Showing 1 words to 3000 words out of 52374 words

Chapter 1 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

[10/14, 20:00] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_

*Intelligent Writer's Asso.*


*DEDICATED TO: My Mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are I so much luv u my mommah*


*Wannan littafin ba Sabon Novel bane Tsohon Novel dina ne na Dawo dashi,saboda zan sake
gyarashi,na fadadashi domin masoyana wadanda basu karanta ba Dama wadanda suka
karanta...Ina godiya sosai domin kun nuna min One love�kuna ma kan nunamin SON SO
FISABILILLAH..*

*Typing 1 january 2019*



*Chapter 1*

*Kaduna*

  ⭐Da gudu wata mota 320 kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital mai suna *S&S
SAFANA SPECIALIST HOSPITAL*


Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku taimakamin
kada y'ata ta mutu ku taimaka min.." Nurses suka biyota aguje da gadon daukan marasa
lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga cikin motan tareda wata dattijuwan
mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya
karfinta tareda wasu maganganu marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour
room,Hajiya karima takalli Momma tace"To ai sai kira d'anki shafaffe da mai ya taho ya girbi
abunda ya shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah
Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani abun ne ya
tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zatayi magana kenan Kamshin turaren
azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba sunsan mamallakin kamshin.


Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin shigar suit
Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya Karisa yana Fadin"Momma

Har kun iso?


Cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin daya katsesu
kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu Harara,tace cikin kallon
raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata nakeson nasan Halin data ke cike,tundazu
anshiga da ita bawani labari"Tsam dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame
Hannunta tana Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Halin da *SAKINATU* take ciki.

cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kenan dogon bufullatani mai cikar zati
da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya mallaka tareda madaidaitan
dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf
dashi,zagayayyen sajensa yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa
goshinsa dauke da tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine
mai karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan Namiji
ne mai cikar zati da Haiba

*DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda yashafi mata
wato gynea Doctor wanda ke tare dashi *DR TAHIR* ne Abokine kuma Amini garesa kuma
abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr safwan din.


Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da zuwa Haji......."

"wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga da ita
tundazu naji shuru'"

takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin yamike cikin sanyin
jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din kenan Wata murya cikin karaji da
azaba yaji tana fadin

"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin Haihuwa babu
wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala  kai babu abunda kasani sai cikamar tuwo wlh
bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara
Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin
ihun da sakina takeyi ne....".Ina ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga
gurin.


Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga uku"kan ta isa
kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin wulakancin da d'anki yayi ma y'ata
ammh kin gagara mai magana,saboda yagama cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"?

Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki kam tayi
magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u sakina Zata Haihu
lafy"yana gama fadar  haka ya bude Kofar Labour Room din ya Shiga.



Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma kansa shower
ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti talati ahaka so yake yarage
radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office
din yafada yana maida Numfashi.

Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta ba,baisan yaushe
sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci  ba shida mahaifiyarsa ba,baisan sai
yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai sani ba,bai sani ba,yafada da karfi
idanuwansa sun canza launi.

Yafi minti Hudu acikin wannan yanayin kafin ya sake Bude idanuwansa,gabadaya Zuciyarsa ta
gama cika da wani kunci kansa na sarawa lokaci daya jijiyoyin kansa suka Dago,kansa ya Dafe
lokaci daya yana Share Ruwan Dake Diga daga saman kansa,kafin ya sake komawa ya jingina
da jikin kujeran yana maida Numfashi a jere kamar wanda yayi gudun tsere.

Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya Lokaci daya yana Saukar Da Numfashi Daga ganin
yadda yake yi zaka fahimci yanayin Dayake ciki na bacin rai da dacin Zuciya,idanuwansa ya
bude yana bin Kofar shigowa da kallo lokaci Daya Abubuwan da suka Faru abaya suka fara
dawowamai daki daki kamar alokacin Abun ke Faruwa tamkar yana kallo cikin magijin talabijin.

