Showing 51001 words to 52374 words out of 52374 words

Chapter 18 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

suka iso an hadata badadewa aka isa da hajiya makwancinta na dindin wanda
safwan ya durkushe gaban kabarin yana fitar da kwallah Tahir yakamasa suka shiga mota suka
koma gida ko mgana bai iya ko gaisuwa aka mai saidai ya jinjina kai cikin gida suka yana yin
sallama afalon da suke kuka yakara kecewa kai tsaye momma ya nufa yana zuwa gabanta ya
durkusa yace cikin shakakiyar murya"Momma ya mukaji da hakuri..?


"Momma tadago idanunta jawur tace cikin kuka"Hakuri namune gabadaya Safwan Hajiya tatafi
ta barmu tabarmu da kewa"Tafada tana fashewa da kuka Safwan ya runtse ido hawaye suka
xubomai yace cikin muryan tsausayi"Momma mun sake yin rashi akaro na biyu...Mun rasa
jigonmu hakika kekika haifeni ammh dukkan wahalata Hajiya tayisa ta kasance jigoce agareni
wacce tazame min makwafin mahaifi wlh tallahi hajiya ce komai na itace ginshikina momma
rawar data taka arayuwarmu mai yawa sai dai Muyi mata Fatan ubangiji ya amshi
bakuntarta"Yafada yana zama dirshan ya tusa kansa atsakanin kafafunshi yana kuka gabadaya
dakin jikin kowa yei sanyi kuka kawai akeyi Tahir dake tsaye shima sharar kwallah yake iyami
ne tataso tazo tadagosa tana fadin'Kadaina kuka Safwan yanzu hajiya tafi bukatar addu'an mu
akan kukanmu...Ta tafi ga ubangijinta ammh wlh tatafi dakai abakinta tana sa maka albarka da
fatan gamawa da duniya lpy sannan ta horeka da kakwatanta adalci atsakanin matanka"Safwan
ye wuf ya mike yana tangadi yafice kuka keneman kwacemasa safeena da Sakina suka bi
mijinsu da kallon tsausayi domin wannan mutuwar shi aka mawa.


Baki tako ina sun zo hatta da Ummi da mallam Aliyu sunzo gaisuwa tako ina Sai da akayi
addu"an bakwai kana aka watse aka bar masu gida da kewa momma sai dai kaga tazauna
shuru domin tunda aka aurota bata taba rabuwa da hajiya kona kwana daya ba sai gashi yau
mai rabawa ta raba yan"uwa na adamawa sunso tafiya da ita Safwan ya hana ammh yace
tabisu tayi kwana biyu ko tasamu saukin damuwa.



Safwan shi kadai yakema kansa shiri domin Nageria tafuta aransa kwata kwata babu hajiya
mama babu mahaifinsa momma kadai tarage masa to shikuwa zaman mai zaiyi chukun chukun
kai Adil garin manchester ne ya kammallah dama primary 4,yake ammh saboda hazakar sa
yasa yazana common...Makrantar aikin sojane suma matan basu sani ba sai da Tafiyar ya rage
sati daya kana yake fada musu to yazasuyi tunda mai afkuwa ta afku..Adil dayaji yayi ta murna
ammh dayaga Tafiyar ce tabbas sai ya hau kuka Safwan dashi da Tahir suka isa dashi har
kasar suka kuma barsa suka dawo ammh safwan yafadamasa ko awani hali yake kar ya manta
da KASARSA NAGERIA.


Yagama musu kowani shirye shirye dama yajirane Safeena ta kamallah jarabawansu na

karshene to Alhamdulillah ta kammallah bai fada musu komai ba sai da komai yazama Normal
yaje yadauko momma daga gun yan"uwanta anan yake cemata ta musu sallama don jibi zasu
koma Portugal da zama na dindin...Momma ta kallesa zatayi mgana yace"Momma yazanyi
banda zabi...Babu hajiya to mai zaki zauna kiyi gani ni danki ina wata uwa duniya...Tafiya zanyi
dake momma ayanzu ke kadai nake dashi yanzu"momma tashare hawayenta tana shafa kansa
tace"Allah yamaka albarka da zuru"arka gabadaya...hakanan ta musu sallama sunso suyi
gaddama ammh kuma duba ga shi dantane bata da wanda yafishi ahaka suka rabu cikin kewa.



Dama tuni yaje Safana yayi musu sallama suka musu Fatan alheri washegari kuwa
gabadayansu yasasu amota sai zurmi basu wani jima ba yace suzo su wuce anan yake fadama
su Ummi zencen tafiyar Sakina da Safeena suka kalli juna cikin alhini domin tunda akayi
rasuwar nan suka kasa gane kan safwan komai nashi ya chanza...Fatan alheri suka musu
daganan suka nufa kt suma chan din fatan alheri sukama kwamishina fatan Allah sa yazama
alheri domin anyi canji gwannati gwannatinsu takare yanzu kasuwanci yakeyi..Suma din fatan
alheri suka musu kawai domin babu tacewa.



Sakina da Safeena kowacce kayan sawanta kawai yace su dauka...awhegari karfe goma ta
musu abuja ta chan zasu tashi Tahir ne da mami mahaifiyarsa da Matarsa Aisha wacce keda
tsohon ciki suka musu Rakiya harsai da jirginsu ya tashi zuwa sama safeena da Sakina sai da
hawaye ya xuraro musu domin kasa kasace....Yabar amanar asibitinsa da komai ahannu Tahir
yace zasu dunga zuwa lokaci bayan lokaci shikanshi tahir yaji kewa sosai na rabuwa da
Amininsa to yazaiyi Kwatakwata safwan yaji Nageria ta fitar mai aka.



