Showing 15001 words to 18000 words out of 41364 words
d'in , duban Hanan tayi wacce tashiga tura ice cikin
Murhu tana goge gumin dake zubo mata na tsoro , ta dad'e a tsaye a gurin tana k'arewa
kitchen d'in kallo kafin tajuya ta fita batare da tacewa Hanan ci kanki ba , tana fita Hanan ta
sauke wata ajiyar zuciya tana Hamdala da godiya ga Allah dayasa Hajiya Hajjo bataga Nasma
ba , Nasma itama fitowa tayi sannn ta lek'a taga ba kowa tadawo suka ci gaba da aikin ,
Hanan tace " nifah kawai ina ganin yakamata Aunty Nasma kibar aikin nan haka ki fita kar
Hajiya Hajjo tadawo , Nasma tace " to bari na kad'a miki miyar sai nafita inyaso saiki sauketa ,
tuni Nasma ta mik'e ta hau kad'a miya tana gamawa ta lek'a taga ba kowa ta fice da saurin ta
.....
Nasma tana fita ba dad'ewa Hanan taje tafad'awa Hajiya Hajjo ta kammala girkin , Hajiya
Hajjo tace " kije palor cikin gida ganinan zuwa yanzu , Hanan tace to sannan tafita daga cikin
d'akin Hajiya Hajjo d'in ,
d'akin Nasma Hanan ta nufa , tana zuwa taga Nasma na zaune tana karatun Alkur'ani ,
zama tayi har saida Nasma takai aya sannan tadubi Hanan tace " ina fatan bawanda yaganki
lokacin dazaki shigo d'akina ? Hanan tace gaskiya babu kowa a tsakar gida , nima yanzu zuwa
nayi kirakani palor cikin gida dan bansan ina ne ba , Nasma tace " Hajiya Hajjo ce tace kije can
kenan ? Hanan tace ae itace inafatan dai lafiya bawani laifin nayi ba , Murmushi Nasma tayi
sannan tace " ba laifin da kikayi sai dai yau zaki fara cin Abinci cikin Jama'ar gidan nan , Hanan
tayi jugum tana kallon Nasma , Nasma ta mik'e taje tayiwa kur'anin ta wajen zama sannan tace
" tashi muje karta rigamu zuwa , Hanan ta mik'e suka fito suka yi hanyar Babban palor cikin
gida.....
Suna shiga cikin palor Kowa na cikin palor yafara kallon Hanan , dayawa wasu yaran dake
cikin gidan basusan Daddyn nasu yakuma wani auren ba sai yau , yarane k'ananu zasuyi su
Ashirin a zune kufi kufi dasu , kana kallon sai sunbaka tausayi saboda yadda suke , kayan
arzik'i babu ajikinsu kowanne yana zaune yayi jigum ko walwala basu da ita irin ta sauran yara ,
Nasma tasamu guri ta zauna sannan ta dubi Hanan tace " ki zauna kema , palor babu komai a
cikinsa sai capet da aka shimfid'a dukansa , sai wata Tv 'yar k'arama da ita kuma irin ta dacan ,
Hanan zama tayi itama tana kallon yaran tamkar wad'anda suke a gidan birsin , cikin zuciyarta
take fad'in " Anya Alhaji Nasir zaiga Rahamar Allah kuwa cikin lamarinsa ? wannan zalincin har
ina kalli yara wad'an da yadace ace suna tare da iyayen su Mata suna basu kulawa amman ji
yadda suke rayuwa , tabbas da wannan rayuwar wanda ace a gidan marayu suke watak'ila
zasu samu gata fiye da nan , tunda ta zauna bata k'ara cewa komai ba , can sai ga Hajiya Hajjo
d'auke da k'atuwar Roba a hannu , tana shigowa ta dubi Nasma tace " kije kicewa su Alawiyya
da Hindatu suzo , Nasma tace to ta mik'e tafita ....
Hajiya Hajjo tashi tayi takuma fita , Hanan hawaye taji yana zubowa a kan kuncinta , tabbas
wannan ba gidan zama bane , a gaskiya Kawu ka cuceni da ka auramin wannan mugun
mutumin , ganin wata yarinya tayi wacce bazata wuce shekara uku ba tazo wajenta tana
gwarancin " Ummata kibani abinci naci da kanki karsu Habibu sucinye , Hanan wani kuka taji
yazo mata ta rungume yarinyar tafara kuka , kana ganin yarinyar kasan wanka ma bayi mata
akeba gashin kanta yayi duk'u duk'u , Nasma ce tashigo cikin palor , tana hango Hanan
rungume da yarinya tayi sauri ta k'araso ta janyeta daga jikinta , komar da ita tayi cikin sauran
yaran sannan tacewa Hanan " meyasa zakiyi hakan ? kinsan hakan zai iya janyo miki matsala
me girma a wajen Daddy da Hajiya Hajjo , duk wani tausayin su da zakiji a yanzu ki adana shi
bayanzu ba , kibari musamu mafita sai musan yadda za'ayi , Hajiya Hajjo ce tashigo shine
yasaka Hanan da Nasma yin shuru , Hajiya Hajko tace " ke Nasma baki gaya musu nace
suzoba ne najisu shuru ? Nasma tace nafad'awa kowa kina kiransu ... shigowar su tasa Nasma
yin shuru , Hajiya Hajjo tadubesu tana hararar su tace " saikun ga dama zakuzo kenan ?
Alawiyya tace " to ke wacece da za'ace kina kiran mutum saiya taho , Hajiya Hajjo tanajin hakan
tasan yau Alawiyya ta gaji sotakeyi tayi abinda Alhaji zai saketa , batabi ta kanta ba ta hau
zubawa yara Abinci , duka wannan bataliyar yaran ahad'e sukecin Abinci , sannan ta zubowa
wa 'Yan matan ciki tare da Nasma suma tabasu , saikuma ta zubo musu ita da Hindatu da
Alawiyya sai kuma Hanan , tuni kowa yafara cin Abincin sukayi tsit dasu .....
Kafin kace meye tuni yaran nan suncinye nasu tuwon, sai faman sid'e hannu suke suna zare
ido alamar basu k'oshiba , wamnan Yarinyar datazo gun Hanan itace take kuka tana duban
Hanan tana cewa Umma ban k'oshi ba suncinye , Hanan hawaye ya ciko idanunta tasaci kallon
Nasma wacce keyi mata nuni da karta kula yarinyar nan , Hanan kwata kwata kasa cin Abincin
tayi tana duban yarinyar , tuni su Hajiya Hajjo sunkusa cinyewa dan ko sau d'aya basu kulataba
, Suna gama cinyewa Alawiyya ta mik'e tana harare harare tafice abinta , itama dai Hindatun
tashi tayi ta fice Abinta , saida Hajiya Hajjo tagama sid'e kwano sannan ta mik'e tacewa su
Nasma kufito da kwanuka inkungama tasa kai ta fice......
Hanan ko kallon wajen da Nasma take batayi ba ta mik'e tafita , d'akinta ta nufa prizer d'inta
ta bud'e ta d'auko wata leda da Alhaji taga yashigo mata da ita yasaka a ciki , tana bud'ewa
taga Balangu ne da biredi , sai kuma damammiyar fura da nono a roba , tuni ta d'auko furar tare
da gutsiro biredi da kuma d'ebo nama takuma fita , tana zuwa wajen k'ofar Babban palor taga
Nasma zata fito , tarar ta tayi sannan tace " Aunty Nasma inaso kisan yadda zaki d'aukomin
yarinyar nan zan bata fura da biredi taci , Nasma ta zare ido tana fad'in " wai meyasa bakyajin
magana Hanan wallahi wannan Abun dakike k'ok'arin yi Babbar kasadace , kuma inhar aka
ganoki wallahi Daddy zaiyi miki hukunci me tsauri , Hanan tace " wallahi koda kasheni zaiyi sai
nabata , bazan tab'a iya bacci ba ina ganin yarinya k'arama tanajin yunwa , inbanda mugunta
taya za'ace adunga had'awa manya da yara abinci , kuma abincin ma bawanda mutum zai
k'oshi ba , Nasma tace " Meye naki nadamuwa Hanan kawai kikoma d'akin ki kiyi musu addu'a
Allah yakawo mafita , Hanan tuni ta shige cikin palor Nasma na ta k'wala mata kira amman tak'i
dawowa , tana zuwa ciki tasamu yaran kowanne ya kwanta yayi lamo alamar dai basu k'oshiba
, can tahango Yarinyar tana tsotar hannunta tana rufe da idonta alamar bacci zatayi , Hanan na
zuwa ta lallab'a ta d'aukota ta fito da ita bayan d'akin sannan tafara bata Fura da biredi tana
ansa , wani irin ci yarinyar takeyiwa biredin da fura tamkar tsohuwar mayya , kafin kace me
harta tada furar da biredin , Naman tabata shima ta cinyeshi tas , Hanan tace kin k'oshi yanzu ?
