Showing 3001 words to 6000 words out of 11442 words
Chapter 2 - TSATSUBA BOOK 1 COMPLETE Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
duniya kuma a wannan lokacine guzurin dake cikin jakarka zai kare, ka iso wani babban
birni inda wata mashahuriyar sarauniya ke mulki. A sannan ne yunwa zata gallabeka don haka
ka nemi hanyar gidan sarauta kana zuwa fada ka wuce kai tsaye zuwa gaban karagar mulkin
kana mai yin bara kana cewa waye zai ciyar dakai yanzu ni kuwa na ciyar dashi iya rayuwarsa?
.
Tabbas wannan sarauniya zata sa a baka abinci da zaka koshi bayan nan ka tambayeta babban
burinta na duniya lallai zata zo maka da batun wani littafi waishi TSATSUBA lallai kaine zakayi
jagora bisa tafiyar da za ayi ta neman wannan littafi tabbas za a samu wannan littafi har bukatar
wannan sarauniya ta biya a sannan ne zaka sami lada mai tsoka daga wajan sarauniyar kamar
yadda tayi alkawarin zata bayar ga wanda duk ya samo mata littafin TSATSUBA,
.
A cikin tafiyar da zakuyine zaka sami daukaka irin wacce babu wani boka da ya taba samunta
har duniya ta shube ba za a manta da kaiba
a cikin tarihi, amma ka sani cewa zaka sha tsananin ukuba a cikin wannan tafiya kuma zakuga
abubuwan Al'ajabi da yawa.
.
Sa adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na cika da Tsananin mamaki na dubeshi cikin
alamun rashin fahimta nace ya kai abbana yanzu nida nake malalaci matsoraci kuma dakiki ya
za ayi na iya jagora a cikin wannan gagarumar tafiya alhalin ma ban san inda za a je ba asamo
wani littafi wai shi TSATSUBA? .
Yayin da mahaifina yaji wannan tambaya saiya ya yunkura domin ya bani amsa amma sai tari
ya sarkeshi yaci gaba da aman jini, Al amarin daya dugunzuma hankalina kenan na dimauce
naci gaba da matsanancin kuna ina mai kankame mahaifina, daga can saiya daina wannan
kumallon sannan ya janyeni daga cikin jikinsa muka fuskanci juna sosai a lokacin da idanunsa
ke lumshewa yana budewa da kyar ya budi baki yace yakai dana abin kaunata kayi sani cewa
muddin kana tare da wannan jaka ta guzurinka babu abinda zai gagareka kuma babu wani
tsautsayi da zai saka rasa rayuwarka.
.
Sai kun shekara daya da rabi sannan zaku isa inda littafin TSATSUBA yake kuma wannan jaka
taka itace zata rinka yi muku jagora , ba zaku sami nasarar zuwa inda wannan littafi yake ba sai
kun hadu da wadansu jarumai guda hudu, uku mata ne daya namijine ma abota wani addini da
ake kira musulunci, wannan jaka taka itace zata kaiku wajen wadannan jarumai guda hudu, sa
adda naji wannan batu saina kara cika da mamaki bisa yadda za ace jaka zatayi magana a cikin
wannan doguwar tafiya alhalin bata kasance abu mai raiba kuma ba magana takeyi ba har na
budi baki zan tambayi mahaifina ta yadda wannan jaka zatayi mana jagora a cikiin tafiyar sai
naji gaba dayan jikinsa ya sandare kamar gunki idanunsa kuwa sun kafe, cikin dimauta na
girgizashi amma ko motsi baiyiba, kawai saina rungumeshi na fashe da kuka cikin sauri na
maida shi shimfidarsa na kwantar dashi sannan na ruga zuwa cikin turakarsa. .
