Showing 21001 words to 24000 words out of 41364 words
dan kama d'aki saidai
Jakar tana gunsa dan bazai iya rabuwa da itaba.......
Hanan harta k'arasa kad'a musu miya amman duk yanayin ta babu dad'i , gashi tunda
tashigo bataga Nasma ba haka tagama ta nufi d'akinta tashiga wanka , tana fitowa tanemi wata
riga marar Nauyi tasaka sannan ta kwanta , tunane tunane tunane tashiga yi akan zamanta a
gidan Alhaji Nasir , tabbas ta tausaya wa Suwaiba mutuk'a Amman yanzu itama abar tausayice
, yau kwata kwata bataje gurin da suke had'uwa suci Abinci ba dan ko yunwar bataji , tunaninta
guda d'ayane shine Aysha dan tasan zata dunga nemanta taga bata ganta ba ....
Washe gari suka tashi dawata annoba a cikin gidan nasu , guda biyu daga cikin yaran Alhaji
antashi dasu duk sun sank'ame ga wani jini nafita ta k'asansu da kuma bakinsu , kafin kace me
tuni sunce ga garinku nan , tuni gida ya cika da koke koken mutuwa , sauran yaran gidan sai
kuka sukeyi na rashin 'Yan uwansu , tashin Hankalin da Hanan tashiga ita da Nasma yayi yawa
, tuni suka keb'e waje guda suka fara tattaunawa akan Mutuwar yaran....
Hanan datake sharar hawaye tace " wallahi nafarajin tsoron zama a cikin gidan nan , cikin
mutuwar wannan yaran wallahi akwai lauje cikin nad'i , Nasma taja Numfashi tadubi Hanan
sannan tace "Nikaina al'amarin Daddy yafara bani tsoro , tunda aka haifeni a cikin gidan Nan
Ummata ta ajiye ta fice daga cikin gidan nan har yanzu bansan a inda take ba , a gurin Hajiya
Hajjo nataso tun ina k'arama na saba da wahalhalun cikin gidan nan har na girma , ba kalar
matar da bangani a cikin gidan nan Daddy ya aura ba , nasha ganin tashin hankali kala kala
amman bantab'a cin karo dana yau ba , tabbas Mutuwar Abbas da Faruq akwai lauje cikin nad'i
, kuka itama takeyi dan tana son k'annan nata duk daba uwa d'ayace ta haifesuba , Suna
zaune suna tunanin yadda zasu b'illowa lamarin cikin gidan sukaji ana ihu.......
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
17.
'Daukota Alhaji Nasir yayi cak a kafad'arsa yafito , karo sukaci da Hajiya Hajjo yadubeta
yace " ki k'arasa aikin batajin dad'i , baijira amsar taba ya juya ya nufi d'akin Hanan d'in . .....
Wata harara Hajiya Hajjo ta rakasu da ita tare da furta " lallai wannan yarinyar wato ni
zakiyiwa kissa , wallahi zakiyi bayanine ai Alhajin zai fita yabarmu cikin gidan sai kingane baki
da wayo mtsss tashige kitchen d'in .......
