Showing 9001 words to 11442 words out of 11442 words
Chapter 4 - TSATSUBA BOOK 1 COMPLETE Littafin Yaki BY Abdulaziz Madakin Gini .pdf
fuskarsa
yana mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai kare hancinsa da hannu sakamakon
iska mai karfi dake kadawa yace yakai mai gidana me kake takama dashi har da zaka fito ka
tsaya a cikin wannan sansani alhalin kana gani cewar jaruman ma da suka yarda da kansu
kwanciya sukayi a kasa sukayi lambo ko kuwa kunnenka baya jiyo sautin gurnani halittun dake
shirin kawo farmaki izuwa wannan sansanin?
.
Lokacin da tsoho huzallatul marwas ya ji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace
haba yakai subauratu in banda abinka akan wane dalili tsoho zaiji tsoron mutuwa musamman
ma kamata wanda bashi da kowa kuma bashi da komai ka tuna fa cewa ni yanzu na rasa
babban masoyina wato mahaifina kuma na rasa uwata tun ma ina jariri na rabu da yan uwana
na jini wadanda a halin yanzu ma bani da tabbacin suna raye ko sun mutu idan ma suna raye
basu da wani amfani a gareni tunda sun kasance manyan makiyana a doron kasa.
.
Lokacin da tsoho huzallatul marwas yazo nan a zancensa sai Aljani subauratu ya dubeshi yayi
murmushi yace ai yan uwanka suna nan a raye duk su hudun amma a halin yanzu duk duniyar
nan babu matsafan da suka fisu karfin sihirin tsafi amma hadin kansu ya watse sun zama
abokan gabar juna ba don komai ba sai saboda kowannansu yana son ya mallaki littafin tsatsuba shi kadai saboda ya mulki komai da kowa na cikin wannan
duniya.
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama huzallatul marwas kuma hankalinsa ya tashi ya dubi
Aljani subauratu cikin alamun tsananin damuwa yace kai kuwa menene dalilin da yasa tuntuni
baka labarta mini wannan labari ba tun ina da sauran kuruciyata da karfin jikina ba yanzu ba da
shekaruna suka haura hamsin? .
Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya sannan yace ai gaya
makan bashine wani amfani tunda ba zaka iya yin komai ba akan lamarin dolene ka jira har
zuwa lokacin da zaka sami daukakar da tafi tasu kafin huzallatul marwas ya budi baki ya kara
cewa wani abu sai kawai sukaji kasa ta kama girgiza tamkar zata tsatstsage su rufta cikinta
kuma sai gurnanin da suke jiyowa a can nesa ya kara kusantosu sosai bayan kamar dakika
hamsin sai sukaji gurnanin ya cigaba da wanzuwa a lokacin da yake kara kusantosu suna nan a
tsaye sai kawai suka ga dandazon cincirindon tarin birirrika sun durfafo inda suke kai tsaye
yayinda huzallatul marwas yaga haka sai yayi maza ya mayar da Aljani Subauratu cikin jakar sa
a lokacin da sarauniya larbisa ta fito daga cikin tantinta suma sauran dakaru haka suna fitowa
ne sukayi Arba da tahowar wadannan birirrika nanfa hantar cikin kowa ta kada Amma banda na
sarauniya larbisa saboda ita tasan cewa Jarumar gaske ce
amma kuma matsalar itace basu da zafin nama da jarumtakar da zasu iya yakar wadannan
birirrika nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa bitowar da tayi neman wannan
littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta....
Wow nima AlQuyraemey a nan zan dakata sbd ganin wadannan birirrikan kuma nake cewa sai
Allah ya kaimu gobe zan ci gaba.
TSATSUBA
Book 1
Part F
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.
.
https://www.facebook.com/AlQuyraemey360
.
Nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa fitowar da tayi neman wannan littafi na
tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta, gama aiyana hakan
keda wuya sai wani daga cikin birirrikan ya shammaceta ya gabza mata naushi a haba saboda
karfin dukan sai da tayi sama tamkar an janyeta da majajjawa koda shugaban dakarun nata
sadauki Humairu ya hango shugabarsu a can sama kuma ya tabbatar da cewa idan ta fado
kasa cikin wadannan birirrika ta zama gawa sai ya falfala da gudu izuwa kan birirrikan yana mai
kwalla ihu.
