Showing 6001 words to 9000 words out of 41364 words
'Dan Yayan Ammi ya girmeni sosai , sai Mai bimasa shima yad'an girmeni sai kuma
K'anwarsu wacce zamuyi sa'anni da ita , Sunan Babban Usman suke ce masa Zunnur , saboda
sunan Baban su Ammi ne , me binsa kuwa sunan sa Haidar , sai k'aramar su Afra , Maman su
tana da kirki sosai , tasaki jiki da Ammi sai hira suke tamkar daman sun san juna , nima nida
Afrah tuni muka saba dan kusan kanmu d'aya da ita , Zunnur bashi da yawan Magana
kaganinsa kaga miskili , shikuwa Haidar yana da sakin fuska sosai , kwanan su Biyu sukace
zasu tafi saboda sch . Ammi tayi tayi suk'ara kwana Amman yace tabari in sunsamu hutu
zaikawo su suyi anan , Yayan Ammi yayi mata fad'an tayi Aure zaman haka babu dad'i ,
kokuma takoma gabansa can lagos d'in ta zauna , Ammi tace zatayi Shawara akan hakan duk
abinda ta yanke zata gaya masa , lokacin da zasu tafi sosai nasha Kuka sai nabisu nima , Afrah
itama kukan take tana rok'on Ataimaka ataho dani , da k'yar Maman su ta lallab'amu akan zasu
dawo nan badadad'ewa ba , Yayan Ammi yabata dubu talatin yace tak'ara ajarin nata , sannan
yabawa Kawu Idi dubu goma , sai kuma yabawa Safara 'u dubu biyar , sunyi godiya Kawu Idi
yabasu tsarabar kayan Gwari , lokacin da muka rakosu waje Na kalli Zunnur nace " Ya Zunnur
sai wata rana tunda kai murna kake zaku tafi , daman tunda kuka zo kake jin Haushi to yau
saika saki ranka , kowa a wajen sai dayayi dariya , shikuma murmushi yayi bai ce komai ba har
suka tafi....
Bayan wasu shekaru.
Lokacin Na zama 'Yan mata ina Ss 2 a secondry sch , duk wata hailtta ta jikina ta bayyana ,
nakasan ce Doguwa Fara me d'auke da doguwar fuska , ina da Hanci har baka ga bakina
k'arami dashi , idanuwana dara dara dasu cikinsu fari fat sai k'wayar idon bak'a k'irin , ina da
siririyar wushirya a tsakiyar hak'ora na , sannan ina da Dimple a gefen kumatuna , Bani da jiki
amman kuma ina da k'ugu sosai , Banda cikar K'irji dai dai suke abina , tunda nazama Budurwa
Samari suka fara kawomin hari , kuma har lokacin Ammi na tana suyar k'osai a k'ofar gida ,
Tunda lokacin Kawu Idi yasakoni gaba saboda madu zuwa ta wajen sa, Wata ranar Friday na
dawo daga Sch ina tafiya naji ana min magana , dak'yar na tsaya saboda cikamin idanuwan da
yayi mutumin , mungai sa yace min dan Allah inbashi kwatancen gidan mu , yanaso yazo dan
tsayuwa a hanya ba mutunci bane , Nan na daure nagaya masa kwatancen gidan mu , ya
fad'amin sunan sa Kamal nan muka rabu akan zaizo gida.....
Bayan kwana biyu ina zaune nida Ammi muna hirar tafiyar mu Lagos da zamuyi inna samu
hutu , kawai sai ga yaro yashigo wai ana sallama da Hanan a waje , Nan nacewa yaron yace
Bananan , Ammi tace ace ina nan , turo baki nayi ina fad'in "Nifah Ammi bazanje ko inah ba ,
kallo na tayi sannan tace " yanzu Hanan inbaki fita ba taya zaki samu mijim da zakiyi aure ?
kinsan dai nafad'a miki cewa iya secondry sch zaki gama in aurar dake Hanan , yakamata kifara
kula samari ko zaki samu wanda zakuyi daidai , kalaman Ammi sun shigeni sosai dan haka na
mik'e nasaka hijan d'ina na fice , Nasan Ammi bata da k'arfin dazata biyamin kud'i nayi karatu
sosai , dan haka nima na amince da zancenta ......
Ina fitowa naga Kamal a tsaye , yana ganina yafara sakarmin Murmushi yana cewa "
Gimbiya sarauniya gaskiya nazama sarki acikin masoya tunda har aka fito wajena , murmushi
nayi sannan na gaidashi cike dajin kunya , Nan ya amsa yafara gabatarmin da kansa , Sosai
nasaki jiki da Kamal , kodan yana da Abin dariya ne oho , haka mukaita hira haryamin sallama
yatafi , tunda ganan Soyayya ta k'ullu tsakanin mu nidashi , har muka samu hutun Sch muka
tafi Lagos da Ammi .....
