Showing 6001 words to 9000 words out of 11442 words
Chapter 3 - TSATSUBA BOOK 1 COMPLETE Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
Yaƙi Contact 08138873799.
.
.
Da farko dai abokin tafiyarmu wanda zamu fara tafiya nema ba wani bane face JARUMA
SHUMAIRA yar mafarauci IMSHAL, a halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki wanda yafi
shumaira ibn imshal sanin sirrin daji da iya farauta da kuma juriyar wahala kafin mu isa kogon
kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba sai mun keta ta cikin wadansu dazuzzuka guda uku a
cikin daji na farko sai mun shafe wata shida muna tafiya sannan zamuje karshensa,
.
A cikin wannan daji wanda aka yiwa lakabi da shajarul shaljuma akwai
mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye wadanda kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu hakama
tsafi baya aiki a kansu babu abinda zai ceci mutum daga sharrinsu face wanda ya san sirrinsu
kuma ya kware a iya farauta gami da jurewa wahala lallai idan babu jagorancin jaruma
Shumaira bamu isa mu ratsa ta cikin dajin shajarul shaljuma ba a raye .
Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba kowa bane face jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen
nesa gami da jiyo takun sawu komai nisansa Daji na biyu wanda ke gaban dajin Shajarul
shaljun ana kiransa da suna Ujurul majnan babu komai a cikin wannan daji face wadansu irin
gabza gabzan dodanni masu cin naman mutane da na aljanu da dabbobi suna da kaifin basira
wajan dana mugayen tarkuna kuma suna da tsananin gudun tsiya yadda komai tazarar dake
tsakaninsu da mutum suna iya cinmmasa jaruma larifat ce kadai zata iya gano duk irin tarkunan
da wadannan dodanni suka dana kuma ta iya jiyo sautin sawayen dodannin suke sannan ta iya
jiyo sawayensu a duk sa adda suka rugo don kawo farmaki.
.
Daji na uku wanda ke gaban dajin Ujurul majnan ana kiransa da suna Darul Maut Babu komai a
cikin darul maut face wadansu mugayen kunamai da macizai bakake wadanda da zarar sun
sami nasarar sarar mutum ko harbinsa sau daya take jikinsa ke zagwanyewa ya narke Abokiyar
tafiyarmu ta uku itace jaruma Lubaina Yar sadauki Sulzainu Jaruma lubaina ce kadai zata iya
yakar wadannan kunamu da macizai ta hanasu cutar damu saboda duk duniya babu wani
jarumi mai zafin namanta kuma tana da wata rantsatstsiyar takobi da babu abin da bazata iya
tsargeshi ba koda kuwa dutse ne ko karfe, muna fita daga cikin dajin darul maut Bayan tafiyar
wata Hudu zamu riski Kogon kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba.
.
Ya shugabata kiyi sani cewa shiga cikin kogon kitabul sihir dai dai yake da mutum ya siyi
ajalinsa da kudinsa saboda tsananin masiful dake cikinsa da kuma irin gagarumin tsaron da aka
yiwa littafin tsatsuba babu wanda zai iya samun nasarar shiga har cikin kogon kitabul sihir.ya isa
har inda littafin tsatsuba yake a raye kuma cikin kuzari face jarumi Ruhaisu ibn Zaiyanu daga
Sarkin Birnin Kufa.
.
A halin yanzu duk duniya babu wani jarumi mai karfin damtsensa sannan kuma yana da
tsananin sa a da rabo bisa dukan abinda yasa a gabansa a yanzu haka yana cikin tsananin
bakin ciki bisa mutuwar masoyiyarsa wacce yake tsananin kauna fiye da komai a duniya, duk
da cewa kama da wane bata wane. Ya shugabata ni ina da tabbavin cewar zaki iya yaudarar
jarumi Ruhaisu da tsananin kyawunki ki nuna masa soyayya da haka ne kadai zaki iya ribatarsa
ya amince yayi wannan tafiya har ya shiga cikin kogon kitabul sihir ya dauko mana littafin
tsatsuba.
.