.
Ai kuwa sai birirrikan suka raba hankulansu biyu ya zamana cewa wasunsu sun daga
kawunansu sama suna jiran sarauniya larbisa ta fado cikinsu su dasa mata wawa
wasunsu kuma sai suka ruga izuwa kan sadauki Humaisu
yayinda ya rage saura yan dakiku kadan larbisa ta fado kan birirrikan shi kuma humaisu yayi
karo dasu sai kawai humaisu da larbisa sukaji an suresu anyi sama dasu cikin tsananin gudu na
ban al ajabi tamkar za a taba hadari dasu kawai sai gani sukayi an diresu a tsakiyar sansaninsu
nan take Aljani subauratu ya baiyana tsulum a gabansu yana mai kyalkyala dariya ya risina ga
tsoho huzallatul marwas yace yanzu na cecesu ya shugabana amma kayi sani cewa anan ne
kawai zan iya taimakonku amma da zararr mun kara gaba sai dai ku ceci kanku kafin larbisa ko
tsoho huzallatul marwas dayansu yace wani abu tuni Aljani subauratu ya rikide ya zama
guguwa. Guguwar ta tafi da tsananin gudu irin na tauraruwa mai wutsiya ta fada cikin dandazon
birirrikan kawai sai gani akayi kawunan birirrikan suna guntulewa suna faduwa kasa gangar jiki
na bingirewa sai dai kaga jini na tsiri da feshi daga cikin wuyansu koda birirrikan suka ga suna
ta mutuwa kuma sun rasa wanda yake yi musu wannan barna sai suka haukace suka rinka ruri
da kururuwa suna kaiwa iska duka amma duk a banza domin dada ragargazarsu ake yi suna
zama gawa tabbas wuya ba dadi kuma idan kaji ana cewa ga ki gudu to tabbas sa gudu ne
baizo ba lokacin da wadannan birirrika sukaga sun kasa kare kansu daga sharrin guguwar da ta
addabesu sai suka
fara juyawa da baya a guje suna kokarin komawa inda suka fito amma sai guguwar ta rinka
kure musu gudu tana ci gaba da cire musu kawuna har saida ya zamana cewa babu sauran
daya daga cikinsu wanda ya tsira da rayuwarsa.
.
A wannan lokacine dakarun sarauniya larbisa suka fara firfitowa daga cikin wuraren da suka
buya cikin alamun kunya suna masu sunkui da kai kas cikin fushi sadauki Humaisu ya rufesu da
fada yana kokarin hukuntasu kawai sai sarauniya ta tari numfashinsa tana mai kallonsa cikin
murmushi tace kada ka hukunta su domin banga laifinsu ba bisa guduwar da sukayi suka buya
kai kanka ai kasa tarar birirrikan kayi sai da kaga zan hallaka sannan kayi kundunbala ka rugo
domin ka kawo mini dauki hakika kayi gagarumar gwaninta wacce ta burgeni don haka idan
mun koma gida zan yi maka wata gagarumar kyauta wacce ban taba yiwa wani mahaluki ba.
.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Humaisu ya zube kasa bisa guowoyinsa a
gaban larbisa yana godiya nan dai larbisa ta bayar da umarnin aje a kwanta ba tare da wani
bata lokaci ba kuwa kowa yaje ya kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba.
.
Kashe gari kuwa da sassafe aka kimtsa bayan an yi kalaci
sai sarauniya larbisa tsoho huzallatul marwas tace aljaninka ya gaya mana cewar tafiyar yini
biyu da rabi zamuyi mu riski dajin da jaruma shumaira take tabbas yanzu mun shafe tafiyar yini
daya kunga kenan saura ta yini daya jal a gabanmu shin akwai sauran wani mugun abune da
zamu hadu dashi kafin mu isa dajin da jaruma shumaira take?
.