Da shigata sai naje na dafa bakar akwatin mahaifin namu da hannu na na hagu faruwar hakan
keda wuya sai akwatin ya bude nayi arba da wata jaka wadda akayi ta da fatar damisa koda na
dauki jakar sai naji tana da dan nauyi kawai saina rataya jakar a kafadata na fita da sauri daga
cikin gidan, ai kuwa ina fita sai naga gidan namu ya kama nutsewa cikin karkashin kasa har
saida ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine hawaye ya zubo mini saboda na san
cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan uwana har abada yanzu ne zan fuskanci
sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki kamar yadda mahaifina yayi mini
bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba
haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al'ajabi da
yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu
iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga
dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta
tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane
face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar
harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face
tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a
ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa
na tunkari wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina
bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani
dan mitsitsin Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin
firgici na yarda jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan
sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na
yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan
yatsanan hannuna take naga wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai
kyalkyala dariya wani abin mamaki Shi ne mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya
ganin Aljanin kuma ba a jin dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai
HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar
duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA,
nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa'in da tara nine kadai a cikin fadin
duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni
kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne
kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin abincin kuma ka
sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.
TSATSUBA
Book 1
Part C
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.
Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da ke hannunka domin idan na haura rabin sa a a
waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana.
.
Koda gama fadin hakan sai nayi sauri na dauke aljani subauratu da yan yatsan hannuna biyu
ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka sannan na rataya jakar akan kafadata ka
tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da Huzallatul Marwasu yazo nan
a labarinsa sai sarauniya Larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki a karon farko a
rayuwarta sai ta kama Huzallatul Marwasu da hannayanta biyu ta rungumeshi tana mai cewa
tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida Larbisa da huzallatul marwasu suka
shafe sa a bakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare sannan tasa aka kaishi
masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya baiwa larbisa mamaki
shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal Huzallatul Marwasu yayi yace ba zai iya cin komai
ba.
.
Sa adda Huzallatul Marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen daki bisa kan luntsumemen
gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin
ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.
.
A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito
fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo
Huzallatul Marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai
tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa
har saiya farka da kansa. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin
sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai Sarauniya Larbisa da fadawanta sukaci
gaba da jiran Huzallatul Marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa
sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan
fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba
cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki Larbisa
ta mike tsaye ta taryo Huzallatul Marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi
sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL
LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine
hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan
uwana har abada yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a
ciki kamar yadda mahaifina yayi mini bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini
a cikinta banyi wasa da guda daya ba
haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al'ajabi da
yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu
iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga
dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta
tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane
face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar
harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face
tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a
ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa na tunkari
wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina bude jakar
duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin
Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin firgici na yarda
jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai
naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na yunkura da nufin na juya
da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan yatsanan hannuna take naga
wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai kyalkyala dariya wani abin
mamaki. Shine mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya ganin Aljanin kuma ba a jin
dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai
HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar
duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA,
nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa'in da tara nine kadai a cikin fadin
duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni
kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne
kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin
abincin kuma ka sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.
.
Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da hannunka domin idan na haura rabin sa a a waje
iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana koda gama fadin hakan sai
nayi sauri na dauke aljani
subauratu da yan yatsan hannuna biyu ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka
sannan na rataya jakar akan kafadata ka tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da
huzallatul marwasu yazo nan a labarinsa sai sarauniya larbisa ta cika da tsananin mamaki da
farin ciki a karon farko a rayuwarta sai ta kama huzallatul marwasu da hannayanta biyu ta
rungumeshi tana mai cewa tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida larbisa da
huzallatul marwasu suka shafe sa abakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare
sannan tasa aka kaishi masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya
baiwa larbisa mamaki shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal huzallatul marwasu yayi
yace ba zai iya cin komai ba sa adda huzallatul marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen
daki bisa kan luntsumemen gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya
kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.
.