Lokacin da Aljani subauratu yazo nan a zancensa sai sarauniya larbisa tayi shiru tana mai
sunkui da kanta kas ta fada cikin kogin tunani mai zurfi har izuwa tsawon wani dan lokaci daga
can kuma sai ta dago kanta ta dubi Aljani subauratu tana mai ajiyar zuciya tace yakai subauratu
kayi sani cewa hakika kazo mini da babban al amari mai wuyar fahimta da gamsuwa wanda
dole sai dai mutum yayi kundunbala ya aikata shi ni kam babu gudu kuma babu ja da baya a
cikin wannan Al amari amma ina da sauran tambaya guda.daya rak a gareka yanzu wacce idan
ka gamsar dani da amsarta bani da sauran fargaba tambayar tawa kuwa itace tayaya zamu
hada wadannan abokan tafiya tamu su hudu a cikin kankanin lokacin Alhalin kowannansu yana
can wani bangaren daban na duniya har muyi wannan tafiya tare dasu wacce takai ta tsawon
shekara guda?
.
Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya , lokaci guda kuma ya
hada rai yace ai riskar wadannan jarumai hudu a cikin yini daya jal a wajena dai dai yake da
shan ruwa a gareki makurwa daya don haka ki kwantar da hankalinki kawai ki fara shirye
shiryen wannan tafiya. .
Koda jin wannan batu sai fuskar sarauniya larbisa ta fadada da murmushi bata san sa adda ta
kama kyalkyala dariya ba koda ganin haka sai tsoho huzallatu marwasu da Aljani subauratu ma
suka tayata kyalkyala dariyar... Kamar yadda sarauniya larbisa ta fada haka al amarin ya
kasance wato a cikin kwanaki uku dai dai suka kammala dukkan tanadi na wannan tafiya ita da
tsoho huzallatul marwasu suka hau bisa wadansu ingarmun dawakai guda biyu sannan aka
debi dakaru mutum arba in kacal tare da kuyangi goma masu yi mata hidima gami da isashshen
guzuri na abinci da dinare mai yawa aka kama hanya aka fice daga cikin birninta bayanta yiwa
ta yiwa fadawanta da jama arta sallama akan cewar ba zata dawo ba sai bayan shekara guda
sarauniya larbisa tayi shiga ne ta kayan yaki masu matukar kyau da kwarjini kuma ta rufe
fuskarta da wani bakin kyalle idanunta kadai ake gani shi kuwa tsoho huzallatul marwasu kaya
na alfarma aka bashi ya sanya irin na sarakai kai kace ma shine da mulkin ba Larbisa ba
lokacin da wannan tawaga ta shafe sa a uku ana tafiya a cikin daji ba tare da sanin inda aka
dosa ba kuma dama larbisa ce akan gaba saitaja linzamin dokinta ta tsaya cak, Al amarin da ya
baiwa huzallatul marwas da sauran abokan tafiyar mamaki kenan kowa ma ya tsaida nasa
dokin, huzallatul marwas ya risina a gareta cikin girmamawa yace.ya shugabata lafiya kuwa
kika tsayar mana da tafiyarmu a nan?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya larbisa ta dakawa tsoho huzallatul marwas tsawa tace
akan wane dalili zamu ci gaba da tafiyar da bamu san inda muka dosa ba ka yiwa Aljani
Sabauratu ibn kimasasa magana ya gaya mana inda zamu fara dosa domin nemo abokin
tafiyarmu koda jin wannan batu sai huzallatil marwas ya bugi jakar hannunsa take aljani
subauratu yayi magana yace ku nufi kudu zamu gajarce muku tafiyar wata uku izuwa yini biyu
da rabi inda zaku
riski Dajin Falmaz anan ne inda jaruma shumaira take wacce ita ce kadai zata iya wucewa
damu ta cikin dajin shajarul Shaljum a saboda kwarewarta a iya farauta sanin sirrin daji dakuma
jurewa wahala lallai kusan yadda zaku lallami jaruma shumaira a kan ta amince da yin wannan
tafiya tare damu kada ku nuna mata isa ko iko ko dukiya domin in saboda sune ba zata amince
ba koda gama fadin hakan sai aljani subauratu yayi shiru ba kara cewa uffan ba nan take
sarauniya larbisa ta bayar da umarni aka sauya akalar tafiya aka durfafi kudu aka ci gaba da
tafiya ba sassauci bisa mamaki sai kowa yaga tafiyar tana matukar yin sauri fiye da hasashen
