Showing 12001 words to 15000 words out of 52374 words

Chapter 5 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

tace"masha Allahu Allah yasa albarka iyami ta
Amsa da Amin.




Wuni sukayi tare suna hiransu cikin hirar ne iyami ke tambayan Safwan da iyalansa nan Hajiya
ta zayyanemata komai da dalilin zuwanta garin ta kareshe da cewa"wlh iyami yarinyarnan in
aka barta da yaron zata iya kasheshi da bakincikinta"iyami tayi shuru tana kallon Aminyarta
tana sharen hawaye kan ta jinjina kai tarike hannun Hajiya tace"maryama kidaina kuka kin kawo
kuka a inda za'a share miki hawayenki.."

haj.Mama ta saurara tana kallon iyami kai ta gyada mata kan tace"kwarai share hawayen ki
muyi mgana"ta share hawayenta tagyara zama tana Fuskartanta.


iyami tayi ajiyar zuciya tace"nidai bani dawata y'a balle in dauketa in bawa Safwan domin
sharemai hawaye ko? tafada da sigar tambaya haj.Mama tace"Nasani iyami...Meyasa kikace
haka.." iyami taci gaba da fadin"Saboda ina so na kore miki damuwar dana gani a
idanunwanki,mezai hana mu Nemamasa SAFINA"
Da sauri Haj.Mama tamaimaita"SAFINA..."iyami tace"kwarai Hajiya ita kadai ce zan iya
sharemiki hawaye da ita duk da bani na haifeta ba Nasan mahaifinta bazai ki ba"shuru
haj.Mama tayi tana bin iyami da kallo iyami tace"maryama ko..."".da sauri Haj.Mama tace"kar
kice komai iyami nakasa mgana ne kingama min komai na rasa dawata kalma zan gode miki
lalle Safina itace Hasken dana dade ina gani agidan Sufiyanu Allah na godemaka,iyami
tace"babu komai ai yadda safina take awurina haka Safwan yake awajena yaron nan duk sanda
sakonsa zai iso Safana dani aciki musamman zai zo ya gaisheni to meye ake nema gun Namiji
wanda yawuce wannan Allah dai yasa alheri zamu kullah

Cikin farin ciki Haj.Mama ta amsa,da Amin Amin

*Topha ya kuke hango abun yayi,?zai bada kala?kudai ku biyoni dan kuga yadda badakalar
zata kaya*









*Commet and share domin shine abincinmu da gwarin gwiwanmu*

*Janafty..*
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*13*



----Basu samu zama ba sai zuwa dare,dawowar Dr Safwan kenan daga Asibiti yasamu kiran
gaggawa,Shiyasa ya Tafi batare da ya Tsaya jin dame Hajiya mama ta dawo ba


Wajen karfe 9:30pm na Dare ya Shigo Gidan Habu mai gadi na barka da dawowa ya amsa
cikinn Sakin Fuska kafin ya Nufi Shashen Mommah Saboda Sanin Bakin Hajiya mama akwai
mgana



Zaune ya iske su suna mgana yayi sallama suka amsa ya cire takalmi ya kariso ciki Kafadansa
Sabe da Lapcoat dinsa kusa da Momma ya zauna yana gaisheta ta amsa tana mika masa Adil

Haj.Mama dake kan kujera zaune tayi gyaran murya tace"Mgnar dana ce zamuyi mganace data
shafemu dukkanmu shiyasa naga yakamata na taraku mu tattauna


"kai Sufiyanu mganar duk akankane..."yadago yana kallonta bai yi ba mgana tacigaba da
cewa"kwarai da gaske ni wacece agareka? tafada tana kallonsa Da sigar tambaya cikin daure
kai yace"ke kakatace wacce ta haifi mahaifina ammh hajiya mai yakawo wannan m....."?Daga
masa hannu tayi kan tace tana kallon momma"Na isa in zartar da hukunci a gidan nan Ko Ban
isa ba..?

Momma tace"haba hajiya ai dani da babana a karkashin ikon ki muke...Kifadi bukatarki umarni
kawai zaki bada insha Allahu zaki samemu masu biyayyah".



Haj.Mama ta rausayar dakai cikin farinciki tace"Masha Allahu naji dadi dama nasanki Hadiza
bazan samu mtsala dake ba,zuwana Safana dalinlinkane Sufiyanu"Ta fada tana kallonshi shima
dagowa yayi yana kallonta kan yayi mgana ta rigasa dacewa"Matarka tafadamun mganar daya
zaburar dani na farka daga barcin daya kwasheni,na tabbata in sakina tafi karfin iyayenta da
mijinta to mu d'anmu bai fi karfin mu ba"



tayi shuru kan taci gaba da cewa"Naje da Niyyar Neman Safiyanu Aure ne....""Arazane Dr
Safwan yadago yana fadin"Neman aure kuma hajiya"?

yafada da sigar maimaitawa da Tambaya Haj.Mama tamike tsaye tace"Kwarai kuwa.. kuma sai
kayi sa'a gidan dattako,ne daga Neman aure kuma aka Dauro Aure"Ras gaban Dr Safwan ya
buga momma tace cikin mamaki"aure...Kina Nufin yanzu Babana mata biyu garesa
kenan"Haj.Mama tace"ya wuce wai Hadiza ina fatan wannan aure shi zai kawo chanji arayuwar
yaron nan" Nan tashiga labarta musu daga farko har karshen abunda ya Faru takareshe da
cewa"Ka shirya ranar sati Attahiru ya raka ka kaje ku ga juna ina so ayi ayi tatare ne cikin
lokaci"tafada da bada umarni.