*Domin samun kasancewa cikin masu karanta Sanyaya biyu na Mr Bello da Matar Naseer kan
350 duka biyun Single 1 kuma 200 vips kuma 400 ne Duka biyu kuma 600 ne Muna maraba
daku masoyanmu Sai kunzo*


Commets,share,like and vote....


*Anitha..*
[10/14, 20:00] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_

*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*

*02*

*SHEKARUN BAYA*

" *DR SALE HABULE SAFANA* shine cikakken sunan Mahaifin Dr Safwan wanda d'ane ga
marigayi Justice Habule safana kafin Allah yamai Rasuwa,yayi gwagwarmaya agwannati har
kawo mutuwarsa

Dr sale habule safana Haifaffan garin safana ne dake jihar katsina,yana da shekara bakwai
aduniya Allah yadauki ran mahaifinsa,Mahaifiyarsa Hajiya Maryam wacce suke kirada Hajiya
mama ita tadinga kula da danta har yagirma,Yayi sakandiri sch dinsa a barewa college dake
zaria anan kuma yahadu da Aminsa kabir kankia ganin sun fito daga jaha daya yasanya
abotarsu tafi tafiya daidai.

Bayan sun kamallah makaranta suka Fada ABU ZARIA a inda Sale ke karantan medicine
shikuma kabir political science,ammh duk da haka suna Haduwa in basuda lectures,Haka
rayuwa tacigada da tafiya Har kabir ya kammala digirin dinsa ya dora masters dinshi shikuma
alokacin sale yatafi Bautar kasa.
Sale a garin adamawa yatafi bautar kasa kuma achan Allah yahadasa da mahaifiyar Safwan
Hadiza,Hadiza mahaifaffiyar Adamawa ce bafullatanan asali, marainiya bata uwa ba uba sai
kanin mahaifinta wanda yariketa mai suna Baffa Sani Hadiz bata zurfafa lilimi ba iyakarta
sakandiri ammh masaniya littafan Addinin muslunci tana da ilimi fiye da tunanin mai karatu bai
kammala bautar kasa ba Allah ya kulla aurensu tareda jajircewan Hajiya mama.

Lokacin da'akayi bikin kabir kankia na kasar spain yaje yin phd dinsa,sai da yadawo yaji
amininsa yayi aure hakika ya tayasa murna kwarai matuka samun mace irin Hadiza,Macece
kyakyawa dogowa mai dogon Hanci da gashi,Bayan kammala bautar kasarsa yafara aiki da
Aminu kano,Yaso ya dauki iyalansa sukoma kano da zama Hajiya mama taki amincewa dole
yasa yabarsu nan safana yana zuwa musu weeked

Bayan kammala karatun kabir kankia yafada siyasa kadangadan akuma lokacin iyayensa suka
masa aure da yar uwarsa Karimatu,karimatu tun tana karimar shegiyar makirace,gata bawani
kyau ba bakace mummuna ga gajarta,tun tana yarinyanta take bala'in son auren mai kudi bata
shiri da takala,gata da kyashi da hassada ga bariki kala kala dan dai babu yadda zai yine yasa
yahakura ya amshi karima.

Yafara rike mukamin sakataren gwannatin janar katsina akuma lokacin Hadiza ta haifi Safwan
Hakika tunganin Farko da karima tama Hadiza taji ta tsaneta saboda tafita kyau uwa uba
hankali Natsuwa da tarbiya kai akomai tadarata shiyasa lokaci guda kyashi ya shigeta,batawani
sakarmata sai kiga tawani yamutse yamutse kamar taga kashi shiyasa Hajiya mama ganin
Farko tace"Kabiru ina karoro wannnan ruwan yan Duniyan"kai tsaye agabanta mirmishi kawai
yayi itakuma karima tadago tana karema Hajiya kallo ta kasan ido.





safwan yazo cikin gata,badewa mahaifinsa ya tafi london karo karatu sai da ya shekara uku
kana yadawo lokacin yazama consultand,Safwan nada shekara biyar iyayensa suka kaisa
Nigeria turkish.tunda Hadiza ta haifi safwan bata kara Haihuwa.





