me iya sheqeka ne burinka bai cikaba biyu
babuuu" hhhhhhh ya sake kwashewa da dariya.
Sosai Haisam ya shiga rudani tare da zama domin a karanta masa hanyar cikar burinsa bayan
aljani Hundar ya gama qare masa kallo yace “matakin farko na cikar burinka shine kashe
Yarimah Yazeed wanda babanku yake burin ya zama sarki idan ka kasheshi ka taromin jininsa
ka kawomin zan hada maka siddabarun da zai karya tsafin karagar mulkinku, Abu na biyu shine
zan hadaka da yammatan aljanu guda uku kowacce inaso kayi Mata ciki ta haihu biyu zasu haifi
maza daya Kuma zata dauki cikin amma bazaizo darai ba to wannan da baizo da ran ba shi
muke buqata zaayi maka dabgensa ka cinye sukuma sauran biyun nan zaa yankasu ka shanye
jininsu idan kayi haka kazama sarki ka gama, Amma fah kasani akwai wata caca bayan tiya
wannan aljanun biyu ni da kaina zan kashesu dayar data haifi danta babu rai zaka aureta zaku
zauna zaman Mata da miji bayan dogon lkc zata qara samun ciki to kasani idan ta tashi
haihuwa zata haifi Æ´a mace to wannan Æ´ar itace tukuicina zaka fansarmin da ita tun tana ciki
bayan haihuwarta zan raineta har zuwa lkcn da zata zama cikakkiyar budurwa inda nima zan
cika nawa burin da bazan faÉ—eshi duniya taji ba"
Shiru ce ta ratsa na wani dogon lkc kafin Yarimah Haisam ya dago yace “kashe Yarimah
Yazeed yafi shaqar numfashi sauqi a gurina Amma sharadi na biyu shine abin jinjinawa ya zanyi
nayi tarayya da Matan aljanu bayan na kasance bani adamu?"
Dariya Aljani Hundar ya sheqe da ita yace “wannan yafi kashe Yarimah Yazeed sauqi ni a
gurina ka tafi a daren nan kaje ka aiwatar da abinda nace maka idan ka aiwatar ka jira na dan
lkc kamar sa'a biyu ni da kaina zansa a kawo maka kyawawan yammatan biyu bazasu baka
matsala ba saboda su dama yan hanune mun horasu saboda irin wannan lkcn dayar itace zata
baka matsala yar wani babban sarkin aljanu ce ta Misra me suna Nabeel itakuma sunanta
Najeesha dole ka kwantar dakai ka siyi zuciyarta domin itan ta kasance hatsabibiyar gaske
kamar mahaifinta koma fiye shigar da soyayyarka gareta shine zaisa ta sallama maka komai
idan kayi amfani da qarfi zata iya kasheka ma ita batada asara bayan ta haifi wannan yarinyar
itama munada buqatar jininta hakan zaisa ka samu daukaka ka zama Kaine me mulkin babbar
masarautar qasarku qin cika wannan sharadin ko sakacin qin yuwuwar daya daidai yake daka
fanshesu da naka jinin.
Jinjina Kai yayi yace “wannan duk me sauqine Amma...." Katseshi aljani Hundar yayi yace
“tambayarka kada tayi yawa kaje ka fara gwada sa'arka fatan nasara" ana fadimai haka aka
daukeshi cak aka fice dashi daga wannan guri cikin qanqanin lkc sai gashi a garin Futhar ya
fara rarraba idanu dayake akwai duhun dare farkon watane saiya sulale ya shige halwarsa ta
tsafi yaje ya tsuma kansa ya keta qasa ya billa turakar Yarimah Yazeed yana kwance da wata
baiwarsa ya fakaiceshi dake yayi nisa a wata duniya ya luma Masa wani lauje ya tureshi daga
jikin baiwar ya fadi qasa rigis tana Shirin yin ihu yayi samanta shima yaci gaba da cinta bayan
ya gama ya yanke Mata maqogwaro ya zauna har rana ta fito sannan ya Kuma keta qarqashin
qasa ya nufi dakinsa.