Zuwana Lagos shine yafara canzamin Rayuwata tafarko , Muna zuwa gidan Yayan Ammi ,
Sosai muka samu tarba ta musamman , karkuga murnar da Afrah tayi taganina , nima nayi
murna sosai da ganinta , tazama Babba sosai dan harta fini girman jiki , lokacin da mukaje su
Haidar da Zunnur suna Sch amman suna shirin dawowa gida , dukansu suna karatu a B.U.K a
can kano , dagani sai Afrah kullum sai munfita ganin gari , watara rana munje wani Shopping
mukayi karo da wani Saurayi , duk abinda muka siya saida ya biyamana kud'in , bayan munfito
ya biyomu ya gabayar mana da kansa sannan ya nuna yana sona , Afrah tabasa Addrees d'in
gidan su muka wuce muka tafi.....
Tunda ganan Muktar yafara zuwa guna , tun ina sharesa Afrah tasa ni gaba saida nafara
kulasa , Muktar irin samari nan wayayyu , wani lokacin in muna hira sai yanemi tab'amin jikina ,
sai da nanuna b'acin raina Sosai sannan muka dai daita , Ranar dasu Zunnur zadu dawo tun
safe muka gyara musu d'akinsu , sannan muka shiga kitchen muka fara shirya musu Abinci
lafiyayyau , kafin k'arfe biyu mun kammala komai , dayake a jirgi suka taho lokacin Abbansu
har yatafi tahowa dasu , wanka nashiga dana fito na shirya cikin wata doguwar riga da mukaje
Shopping Abbansu Afrah yasiyamin ita , nikaina nasan nayi mugun yin kyau Sosai , da haka
nafito palor ina k'walawa Afrah kira , hanyar k'ofa nataho zan bud'e shikuma dai dai lokacin zai
shigo , aikuwa mukayi karo dashi har wayar hannunsa ta fad'i muka sunkuya atare dan d'aukar
ta , Idanuwan mu ne suka had'u waje guda take kowannen mu zuciyar sa ta buga.......
*littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Layin*
07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* _Karkubari_ _Abaku_ _Labari_ _kusiya_
_kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ ν Ύν΅°ν Ύν΄ν ΌνΏ»
.
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ ν ΌνΌΉν ½νΈ
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Na*
_Zee_ _MD_ βν ΌνΏ»
*Hamdala* *Writer's* *Association* ν ½ν²ͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number*
07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *Kacal* *kukaranta*
_Cikin_ _Aminci_ ν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°
ν ΌνΆ page. 7
Ina zuwa naga Afrah sai hirarsu suke hankali kwance , ganina datayi a firgice yasa ta
zabura itama ta mik'e , cike da tsoro tace min " lafiya kuwa Hanan naganki hakan ? Muryata har
sark'ewa take nace mata " Ya Zunnur ne yazo , tuni Afrah ta firgice tana cewa Anas " Maza
kabar wajen nan wallahi inyazo yaganmu tare zai maka rashin mutunci , kafin Anas yayi wani
yunk'uri saijin shak'a yayi ta wuya , kafin kace me tuni yaji saukar Naushi , Kafin Anas yadawo
Daidai yakuma jin wani Naushin , nida Afrah duk ilahirin jikinmu Rawa yake , tuni munfara
Hawaye saboda tsoro , da k'yar mutane suka kwaci Anas a hannun Zunnur , yadda kasan wani
mayunwacin zaki haka jijiyoyin jikinsa suka tashi , kallon mu yayi kawai ya nufi wajen da yayi
parking d'in mota , sai abakin mutanen dasuka k'waci Anas naji suna cewa " wanda yafara
rik'ewa yana dukansa da k'yar yasamu ya turesa ya gudu Muktar kenan , jikin mu a sanyaye
muka nufi hanyar fita daga cikin Garden d'in , wani wawan burki da'aka ja a gabanmu take
muka had'e jikinmu waje d'aya muna karkarwa , bamu gama dawowa dai dai ba mukaji an
finciki Hannuwan mu an bud'e motar ansaka mu , muna bud'e ido mukayi ido biyu da Zunnur
tamkar mayun wacin zaki , shiga motar yayi ya figeta a miliyan yabar wajen......
