Showing 24001 words to 27000 words out of 41364 words

Chapter 9 - NI BORA CE BY ZEE MD COMPLETE.pdf

Zee MD   

12 Jul 2025

1604

duka k'arfinsa , ai tuni Hanan tafara kuka tana fad'in " dan Allah kad'agani
karka kusance ni , wallahi bazan iyaba nagaji da aurenka kasakeni mugu azzalumi kawai .......
Alhaji Nasir tuni yaji ransa yayi mugun b'aci , Wato itama tafara shirin komawa tamkar sauran
matan dayasaka , to tabbas zata yabawa aya zak'inta , dole zaiyi bincike a kanta ko tasan wani
abu a game dashi , a haka ya danneta sai daya biya buk'atar sa ta inda yasaba wato bayanta
.......
Bayan ya kammala ya mik'e tare da dubanta tamkar ta suma haka ya maida kayansa ya gice
, daman indai Alhaji Nasir ya kusanci matansa to baya wani tsarki , a haka yake maida kayansa
sannan yanufi d'akinsa yaje yayi tsarkin akan k'waryar tsafi ......
Hanan ta dad'e a hakan kafin ta mik'e k'afarta tace batasan zancen nan ba , kuka takeyi
sosai tana fad'in " wayyo Allah Ammi na dan Allah kizo ki ceceni zasu kasheni , Kuka take sosai
har muryar ta tadashe ta daina fita ....
A hankali ta lallab'a ta sauko tashiga toilet d'in dake cikin d'akin ta gyara jikinta , wanka tayi
tagasa jikinta da ruwan zafi sosai , k'atarta tak'i takuwa sosai ta rik'e . Haka ta dunga d'ingisawa
har tafito daga toilet d'in , saka kayanta tayi sannan ta kwanta saboda wani zazzab'i dake
barazanar kamata , lullub'a tayi cikin barko tana tunanin yadda za'ayi ta gudu daga cikin
gidan......

Zunnur tunda yakoma Sch yakasa kwanciyar hankali , kullum tunanin Hanan ga yawan
mafarkinta dayakeyi tana kuka , tabbas duk inda Hanan take bata cikin kwanciyar hankali ,
Haidar har saida ya fahimci d'an uwan nasa yana cikin damuwa , haka yasashi a gaba da
tambaya amman fir Zunnur yace bakomai kawai bayajin dad'i ne ...
Hanan tana ta tunane tunanenta har bacci yayi awon gaba da ita , Nasma so biyu tana
shigowa cikin d'akin tana ganin Hanan nayin Bacci , ana biyun ne ta zauna tana jiran ko Allah
zaisa ta farka , Ihu Nasma taji an kurma a tsakar gida , da sauri ta mik'e ta fito dan taga
menene , ihun da aka cigaba dayi yasa Hanan ta farka a tsorace , da sauri ta mik'e daga kan
gadonta tana d'ingisa k'afa tayo hanyar waje ,
Lokacin duka yaran gida sunfito sai kuka sukeyi , Hanan naganin Haka taji gabanta ya yanke
ya fad'i tuni tafara Kukan itama tana tambayar meye , Yarinyar da Hanan d'in ke mutuk'ar so
wato Aysha itace ta mutu , kuma itama mutuwar ta tamkar yadda sauran 'Yan uwanta sukayi
haka tayi , Hanan yanke jiki tayi tafad'i tuni Nasma tayo kanta da gudu , Nan tashiga yayyafa
mata ruwa amman shuru ko motsi , Nasma kuka tashiga yi sosai tana fad'in " dan Allah Aunty

Hanan kitashi karki tafi kibarni plss , nariga na saba dake kece nake gani nasamu farin ciki ki
taimaka plss , shuru Hanan ta daina motsi Yaran gida tuni sunzagaye ta sai kuka sukeyi suma
, Nasma takuma zubawa Hanan Ruwa tana jijjigata tana fad'in " kitashi Hanan karki mutu
bakiga mutuwar Daddy ba , tabbas nasan bazaki mutu yanxu ba har sai munga irin mutuwar
wulak'ancin da Daddy zaiyi , kitashi dan Allah mucika burin mu kar mubari sauran yaran ma su
Mutu , kwata kwata Nasma ta fita a hayyacin ta batasan Alhaji Nasir yazo wajen ba tuni ......