*****

*Bayan shekaru biyar..*



Wani saurayi ne dan kimanin shekara sha biyu ya fito daga wani daki da gudu yana bin wata
yarinya yar shekara shida da gudu Safeena ce zaune afalo tana sanye da wani gilas jaridace
ahannunta tana karantawa kallo daya zakamata kagane girma tareda natsuwa sunkara shigarta
ayanzu haka babbar Nurse ce a asibitin da Safwan yake aiki. Fadawa jikinta tayi tana
Fadin"Mami..Kinga ya Adil ko"Tsaki taja ta tureta tana Fadin"Ke dagani Sa"anki ne"Tafara tura
baki tafashe da kuka Sakina ta fito daga kichen tana cewa"To sarkin cin zali mai kuma
tamaka"Yace"Ammi cewa fa tayi badani za'a Nageria ba"Harara ta zabgamai kan tayi mgana Dr
Safwan yayi sallma ya shigo hannunsa sabe da wata karamar yarinya ga wasu biyu suna binsa

abaya duka matane dauke da lodoji justice dake kan kujera zaune ya mike yana tsallen murna
ankawo ice cream Dr Safwan dayazama babban mutum wanda hutu da naira tagama ratsasa
ya zauna yana fadin"Waya tabanin Hajiyata"Sakina tace"Babban banza...Safwan ya kalli Adil
dake cika yana batsewa yace"Kai...Meke damunkane baka da wayau ko bakasan kannenka
bako...?

Safeena tace"Haba Daddy yazaka hau mai Fada ai sune suke jansa ko"Safwan yace"Ke kuma
uwarsa baki son laifin danki...To kidinga mai fada nan fa bariki bane ato"Gabadaya suka kece
da dariya tashi tayi ta kama hannunsa tana Fadin"Mutafi daki my son...Duk munsan zaman
dazamuyi dasu tunda ba"a sonmu"kansa ya aza kan kafadarta yana cewa,"I love u mamina..."
tace tana shafa kansa"me too my son...Suka wuce daki Safwan yabisu da kallo yanzu wazaice
ba Safeena ta i ta haifesa ba sai wanda yasani...Shikanshi yasani ammh kuma ko afusaka
baya nuna ma Sakina ce uwarsa.,suna zuwa nageria lokaci bayan lokaci don Safwan bai manta
da Gida ba.



Sakina ta matso ta amshi little keena wacce Safeena ta haifamata takwara tana dagata sai ga
Tahir shima ya Matso ta hadasu ta daukesu ai sai kowa ya taso Ammi nima Ammi nima Haka ta
hada ta daukesu dukkansu Hajiya justice,kabir,tahir,da keena masha Allahu da zarar safeena ta
yaye zata mikama Sakina itace maman yara momma ce tafito daga wani daki takara manyanta
ammh jin dadi yasa ba"a ganewa tana fadin"Don kaniyarku kashe ta zakuyi rai biyar "Tashi
sukayi da gudu suna fadin"ehhhh...Momma nine first suna fadi suka fada mata suna shirin
kadata Safwan yace"Kai karfa ku karyamin uwa"momma tayi dariya hakoran makkanta suka
bayyana tace"kyalesu safwan Rai ne yakai barsu suyi" Sakina tayi dariya tace"Hakane
mommanmu Allah dai yakara miki lpy safwan ya amsa da Amin yana kallonta tabbas sakina
bata kara haihuwa ba ammh ya"yan Safeena kadai sun koremata kishirruwan ya"ya tana kara
godema Allah akoda yaushe daya bata ikon gane TA TAFKA KUSKURE....Safwan dake binsu
da kallo ya furta A hankali"ALHAMDULILLAH!




Toni ma Anan zance ALHAMDULILLAH....



*Nan nakawo karshen lbrin NA TAFKA KUSKURE Abunda nafada dai dai Allah yabani ladansa
kuskuren dake ciki Allah ka yafemin,Godiya ta mussamman ga grouops din dasuka bini
tundaga farkon lbrin har zuwa karshe,Ina godiya ga Duka Masoyana na Wsop da Wattpad masu
Sharhin da Voting ina godiya Sosai Allah bar zumunci Ameen*

Domin samar damar kasancewa Daya daga cikin wadanda zasu karu da Littafinmu na Silar
Hallaci wanda muke kan Rubutashi Nida Sister Aisha Alto zaki iya biyan kudin karatu akan
₦300 kachal,Domin karin bayani zaku iya nemata ta wannan Layin 09069067488



*Akwai sabbin Littafaina da zasu Fito ammh sai mun Shiga Sabuwar Shekarar 2021 in Allah
yasa muna da Rabon gani Daya zai kasance Free daya kuma na Biyan kudin karatu ne bana
mallaka ba Zasu zo da Sabon salo wanda zai Nishadantar da masu karatu ina Fatan Bazaku
bani kunya ba zaku nuna min cewa Ana tare*



Comments
Share
Vote
Share


*Shakira..*
*Anitha..*
*Paro..*
*Janafty*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login