Yanayin gudun da Zunnur yake yasa muka tsure kowacce cikin mu addu'ar cikawa da imani
take , bud'e gate kawai mukaji anyi sannan mukaji ya kashe motar , muna cikin Motar dukan
mu harshi daya had'a kai da sitiyarin d'in mota , sai da aka kwashi Minty 20 sannan ya juyo ya
dubemu yace " daman Abinda kukeyi kenan ? Yaushe kuka zama 'Yan matan dazaku ringa
had'uwa da Samari a wani wajen ? tunda naga yadda Afrahbke rawar kai akan tafiya aiken nan
nasan da abinda kuke k'ullawa , wato kunyi da samarin ku zaku had'u a wani wajen kenan ?
shuru mukayi inbada rawar jiki babu abinda jikinmu keyi , wata tsawa ya daka mana wanda
fitsarin danake rik'ewa tuni saiga shi nasakeshi , aikuwa Afrah tace " Dan Allah Ya Zunnur kayi
hak'uri wallahi bamu tab'ayin hakan ba sai yau , wani Mari ya d'auketa dashi har saida tayi wata
k'ara , yace " ai kece mara mutuncin dakika d'auketa kuja tafi , inaso insanar muku wallahi
wannan ne na k'arshe fita ma bazaku k'araba bare ku had'u da wasu 'Yan iska , kufice min
daga cikin Motar tun ban zaneku ba wallahi , ya dubi Afrah yace " Bani wayar hannunki ke
kuma ki tsaya ki wankemin motata saboda fitsarin dakikamin , wata kunya ce naji ta rufeni
tamkar na nutse a wajen , Afrah kuwa tana bashi wayar ta fice da tana Kuka , nikam kasa
motsawa nayi saboda Kunyar danakeji gashi jikina a jik'e yake da fitsari , Ruwa ya mik'omin a
robar Faro sannan ya bud'e motar ya fice , yana fita nasaki ajiyar zuciya sannan nasaka ruwa a
cikin jikina nafice daga cikin motar .....
Koda na shiga palor nayi sa'a babu kowa , dasauri na nufi d'akin Afrah na shiga , ina shiga
toilet na fad'a nafara wanka , Bayan nagama na fito d'aure da tawul na nufi wordrup na d'auki
wasu riga da siket na Atamfa nasaka , dawowa nayi na zauna kan Mudubi nafara shafa mai ,
ina cikin shafawa naji anturo k'ofar d'akin anshigo , ta cikin Madubi naga Zunnur tsaye ya goya
hannuwansa a k'irji sai kallona yake , tuni na mik'e tsaye ina juyawa dukana ina kallonsa nima ,
dan wani tsoronsa nakeji tamkar dodo yazamar min , ganin tsoronsa k'irik'iri a idonta yasa
yad'an saki fuska yace " kinyi wanka kenan to ita kuma motar tawa waye zai yimata wankan ?
k'asa nayi da kaina sannan nace " sallah zanyi yanzu inna idar zanzo na wanke mska ita ,
Murmushi yayi sannam yace " inajiranki karki k'i zuwa kuma kinji , kai na gyad'a masa tamkar
k'adangare ya juya yafice.....
Yana fita nabi Bayansa da Harara ina fad'in " mugu azzalimi kawai , wallahi bari naje nasamu
Ammi kawai tashirya gobe mukoma gida , dan bazan iya zama da wannan mugun ba , ina
cikin zancen zuci saiga Afrah tashigo fuskar ta tayi ja alamar tasha Kuka , dubanta nayi nace "
kiyi hak'uri Sister gaskiya wannan Zunnur d'in mugune sosai , Ni wallahi har nafara jin tafiya
zamuyi gobe mubar garin nan saboda shi , Afrah ta dubi Hanan tace "Dan Allah karkice zaku
tafi saboda Zunnur , nasan hutun nan nasu badadewa zasuyi ba zasu tafi , duban ta nayi nace
" to ko sudad'e ko kar su dad'e ai saura sati mukoma gida , Afrah tasamu waje ta zauna tana
fad'in " wallahi shiyasa banason du dawo , musamman Ya Zunnur akwaishi da mugunta sosai ,
Nace " ai koni yau na tabbatar dahakan , yanzuma yafita daga d'akin nan wai yana jiran inje in
wanke masa motar , dariya Afrah tafara tana fad'in " wai ke ya akayi kikayi fitsari ? kinsan
kad'an yarage nayi dariya kawai sai naji ya mareni , Nima dariyar nayi nace " ke kuwa wannan
Uwar tsawar dayake daka mana ai dole nayi fitsari , gaskiya Matar Ya Zunnur tashiga Uku da
Muguntar sa , Afrah tace " irinsu ai basa yiwa matansu haka sai dai tarairaya da nuna Soyayya
, Nan mukaci gaba da hirar mu wacce rabi duk akan Ya Zunnur ce.......