Hankalin Ammi kwata kwata ba a kwance yake ba , dan kwana biyun nan mafarkin datakeyi
na Hanan yayi yawa , koyaushe sai taga anbiyo Hanan d'in wasu jibga jibgan maza , kuma
koyaushe tana ihu tana fad'in " Ammi na kizo ki ceceni karsukasheni , shiyasa yau da tatashi ta
k'udurta aranta tabbas gobe zata tafi Jos dan gano halin da 'Yar ta take ciki ........
A b'angaren Zunnur ma tuni ya shirya tsaf dan k'ara dawowa Jos , dan wannan karan bazai
k'yale Kawun Hanan ba duk inda take saiya kaisa yagaji da rainin hankali , batare da yakuma
gayawa Haidar ba ya kuma shiryawa dan yana so gobe da sassafe ya wuce garin Jos......

Safara'u tuni anshirya Had'uwa da Alhaji Nasir , dan ta k'udurta a ranta ko ta halin k'ak'a
saita shiga cikin gidansa , in ma yace bazai aureta ba to tabbas zatasan yadda tayi yadunga
kusantar ta harta samu rabonta itama , ai tunda Hanan ta wulak'an tata tabbas saita d'au fansa
itama.....
Alhaji Nasir duk irin maganganun da Nasma tayi yajisu , amman dayake d'an duniya ne
saiya share ya k'araso wajen tamkar baijiba , lokacin Hanan ta farfad'o Nasma na rik'e da
Hannunta , duban Nasma Hanan tayi sannan cikin muryar Kuka tafara magana " Aysha itama ta
Rasu irin yadda su Abbas sukayi ? meyasa Alhaji yake kashe Yaransa da Matansa ? Alhaji
Nasir dayake tsaye yana jinsu cikin ransa yace " tunda har kuka riga kuka ganeni to tabbas
kuma taku tazo k'arshe , daman kune wad'an da kuka shigarmin d'aki to tabbas saikun bisu
kuma , dan barinku a raye barazana ne ga dukkan wani burina danake dashi , a fili kuwa tuni
yabar wajen dan kar su ganshi ma bare su fahimci yaji abinda suke fad'i.......

Sosai mutuwar Aysha ta kuma hargitsa Hanan , nan tak'arajin tsoron Alhaji mutuk'a Koda
yaushe tana tare da Nasma , yanzu kwata kwata ma tadaina kwana a d'akinta ta koma d'akin
Nasma , ita yanzu Nasma ta daina tsoron komai ga wata muguwar tsana datayiwa Mahaifin
nata , tabbas tayi danasanin zuwa duniya ta tsatson azzalumin Mahaifi irin Alhaji Nasir....

Bayan anyi sadakar Ukun Aysha komai ya lafa , amman duk wanda zaka gani a cikin gidan
Alhaji Nasir a tsorace yake , walau Babba walau yaro kowa yatsorata da gidan , Yauma kamar
kullum dare yayi kowa ya koma bacci da ido d'aya , yaran ne masuyin bacci saboda yarinta ,
Hanan da Nasma suna kwance amman ko wanne a cikinsu tunani yakeyi , dan rabonsu da
bacci tun randa Aysha ta Rasu , wajen k'arfe d'ayan dare sukaji anbud'e k'ofar d'akin dasuke
ciki , tuni suka mik'e tare da kashe k'wan d'akin , da sauri Hanan tace " Nasma shikenan muma
kashemu zaiyi wallahi Alhaji ne , Nasma ta toshewa Hanan baki a hankali tace " bazai

