Showing 36001 words to 39000 words out of 52374 words

Chapter 13 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

ruguza naka"Ransa ya baci yasa hannu ya fizge
rigarsa kafin ya tunkudata ta fadi kan gado yace rai bace"Nafi karfi inyi abu saboda ke
Sakina..kina sona kikemin abunda kikemin kike banzarta dani kamar wani wawanki wani dama
ne banbaki ba eye..?Ammh kika sa kafa kika shure kekina ganin kin isa kowa to wlh bari kiji
infada miki in wani abu yasamu matata wlh tallahi kinji na rantse kotu ce zata rabamu ni dake
kuma in kin musa ki kwatanta Nonsess kawai"Yana gama fadar haka yajawo blanket din dake
kan gadon da filo ya jefa kasa yashimfida kashe wutar yayi yakoma ya kwanta ransa na masa
kuna.




Daskarewa sakina tayi akwance kukanma ya kasa zuwa mata gyada kai kawai takeyi tanaji
aranta zama bai ganta ba itace yau Safwan yama wannan bangazan yake kuma yabamata
mgana son ransa harda kotuce ce zata rabasu in Tatabamai mata tabdijim wlh yadebo ruwan
dafa kansa don kowa agidanan sai ya gane kuransa,kwanciya tayi tana sake saken zucci na
yadda zata rama dukkankan abunda aka mata.





Kiran sallar farko ya farka dama akagare yake yatashi ya fice dakinsa yayi alwala kan yafice
zuwa massallaci kotan sakina bai bi ba koda yadawo yasamu kira daga asibiti ashiryeshi ya
iske Safeena ita da danta akichen suna soya wainar kwai Adil yadauka yana masa wasa ita
kuma Safeena natsaye sanye da riga da sikat yan kati da hula akanta ta harde hannunta akirji
tana kallonsu dagowa yayi suka hada ido tasakarmai murmishi,shima ya mayarmata sanye cikin
american suit red and blck suit dinsun amsheshi matuka yar briefcase dinsa ke makale
akafadarsa kallo daya tamai ta fahimci baida fara"a kallonsa tayi kan tace'ina kwana....Ya amsa
da "Lpy kalau ummi Adil yakuka tashi ta amsa da lpy tana kallonsa saurin fita yayi yana
fadin"Zan makara yanmatana zo ki karbi danki"kashe gas din tayi kan ta fito tana fadin"Unku
baka fa karya ba zaka fita"Kallonta yayi kan yace"Na makara sai dai in nadawo....Yana fadar
haka ya mikamata Adil ta amsheshi shikuma ya fice binsa tayi da kallo tana mamakin mai ya
batamasa rai haka.





Ko achan hospital kowa ya fahimci baida walwala hatta tahir wanda bai ma tambayesa ba
domin yasan duk sanda yaga Dr Safana awannan yanayin yasan mutum dayane ke sauya Dr
Safana wato SAKINA.

Koda yadawo baiwani sake ba saida Safeena tadinga jansa da hira shiyasa yasaki ransa yau
ma abun jiya aka maimata akasa ya kwana wanda ko mgana bata hadasu da sakina ba shi da
badon yasan darajar aure da adalchi ba har Sakina ta wulakantasa never domin yanzu ba da
bane.




*****




Kwanchi tashi Asarar mai rai gashi yanzu watan su Safeena biyu da tarewa gabadaya
rayuwarsu ta chanza ita da Safwan da Adil domin suna cikin farinciki da Annushuwa hatta su
momma suma sun ga chanji saboda su yanzu girki sai sunga daman yi domin Safeena ta
daukemusu komai ita keyi in tagama abunda zatayi sai takoma shashensu suta hira da dariya
da hajiya mama.





Ga Adil yanzu watansa goma sha daya gudu ba inda baya zuwa mami kuwa abakinsa da Abbu
da hajiya da momma radam abakinsa ya Iya fada safeena ta shaku da Adil matuka bata son
abunda zai tabashi kwatakwata tana jin dadin zaman gidan fiye da komai gashi Dr ya siyamata
sabon waya kullum sai sunyi waya Da Ummi tana kara bata shawarwari wa'inda zasu amfaneta.



Ada Sakina bata cika fitowa ba ammh yanzu tachanza taku domin afalo take wuni in ko Adil ya
kuskura yayi gefenta wlh sai yadawo da kuka itakuwa Safeena ko kallo bata isheta ba domin
har abada bata da lokacinta kawai tana gama basu dama ne saura kiris abunda ta dana musu
yatashi dasu.