Kuyi maneji ν ½νΈ
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ ν ΌνΌΉν ½νΈ
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Na*
_Zee_ _MD_ βν ΌνΏ»
*Hamdala* *Writer's* *Association* ν ½ν²ͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}* β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Tawannan* *Number*
07046107812 *kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* *Kukaranta* _Cikin_
_Aminci_ ν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°
ν ΌνΆ page. 9
Dasauri Ya Haidar ya bud'e dan ganin waye meyi musu wannan bugu , nikuwa nida Afrah
daman munsan kwanan zancen , tuni Afrah ta kama Hannu na tace " inkin shirya kibuyoni dan
wallahi da gudu zanfita ba tsayawa , nima kai na gyad'a mata alamar na shirya , aikuwa muka
bud'e murfin k'ofa ta b'angaren da ba anan Ya Zunnur yake ba , tuni muka kwasa da gudu cikin
gida muka bar Ya Haidar da Ya Zunnur suna cacar baki......
Muna shiga maka tarar da Umma da Ammi suna hira , suna ganinmu sukace " kukuma
meye hakan kuke wannan gudu tamkar wasu k'ananun Yara ? Afrah tace " wallahi Umma muda
Ya Zunnur ne wai dan munje unguwa da Ya Haidar , Ammi tace " ai kunyi laifi tunda baku gaya
masa zaku fita ba yana matsayin Babba a cikin gidannan nan , mudai bamu tsaya ba muka nufi
cikin d'aki muka saka key abinmu ......
Wanka kowaccen mu tayi sannan muka saka kaya marasa nauyi , sai lokacin muka fara jin
cikinmu na kiran chiroma , Afrah tadubeni tace " Hanan kije ki d'ebo mana Abinci dan wallahi ni
tsoron fita nake nahad'u da Boss , duban Afrah nayi nace "Tabd'ijam wato nikuma inje ya ritsani
a hanya yamin dukan tsiya , muna zaune muna ta jayayya mukaji ana buga k'ofah , da sauri na
haye saman gado ina duban Afrah , dariya tahau yimin tana cewa " Sannu farar kura irin
wannan gudu haka , k'ofar d'akin taje ta tsaya tana tambayar waye ? muryar Umma taji tana
cewa " bansaniba yau ku bakwajin yunwa ne tund'azu kun k'ule a d'aki kunk'i fitowa ? da sauri
Afrah ta bud'e d'akin tana fad'in " Wallahi muna ji Umma , tsoron Ya Zunnur yahamu fitowa ,
tasowa nayi muka fito palor dan cin Abinci , aikuwa Ya Zunnur suna tare da Ammi sai hira
sukeyi tamkar bashi ba , wucewa mukayi sai sinsik'e kai muke tamkar muna fukai , shikuwa
gogan ko kallon mu baiyi har muka wuce kan Dinning......
Bayan wasu kwanaki har munwuce lokacin da zamu koma gida , lokacin Su Ya Zunnur
hutunsu ya k'are suna shirin komawa Sch , A lokacin Daddynsu tafiya ta taso masa zuwa Dubai
, har an samar min komai da komai zanfara zuwa sch d'insu Afrah , Duk da ina kewar Garin
Jos da kuma k'awayena , Ya Zunnur tunda ga randa mukaje wannan party da Ya Haidar bai
k'ara shiga sabgar muba , muma kuma duk abinda zai had'amu dashi bama nema , Ana Gobe
zasu tafi muna zaune nida Afrah a cikin kitchen tana ta bani labarin yadda sch d'in su take ,
ganin mutum mukayi a tsaye kofar kitchen rungume da hannunsa a k'irji sai kallona yake , Tuni
na dabarbar ce nakama 'Yan kame kame , Afrah kuwa yankan salad d'inta taci gaba dayi batare
da tak'ara magana ba , sai da ya dad'e a haka sannan yace " Hanan kizo yanzu inason ganinki ,
saura kuma injiki kink'i zuwa kiga yadda zanyi dake , a hankali na furta masa to ganinan zuwa ,
shigewa yayi yafita yabar mu , Afrah tana ganin ya fita tafara doka tsalle tana murna wai yau
zataji kukana , Hararar ta nayi ina fad'in " ai dayake yace miki dukana zaiyi , Tace " kikama
hanya kije wallahi karki janyo wa kanki wani laifin , ficewa nayi batare da nayi magana ba ......
'Bangaren su Ya Zunnur na nufa ina sand'a tamkar muna fika , ina zuwa k'ofar d'akin nayi
sallama cikin