A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito
fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo
huzallatul marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai
tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa
har saiya farka da kansa Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin
sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai sarauniya larbisa da fadawanta sukaci
gaba da jiran huzallatul marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa
sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan
fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba
cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki larbisa
ta mike tsaye ta taryo huzallatul marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi
sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL
LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da yaZo ya nemi abincin da zaici a wajena shine
wanda zai cika mini babban burina na duniya koda jin wannan batu sai fadawan suka sake cika
da mamaki larbisa taci gaba da bayani tana mai cewa yaku yan majalisata ina so ku sani cewa
na taraku ne a nan domin na sanar daku cewanan da kwana uku zanyi shiri nida wannan bako
nawa mai daraja domin mu yi tafiya izuwa neman abinda zai biya mini bukatata saboda haka
zan bar amanar kasata a hannunku kuci gaba da tafiyar da mulki kamar yadda nake gudanar
dashi ku sani cewa ina daga can inda nake zan rinka ganin duk abinda kuke yi duk wanda yayi
mini wani abu ba dai dai ba sai dai a wayi gari aga gawarsa idan akwai wani mai korafi a cikinku
bisa wannan hukunci da na yanke sai yayi yanzu naji?
.
Lokacin da fadawan Sarauniya Larbisa sukaji wannan batu sai sukayi shiru suka kama kallon
junansu aka rasa wanda zaice kala koda ganin haka sai larbisa ta sallami dukkanin fadawan
nata suka fita suka barsu su biyu kacal ita da almajiiri Huzallatul marwasu tsawon yan dakiku da
fitar fadawan sai larbisa ta dubi huzallatul marwasu tace yakai dan boka mai daraja ina son ka
fito da in aljani sabauratu ibn kimasasa daga cikin jakarka ta sihiri domin ina da wadansu
tambayoyi masu matukar muhimmanci da nake son zanyi masa dangane da wannan
gagarumar tafiya da zamuyi koda jin wannan batu sai huzallatul marwasu ya fiddo jakar
sihirinsa daga cikin babbar rigar jikinsa ya ajiyeta a gabansa sannan ya bude ya zura hannunsa
a ciki ya dauko aljani subauratu bn kimasasa ya ajiyeshi a kan dan karamin tebur na zinare
dake gaban sarauniya larbisa.
.
Nan take subauratu yayi sujjada ga sarauniya larbisa yana mai bude fukafukansa ya kwashi
gaisuwa sannan yace da ita yake sarauniyar duniya fadi duk irin tambayoyin da kike son ki
gabatar dasu a gareni ko kuwa adadin su yakai na yawan gashin dake jikin rago ko tinkiya
domin babu wata iska anan wacce zata dami tsufana. Lallai zan baki amsoshin tambayoyinki ko
da kuwa zan kwana dubu a zaune ina yi miki jawabinsu koda jin wannan batu sai sarauniya
larbisa ta bushe da da dariya sannan tace aini tambayoyina guda uku ne kacal tambaya ta farko
itace naji Huzallatul marwasu yace abokan tafiyarmu izuwa inda zamu samo littafin Tsatsuba su
hudu ne kuma ukun cikinsu matane na hudun kuma namijine to wai shin menene amfanin
kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya kuma a wane garuruwa zamu riskesu,
.
Tambaya ta ta biyu itace akan wane dalili wadannan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda
suyi mana rakiya zuwa wannan tafiya mai tsananin hadari?
.
Tambaya ta ta uku itace ta karshe shin kasan dalasiman tsafin da za a karanta a lalata gaba
dayan tsafin dake cikin littafin tsatsuba?
.
Sa adda Aljani saubaratu yaji wadannan tambayoyi guda uku daga bakin sarauniya larbisa sai
yayi shiru yana mai kura mata idanu cikin Al ajabi ba wani abu bane ya sa yayi shiru ba kuma
ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta da ya dimautashi.
.
Koda larbisa ta fahimci halin da Aljani saubaratu ya shiga saita daka masa tsawa ta ce shin
zaka bani amsar tambayoyina ne ko kuwa zakaci gaba da kallona ne har saika gaji nan take
Aljani saubaratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa cikin nutsuwa ya ce ki gafarceni ya
shugabata kiyi sani kinyi mini tambayoyi ne masu matukar mahimmanci a cikin wannan
tafiyartamu kuma wadanda zasu dauki dogon lokaci ina yi miki bayaninsu to nima jin wannan
tambayoyi yasa zan dakata sai kuma gobe idan mai duka ya kaimu, a huta lafiya.
TSATSUBA
Book 1
Part D
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan