Showing 1 words to 3000 words out of 11442 words

Chapter 1 - TSATSUBA BOOK 1 COMPLETE Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf

TSATSUBA
Book 1
Part A
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.


Marubucin ya fara da cewa....
Sarauniya Larbisa ta kasance gagarumar attajira, kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata
kasa babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya girma da yawan jama ah a zamaninta
sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA
domin duk kasar da suka durfafa da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta babbar
matsalar sarauniya larbisa itace bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun tabbatar mata da
cewa ba zata taba haihuwa ba sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya idan kuwa
tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo mata wani littafi mai suna
TSATSUBA wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata.
.
Asalin wannan littafin mallakin sarkin bokayan Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro
dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba'in daya rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa
littafin lakabi da suna TSATSUBA. Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma makarinsa
na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da suka gabata bokayen duniya da
yawansu suka bazama neman wannan littafi har suka hallaka bisa wannan tafarkkuma duk
wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin. Lokacin
da sarauniya sarauniya Larbisa taji wannan batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya
dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya bayan tayi dogon tunani da nazari saita
watsa shela a ko ina a cikin duniya cewa duk wanda ya samo mata wannan littafin na
TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya shidai
wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya
hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan
dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai suka bazama neman littafin TSATSUBA suka
rinka mutuwa a kokarin neman nasa.
.
Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa sarauniya Larbisa littafin TSATSUBA alhalin
yasan cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya mallakarta kuma zai sami kowace irin
dukiya da yake so ko matsayi?
.
Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar
gimbiya Larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci data bayar da shelar a nemo mata littafin
TSATSUBA shekaranta ashirin daidai a duniya kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau
kan karagar mulki. .
Sarauniya Larbisa bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin tsufa ya risketa don

kada mulkinta ya tafi hannun wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage a irin zuri ar
gidansu. Wata rana sarauniya Larbisa na zaune a fadarta ana tafiyar da harkokin mulki kamar
yadda aka saba saiga wani almajiri ya shigo yana bara har dakaru sun tareshi zasu koreshi
waje sai sarauniya Larbisa tayi musu tsawa suka kyaleshi nan take Larbisa ta mike tsaye daga
kan karagar ta taka taje har wajen almajirin ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace zan baka
abinci kaci ka koshi yanzu ya kai wannan tsoho amma ba zaka iya biyana ba da komai domin ni
bana bukatar abinci ko dukiya koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta ja tsohon
har zuwa cikin gidan sarauta. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta mutanan gari da
sauran masu fada aji saboda ita dai sarauniya larbisa bata kasance mai tausayi da jin kan
talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar da abin hannunta face akan bukatarta
kawai.
.
Lokacin da sarauniya Larbisa takai wannan almajiri cikin babban falo na turakarta wanda
girmansa yakai na wani gida guda sai tsohon ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalle
domin bai taba tsintar kansa a cikin waje mai ni ima da daula ba irin wannan gaba daya falon a
shimfide yake da wata irin dadduma mai tsananin laushi da zarar ka taka daddumar sai kaji
kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi kujerun dake zagaye a falon gaba daya anyi sune da
zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu. A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun
dawisu akayi shi da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima ruwa
na ta zuba a cikin dawisun yana taruwa akan wani katon faranti na lu'u lu'u abin dai akwai ban
sha awa da ban al ajabi.
.
A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya wadanda suma da lu u
lu u akayisu sai sheki da walwali suke tayi. Baya ga wannan wani irin kamshi na tashi a cikin
falon wanda mutum bai san ko daga ina yake fitowa ba duk inda almajirin ya duba a cikin falon
sai yaga kuyangi ne tsala tsala sunata hidimar goge goge da gyare gyare tabbas wannan wuri
Ya cika aljannar duniya. Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini ainun ya ga cewa shidai
bai kasance basarake ba ina shi ina zama akan irin wannan kujera kawai sai ya zauna a kasa
dirshan bisa wannan darduma mai taushi koda ganin haka sai sarauniya Larbisa da kuyanginta
suka bushe da dariya domin basu taba ganin wanda yayi wannan kauyancin ba. Sarauniya
Larbisa ta dubi shugabar kuyangin wacce ake kira da suna HULAIRA tace da ita aje a kawowa
bakona duk irin kalar abincin dake gidan nan hulaira tace an gama ya shugabata nan take
hulaira ta juya ta fice daga cikin falon ita kuma sarauniya larbisa saita dubi almajirin tace bayan
ka huta zan dawo gareka da yamma domin muyi yar hira kafin na sallameka ka tafi saboda
kazo mini da bayani wanda yaje fani a cikin wasi wasi da kace idan na ciyar da kai zaka ciyar
dani har abada alhalin ni babu abinda na nema na rasa na gada abinci ko dukiya lallai ba zaka
tafi ka barni a cikin duhu ba saika wayar mini da kai.
.
Koda gama fadin haka sai sarauniya ta wuce izuwa can cikin turakarta sai data jima tana tafiya
sannan ta kule almajirin ya daina hangota nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa a
ransa wai shin yaya cikin turakar sarauniya zai kasance a kyau da kawatuwa?
.
Lallai dole ne ya ninka nan falon a komai jim kadan da tafiyar sarauniya Larbisa saiga wadansu