*Janafty...*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*30*




"Mtsala ta farko da sakina tafara fuskanta shine na danta ADIL....wanda indai yana wasa afalo
tashigo yanzu zai yanka ihu yatashi da gudu yabi safeena daki ko kichen inko tace zata
daukeshi yadinga yanka ihu kenan kamar yaga dodo sai Safeena tazo ta daukeshi tana rarashi
yana kuka yana fadin"Mami....Yana nuna sakina,sai Safeena tasabashi su koma daki kana zaiyi
shuru.




Abun yana damun Sakina matuka domin koda take rashin kula Adil bawai batason shibane
yaza'ayi mutum yahaifi da da cikinsa yace bayason shi wannan ma ai karyane,tana son danta
kawai abubuwane suka mata yawa ciwon abu biyu tahade mata ga na kwatar miji gana d'a
domin yanzu Safwan tsakanin shi da Sakina ido ko kula da yadda take rayuwarta bayayi
saboda shi yanzu kwanciyar hankalinsa kwanciyar hankali Safeena da gudun jininsa.Hatta da
su momma sai suyi sati basu sata a ido ba Hajiya mama ko aranar data shigo shashen ta iske
Sakina zaune afalo dariya tahau tsintsurawa tana fadin agaida uwargida sarautar mata shiyasa
bahaushe yace kada kayi wasa da damarka domin watarana matsayin daka ke adama rasashi

kakeyi,babu shakka tasan da ita takeyi shiyaasa sum sum ta shige daki ranta na mata suya
tana son tadawo Sakinarta tada ammh tarasa yazatayi.





Yau Tun safe Dr Safwan ya fice bayan yar rigiman sa Safeena tagama kukan Ita Umminta
takeson gani tun yana lallashinta har yazo yana binta da ido domin kowani dakika kaunarta kara
zurfi take aranshi,bawai bayason tafiyar nata bane A'a yadda Safeena tazama tallafinsu shida
danshi yakeji kada suyi maraici,tana fushin yafice ya barta.


Sau wurin sha biyu tafito daga daknta Adil na biye da ita kamar jela yana mata gwarancinshi
sanye take da wata atamfa milk and green riga da sikat kayan sun amsheta tayi daurin ture
kaga tsiya ta daure gashinrta da band,tarasa mai zata dafa kawai sai ta soya musu doya tayi
miyar kwai ta kammallah kenan taji ana sallama da sauri ta fito tana amsawa.


Wasu mata tagani guda biyu dayar tafi manyanta dayar kuma yarinyace dukkansu kallon banza
suke binta dashi kamar sunga kashi Safeena taji gwiwarta ta sake tace cikin sanyi
murya"Sannunku da zuwa...Ku....ke dallah rufema mutane baki"Anty laila kenan ta katseta tana
binta dawani matsiyacin kallo Hajiya kari tace'yo kekuwa dole tamana sanabe mana anzo gidan
daula anrabu da cin gabza"safeena taji wani abu ya tsayama amakogwaro kafin tace wani abu
Adil ya fito daga daki dagudu da wayarta yana fadin"Mami....Mami...Abbu...Yana mikamata
wayar alamar ana kira Amsa tayi tana shafa kanshi Dr ne ke kira shiyasa ta barshi.

Hajiya kari da laila suka hada ido suka futar lokaci daya"MAMI....."da mamaki afuskarsu kafin
Laila tace"Hajiya kamar fa Adil ne fa yagirma hajiya kari tace"Shine Nima nayi mamakin
girmansa rabona fa dashi tun haihuwarsa"Laila tace"Nima inaganin tun lokaci ammh naji yana
cema watanan mami fa"Tafada tana kallon Safeena datake rumgume da Adil dake binsu da
kallon rashin sani.



Hajiya kari tace'Ato sakarcin sakina ne baki sani ba"Tafada rai bace ai laila da hanzari ta
ficikosa tana fadin"Bazai yuyuba kin asirce uba kuma ki asirce d"a ba.."Yako tsandara ihu iya
karfinsa hajiya kari ta dunguremasa kai tace"Kinganin mun munafukin yaro kaci gidanku ni nan
daka ganni kakankace ita kuma wannan yayar uwarka"Tafada tana nuna laila kana ta nuna
Safeena dake daskare awurin hawaye sun taru a idanunta tace"Ita kuma wannan kishiyar
uwarkace ga uwarka chan wacce tayi nakudarta"tafada tana figan hannunshi ta wuce dakin

Sakina dashi laila ta marata baya shikuwa Adil kuka yake yana mika hannu yana ta
kiran"Mami.....Mami...ita kuwa hajiya kari nakara jansa tana fadin"Ko zaka mutu sai kabar
mamin don ubanka".