Yana shiga d'akin ya shimfid'eta a kan gado tare da d'auko ruwa ya yayyafa mata , wata
ajiyar zuciya tasaki tare da mik'ewa zaune , koda taga Alhaji Nasir sai gabanta yakuma fad'uwa
tafara ja da baya , dubanta yayi na wasu Minty na sannan yace " meyasa kike matsawa baya
saboda kinganni ? sannan kuma fasa k'arar da kikayi itama saboda meye ? Hanan jitayi hanjin
cikinta ya ya mutsa wata gudawa taji tana niyyar zubo mata tuni ta matse k'afarta , wata dabara
ce ta fad'o mata tacewa Alhaji Nasir " dan Allah karka ce zaka kwanta dani wallahi jini nakeyi
kuma banajin dad'in jikina ga aiki inayi , share hawayen fuskar ta tayi tana sunkuyar da kai k'asa
, Alhaji tsayawa yayi sosai yana nazarin maganganunta sannan yace " saboda kar na kusance
ki shine kina ganina kika fasa k'ara ? Hanan ta had'iyi wani muyau k'ut sannan tace " badan
hakan bane saboda kaina yana min ciwone sosai kuma lokacin daka shigo tsoro naji sanake
Hajiya Hajjo ce , take Alhaji Nasir ya gamsu da maganar Hanan yace " inbaki da lafiya basai
kifad'iba akai ki asibiti kya zauna da ciwo , kuma zanyiwa Hajiya Hajjo magana kwata kwata
tadaina sakaki aiki anemo meyin aiki inyaso na dunga biya , tashi tsaye yayi yadubeta sannan
yace " kishirya yanxu Nasma tazo ta rakaki ki ga likita yasa kai ya fita.....
Hanan bin bayansa tayi da kallo tana furta " Allah yafitar dani daga wannan bak'in gidan
naka me tarin hatsari , kuka taci gaba dayi marar sauti tana Allah ya isa tsakaninta da Kawu Idi
....
Alhaji Nasir yana fita ya tsaya yana nazari sosai akan waye ya shigar masa d'aki , ganin
Nasma yayi tazo zata wuce ya kirata , tana zuwa ta rissina tace " gani Daddy , dubanta yayi
yace " kije d'akin Hanan tashirya ki kaita wajen Likitana yabata magani batajin dad'i , Nasma
tace to sannan ta mik'e ta nufi d'akin Hanan d'in...
Nasma na shiga ta tarar da Hanan na zaune sai goge hawaye takeyi , Hanan naganinta ta
mik'e ta rik'o hannun Nasma suka zauna nan tashiga gaya mata komai daya faru tsakaninta da
Alhaji , Nasma tace " yakamata ki nutsu Hanan karya fuskanci mune muka shigar masa d'aki ,
wallahi yanzu mukayi waya da Aunty Suwaiba ita saida tasake gayamin akan inja kunnenki
karki kuskura yagane munsan labarinsa , Hanan tace " wallahi a mugun tsorace nake a cikin
gidan nan , gani nake tamkar Alhaji zai maidamu irin yadda yamaida su Aunty Hindatu , kuka
tasaka sosai tana fad'awa jikin Nasma , ita Nasma Hawaye tashiga yi sosai tabbas tasan Hanan
tafita shiga tashin hankali , domin ita taga abinda yake cikin k'waryar tsafin Daddyn nata dole
zata fita shiga damuwa ......
Rarrashin ta tayi tace " kuka bazai zamo mana mafita ba Hanan , kawai dagewa zamuyi da
addu'a Allah yakaremu da kariyar sa , Yanzu tashi zamuyi muje kiga likitan karya shigo
yasamemu a hakan.....
Safara'u sosai ta canzawa Kawu Idi , kullum cikin neman rigima take dashi saboda yasaketa
, tariga ta k'udurta a ranta mutuk'ar tana numfashi sai tayi rayuwa a gidan Alhaji Nasir ko
tahalin k'ak'a , yauma tunda tatashi take cika tana batsewa , can wata dabara ta fad'o mata
akan tasan yadda zatayi tasamu Number Alhaji Nasir , lokacin Kawu Idi na kwance cikin d'aki
Safara'u ta shiga , wani murmushi ta k'ak'alo na kissa ta nufi wajensa , tuni Kawu Idi yafara
murna cikin ransa sayake Safara'u ta sauko yanzu , da jikinta ta rud'esa har saida ya gamsu da
ita sannan ya mik'e ya nufi toilet yin wanka , yana fita tayi sauri ta d'au wayarsa ta nemo
Number Alhaji Nasir ta kwafa , tana gama kwafa ta ajiye sannan ta tashi tafita daga cikin
d'akin.....
A b'angaren Ammin Hanan kuwa tunda ta tare gidan Alhaji Murtala bata da wata matsala ,
kawai dai kullum cikin tunanin Hanan take da yawan mafarkinta , zaman su lafiya lau da
Abokiyar zamanta da kuma mijinsu , Hajiya Asma'u bata da damuwa ta d'auki Ammi tamkar
'yar uwarta sun had'e kansu , 'Ya'yan Hajiya Asma'u hud'u dukansu bawasu Manya bane ,
kamar kullum yauma suna zaune su uku a palor suna hira Alhaji Murtala yace " wai Hadiza
yaushe zamuje Jos muga 'Yar tamu ne ? Ammi itace Hadiza , k'asa tayi da kanta tana
murmushi batare da tabawa Alhaji Murtala amsa ba , Hajiya Asma'u jin an ambaci Jos saida
k'irjinta ya buga , ko kad'an batason sunan garin bare wata k'addarar ta maidata , kallon Alhajin
tayi sannan tace " wai dama Hanan A jos ake rik'onta ? Alhaji yace " a can ake rik'onta wajen
k'anin Babanta , Hajiya Asma'u tace " yakamata ace kuje kuganta daga nan kunga kwataho
manada ita muma muganta , wani dad'i Ammi taji cikin ranta yadda taga suna son 'Yar tata
wacce ko ganinta basu tab'ayi ba , Nan Alhaji Murtala ya tsaida maganar k'arshen sabon wata
zasuje suganta , sosai Ammi taji dad'i har saida tayi murmushi , nan suka shiga tsokanar ta
kafin Alhajin yatashi ya fita .......
Hajiya Asma'u take zuciyarta tafara tunano mata rayuwar datayi a jos , haka kawai taji
zuciyarta duk ta dagule mik'ewa tayi tacewa Ammi zataje ta kwanta....
Bayan Hanan sunje Asibiti Likita yadubata sannan yabata Magani , bayan sunfito daga
asibiti a hanya Hanan ta dubi Nasma tace " Nifah inajin bazan koma gidan kuba , daga nan
zanwuce duk inda Allah yakaini , dubanta Nasma tayi a tsorace sannan tace "haba Aunty
Hanan wanne irin maganace wannan haka ? kinsan abinda kikeson yi kuwa ? ko kinmanta
waye Daddy tsafi fa yakeyi kinga kuwa duk inda kikaje saiya dawo dake garesa , ko kinmanta
da labarin da Aunty Suwaiba ta bamu , ko kuma kinaso kikamu da ciwo irin na Aunty Suwaiba
ne ? dan Allah kiyi hak'uri mukoma gida inyaso sai musan ta inda zamu b'illo wa lamarin ,
Hanan ta tsaya tana duban Nasma sannan tace " Nasma kinaso muma a waye gari damu
munkoma tamkar su Aunty Hindatu ? koda yake banga laifinki na rashin damuwa da halin da
muke cikiba , ke kinsan bazai tab'a yi miki komai ba , sannan kina sane da ta inda Daddyn naki
yake kusanta ta , inhar zanci gaba da zama wallahi sai narasa raina koda azabar mu'amala dani
ta baya , Nasma tace " karki manta da cewa 'Yayansa ma Alhaji ba k'yalesu yayi ba , ko
kinmanta su Abbas daya badasu suma , inaso kisani guduwar da zakiyi itace zata janyo yayi
miki wani mugun abun , kinga kenan wanda ki zauna muci gaba da addu'ar neman mafita .......
Da wannan shawarwari Nasma ta shawo kan Hanan suka koma gida .....