kuyangi daban su goma sha biyu sun shigo cikin turakar kuma kowacce na
dauke da katon faranti abinci akan kowanne faranti akwai abinci kala shida nan take kuyangin
suka ajiyewa almajirin farantin abincin a gabansa suka juya suka fice.
.
Al amarin daya firgita gaba dayan kuyangin dake cikin falon kenan suka fara tunanin anya kuwa
wannan almajirin mutunne a iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin
mutumin da ya taba cinye koda kwano daya na abincin kasancewar kwanukan manya ne kuma
cike suke taf da abinci sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye kwano daya lokacin da
almajirin ya gama da abincin farantin dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya gwamutsa
abincin kwanon shidan akan farantin duka ya kama ci nan da nan ya karar da abincin ya janyo
faranti na uku koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin suka firgice suka ruga wajen falon a
dimauce suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin.
.
Abu dai kamar wasa sai da almajirin ya cinye gaba dayan abincin dake kan farantin yayi gyatsa
dama an kawo masa ruwan inibi cikin tambulan guda koda ya kafa tambulan din a bakinsa sai
yayi masa kurba uku ya zukeshi duka shi kuma wannan tambulan din sau tari idan aka cikoshi
da ruwan inibi komai yawan bakin da sukazo gidan basa shanye shi gaba daya sai kaga sun
rage wani abu sa adda kuyangi sukaga almajirin ya cinye gaba dayan abinci kuma ya shanye
ruwan inibin sai suka kara dimaucewa suka ruga izuwa cikin gidan sarautar suna ihu da fadin
cewa tabbas Aljani ne a cikin falon sarauniya ba mutum bane koda jin wannan bushara sai
dakarun tsaro na gidan sarautar suka zare makamansu suka ruga zuwa cikin falon sarauniya
larbisa suka yiwa almajirin kawanya.
.
Al amarin da ya matukar baiwa almajirin mamaki kenan kuma ya tsorata shi domin bai san laifin
da ya aikataba har akazo aka yanyameshi haka.
.
Ana cikin wannan haline sarauniya Larbisa taji wannan abin Al ajabi sai itama ta cika da
tsananin mamaki cikin hanzari ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta taho cikin falon
nata da shigowarta cikin falon ta iske dakarunta sun yiwa almajirin kawanya suna tsuma ba tare
da sun afka masa ba ga dukkan alamu suma sun tsorata ne bisa ganin gagarumin aikin da yayi
nan take sarauniya larbisa ta dakawa dakarun tsawa suka ja da baya har ta hango almajirin
zaune a tsakiyar su yana kyarma cikin alamun tsananin tsoro har ya jike sharkaf da gumi.
.
Al amarin da ya baiwa sarauniya larbisa mamaki kenan nan take ta gamsu a cikin zuciyarta
cewa lallai wannan almajiri ba aljani bane mutum ne domin inda aljani ne babu abinda zai sa ya
tsorata bisa ganin dakarunta izuwa kansa Larbisa ta dubi dakarun nata da dukkan kuyangin
dake cikin falon tace kowa ya fita ya barsu cikin gaggawa suka bi wannan umarnin falon yayi tsit
tamkar mutuwace ta gifta.
.
A wannan lokacine sarauniya larbisa ta tashi taje har daf da almajirin ta zauna tana mai yi masa
wani irin kallo na rashin yarda tace yakai wannan tsoho bani labarinka ka sanar dani komai bisa
gaskiya idan kuwa kayi mini karya ba zaka fita daga nan a raye ba. Lokacin da almajirin yaji
wannan tambaya sai yayi ajiyar numfashi nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye

ya zubo masa sannan ya dubi sarauniya yace ni dai sunana HUZAILATUL MARWASU kuma na
fito ne daga can kudancin duniya a wata kasa da ake kira MADINATUL SAUWABA mahaifina
ya kasance kasurgumin matsafi wanda yayi nisan kwana a duniya domin sai da ya shekara dari
hudu da arba in da uku a duniya sannan ya mutu lokacin ina da shekara shida kacal a duniya.
Duniya kuma nine dan auta kuma tun ina jariri uwata ta mutu ta barni a wannan lokaci ragowar
yan uwana su hudu duk sun haura shekara ashirin sai mai ashirin da yaya wadannan yayye
nawa sun taso da hikima gami da saurin daukar ilimin tsafi a wajen ubanmu nan da nan
kowannansu ya zamo shahararren boka ni kuwa saina taso da dakikanci duk abinda aka koya
mini bana iya yi ko karanta mini dalasiman tsafi mahaifina yayi bana iya biyawa kamar yadda ya
biya haka kuma na kasance malalacin gaske bana iya yin aikin komai ko da kuwa sharar gida
ne bisa wannan daliline sauran yan uwana suka tsaneni bugu da kari saina taso da tsanancin
cin abinci mai yawan gaske amma kuma idan naci na koshi ina iya yin kwana ashirin da daya
ban kara cin komai ba sai dai nayi ta shan ruwa wani abin mamaki kuwa shine a tsawon kwana
ashirin da dayan bana kawai da bukatar bawali ko bayan gida sai dai ta kai cewa an cinye gaba
dayan abincin dake gidanmu wanda mahaifimu ya tanada a rumbu wanda a takaice zamu
iya.shekara goma muna amfani dashi duk wani halaiya tawa bata taba sa mahaifina ya tsaneni
ba face ma yana dada nuna mini soyayya da janyoni a jikinsa su kuwa yan uwan nawa sai haka
yasa suka dada tsanata ya zamana cewa idan mahaifinmu ya aikemu cikin gari ko kasuwa sai
suyi mini dukan tsiya akan hanya wani lokacin ma dukan kawo wuka sukeyi mini har sai jama ar
gari sun kwaceni sai dai a dawo dani gida jina jina kafin a kawoni gida sai yan uwan nawa su
rigani komawa suce da mahaifinmu sun hadune da abokan gabarmu yayan wani bokan garinmu
an fafata yaki sau uku hakan na faruwa don haka sai mahaifin nawa ya hanani fita ko ina ya
zamana cewa kullum muna tare dare da rana ko barci mahaifina zaiyi sai ya tabbatar da cewar
ina kwance akan kirjinsa...

Zan dakata anan sai kuma gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu a huta lafiya.

TSATSUBA
Book 1
Part B
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.


A kullum idan na tuna irin yanayin halittar da na taso ciki na dakikanci lalaci da cin tsiya saina
kamu da tsananin bakin ciki nayi ta kuka shi kuwa mahaifin mau sai yayi ta rarrashina yana mai
cewa ya kai dana kayi sani cewa akwai ranar da zaka rabu da duk wadannan matsaloli amma
sai a bayan mutuwata bayan kayi wata doguwar tafiya lallai kafin mutuwata zan sanar dakai
bangaren da zakaje a cikin duniya domin ka rabu da wannan matsaloli A sannan ne zaka sami
wata gagarumar daukaka irin wacce ni kaina ban samu ba kayi hakuri da duk irin musgunawar
da yan uwanka zasuyi maka daga nan har izuwa ranar mutuwata domin hakuri naka shine zai
kaika izuwa kan tafarkin daukakarka nasan cewa yan uwanka basu da wani buri wanda yafi su