mai hasashe kai kace akan isaka suke tafiyar ba bisa doron kasa ba nan da nan suka wuce
dazuzzuka da yawa har magariba ta riskesu basu hadu da wani mugun abu ba a sannan ne
sarauniya ta bayar da umarnin a tsaya a yada zango domin A ci abinci a huta nan take kuwa
akabi wannan umarnin bayan an kafa tantuna an dafa abinci sai sarauniya larbisa ta kirawo
tsoho huzallatul marwas izuwa cikin tantinta domin suci abinci tare koda jin wannan tayi sai
huzallatul marwas ya risina cikin girmamawa yace ya shugabata ashe har kin manta da ka
idata? Ai idan har naci na koshi ba zan sake bukatar abinci ba sai bayan kwanaki ashirin da
biyar sai dai kawai nayi ta shan ruwa koda jin wannan batu sai larbisa tayi murmushi tace
tabbas haka zancenka yake na sha afat ne amma duk da haka bana son kadaici a yanzu zauna
ka debe mini kewa cikin murna tsoho huzallatul marwas ya zauna a gefe guda a lokacin da
sarauniya larbisa ta mike tsam ta kwabe kayan yakin dake jikinta ta ajiyesu a gefen shimfidarta
ta alfarma ya rage daga ita sai wata riga mai shara shara a jikinta wacce ta baiyana dukkan
surar jikinta.
.
Koda tsoho huzallatul marwas yayi arba da wannan kyakkyawar sura ta sarauniya larbisa sai ya
rude ya dimauce har kwallar takaici ta ciko a idanunsa. A cikin ransa yace kash amma mazan
duniya sun yi asara da basu mallaki wannan kyakkyawar mace ba tabbas inda ni saurayi ne
kuma jarumi mai jini a jika to ko da zan rasa rayuwata sai nayi iya kokarina wajen ganin na
mallaki wannan sarauniya ta kowane hali
..
Zan dakata anan sai Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba kada ku manta da comments, likes da
sharing domin hakan shi zai ƙara mana ƙwarin gwiywa.
TSATSUBA
Book 1
Part E
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.
.
https://www.facebook.com/AlQuyraemey360
.
Haka dai tsoho huzallatul marwas ya ci gaba da zancen zuci gami da sambatu har sarauniya
larbisa ta zauna tana mai harde kafafunta a gaban kwanukan abincin dake gabanta ta fuskance
shi, koda tasa hannu ta debo loma guda ta bude baki, huzallatul marwas yayi arba da
kyawawan hakoranta masu tsananin kyau da haske sai ya sake dimaucewa fiye da ko yaushe
bai san sa adda kafafunsa suka kasa daukar nauyin jikinsa ba ya zame kasa kawai sai ji yayi
sarauniya larbisa ta kece da dariya, cikin sauri tsoho huzallatul marwas ya mike zaune yana mai
zazzaro idanu ya dubeta yace ya shugabata ina dalilin yin wannan dariya taki.
..
Koda jin wannan tambaya sai larbisa ta hade fuska kamar zatayi kuka sannan ta ce yakai
wannan tsoho kayi sani cewa ina sane na baiyana surar jikina a gareka ba don komai ba sai
domin na tabbatar da abin
da bokaye suka fada mini idan gaskiya ne cewar babu wani da namiji da zai ganni bai rude ba
saboda kyawuna kaine namijin farko a duniya da ya taba ganin wannan jiki nawa kuma kaima
na yarje maka hakanne saboda ka manyanta a kaina tunda ka isa ka haifi kamata yau shekara
goma sha tara kacal a duniya kuma gashi babu abin da ban mallaka ba najin dadin duniya
tunda gashi ina sarauta ta birnin da babu kamarsa a duniya sannan ina da dukiya mai tsananin
yawan da ni kain ban san iyakarta ba abin da ya rage mini kawai shine na sami abokin rayuwa
wato mijin da zan aura domin na sami magaji bokaye sun tabbatar mini da cewar ba zan taba
haihuwa ba har sai bayan na lalata duk sihirin tsafin da yake cikin littafin tsatsuba bisa wannan
dalili ne na ki yarda nayi soyayya da wani da namiji a rayuwata har sai bayan wannan buri nawa
ya cika. Abinda nake tsoro shine kada soyayya tasa idanuna su rufe har nayi aure ba tare da na
lalata sihirin littafin tsatsuba ba kaga kenan ba zan taba samun haihuwa ba..