Alhaji Nasir yana tare da wani Abokinsa suna aikata tsafinsu kiran wayar Safara' u ya shigo ,
baid'aga ba har saida aka bashi umarni dodon tsafinsu sannan ya d'aga , Kashe murya
Safara'u tafara tare da shedawa Alhaji tanason magana dashi , Alhaji Nasir yace " kiyi hak'uri
ina aiki zankira zuwa wani lokacin , katse wayar yayi batare da yajira amsar tana , nan dodon
tsafinsu ya kawo hoton Safara'u tare da cewa Alhaji Nasir ya amince mata dan suna son amfani
da jinin mace irinta.........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
βν ΌνΏ» *MD*.
16.
Muryar Nasma taji tana cewa " me ya kawoki Hanan kinsan irin hatsarin da muke ciki kuwa
? sai sannan Hanan tayi ajiyar Zuciya tare da fitar da wani gauron numfashi , jiyowa tayi ta dubi
Nasma tare da fad'awa jikinta tasaka wani kuka marar sauti , cikin kukan take cewa " Aunty
Nasma dan Allah kifitar dani daga wannan gidan , kinsan meye acikin k'waryar can kuwa ? to
wallahi kawunan su Aunty Hindu ne a ciki dukansu jini nafitowa ta idanunsu , da sauri Nasma
tad'ago da Hanan tana fad'in " dagaske kike Hanan su Hindatu ne cikin waccan k'warya ? kai
Hanan ta gyad'a mata batare datayi magana ba , wani tsoro ne yakama Nasma a hankali ta nufi
wajen zata lek'a , motsin shigowa sukaji da alamar anshigo cikin d'akin , da sauri Nasma tayo
baya tare da jan hannun Hanan wacce tuni tafara sakin fitsari saboda tsoro , Bayan labule suka
shige tare da d'auke numfashinsu.....
Alhaji Nasir ne ya shigo tare da wani Matashin saurayi wanda bazai wuce 25 year ba , suna
shigowa Alhaji yafara cire kaya shima saurayin haka , Nan sukayi wannan d'an lungun suka fara
aikata Mad'igo abinsu , su Hanan mutuwar tsaye sukayi dan komai akan idonsu akeyi , Hanan
kuwa hawaye tuni ya kuma wanke mata fuska , wata k'ara Saurayin nan yasaki shida Alhaji
sannan suka juye Abinsu cikin k'warya , Sake komawa sukayi suna surutai tare da fara wani
zance , Nasma tuni tarik'e Hannun Hanan suka dunga bin labule harsuka k'araso k'ofah ,
dasauri suka bud'e zasu fita a dai dai lokacin Alhaji ya kallo wajen jin ana motsi , giftawar
mutane yagani sunfita da gudu aikuwa tuni hankalinsa ya tashi yad'aga wannan saurayin sai dai
lokacin da yataho k'ofar tuni su Hanan sun fice daga ciki .....
Alhaji cikin ransa yake fad'in " wato daman ana shigo masa d'aki har ana ganin sirrinsa , to
suwaye da irin wannan k'ok'arin ? tabbas saiya nemo ko suwaye dan dole a cikin gidan nan
suke.......
Hanan da Nasma suna fitowa da sand'a suka shige d'akin Hanan , Kowacce kanta ya kulle
sunkasa furta komai , can Nasma ta nisa tace " tabbas lokacin barin gidan mu yayi Hanan ,
nikaina da bansan dangina ba na wajen Uwa dole nabar gidan nan, bazan iya zama anaci dani
da haram ba kuma kud'in tsafi , Hanan tace " kema kenan dayake mahaifinki inah gani kuma
tabbas da da hali yau zanbar gidan nan na gudu wajen Ammina , Nasma ta dubi Hanan tace "
a wajen fitowar mu Daddy yaganmu dan naga lokacin daya juyo , sai dai baiga jikinmu ba
motsin fitar mu kawai yagani , dan haka barin gidan mu adai dai lokacin nan bazai yuwuba ,
yanzuma haka tashi nakeso nayi na wuce d'akina dan karya fito yayo nan d'akin yaganmu ,
Hanan tuni taji wani tsoro ya kamata tace " dan Allah inbiyoki d'akinki Aunty Nasma wallahi
tsoro nakeji , Nasma tace " zaman mu waje d'aya yanzu hatsarine kiyi hak'uri ki zauna a d'akin
ki , kawai abinda nakeso dake kiyawaita addu'a , ji sukayi anyi sallama muryar Islam d'aya daga
cikin 'Yayan Alhajin tace " Aunty Hanan kizo inji Hajiya Hajjo zaki d'ora girki , Nasma ta dubi
Islam tace " kice gatan zuwa kuma karki nuna kinganni cikin d'akin nan kinji , kai Islam ta d'aga
alamar taji sannan tafita , Hanan ta dubi Nasma tace " wallahi bazan iya girkiba banajin dad'in
jikina , dafa kafad'ar ta Nasma tayi sannan tace mata " ki daure kije kiyi zamanki cikin d'akin
shima hatsari ne , kuma indai naga bakowa ai zanzo intayaki , tashi kije nima yanzu zantaho ,
Nasma sai da ta lek'a taga babu kowa sannan tafice daga d'akin......