kashemu ba insha Allah zo mushiga toilet mufita ta windor ciki , a hankali suka sauko daga kan
gado rik'e da Hannun juna suka shige toilet d'in , suna shiga sukayi maza suka saka masa
sakata sannan suka nufi wajen windon ciki , Hanan tace " wannan windon yanzu kina ganin
zamu iya fita ta cikinsa ? Nasma tuni ta taka kan tudun abin wanka tafara k'ok'arin b'allo glass
d'in , Hanan itama takowa tayi tahawo wajen tafara taimakawa Nasman , aikuwa dai dai lokacin
glass d'in ya yanki Hanan tayi wata k'ara da sauri Nasma ta toshe mata baki gudun kar aji suna
ciki , aikuwa sai ji sukayi anfara girgiza k'ofar Toilet d'in ..........


*Juma'at Kareeem Mutanena* ν Ύν΄ν ΌνΏ»ν Ύν΅°

*Karku Manta da Karanta Suratul Khafi Aya Gomar Farko*

*Yin Salati Ga Shugaban Halitta Annabi Muhammad S.A.W*🙏🏻🙏🏻


*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 🌹😍
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβ€ν ΎνΆ³


*Zee* *MD* ✍🏻


20.

Da sauri Nasma ta dubi Hanan tace " meye hakan ke kuma kodai bakya gani ne ?
sai a lokacin Hanan ta dawo dai dai tana maida numfashi , maganar Direbance ta katsesu
yace musu " Bayin Allah ku kuwa me kukayiwa wad'an can garadan mazan suke binku ?
Nasma tace " wallahi babu abinda mukayi musu kawai 'yan iska ne , Dayake gari bai fara
haske ba shiyasa har suka shigo cikin tasha Hanan bata kula da wanda ta fad'a jikinsa ba ,
suna iso ciki kowa ya fito daga cikin motar Hanan tadubi Nasma tace " kinsan a koda yaushe
Alhaji zai iya sakawa a kuma biyomu, wallahi da da kud'i a hannun mu da Lagos zamu tafi
wajen Ammi , Nasma tace " yanzu yadda za'ayi muje gidan Kawun ki sai mugaya masa komai
kozai samo mana mafita , Dasauri Hanan ta dubi Nasma tace " anan gurin dai baki kawo
shawara wacce zata yiwuba , ai zuwan mu gidan Kawu tamkar komawace gidan Alhaji Nasir ,
dan ko me zamuce wallahi Kawu bazai yadda ba......

Shuru sukayi suna nazari dan basu san ta yadda za'ayi suje Lagos ba , can Hanan taga
giftawar wani Saurayi ta kusa dasu zai wuce , da sauri ta mik'e tana nufar wajensa tana fad'in "
Dan Allah bawan Allah muna neman taimakon ka , juyowa yayi saboda jin muryar wacce a ko
yaushe yake mafarkinta , aikuwa Idanunsu suka had'e waje d'aya , da sauru Zunnur yace "
Hanan kece haka ? Hanan batasan sanda tafad'a jikinsa ba tare da fashewa da kuka wanda

batasan na meye ba......

Yaran Alhaji Nasir tuni suka kirasa a waya suka gaya masa komai daya faru , cikin fusata
yadunga yi musu fad'a akan sakacin dasukayi har su Hanan suka gudu , Anan suka yi masa
Alk'awarin zasu duba kaf cikin gari dan nemo masa su , kashe wayar yayi batare da yace komai
ba tabbas yayi mugun sake da har yabari su Hanan suka san sirrinsa , dole zai nemosu duk
inda suke a fad'in Nageria jininsu ya riga dayayiwa dodonsu Alk'awarinsa..........