.
Lokacin da sarauniya larbisa tazo nan a jawabinta sai tsoho huzallatul marwas yaji ya kamu da
tsananin tausayinta cikin alamun tausayawa da murmai mai sanyi ya dubeta ya ce ya
shugabata hakika akwai tausayi a cikin lamarinki kuma samun biyan bukatarki ba abune mai
sauki ba sannan ina mai shawartarki daki taka tsantsan da wannan kalma ta soyayya domin
abace mai hadarin gaske duk da cewar kin danne zuciyarki kin hanata yin soyayya yanzu nan
gaba zata iya tankwaraki domin shi so abune wanda baya sallama kuma baya iso zai iya
mamayarki a lokaci guda kamar yadda barci yake sace mutum
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da dariya har ta tafa hannayanta.
.
Al amarin da yayi matukar baiwa huzallattul marwas mamaki kenan daga can sai sarauniya
larbisa ta nutsu ta daina dariyar ta dubeshi tace ni sarauniya larbisa na cika maka baki babu
wani da namiji a wannan doron kasa wanda zai burgeni har na kamu da son sa saboda na
tabbatar da cewar duk abinda yake takama dashi na fishi walau kyau, jarumtaka, mulki da
dukiya yayin da huzallatul marwas yaji haka sai yayi murmushi yace ya shugabata abin da yasa
kika fadi haka akwai kuruciya a tare dake kuma bakisan menene so ba to ki sani cewa shi so na
gaskiya babu ruwansa da kyau ko matsayi abu ne kawai na haduwar jini wanda mutum ko aljan
baya iya hadashi ko ya rabashi babu wani mai misali ko mai hange wanda zai iya tantance miki
karfinsa ko yanayinsa face wanda ya tsinci kansa a cikinsa koda huzallatul marwas yazo nan a
zancensa sai ran sarauniya Larbisa ya baci bata san sa adda ta daka masa tsawa ba ta
umarceshi da ya tashi ya fice daga cikin tantinsa.
.
Cikin firgita da biyayya tsoho huzallatul marwas ya risina yace ki gafarceni ya shugabata lallai
nayi kuskure.
.
Nan take ya mike tsaye da sauri ya juya ya fice daga cikin tantin amma a cikin zuciyarsa dariya
yake yiwa sarauniya larbisa yana mai cewa hakika yaro man kaza ne bai san rana ba sai ta
gasashi da sannu zaki san cewa wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi a wannan
wuri da aka yada zango aka kwana sai kashe gari da safe bayan anyi kalaci sannan akayi shiri
aka ci gaba da tafiya ba sassauci
tun da aka fara wannan tafiya sarauniya larbisa bata kara cewa uffan ba kuma fuskarta a
murtuke take ko kadan babu annuri alamar cewa tana cikin fishi.
.
Al amarin da ya dugunzuma hankalin dakarunta da kuyanginta kenan shi kuwa tsoho huzallatul
marwas da yake yasan dalilin fishin nata sai ya kau da kai ga barin kallonta yama kara gaba
yaki yarda su jera tare
yaci gaba da sha aninsa kawai HAKAN NE YASA ITAMA jikinta yayi sanyi kuma taji a zuciyarta
cewar abinda ta yiwa tsohon bata kyauta ba don ya fadi gaskiya amma saboda girman kai irin
na masu sarauta sai ta basar taki yarda tayi masa magana har suka shafe yini na biyu aka yada
zango na biyu. .