Safeena da kuka yakwacema tashige daki da sauri tana maida kuka gefen gado tazauna tana
sharen hawaye aranta tana addu"an kada Allah yabasu ikon Rabata da Adil domin wlh bazata
iya rayuwar gidannan ba yaron nan akusa da ita ba.




Sakina na kwance akan gado su laila suka shigo cikin mamaki ta mike tana kallonsu rike da adil
dake ta kuka harda hawaye,cikin mamaki su hajiya ke kallon sakina tareda bin dakin da kallo
laila tace"Sakina....Haka kika maida kanki ashe..?"Sakina ta tabe baki kafin tadiro daga kan
gado sanye da breziya da under bako kaya tace"Eh....Haka Safwan ya maidani Anty"Tafada
tana fashewa da kuka rumgumarta Anty laila tayi tana lallashinta hajiya kari ta damkafar da adil
akasa tana fadin"Kama ma mutane baki wlh ko in mauje ka munafinki yaro"Sakina ta saki laila
tana fadin"Hajiya kuma kungani ko wlh yaron nan in yaganni kamar yaga dodo"Tafada hawaye
yana zubo mata hajiya kari tace"badole yamaidake dodo ba tunda kin zauna kin maida kanki
sakarya mara wayo har ita waccan sillan kara wata abace dazaki zauna su ruguza miki
rayuwa'Sakina ta tsananta kukanta tana fadin"Ya zanyi hajiya ya zanyi wlh narasa ma ni mai
zanyi"Anty laila ta riko hannunta zuwa gefen gadon tazaunar da ita tana fadin"shine dalilin
dakika bar kasuwancinki ya ruguje ayanzu haka shagonki na kano an rufesa coz bbu kaya why
sakina zaki sakaci da rayuwarki ta tarwatse lokaci daya"Sakina ta share hawayenta tace"Ni bata
shago nake ba ta yadda na zama bola agidan nan shi yafi damuna ku fadamun yazanyi"tafada
hawaye na kwaranyomata Hajiya kari tace"Abunda zaki ki mike ga kanki kidawo sakinarki danki
kuma da ake miki iko dashi ki karbi abunki domin ba uwar wani ya haifar miki ba wlh sakina in
har baki mike kin kwaci yancinki agidan nan ba to na yarda ke ba nonon karimatu kika sha
ba"Takareshe fada da bacin rai Sakina tace cikin kuka'zanyi hajiya zan nuna miki nidin yar
karimace ta halas ma kuwa"Hajiya kari tace"ke kefa kici mutumci duk wanda yanemi yadakatar
dake koda uwarsa cw"Laila tace"Ai sune munafukai baran wannan katafiriyar tsohuwar mai
kalan yan duniya"Sakina tace"Ai itace ke juya safwan din inaji ko auren nan ita tayimai shi"Laila
tace"Yar tasha ita lokacinta ubanwa yasa amata kishiya"Hajiya kari tace'ai karta aragama kowa
harda ita tahada taci uban shegiya kota koma kauye inda aka fito tana wani ji da baki kamar
fanteka🤣🤣gabadayansu dariya sukasa harda tafawa.


Koda suka waiga ba Adil ba dalinlinsa ashe suna chan suna mgana ya sulale yakoma gun
Safeena wacce taci kuka ta koshi yana ko shigowa yatafi ya rumgumeta yana ajiyar zuciya
alamar yasha kuka rumgumesa tayi tana dariyar farinciki.

gabda la'asar sukayi shirin tafiya bayan sun cika sakina da mugayan shawaransu wanda bazai
bulle da ita ba saima karin jawoma kanta wata fitinar...kwamishina bayanan yaraka gwanna
jigawa shiyasa sukasamu zuwa domin ido yasanya musu ko laila yace tadaina zuwa sai anyi
wani abu kwakkwara tukun..