hallakaka saboda ya zamana cewa ba zaka mallaki komai ba daga cikin dukiyar dana tara babu
yadda basuyi ba don su hallakaka amma sun kasa domin ina baka kariya ta musamman duk
abin dake faruwa ayayin da kuka fita kasuwa ina gani daga nan a cikin madubin tsafina duk sa
adda kaga jama ar gari sunzo sun ceci rayuwarka daga hannun yan uwanka toba mutane bane
sukazo nine na rikide zuwa siffar mutane nazo na muku, wannan bakar wahalar da kake sha a
hannunsu itace alamun samun daukakarka tanan gaba.
.
A duk sa adda mahaifin namu yazo nan a zancensa sai na fashe da kuka nace ya kai abbana
yanzu idan ka mutu waye zai iya ci gaba da ciyar dani alhalin yanzu kana ciyar da nine da karfin
Sihirin tsafinka ?
Idan baka nan ya za ayi na tsira daga sharrin yan uwana?
.
Dajin wannan tambaya sai mahaifina yayi murmushi yace nayi maka alkawari ko a bayan raina
ba zaka fuskanci matsalar komai ba kuma ba zaka sha wahalar komaiba sannan wahalar ba
zata yi dogon lokaci ba.
.
Haka dai mahaifina yaci gaba da rarrashina yana bani mamaki a duk sa adda nake cikin
damuwa ko tashin hankali wata rana da farkon dare sai mahaifina ya kamu da matsananncin
rashin lafiya har ya kama kumallon jini nan fa muka hadu mu biyar din a kansa a lokacin da
hankalina ya yi matukar dugunzuma na fara kuka su kuwa sauran yan uwan nawa ko kadan
babu alamar wata damuwa a fuskarsu kawai sai suka kama yake mahaifin namu ya dubi sauran
yan uwan nawa yace dasu ku tafi izuwa cikin daji ku nemo mini ganyen bishiyar Suljara Shine
kadai abinda za a jika mini nasha na sami sauki koda jin wannan batu sai hankalin yan uwan
nawa ya tashi babban cikinsu ya dubi mahaifin namu cikin Alamun matukar damuwa yace yakai
abbanmu ka sani cewa bishiyar suljara yana da matukar wuyar samu a duk cikin dazuzzukan
garinmu zamu iya kwana a cikin daji muna nemansa dajin haka sai mahaifinmu ya fusata yace
shin yanzu wahalar da zaku sha a cikin daji tafi lafiya ta muhinmanci kenan a wajanku idan har
ba zaku tafi neman wannan ganye ba yanzu take zan lalata dukkan sirrin tsafin da kuka mallaka
kuma ta kone dukkan dukiyata dake cikin gidan nan koda jin wannan batu sai yan uwan nawa
suka juya suka fice daga cikin dakin suna gunaguni cikin fishi sai bayan yan uwana sun dade da
tafiya daji sannan mahaifina ya mike zaune da kyar sannan ya janyoni izuwa jikinsa ya
rungumeni akan kirjinsa kawai sai naji hawayen idanunsa na zuba akan fuskata cikin karfin hali
ya budi baki yace yakai dana ka saurara Da kyau ka nutsu kaji jawabin da zan maka idan har ka
ka rike abin da zan gaya maka yanzu lallai zaka sami daukakar da tafi tawama kayi sani cewa
na aiki yan uwanka ne izuwa daji domin na sami damar da zan sanar dakai babban sirrin dana
adana maka a cikin zuciyata tsawon shekara da shekara ka sani cewa tsananin kaunarka da
tausayinka da nake ji bisa.yanayin halittar da ka kasance ne yasa na adana maka wannan
babban sirri. A yau kuma nan bada dadewa ba wa adina zai cika na bar wannan duniya da
zarar kaga na mutu kayi sauri ka shiga cikin turakata ka dafa bakin akwatina na karfe da
hannunka na hagu take akwatin zai bude zakaga wata jakar gata a ciki saika dauki jakar ka
ratayata a kafadarka ka fice daga gidan nan, kana fita zakaga gidan nan ya nutse izuwa cikin
karkashin kasa ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba awajen, daga nan sai ka juya ka
nausa yamma kayi ta tafiya har saika fita daga cikin garin nan ka nausa daji, duk iya tsawon

tafiyar da zakayi ka da kayi wage ko da zakaji sukuwar giwaye a bayanka, duk inda ka gamu da
mutum ko aljan kada kayi masa magana kuma idan yayi maka magana kada ka amsa ba zaka
riski wani gari ba sai bayan kwana ashirin da daya , kana shiga garin ka bude wannan jaka zaka
iske babu komai a cikinta face dinare mai yawan gaske saika nemi abinci mai yawa wanda zai
isheka ka koshi ka siya amma ka tabbata cewa a boye zaka cinye wannan abinci ba a gaban
jama ba, kada ka kuskura ka kwana a wannan gari da zarar ka koshi saikayi harama ka sayi
doki kahau kaci gaba da tafiya ina mai tabbatar maka da cewa saika shekara Arba'n da biyar
kana wannan tafiya kana ta keta dazuzzuka da birane a sannane zaka cika shekara hamsin da
daya a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login