A cikin wani daji mai yawan bishiyoyi da duhuwoyi tabbas wannan daji yana da kwarjini gami da
ban tsoro domin komai jarumtakar mutum idan ya tsinci kansa a cikinsa dole ne ya san cewa ya
shigo wuri ma hadari, bayan an kafa tantuna sai sarauniya larbisa ta tara gabadayan
dakarunta ta shaida musu dacewa kada dayansu ya kuskura yayi barci domin akwai alamun
mugayen abubuwa a cikin wannan daji saboda haka wani abun zai iya kawo harin sumame a
yayin da dare yayi koda jin wannan batu sai shugaban dakarun nata wanda ake kira da sadauki
muhairu ya risina ya ce ya shugabata kiyi mini izini mu kewaye sansaninmu da dogayen
manyan itatuwa domin samar da cikakken tsaro kinga indai wani abune mai rai zai kawo mana
harin ba zai samu damar afko mana ba kai tsaye koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi
murmushi tace hakika kazo da shawara mai kyau amma idan ta nine ban damu da sai an
kewaye sansanin ba sai dai saboda ku da kuyangina koda gama fadin haka sai sarauniya
larbisa ta juya ta tafi izuwa cikin tantina nan take sadauki muhairu ya umarci wadansu daga
cikin dakarunsa dasu je su saro manyan bishiyoyin da za a kewaye su haka ramukan da za a
sanya itatuwan. .
Nan take kuwa dakaru suka kama aiki ba lalaci a lokacin dasu kuma kuyangi suka kama aikin
dafa abinci ai kuwa kafin magariba tayi an kammala dukkan aikin ya zamana cewa an kewaye
gaba dayan sansanin da manyan bishiyoyi yadda koda giwaye ne suka zo sai sun sha wahalar
gaske kafin su sami damar ture bishiyoyin da aka kewaye sansanin bayan anci abinci sai
dakaru suka ki su kwanta sukayi lambo suna masu dana kwari da bakansu masu takubba ma
suka zauna a cikin shiri kuma aka kashe dukkanin fitilun iccen dake ci a sansanin ko ina yayi
duhu dundum sarauniya larbisa kuwa kayan yakinta ta sanya ta zare takubba guda biyu tayi
lambo a gaban dakarun nata saboda ita a jikinta ta san cewa lallai ba za a rasa wani mugun
abu ba a cikin wannan daji kuma lallai abin zai iya kawo hari a koda yaushe har dare ya raba ba
a ji wani bakon motsi ba a cikin dajin. Al amarin da ya karya zuciyar dakarun sarauniya larbisa
kenan suka fara tunanin cewar babu wani mugun abu da zai kawo hari dama a wannan lokaci
da yawa daga cikinsu sun fara hamma saboda jin barci.
.
Koda sarauniya larbisa ta lura da halin da dakarunta ke ciki sai ta dubi sadauki muhairu wanda
yayi kwanciyar lambo kusa da ita tace maza ka gayawa sauran yaranka cewar duk wanda ya
kuskura yayi gyangyadi na dakika daya ni zan sareshi da hannuna.
.
Nan take muhairu ya radawa daya daga cikin wannan batu shima sai ya radawa na kusa dashi
a haka sauran gaba dayan dakarun suka sami wannan sako bayan faruwar hakan da kamar
nisan dakika dari uku sai kawai kawai su sarauniya larbisa suka fara jiyo wani irin gurnani mai
yawan gaske daga can nesa gurnani ne na wadansu irin halittu masu yawan gaske kamar na
dodanni ko manyan birirrika inka dauke sarauniya larbisa da sadauki muhairu babu wanda
hantar cikinsa bata kada ba a sansanin shikuwa tsoho huzallatul marwas kuwa fitowa yayi daga
cikin tantinsa ya tsaya a tsaye yana mai rike kugunsa yana kallon can bakin kofar sansanin don
yaga abinda zai faru alhalin kowa ya sami wuri ya buya a wannan lokaci.
.
kwatsam! sai yaji jakarsa ta sihiri ta bude aljani subauratu ya baiyana a sama dai dai