Da k'yar Hanan ta saki Zunnur tana share hawayen murna , dan yazo musu a lokacin
dasuke da buk'atarsa , Nan yajasu gefe yana dubansu yace " dama kune aka biyoku kuka shigo
cikin motar mu ? Nasma tace " mune . Zunnur yace " me kukayi musu haka suke binku kuma
ke Hanan ai ance anyi miki aure ina mijin naki yake ? Nasma tace " wannan zancen ba na nan
bane yanzu dai dan Allah ka kaimu wani gurin ka b'oyemu , da sauri yadu besu yaga jikinsu
duk yabaci gashi kowacce da ciwo a jikinta , cikin zuciyar sa yafara tunanin yanzu ina zai kaisu
Kano ko kuma Lagos ? wata zuciyar tace inka kaisu kano a inah zaka ajiyesu kawai ku nufi
Lagos , da sauri yadubesu yace " kujirani Anan ina zuwa yanzu zandawo , da sauri ya juya
yanufi cikin tasha lokacin har mutane sunfafa fitowa , wani P.O.S na cikin Tasha yashiga Nan
ya kira wani Abokinsa yagaya masa ya turo masa kud'i , Baijima ma ya turo masa kud'in nan ya
ansa tare da nufar wani guri yasiya musu Hijabai manya dan kayan jikinsu ma duk sun yage ,
koda yadawo samunsu yayi cikin wani lungu wanda ba yawan mutane , basu Hijab d'in yayi
yace susaka sai su tafi , ansa sukayi suka saka sannan yabasu face mark shima suka saka
nan suka bar cikin Tashar , a hanyarsu ta fita daga cikin tashar sukayi karo da Yaran Alhaji
sukuma zasu shigo......
Ta gaban su Hanan suka wuce batare da sun gansu ba , su Hanan suka kuma tsorata sosai
Zunnur yace " ku nutsu kar kuyi abinda zaisa aganeku , haka suka hau motar yace akaisu
airpot dan Lagos yakeso su nufah.....


A can b'angaren Ammin Hanan kuwa tashi tayi da zazzab'i da Amai , dan haka ta d'aga
tafiya zuwa gobe ko jibi intaji sauk'i , sai dai tunda tatashi gabanta yake mutuk'ar fad'uwa ,
kwata kwata batajin dad'in komai , Hajiya Asma'u tana ganinta hakan ta anshi aikin girki tace
mata taje ta kwanta ta huta ......
Tafiyar Awa d'aya da Rabi sukayi a jirgi suka isa Lagos , sosai Nasma take mamakin garin
Lagos d'in , mutane sutacewa akwai cunkoso a lagos babu gidaje masu kyau to itadai bata
cunkoso ba sai kyau da kuma tsaruwa, Tunani Zunnur ya shiga akan inah zai kai su yanzu
gidansu ko kuma gidan Ammi , kawai ya yanke ya kaisu gidan Ammi tunda yasan gidan daman
, hawa motar da zata kaisu gidan Ammi sukayi suka nufi can , Hanan batasan inah zasuje ba
tunda basanin gari tayi ba kawai dai jitake kamar ta mik'e ta hau taka rawa saboda farin cikin
zataga Ammin ta , duk wata fargaba da suka taho da ita kwata kwata babu a gun Hanan dan
har wani murmushi takeyi da jin dad'in zataga Ammin ta yau.....