kai ta d'aga alamar ta k'oshi sannan Hanan tace " muje ki kwanta kinji Saikuma dasafe , cikin
hausar ta ta gwaranci tace " zaki kuma kawomin wani da safe Ummata ? Hawaye Hanan taji
yana zuba a kuncinta sannan tace " ae zankawo miki , maidat cikin 'Yan uwanta tayi sannan
tafito taga Nasma a inda tabarta , dubanta Nasma tayi tace " kinbata taci kinji dad'i , inaso kisani
karkisaba mata da abinda kikasan ba d'orewa zaiyiba , dakin barta a haka zata saba tamkar
yadda muka saba kuma gashi har muka rayu ahaka , Hanan tace " Nasan koda bazai d'oreba
nidai zancigaba da kulawa da ita , dan duk cikin yaran ai ita tafisu k'ank'anta dole a tausaya
mata....
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
βν ΌνΏ» *MD*.
13.
Bayan kwana biyu tuni Hanan tasaba da aikin wahalar gidan Alhaji Nasir , Sosai Hanan
take kula da wannan k'aramar yarinyar me suna Aisha , koda yaushe sai sungama cin Abinci a
had'e da sauran 'Yan uwanta sun kwanta sannan Hanan zata lallab'o tazo takuma bata , tuni
Aysha tasaba da Hanan wacce take kira da Umma , duk wannan Abin da Hanan keyi sauran
matan gidan bawacce tasani sai Nasma kad'ai , Hanan tana zaune a cikin d'akinta tana tsefe
kanta saiga Nasma tashigo cikin d'akin d'auke da Sallama , amsa Hanan tayi Nasma tasamu
guri ta zauna , duban Hanan tayi tace " yau tsifar kai kikeyi kenan ? Hanan tace "ae wallahi kan
nawa yayi datti dayawa shiyasa na tsefeshi kuma gashi bansan waye zaiyi min kitsoba , Nasma
tace " wannan ma wata dama ce daza musamu dan muje gurin Matar da Daddy yasaka , Hanan
ta dubi Nasma cike da son jin k'arin bayani , Nasma tace "kin manta nagaya miki cewa wacce
Daddy ya saketa sannan ya aureki tana nan yanzu haka ita bata mutu ba , Hanan da sauri tace
" ea na tuna wacce kikace sunanta Suwaiba ko ? Nasma tace ea "ita nake nufi yanzu kinsan
yadda za'ayi ? Hanan ta girgiza kanta alamar A'a . Nasma tace " yanzu tashi zakiyi kije d'akin
Hajiya Hajjo tunda Daddy baya gari kice mata zakije kitso , Nasan bazata hanakiba saboda
tanason taga ana fita in Daddy bay nan saboda tasamu shedar ce masa mace nafita yawo in
baya nan , kinsan a kullum ajin haushin auren da Daddy yakeyi take , intaji yayi saki har murna
take sosai ranar saboda jin dad'i , Hanan tace " ni wallahi mamaki ma take bani akan wannan
kishin nata da takeyi , yanzu inbanda Abinta meye abin kishi a wajen Alhaji Nasir ? Mutumin
dayake mu'amalar aure da mace ta baya sannan cikin gidan sa bawani kwanciyar hankali , irin
wannan rayuwar ta gidan nan yanzu har wata abar so ce , Nasma tayi d'an Murmushi dan
tanajin ciwon halin Mahaifin nata dayakeyi , sai lokacin Hanan ta tuna da cewa Alhaji Nasir fa
Mahaifin Nasma ne kuma duk lalacewar sa dole zata kirasa da sunan Uba , cike da jin Nauyin
Nasman tace " kiyi hak'uri Aunty Nasma dan Allah akan abinda na fad'a game da Mahaifinki ,
Nasma tayi Murmushi sannan tadafa kafad'ar Hanan tace " babu komai ai halinsa ne kuma
nima na tsani halin nasa , yanzu dai tashi kije kitambayi Hajiya Hajjo d'in sai kisameni a k'ofar
gate ina jiranki .......