Baijima da shigaba yaji fada ta kaure da ihun mutuwar me jiran gado yayi mursisi dashi bai
fitaba bai tanka ba can yaji sama na girgiza kawai saiga bullar wasu kyawawan Mata guda uku
mafi kyauwun cikinsu itace qarshen shigowa dukka biyun murmushi sukeyi Amma ita hawaye
takeyi balarabiyar asali
Numfashi ya sauke ya miqe da sauri ya nufeta taja da baya da sauri ya tsaya tare da narkar
dakai yace “ina tausayin mace a irin wannan yanayin na fansheki ne saboda sanin cewa idan
na barki kasheki zaayi Kuma ke kadai mahaifinki ya Haifa yanada buqatarki"
Kallonsa takeyi da yanayi na rashin yarda ya matsa ya riqe hannunta yace “kiyi rayuwa me
aminci nabar Miki wancan dakin ke kadai bana buqatar ganinki cikin damuwa" haka Yarimah
Haisam ya rinqa amfani da hikima da dabara hardai yayi nasarar shawokan Aljana Najeesha
ranar da aljani Hundar ya umarceshi da kusantarsu maganin bacci yabata ya fara amfani da ita
sannan sauran tun daga wannan Basu farka ba tsayin watanni tara babu wanda yasan da
zamansu a gidan sarautar har zuwa ranar da naquda ta kamasu a cikin wannan sihirtacce
bacci.
Zuwa akayi daga fadar aljani Hundar aka debesu kowaccensu ta haihu Najeesha nata baizo
darai ba aka daukeshi aka sanyashi amurhu ka fara dabgensa wadands sukazo darai Kuma
aka soke musu maqoshi dukka aka tsiyaye jininsu aka cillawa wasu halittu suka cinyesu bayan
an gama dafge aka bawa Yarimah Haisam ya cinye ya kora da jinin yayansa, sauran yammatan
Kuma aka daukesh akabar dasu nahiyar ya rage saura Najeesha ita kadai nanfa aka shiga da
ita halwar tsafe suka tsafaceta tsaf bayan an fito da ita ta maqalewa Haisam duk uban yamutsa
gashin bakin da akeyi da dakarun nahaifinta tace itafa taji ta gani saboda tsananin son da
mahaifinta yakeyi Mata haka ransa baiso ya daura Mata aure da Haisam suka koma garin
Futhar inda a daren ya aika mahaifinsa Sarki Naumal lahira ya dane kan karagar mulki babu
wanda ya iya cewa dashi qala.
*_Ummuh Hairan_*
[12/26/2020, 4:58 PM] Real Oum Hairan: https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
*_ZAMAN_*
*_Period_*
*_09013718241_*
*_Ummuh Hairan_*
_Wannan book na kudine please ki biya before ki karanta 200 VIP 500 ta account dinnan_
í ½í±‡í ¼í¿»
_Fauziyya Tasi'u Umar_
_0255526235_
_GTBank_
_Ko katin waya MTN ta_ _WhatsApp number_
_09013718241_
_Ko VTU ta wannan number 09031307566_
_Daga wannan page din don Allah kada ki qara karantamin baki biya ba_
*_29-30_*
Haka Sarki Haisam ya rinqa gabatar da mulkinsa cikin tsananin zalumci da rashin tausayin
talakawansa sosai mutane suke karbar gashi wai a hakama don yana tsananin taoron matarsa
Najeesha wadda take qoqarin takawa zalumcinsa burki to yariga ya tsafaceta sai yanda yayi da
ita ya cire Mata tunanin kowa da komai sai nashi duk wani hatta addininta na asali na Muslumci
saida ya fitar da ita daga cikinsa ya dorata akan addinin tsafi.
A wannan yanayine shekaru sukayita turawa wayewa na zuwa inda mutanen garin Futhar suka
fara qoqarin yin bore daga wannan azzalumar masarauta tasu suka fara baro garin inda a cikin
shekara ta ashirin da bakwai da juyin juya halin mulkin nan na mahaifina Sarki Haisam ne Allah
ya azurta mahaifiyata aljana Najeesha da samun cikina lamarin da yayiwa Sarki Haisam dadi
saboda aljani Hundar ya matsa masa kan saiya fansar masa da mahaifiyata tunda taqi sake
haihuwa.