Alhaji Nasir tuni ya hau motar sa ya nufi gidan Kawu Idi , tunani yakeyi ko su Hanan suje
can su gaya masa abinda yafaru dasu....
Yana zuwa yasamu Kawu Idi yana k'ok'arin fita , yana ganin motar Alhaji ta tsaya yafara
fara'a ya nufi wajen motar , Alhaji Nasir ya fito fuskar sa kadaran kadahan ya mik'awa Kawu
hannu sukayi musabiha , Kawu yace " ina fatan dai lafiya ba Wannan ja'irar yarinyar ce tayi ma
wani Abunba ? Alhaji Nasir najin haka yasan Hanan basuzo gidan Kawu ba , wata zuciyar tace "
kodai sunzo sunfad'a masa shine yakeso ya raina masa hankali , gyara murya Alhaji Nasir yayi
sannan yace " daman neman su nazoyi ita da yarinyar wajena , dan tuntuni suka gudo daga
gidan ba inda ba'a duba ba amman ba'a gansuba shine nayi tunanin ko sunzo Nan , salati
Kawu Idi ya shiga yi yana duban Alhaji sannan yace " wallahi basu zoba amman lafiya kuwa
suka gudu ko wani laifin suka aikata ? Alhaji Nasir yashiga shirgawa Kawu k'arya ganin baisan
komai ba yace " wallahi sunyiwa Uwargidana duka akan rabon Abinci , kuma ni ba dukan da
sukayi bane damuwa a'a ba'asan inah suka nufa ba shine damuwar , ko kuna da wasu 'Yan
uwan a nan ko can sukaje ? Kawu yana salati yace " tabbas wannan aikin Hanan ne itace zata
kawo wannan banzar shawara ta dukan Hajiyar , Maganar 'Yan uwa kuwa bamu da kowa sai
dai gidan su Safara'u me d'akina , dan ko ita Uwar Hanan d'in kasan na fad'a maka cewa tana
can Lagos wajen d'an uwanta , kuma bana tunanin zasu gudu can d'in , sai dai ko ita yarinyar
wajen naka ko tajata sunje danginka , Alhaji Nasir yace " gaskiya ba wasu dangina da Nasma
ta sani bare suje , amman kakira min me d'akin naka kozata yiwa 'yan gidan nasu waya muji ,
da sauri Kawu Idi ya nufi cikin gida dan yiwa Safara'u magana........


Suna zuwa gidan su Ammi Hanan tadunga kallon gidan , cikin ranta tafara tunani tabbas
tasan gidan su Zunnur yafi haka kyau sosai , to nan suka daso kuma duk da wannan d'in ma
yana da kyau , suna k'arasawa palor gidan sukayi sallama daga ciki aka basu umarni su shigo ,
suna shiga suka samu Hajiya Asma'u da Alhaji Murtala a zaune suna hira , koda sukaga
Zannur suka tareshi da fara'a dan sunsan shi sosai tunkafin Alhaji ya auri Ammi , gaishesu yayi
cike da girma mawa amsawa sukayi suna nuna musu wajen zama , Hajiya Asma'u ta dubi su
Hanan wad'an da suke sanye da face mark har lokacin tace " sannunku da zuwa 'Yan mata ,
sai lokacin suka cire Face mark d'in suna gaida su Hajiyar , Hajiya Asma'u tana kallon Nasma
taji gabanta ya fad'i take taji lokaci d'aya yarinyar ta shiga cikin ranta , gaisuwar da suke mata
kwata kwata takasa amsawa saboda kallon da takeyiwa Nasma , A dai dai lokacin Ammi tafito
daga cikin d'akinta tasha wanka cikin wata Atamfa me kyan gaske gashi tayi wani kyau da ita
kana ganinta kaga me yaron ciki , Hanan tana ganin Ammi ta tafi da gudu tana fad'in " Ammi na
I miss u so Much ta fad'a jikinta , sai kuma ta saki kuka tana kuma k'ank'ame Ammin nata
tamkar za'arabasu , A take su Hajiya Asma'u suka gane Hanan , nan suka shiga murna suna
fad'in " kace yau gidan namu muna da manyan bak'in Jasawa sannun ku da zuwa , Ammi itama
ta rik'e Hanan kam tamkar zata maidata cikinta dan murnar ganinta , samun waje sukayi suka
zauna sannan Ammi tafara k'arewa Hanan kallo , gani tayi duk tarame ta lalace gashi kwata
kwata tamkar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login