Haka dai Rayuwan ta cigada juyawa cikin nasara da kwanciyar Hankali lokacin da Safwan ya
kammala secondry sch dinsa lokacin Da Allah ya karbi ran Mahafinsa hatsari yayi ahanyarsa
tadawowa daga kano hakika matuwar Dr sale Habu safasa ta girgiza yan'uwa da abokan
arzika,Alhaji kabir yaji mutuwar Amininsa matuka sai dai Hakuri





Hajiya da Hadiza wacce Safwan kekira da Momma suka dau dangana suka maida Hankalinsu
wurin kula da safwan,Lafawar abun yasa yadage kasar malesia zuwa karatun medicine sai da
ya shafe shekara sha kana yadawo lokacin yazama cikakken likitan mata.








Shima din da Aminun kanon ya fara aikin kan chukun chukun bude asibitinsa ya kammala da
taimakon Dady Alhaji Kabir kanki wanda yake matsayin kwashinan ilimi ta jahar katsina.

Koda bude asibitin ya kammala baida na aiki da Aminu kano ba Saida ya tattaro Su Hajiya suka
dawo garin kaduna kana ya maida Hankalinsa kan asibintinsa,Dr tahir Aminsane wanda suka
Hadu a malesia course daya suka karanta,kuma yan kasa daya shiyasa abotarsu tayi karfo
Shiyasa bayan ya kammala asibitin ya Nemosa don Atafi tare






Alhaji kabir bai yada iyalan Dr sale ba yana kokarin ziyartarsu in yasamu dama,duk abunda
suke bukatu tunkan suyi mgana yake kawo musu Hakika shi mutumin kirkine sai dai Karima
tanajin bakincikin abunda yake musu dan dai bayya zatayi duk da yanxu ta mallakeshi sai
abunda tace yakeyi




*WACECE SAKINATU*

SAKINAT KABIR KANKIA shine cikakken sunanta yace ga kwamishina Alhaji Kabir kankia da
Hajiya karima wacce ake kira Hajiya kari,yayansu hudu salmace babba tana aure a portharcort
wani controller ne sai laila dake auren wani dan kasuwa a kano,sai Sakina daga ita sai Ummi.


Gabadaya ya"yan Hajiya kari laila da sakina,sune suka dauko halayyanta wanda ma harsun
gyasheta Salma ce da Ummi kadai suka fita dabam,dukkansu suna da degree sakina business
admistration takaranta Tana son taga tazama yar kasuwa tana juya kudi ahannunta shiyasa
tana dawo daga london bayan ta kammala masters dinta Mahaifinta ya tallafamata,tafara odar
kaya daga dubai zuwa Nigeria irinsu dogayen riguna da takalma da jaka,kayan maza kai duk
abunda yadanganci sawa da kwalliya,cikin lokaci Allah yasa abun albarka cikin shekara biyu
sakina ta bunkasa tayi kudi tuni takeda dankara dankara shaguna a
kano,kaduna,katsina,zamfara,da gombe,Sakina boutique and costimetics,sakinat shoes,etc.

Gabadaya Hajiy Kari bata kula da tarbiyan yaran ba kwamishina baya zama so komai na
Hannunta,shiyasa sakina tataso tun tana karama bata kunya ga raina na gaba da ita bata da
kunya ko kadan bata iya girmama nagabada da ita ba.



Sakina bawata kyakyawa bace ta azo agani bakace gajera ammh saboda shafen nan na yaran
zamani yasa takoma Fara,Wani gajeran hanci gareta tana da dan tudun baki,kan nan kamar
Hammatar dan iska kullum cikin gashin doki take,tanason mu'amala da abun mai kyau duk da
ita din bamai kyau bace,Sakina bata kaunar talaka ko kadan shiyasa danginsu na kanki kowa
yasanta da rainin arziki shiyasa kaf suka fita harkansu sboda Hajiya kari inrin matan nan ne
masu kyashi arziki daga ita sai mjinta da yayanta.