Koda Hanan ta tambayi Hajiya Hajjo bata samu wata matsala ba ta amince mata , Hanan ta
shirya tasaka Hijab d'in ta tafita , tunda aka kawota gidan Alhaji Nasir yau tafara zuwa k'ofar
gate d'in gidan , tana fita ta hangi Nasma a tsaye sanye da Hijab itama , tana k'arasawa suka
fita titi suka hau Napep suka nufi gidan su Suwaiba , dayake Nasma tasan gidan ta sanadiyyar
Zuwan datayi lokacin da Baban Suwaibar yarasu , suna tafe Hanan tacewa Nasma "yanzu
yazamuyi da kitso kuma ? kar mu koma gida Hajiya Hajjo taga banyi kitsoba fa , Nasma tace "
in munfito daga gidan sai muje gidansu wata k'awata ta iya kitso sosai sai tayi miki , Suna zuwa
suka sauka Nasma tabiya kud'in sannan suka shiga lungun gidan su Suwaiba.....
Zunnur tunda yaji labarin Hanan ta koma Jos hankalinsa duk yabi yatashi, Allah Allah yake
suyi exams. Su samu hutu yanufi Jos dan ganin halin da Hanan ke ciki , Haidar so dayawa zai
saka Zunnur a gaba yana tambayar sa ko lafiya ganin Yadda ya canza gaba d'aya , amman
kwata kwata yak'i fad'a masa sai dai yace ba komai , a haka har suka fara Exams. Suka
kammala , koda suka kammala Zunnur yayi shirin zuwa garin Jos batare da yafad'awa Haidar
ba , kawai yace zaije gurin wani Abokinsa amman kwana biyu zaiyi yadawo , a haka sukayi
sallama ya nufi Hanyar Jos......
Lokacin da Zunnur ya iso Jos dak'yar yagane Unguwar su Hanan , yana zuwa gaya gidan
duk ya canza tamkar ba gidan ba , tsayawa yayi a k'ofar gidan yana neman yaron da zai aika
cikin gidan , yana tsaye saiga wani yaro yazo wucewa . da sauri Zunnur ya tsayar dashi sannan
yace Ya shiga cikin gidan yace ana kiran Hanan inji Yayanta , yaron yashiga cikin gidan ya
sanar da sak'on Zunnur , lokacin Kawu Idi yana zaune yana cin Abinci , duban yaron yayi yace "
wacce Hanan kuma kake nema ? ai Hanan d'ayace a gidan nan kuma anyi mata aure , Yaro
yanajin haka ya fito waje dan sanar da Zunnur , Kawu ya dubi Safara'u yace " kiji wani tsohon
zance wai ana kiran Hanan , ai yanzu Hanan sai dai mufara maganar zuwan 'Danta , Safara'u
ta tab'e baki sannan tace " to katashi ka lek'a kagani ko wani d'an uwan naku ne tunda naji ance
Yayanta , Kawu tuni ya mik'e dan fita yaga waye ke neman Hanan d'in ......