Sakina ta rakosu kenan suka ga hajiya mama zaune adan barandansu ta shimfida tabarma tana
jin radio ta sai gasu sun fito sun yi tsam da suka ga hajiya mama ammh sai suka waske itakuwa
hajiya mama harda cemusu bata gansu wurin biki ba adakile hajiya kari tace"Sunyi tafiyane
shiyasa...Suka shige motarsu laila ke jan motar suka fice hajiya mama tabisu da gwalo.





*Anitha...*


commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*31*

"Sai karfe 10 dawani abu na Dare Dr yadawo wanda Safeena da danta sun cakare suna
tsumayinshi sanye take dawani riga da wando na pakistan pick colour batasanya gyalen kayan
ba sai ta daure gashinta dashi ta sakeshi shikuwa Adil cikin riga da wando yan kati ammh
wando gajerene,yau din tuwon semo tayi mishi da miyar kubewa danya sai lemon abarba
dayake Dr bai cika cin abinci asama ba dat why take shimfida mai babban darduma afalo su
zauna suci ko adaki.


yau din ma haka ta kasance afalon suka baje suna kwasan tuwonsu Dr naci yana zuba santi
safeena da danta suna faman mai dariya kallonsu kawai yake azuciyarsa yana godema Allah
dabai bijirema hajiya mama Ba dako yayi asara abubuwa mafi muhimmanci yau din kam bbu
sauki domin kodaga irin kallon dayake binta dashi tagane akwai bayani dayake yau yadawo
dakinta itama binshi take dawani sirrin kallo mai tsayawa azuciyar masoyi mirmishi yayi yana
dafa hannunta yace"Ko acikin dubban mata keta dabamce yanmatana shiyasa kullum nake
alfaharin samunki amatsayin matar aurena"tsadadden murmishinta ta sakarmai kan tace"Kaima
acikin dubban maza ka bambamta wlh tallahi nafi kowacce mace samun sa"ar Adalin miji irinki
Uncle"Tafada tana mai kura masa ido kuri sukama juna suna aika ma da juna kalamai wanda
baki bai iya furtawa sai dai kawai ido yanuna da kuma hannu ya aikata.


Karar bude kofa ya fargar dasu suka bi inda karan yake Sakina ce tafito cikin wata doguwar
rigar less kayan su amsheta duk da ta rame ammh tayi kyau abunta kallon su takeyi kan tawani
tabe baki tace"Andai ji kunya....Wlh"Wucewa tayi kichen tana sakin tsaki da kallo safwan ya bita
yana mamakin chanzawar sakina kallon Safeena yayi kan yace"Anyi baki ne yau ko..?yafada
idonsa anata cikin inda inda tace"Am....Eh Anty tayi baki"Mirmishi yayi yace"no
wonder...Safeena ta kallesa shima ya kalleta sai ya waske da daukan Adil yana fadin'!maman
Adil me kika ba yaronki ne yazama lukuti haka"Dariya tace"Tuwo miyar
kuka"Yace"wow...Gaskiya kam koda nagani kinganni nan dad dina na biyo domin shi abincinsa
gargajiyane shiyasa nake kara godema Allah daya bani mata daidai da ra'ayina"mirmishi ta mai
kawai mikewa yayi rike da Adil yana fadin"Ke kinga nagaji dawannan jan ran...Kisame ni a
dakina"Mikewa safeena tayi tana cewa"Yau kuma mulki akeji yace"Eh...Nima sai naja ajina.



Kwashe kayan tayi dasukayi amfani dashi takai kichen tana shiga taga Sakina na tsaye tasanya
latifa yar aikinta tana dafamata indomie sai masifa take wai anmaida su gida gidan tuwo sai rufe
hanci take tana fadin"Tsiyar a kawo maka dan kauye agida kenan baisan komai ba sai
kauyanci"Ita dai Safeena kala bata ce mata ta ijiye ta fito tawuce dakinta aranta tana
fadin"Bazan biye miki ba tunda nagane halinKI ko mijin naki ma baki kyale ba.

wanka tayi da Brush kana tazo ta sanya rigar barci wata karamace mai siririn hannu komai na
jikinta ana gani pant kawai tasanya saboda sanin halin dr baison wani abu yamai shamaki,
humranta da inna husai tahado mata ta yi ambaliya dashi zani ta dora kan rigar ta sanya hijabi
tafito taja kofanta ta nufi dakin Dr.