A daren da suka fahimci da samuwar cikina suna tsaka da murna mahaifina ya tafi yayiwa
ubangidansa albishir nan suka shiga halwar tsafi suka buga suka kwashe aljani Hundar yayi
wani ihu yace “ya akayi ka bari ka rigata kawowa ka batamin shirina jinin bani adam yafi qarfi a
jikin jaririyar da zaa Haifa bazata biyamin buqatata ba meyesa ka saba alqawarin da mukayi
tsayin shekaru?
Sunkai ruwa rana kafin su fahimci juna a hakan sukayi alqawarin idan Najeesha ta haihu zaa
bada jaririyar sannan itama jininta zai zama fansa na rashin cika alqawarin mijinta, tun daga
wannan rana mahaifina da mahaifiyata suka fara yar tsama tsakaninsu watannin cikina biyar
mahaifiyar Yarimah Hamdan ta kaiwa aljani Hundar ziyara a lkcn Hamdan ne ya rakota tunda
sukazo ya qurawa kwalbar surata ido da aljani Hundar ya ajiye a fadarsa sama da shekara
talatin budar bakinsa sai yace wannan ta kasance jinin Najeesha ya ga Sarki yas'ul wacce ka
sace ta ka kashe qanin mahaifiyata domin cikar wani boyayyen burinka, tabbas zan tarwatsa
ikonka matuqar baka fansarmin da itaba domin na dade Ina mafarkinta tun samuwar cikinta a
jikin mahaifiyarta"
Sosai akayi dan qaramin yaqi kafin Yarimah Hamdan yayi nasarar karbar wannan kwalba ta
qarfin tsiya yaje ya jefata a cikin tekun fasha wannan dalilin yasa na zama mallakinsa
kasancewar haka tsarin tsafi ya nuna duk wanda yayi nasarar batar da kwalbar nan to shine zai
zama mamallakina lkcn da Najeesha ta haifeni tana kwance babana ya saceni yaje yakaini ga
Aljani Hundar inda shikuma takaici yasashi kashe mahaifina qiri² yaga samu yaga rashi yana
kasheshi ya daukeni yaje ya jefar dani wa wata mararrabar hanya to anan ne Yarimah Hamdan
yazo ya daukeni ya kaini gurin wata tsohuwa mai suna Nana ta tsinceni ta rinqa rainona inda
kakana Sarki yas'ul ya turo aka dauke mahaifiyata daga masarautar mu suka baza komar
nemana Amma Yarimah Hamdan ya boyeni inanan a gurinta kasancewar da suffar bil'adam
Yarimah Hamdan yake zuwa wa tsohuwar nan yace Mata nidin yarsace da ya Haifa bata hanyar
aure ba zai bata ko nawane ta kula masa dani.
Nana musulma ce shima Yarimah Hamdan musulmi ne shiyasa na tashi matsayin musulma
Amma a sangarce na tashi da farko yana zuwa ya daukeni a zummar zai yomin siyayya
yakanzo da manyan motoci yayita zaga gari dani, lkcn dana fara dagawa ne ya fara canza
mu'amalarsa dani sai ya daukeni ya tafi dani wani gdansa dake bayan garinmu yayita wasa da
sassan jikina tun inaqi hardai na sake Masa komai.
Shine ya sabarmin da komai Wai Ashe bansani ba tun ranar daya kawowa Tsohuwa Nana ni a
ranar aka aura masa ni bisa jagorancin mahaifiyarsa da batason bacin ransa shima kamarni
haka yake babarsa aljana babansa mutum Amma shi jinin jinnu yafi qarfi a jikinsa da kashi 80%
sabanin ni da nake da 20% na jinnu a jikina, inada 14 years na gama secondary saboda inada
girman jiki daya zarta qa'ida ta mutuntaka a lkcn ne Kuma na fara gane cewa akai wani abu
game da Yarimah Hamdan wanda ya fara zuwarmin a matsayinsa na jinnu Ina zaune ni kadai
kawai sai ingansa a kusa dani in kwanta a daki najishi a samana yana sarrafa