Sakina yar gayuce ta karshe kullum cikin shigar alfarma zaka ganta,to tazo kaduna duba shop
dinta taji zazzabi ya rufeta tana Hanya shine tafada asibitin Dr safwan ganin farko tamai yasace
zuciyarta wanda dagashi har ita basusan juna ba saboda kowa ba kasar nan yayi karatunsa
ba,Ada ta dauka wasane sai da takoma gida kana ta tabbatar da takamu da son Dr safwan,tayi
kokarin tayakiceshi ammh hakan ya faskara,abinciken da'aka matane tagano dane gun Aminin
Abbanta.


Da tama hajiya kari magnar kin bada goyan baya acewarta baida qualities din auren
yarta,ammh sakinat taki hakura,taci gaba da shisshigemai da kissa da kisisina,Da hajiya taga
yarta taki hakura yasa tashiga tafita har soyayyah mai zafi ta kullu atsakaninsu,Lokacin da
kwamishina yaji labari yayi matukar farinciki dasamun suriki irin Dr safwan,kuma yakara
zumunci tsakaninsa da amininsa duk da baya raye.



Da Hajiya mama taji lbr tadaga tsalle tace bata yarda ba saboda sanin mugun halin Hajiya kari
ammh Dr safwan ya tubure dole tasa ta amince ita daman momma batada matsala cikin lokaci
kankanin komai ya kammallah Amarya tatare a gidanshi dake kaduna,mai dauke da shashi biyu
daya na momma da Hajiya daya shine mallakin sakina




Sunkwashi amarci na tsawon wata guda kafin halayyan,Sakina sufara bayyana.

Commet
And
Share
[10/14, 20:00] Sis Janafty: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/HYlSeJb3pcr33n3fhabu5h


*NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
  
*DEDICATED TO My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*03*

------Hallaya ta farko data fara bayyana shine kazanta da lalaci,kafin Hajiyarta tasamo mata
masu aiki Sai dai shi Safwan inyagaji da ganin kazanta ranar karshen mako yazage ya tsaftace
gidan tun yana mgana har ya zuramata ido.

Girki kuwa baida darajar da sakina zata girkamai abinci to tama iyane banda indomie bata iya
dafa komai ba,kullum sai dai masu aiki su jagwagwala su ijeye sai da kullum yana aikin rab'awa
sashin Mommah yanacin abinci, gashi batason zaman gidan kullum tana Hanyar katsina ko
kano,Ko yamata mgana baji takeyi ba shiyasa ya zuramata ido.
Raininta har Mommah bata kyaleka ba yimata take dayake Mommah macece mai Hakuri da
kawaichi Mommah irin matannan ne masu mugun Hakuri ko zagin ta kayi sai dai tama
mirmishi,ashekaru bata wuce48 ba,shiyasa sakina tayi bala'in rainata tadinga daka mata
tsawa,Hajiya mama ce take shakka domin itace big problem dinta agidan Safwan.
...Hajiya mama Dattijuwa ce yar kimanin shekara saba"in aduniya,Bata daukan raini ko kadan
irin tsofaffun nan ne wanda komai ke ransu gameda kai saisun fada maka sai dai kamutu
tanada faran faran da jama'a dason mutane tun tana safana macece takowa makotanta kuwa
kamar yan'uwanta Haka ta daukesu,tanada fada in aka tabota gata wani lokacin da ashisshigi

koba"ayi da"ita ba,saita tsoma kanta,shiyasa Sakina ta tsaneta saboda tana mata katsalandan a
al"amarinta game da Mijinta Safwan.