Lokacin da Yaron da Zunnur ya aika yadawo masa da zancen wai ance ta dad'e dayin aure
sai da yaji k'irjinsa ya buga , sake tambayar Yaron yayi yace " Hanan kace kuwa ? saiga Kawu
Idi ya fito yana duban Zunnur d'in sannan yace " Sannu da zuwa d'an samari amman bangane
daga inah ba , Zunnur ya gaida Kawu cikin girmamawa , shima amsawa yayi cike da sakin
fuska , Zunnur yace " ni d'an gidan Yayan Ammin Hanan ne daga Lagos , nazo ne inga lafiyar ta
shine abinda yakawoni , Kawu najin hakan ya canza Fuska sannan yace " au to dan na
d'aukota shine aka ce muku bata cikin k'oshin lafiya ? To kasani nafi kowa iko da Hanan shiyasa
naje na d'aukota kuma na Aurar da , wata irin zabura Zunnur yayi yana duban Kawun , cikin
wata murya yace " wanne irin aure kuma ? Hanan d'in nawa take da zaayi mata Aure
fisabililkahi , Kawu yadubi Zunnur yace " sokake saita janyo abin kunya za'ayi mata kenan , to
kasani banshirya d'aukar rainon shege ba a gidana , inaso inka koma ka shedawa Uwar tata
cewa na aurar da Hanan , kuma dama ai nine ma d'aurin aurenta ba wani ba , Zunnur wanda
yakejin zuciyar sa nawani irin tafasa saboda Takaici , jiyake tamkar ya shak'o wuyan Kawun
Hanan d'in ya haushi da duka saboda abinda yayi , taya zai aurar da Hanan alhalin
Mahaifiyarta ma bata saniba , Yanzu yazaiyi da soyayyar Hanan wacce a kullum takeyi masa
Barazana tamkar zata haukatashi , tabbas yasan wannan auren ba inda zaije mutuk'ar yana
Numfashi , dan bazai tab'a barin Hanan tayi rayuwar Aure da wani ba indai ba mutuwa yayi ba ,
kallon Kawun yayi yace " inaso arakani gidan Hanan d'in dan inganta , Kawu Idi yadubi Zunnur
yace " kasan bazan tab'a d'aukar k'afa na raka ka gidan Hanan ba , taya ma zakaje musu gida
kana k'ato dakai ko sokake ka kashe mata auren ne ? Zunnur yace "aa taya zan kashe mata
aure daga zuwa ganinta kawai , Kawu Idi k'eme me yak'i yace baza a raka Zunnur gidan Hanan
ba , dole haka Zunnur ya hak'ura yabar k'ofar gidan , cikin gari yashiga dan yasamu Abinci yaci
yasan Abinda zaiyi ......
Su Hanan suna shiga cikin gidan su Suwaiba suka sameta a zaune jingine da pilo a
bayanta, duk ta rame ta koma wata kala tamkar me cutar Hiv. Sallama sukayi ka yi musu iso
sannan suka gaisa da Mahaifiyar ta suka zauna kan shimfid'ar datake kai , Bayan sungaisheta
sukayi mata yajiki , dubansu Suwaiba tayi tana son sanin fuskokinsu sai Nasma tace " Aunty
Suwaiba nice Nasma fa ko kin manta dani ne ? Suwaiba tanajin muryar Nasma tagane ta take
ta tuno da Alhaji Nasir hawaye suka fara fitowa daga idonta , magana tafara cikin wata irin
Murya wacce take nuni da tanajin jiki sosai , cewa tayi " Nasma yakike ya sauran 'Yan uwanki
kuma ? Nasma tace " lafiyalau kowa yake Aunty Nasma , sannan ta cigaba da magana ,
daman zuwa nayi dubaki nida k'awata kuma Auntyna , Suwaiba ta dubi Hanan tace " Nagode
kinji baiwar Allah , Hanan tayi d'an Murmushi tace "bakomi ai yiwa kaine , Nasma ta gyara zama
tace " Aunty Suwaiba wannan d'in da kike gani matar Daddy ce , ya aurota ne bayan yarabu