Koda jin wannan tambaya sai tsoho huzallatul marwas da sadauki Humaisu suka dubi juna
sukayi shiru larbisa ta dubi huzallatul marwas cikin fishi tace ai kai ne ya kamata ka bani amsar
wannan tambaya. Huzallatul marwas yayi ajiyar numfashi sannan yace ya shugabana aini a
ganina yanzu bai kamata kiyi shakkar wani abu ba tunda dai gashi mun ga bayan wadannan
mugayen birrirrika saboda nasan cewa abu ne mawuyaci mu sake haduwa da wani mugun abu
wanda ya fisu hadari koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta yi murmushi tace tabbas
kazo da magana mai ma ana yanzu kawai saimuci gaba da tafiya ba tare da bata wani lokaci ba
kuwa aka hau kan dawakai bayan an debe komai aka ci gaba da tafiya ba sassauci tsoho
huzallatul marwas ne akan gaba yana jagorantar rundunar, sarauniya larbisa, da sadauki
Humaisu na biye da shi sannan sauran dakarun, Kamar yadda Aljani subauratu ya fada haka Al
amarin ya kasance wato sai da
suka shafe tafiyar rabin yini guda sannan suka iso wani katon daji mai yalwar Bishiyoyi, koramai
da fadamomi, kai da ganin wannan daji kasan cewar dajine mai ni'ima irin wanda mafarauta ke
so domin dole ne a samu dabobin daji da tsuntsaye masu yawa a cikinsa da shigarsu sai suka
hango wani katon garke na ragon dawa cike da raguna da tinkiyoyi abin mamaki shine an
kewaye garken ne da siraran itatuwan bishiya marasa kwari wadanda dabbobin zasu iya
kakkaryasu su watsu amma kuma dabbobin basu ture itatuwan ba sun gudu.
.
Koda dakarun sarauniya larbisa suka hango garken wannan dabbobi sai suka cika da farin ciki
suka ruga izuwa cikin garken suka dasawa dabbobin wawa da nufin kowa ya kama iya rabonsa.
kwatsam! ba zato ba tsammani sai sukaji ana naushinsu ta sama suna zubewa kasa duk wanda
akayi wa naushi daya sai dai kaga yayi sama ya fado kasa a matukar galabaice wanda ke
naushin nasu kuwa a samansu yake shawagi kamar tsuntsu har sai da ya gama bazar dasu
kasa sannan ya duro kasa bisa kafafunsa aka fara kallon kallo tsakaninsa da sarauniya larbisa
ba wani bane yayi wannan gagarumar jarumtakar
ba face jaruma shumaira kai da ganin irin kallon da sarauniya larbisa ke yiwa jaruma shumaira
kai kasan cewa
tana cikin tsananin mamaki ba wani abu bane yasata wannan mamaki ba face a rayuwarta
bata taba zaton cewa zata ga wata ya mace ba mai kyau kamarta ba amma a yanzu da tayi
arba da shumaira saita raina kanta kuma ta tabbatar da cewar babu abinda zata fi shumaira
dashi face mulki da dukiya cikin tsananin fishi shumaira ta dubi su larbisa tace dame kukazo
wannan daji shin yan fashine ku ko kuwa matafiyane wadanda basu san ya kamata ba duk mai
hankali idan ya dubi wadancan dabbobi ya lura da yadda aka kebancesu yasan akwai mai su
duk da cewa kuwa a cikin daji suke kuyi sani cewa wannan daji nawa ne don haka komai na
cikinsa mallakina ne babu wanda yake da ikon yin farauta a cikinsa face ni.
.
A cikin wannan daji kakana na bakwai yayi rayuwarsa kuma tun daga zamaninsa kawo i yanzu
babu wanda ya isa ya taba komai a nan sai da izininmu da yardarmu ku gaya mini abinda ya
shigo daku cikin dajin nan in ba haka ba kuwa sai dai na yakeku koda jaruma shumaira tazo
nan a zancenta sai larbisa ta matso gaba kusa da ita ta sauko daga kan dokinta ta dubi
shumaira cikin murmushi tace yake shumaira yaga mafarauci Imshal ki yi sani cewa nice
Sarauniya Larbisa mai mulkin birnin darul kaizul kuma musamman nazo wannan daji naki
domin na gana dake bisa wata muhimmiyar bukata tawa koda jin wannan batu sai jaruma
shumaira ta gyada kai cikin alamun fishi da rashin yadda tace mu bama mu amala da masu
mulki kuma baki da wani abu wanda zaki iya biyana dashi na taimakeki saboda haka ina mai
shawartarku daku gaggauta fita daga cikin wannan daji nawa idan ba so kuke muyi yaki ba
koda gama fadin hakan sai jaruma shumaira ta juya da baya ta nufi wannan garke na dabbobin
ta ta shiga gyara turakan dake ciki tana daure dabbobin.