A can Lagos kuwa tuni Abban su Zunnur ya d'aurawa Ammi aure da wani Abokinsa , Ammi
kwata kwata batason auren dan ita haryanzu bata cikin nutsuwar ta , tuntafiyar Hanan haryanzu
bata k'arajin muryar 'Yar ta ko kuma ganinta ba , tabbas tasan Hanan duk inda take tana
buk'atar taimako ajikinta taji hakan , Haka tatare da k'udurin bayan kwana biyu zata tambayi
mijinta taje Jos tagano 'Yarta ........
Alhaji yana fitowa daga b'angarensa ya shiga zagaye cikin gida dan gane waye yake shigar
masa d'aki , Hajiya Hajjo yaci karo da ita tana zaune tana yanke farce , dubanta yayi yace "
Hajiya niko bakiga wasu sun gilma ta nan ba ? Hajiya Hajjo ta d'ago ta dubesa sannan tace "
wasu kuma Alhaji to kamar suwa ? wucewa yayi yana fad'in " barsu kawai bari naje .....
Kitchen ya nufo ganin hayak'i yasan girki akeyi , Hanan ta sunkuya tana gyara wuta taji
anrik'eta ta baya , yadda taji rik'on tagane ba Nasma bace Wannan dagaji Namiji ne , da sauri ta
juyo sukayi ido biyu da Alhaji aikuwa sai taga tamkar shima jinin fitowa yake daga cikin idonsa ,
wata k'ara tasaki tare da jan baya zata fad'i da sauri Alhaji ya rik'ota tayo jikinsa a Sume , Take
Alhaji Nasir yasaka ayar tambaya akanta , meyasa dan tagansa zata yi irin wannan k'ara ?
............
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³ν ½ν±©ν ΌνΏΏβν ΎνΆ³
*Zee* *MD* βν ΌνΏ»
18.
Bayan Alhaji Nasir yagama ganawa da dodon tsafinsu fitowa yayi daga cikin dak'insa ,
darak d'akin Hanan ya nufa dan tabiya masa buk'ata , Yana shiga yasa meta a takure a jikin
gado ta had'a kai da guwa tana goge hawayen idonta , motsin shigowa d'akin da akayi yasa ta
d'ago kanta a muk'ar tsorace , ganin Alhaji Nasir ba k'aramin fad'uwar gaba tayi ba , da sauri ta
mik'e tsaye tamkar zata zura da gudu , yana k'arasowa tana matsawa a haka har ta k'urewa
bango , dab da ita ya k'araso numfashinsu na dukan juna yace " meyasa kwana biyun nan kike
guduna ne ? cikin zuciyar Hanan tace " kaid'in matsafine mugu azzalumi , a fili kuma shuru tayi
batare da ta tanka masa ba , ganin hakan yasa Alhaji Nasir fincikota a zuciye ya jefata kan gado
tare da danneta da