Koda taje ta iskeshi har Adil yayi barci ya sanya sa kan dan gadonsa dake dakin dr yana zaune
yana duba abu acikin kwanfutarsa tashigo tana shigowa tayi wurgi da zanin da hijabin tataka
cikin takun ta na kasaita ta isa garesa kamshin turarenta shiyasa yadago yana binta da mayen
kallonsa cikin zakuwa ta rumgumesa ta baya ta sakalo hannunta tazage cikinsa tadora kanta
wuyansa tace cikin karyayyiyar murya"Unku...Gani takareshe cikin shagwaba tagama kashe
mai jiki dat why yamata shuru kashe na'urar yayi ya ijiyeta kan doruwar dake gefensa ya
birkitota yana binta da mayen kallo yace cikin kasala"sai da nagaji da jira to nama fasa"Yafada
harda tura baki dariya tayi tace"Sorry zumata....ga madarar ka nan kasha sai kagaji don
kanka"matse mata baki yayi yana yana fadin"Nine zuma ko"yafada yana kallonta tace"Kafi
zuma dadi ma"Sai da tafada taji kunya dariya yayi yace"ehyye....Yanmatana haka kike"sunne
kai tayi akirjinsa tana dariya rumgumeta yayi yana fadin"to shikenan bari in baki zuma ni kuma
kibani madara daga haka yasanya hannu ya rage wutan dakin yayi saurin doramata nauyinshi
suka fara sumbatar juna cikin kwarewa.




Yau sun makara sai 8,Dr ya fita office cos akwai meeting din da zasuyi da sauran likitochin
asibitin breafsat ma a tsaye safeena ta matsa masa yasha ruwan tea...Ko shashen su momma
ma a tsaye ya shiga.



Tun fitanshi Safeena takoma daki domin yau tun safe taji zazzabi na neman kamata kana
bakinta na tsinkewa batajin dadin komai shiyasa tana yin wanka tama adil takoma ta kwanta ta
hadasa ta kekensa da abun wasansa takoma ta kwanta yafita yana ta wasansa.




Sakina sai yanzu ta fito daga daki tana hamma kichen ta shiga ta hado tea tazo ta zauna afalo
ta kunna talabijin ana wani film a mbc2 tana nan zaune sai ga Adil ya fito kan kekensa yanata
wasansa kuramasa ido sakeena tayi tanajin wani sonsa na kwararamata acikin rai kawai sai ta
mike tsam ta isa kusa da shi ta sanya hannu ta daukesa aikuwa tana daukan shi ya tsala ihu
ranta ya baci tace"kai rufemin baki ina uwarka indauke ka ka hau ihu",shuru yayi yana kallonta
hawaye na zubo masa sai kuma taji tsausayinshi rumgumesa tayi tana fadin"srry my boy...Kaine

kaban haushi"ai tana fadin haka yakara tsala ihu safeena dake barci taji ihunshi kamar amafarki
zumbur ta mike taji kuwa daga falo ne takejin kukan da gudu ta fice hartana bigewa da gado.



Tana fitowa taganshi hannu Sakina tayi saurin isa tana fadin"Me kika mai...?"tafada arude jin
yadda yake tsala kuka yana ko ganinta yafara zillo yana kiran mami yana mika hannu, tasanya
hannu zata rikesa sakina ta jaye tana bin safeena dawani matsiyacin kallo tace"kul.....Kada
kikara dora ahannuki ajikin dana kuma da kike tambayan mai na mai ai dana ne komai na mai
nina haifesa"Galala safeena tayi kwalla ta cika idonta tace"A'a ba nufi kenan Ba...Naji
kukansane nazata faduwa yayi"Sakina tace"to yana hannu uwarsane sai ayi gaba"Tana fadar
haka ta juya zata koma daki ..Kamar daga sama sukaji muryan Dr cikim dakewa yana
fadin"ADIL BA DANKI BANE, SAKINA DAN SAFWAN NE DA SAFEENA"yafada yana takowa
tsakiyar falon mantuwa yayi yazo daukan file yadade tsaye tun farkon mganan yanajinsu.



dawowa sakina tayi kan tace"Da ubanwa ya bata..?"Kai tsaye yace"Uban yaron ya bata shi
halak malak.."Sakina tajuya kawai tasanya Adil adaki ta kulle kana ta dawo tana cewa"Baka isa
ba safwan wannan karan sai dai duk abunda zakayi kayi ammh na amshi dana"Wani sakaran
kallo yake binta dashi kafin yace"Wai ma wanene dan naki ne..?"Cikin dakewa tace"Adil ne
dana mana ko inada wani dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login