.
Koda ganin haka sai sarauniya larbisa ta dubi gaba dayan dakarunta tace duk abinda zai faru
tsakanina da jaruma shumaira kada ku saka baki ko hannu nan take larbisa tabi
shumaira izuwa cikin wannan garken dabbobi ta kama tayata aikin daure dabbobin.
.
Al amarin da ya fusata jaruma shumaira kenan ta kaiwa larbisa wawan duka da kafa a wuya,
cikin bakin zafin nama larbisa ta kaucewa dukan nan fa suka kaceme da azababben fada suka
wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tun da
su jarumi Humaisu suke ganin gumurzu na fadan hannu tsakanin jarumai basu taba ganin fada
mai tsananin ban tsoro ba kamar wannan domin gwanintar ta hadu da gwaninta kuma
sadaukantaka tayi kada da kishiyarta.
.
Sai da wadannan jarumai biyu suka shafe rabin sa a suna naushi da bugun juna hannu da kafa
ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina kuma sun fara galabaita amma saboda
bakar zuciya sunki su daina fadan amma kuma jaruma shumaira tafi sarauniya larbisa jure duka
domin ita tana iya shanye duka uku na larbisa amma data naushi larbisa sau daya sai kaga ta
fadi kasa sai dai tayi hanzari ta mike taci gaba da fadan
.
Al amarin da ya dugunzuma hankalin su sadauki Humaisu kenan domin sun tabbatar da cewa
idan aka ci gaba da wannan fada a haka har zuwa wani dan dogon lokaci shumaira zata iya
sumar da larbisa ko kuma tayi mata wawan rauni Gashi kuma larbisa ta gargadesu akan kada
su kuskura su shiga cikin wannan fadan. .
Ana cikin wannan bakin gumurzune shumaira ta shammaci larbisa ta daka tsalle sama ta doki
fuskarta sau uku da kafa take larbisa ta dimauce kuma ta gigice ko da taji zafin dukan saita zare
takobinta ta kaiwa shumaira sara cikin sa a kuwa ta yanki shumaira a damtsen hannunta na
hagu har wajan ya dan dare kadan jini ya fito shumaira tayi tsalle gefe daya tana mai yin yar kara bisa jin zafi da zugin da taji koda ta dubi
hannun nata taga raunin da larbisa tayi mata sai ta fusata ainun itama ta zaare rantsatstsiyar
takobinta ta ruga izuwa kan larbisa
itama larbisa saita rugo izuwa kanta koda ya rage saura baifi taku uku su hadu ba sai kowacce
ta daka tsalle sama suna masu kai mugun sara Takubbansu na haduwa saita larbisa ta rabe
gida biyu, A saman shumaira ta doki kirjin larbisa ta fado kasa a dimauce kafin larbisa ta mike
tsaye shumaira ta duro kanta da nufin ta soka mata takobinta a gefen jikinta...... .
Wow lallai Yakamata nIma AlQuyraemey nakaiwa Larbisa Dauki Amma bari naje na dauko
Rantsatstsiyar takobina sannan na dawo
.
Anan ne kuma littafin Tsatsuba Na daya yazo Karshe
marubucin yace...
SHIN SHUMAIRA ZATA SAMU DAMAR SOKAWA SARAUNIYA LARBISA TAKOBINTA KUWA?
.
SHINSU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON
KITABUL SIHIR?
.
SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA?
.
Mu Hadu A Tsatsuba Littafi Na Biyu Domin Jin Ci Gaban Wannan Labari. Daga Mai debe muku
kewa a Kullum kuma a ko Yaushe