Wani lokacin Hajiya ke tarema mommah tacima sakinar mutumci intaga tana mata Rashin
kunya,inkuwa dukkansu suka bata haushi tasharesu saboda Takaichin yadda Mommah ke
zama Sakina namata yadda Taga dama kuma tana matar Danta ,Safwan yarasa yadda zaiyi da
sakina daya tashi daukan mataki mommah tahanasa.
Ranshi bai kara baci da Sakina ba saida tayi Rashin lafiya tafara, zubar jinin,Dubar farko ya
fahimci taje anrufemata bakin mahaifa dayake Allah ba'a mai dabara sai ga ciki ya bulla agefen
mahaifan bai mata mgana ba, sai da yayimata operation yamaida cikin,cikin mahaifa ya
sallamota suka koma gida,Sakina taga bacin ran Safwan wanda bata taba gani ba mgana har
kunnin kwamishina shima yacimata mutumci ba'a son ran sakina ba tacigaba da renon cikin
jikinta domin ita atsarinta babu Haihuwa Allah shi kyauta,Shawaran Hajiyarta da laila ne
sunfada mata karta yarda yamaida ita akuya tadinga zazzagamai ya"ya karshen tadurkushe ta
zama Tsohuwa shikuma ya auro wata.

SAFWAN yaci sunan mahaifin momma ne shiyasa bata iya fadar sunansa sai dai da babana,
Mutum ne mai Hakuri saboda Nonon Momma ya tsotsa,shekararsa ta haihuwa 30 yanada
kawaichi da dattako mutum ne mai Nagarta kallo daya zakamai kakirasa ustaz ammh social ne
yana da zurfafan bincike a bangaren ilimin addini duk da matsayinsa na likita yahaddacce
Qur'ani tun yana shekara sha hudu aduniya saboda jajircewan mommah agaresa, da sauran
littafai irinsu,muwadda malik,sahihul bukhari,iziya,sira,fiqhu,dadai sauransu,yana da tsantsane
da addinsa matuka mutum ne mai yalwar fara"a,yana bala"in kaunar mommansa saboda itace
ginshikinsa da kakarsa Hajiya mama.


Abangaren kaya yafison manyan kaya atsarinsa yafison yasanya shadda gezner da yadi mai
stantsi ammh saboda yanayin aikinsa yasanya yake surkawa da suite ammh duk Ranar
jumma"a kowa yasani shigar manyan kayan ne atsararinsa.Yana da zuciya da fushi wanda
yakan dade kafin yayi irinsa fushin kuma in yayi fushi da abu na har abada yakeyi,bangaren
abinci yafison abincin gargajiya,irinsu dambu,fate,fankasau,tuwo miya kubewa da dai sauransu.


Aurensa da sakina babu abunda yakaru dashi sai ci baya tunbayan aurensu matsaloli suka
dunga kunno kai saboda sanyinsa yasa ta rainasa bai isa yamata mgana taji ba shikuma baisan
hayaniya da kwakwazo dat why yake yakyaleta uwa uba yana ganin mutumci mahaifinta,A
yan"uwanta kaf bamai darajashi sai salma da ummi Hajiya kuwa da laila dama sune aminan
sakina duk abunda sukace shi takeyi,ko bangaren auratayyah bazai iya dora komai ba domin
sai inyarasa yadda zaiyi ne yake neman sakina,saboda baya samun gamsuwa bata iya komai
na fanni bama miji kulawa ba,gashi bata rabo dama kanta pixsing kullum suka gama saduwa da
juna sai yakoma yana jinyar kansa saboda tsabar yakusan dayake sha,ita bata damu danashi
bukatan ba nata kawai tadamu dashi tayimai sharf kamar kayan wanki yaci yatashi bawani salo

balle kukan kissa,ita ba abunda tasani sai ci ta kwanta sai gayun kawai awaje ammh aciki sai
takaichi.



Ko Rainan cikin sai abunda yagani sai yayi sati bai nemata ba ammh duk ranar daya nemata
bada son ranta ba sai yakusa kuka saboda takaichi itadai sakina ba abunda tasani sai harkan
kasuwanci ko dan kayan gyaran jiki bata damu data sha ba dan tagyara kanta ba a"a ita abunda
tasama gaba shine agabanta,shiyasa bai rabo da azumin litini da alhamis Domin kare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login