Ajiyar zuciya momma ta sauke tana kallon Dr Safwan dayake kallon Hajiya cikin al"ajabi na
abunda take Fada cikin sanyin murya yace"Hajiya wannan tatsuniyace ko kuwa dai wasan da
kika sabane"?

Harara ta zabgamai kan tace"kai ashe shashashane ban sani ba ana nema maka mafita da
yanci ammh kana sakarci ko?to babu wasa matarka SAFINA ta na chan tana jiranka"zai sake
mgana Momma ta girgiza masa kai tayi saurin cewa"Alhamdulillah...Hajiya Allah ubangiji ya sa
alkhairi aka kullah....Nasan Safina yarinyar kirkice kwarai matuka"

Haj.Mama tawashe baki tace"kwarai da gaske Safina itace daidai da tsarin Rayuwarka,ayanzu
haka tana chan ibadan ita ta wakilci jahar su ta zamfara a gasar alqur'ani ta kasa
gabadaya"Momma ta washe baki tace"Kai hajiya alkhairi ya shigomana gida wlh....Allah yasa
mu amfana da ilimin nata"hajiya ta amsa da Amin

Dr Safwan mutuwar zaune yayi yashiga rudu gani yake kamar amafarki wai ya sake auren wata
bayan Sakina abunda bai taba zato ba ko a mafarki baida sha'awar auren mace fiye da daya to
dayanma ya yakare da ita balle har yayi Tunanin kari,Haj.Mama ta katsemai Tunani
dacewa"baka ce komai ba,ko bakayi murna da alheri dana maka bane"?cikin sanyin murya
yace"na isa Hajiya...Allah yasaka da alheri"ta amsa cikin Farinciki dacewa"ko kaifa dan
Albarka,Allah yama rayuwarka Albarka ya Sanya Safina abokiyar zamankace"momma ta amsa
da Amin mika maka mata Adil yayi kan ya mike ya musu sai da Safe.



Asanyaye ya isa shashensu kai tsaye bedroom din shi ya shiga kan royal bed din dayaji
kayataccen zanin gado,yafada zubewa yayi yana sauke Numfashi yakurama saman dakin ido
yana tunanin makomar Rayuwarsa baisan dawani ido zai kalli wata mace amatsayin matarshi
ba,bawai don yana matukar son sakina ba a"a sai dan gasamasa aya Ahannu da Sakina tayi
shiyasa ya cire kowacce mace a lissafi bai ko tunanin kallo wata mace da sunan kallo sha'awa
duk halinsu daya yake gani yadade kwance kan ya yunkura yafada toilet,yayo wanka ya dauro
al"awala yazo yagabatar da Nafila yadade yana addu',oi kafin ya koma ya kwanta wanda har
barci ya kwasheshi bai tantance wani hali yake ciki ba shi dai ba haushi yake ji ba kuma ba
murna yakeyi ba



Asuba tagari Dr S S Safana






_*TEAM SAFINA_

_*TEAM SAKINA�_

*Anitha...*




commet
share
And
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


_*Hohoho ur Durling Safeena Aliyu zurmi tace karkuji komai,kawai ku bata lokaci tayi alkwarin
chanza Rayuwar Dr S S Safana....iz juz d begining guyzs*_



*14*



----Koda garin Allah ya waye har saida Dr Safwan ya makara kafin ya tashi shima Dr Tahir ne
ya ishesa da kiran kan ankawo musu emergency ,yayi mamakin barcin daya sha wanda
rabonsa da irinshi wlh bazai iya tuna waba( lalle Safeena ke haskece arayuwar Dr S S
Safana)cikin gaggawa yayi wanka ya shirya cikin suit masu rowan toka samfarin DKNY
agurguje ya shiga shashen su momma ya musu sallama suka rakasa da sa albarka.


Wata matace aka kawo zata haifi yan uku to biyu sun danne daya kuma suna kokarin turo kai
atare gashi karfin uwar yafara karewa zuwan Dr Safwan cikin kwarewa da taimakon Allah ta
haifi yaranta cikin salama da kwanciyar Hankali yan"uwan matan sun matukar jinjinama Dr
Safwan ganin yadda tun dazu likitoci ke kara kaina akanta bata haihu ba ammh yana zuwa cikin
mintin da bai gaza goma ba ta haihu hakika sun yaba da jajircewa irinta Dr Safwan Sale Safana

wanda har sai da suka Furtamai.


Aranar Dr Safwan ya wuni aiki a asibiti operation uku yayi duk agajiye yake komawarsa office
kenan ya bude karamin fridge din dake office din ya ciro ruwan faro ya kafa kai sai daya sha fiye
da Rabi kana ya ijiye kan kujeran office din yafada yana maida Numfashi.


Dr Tahir ne ya turo kofar office din ya shigo ya kariso yana kallon Dr Safwan dake kwance
idanunsa a lumshe duk da yasan ba barci yake yi ba file din daya shigo dashi ya ijiye kan
yace"Dr Safana wai meke Faruwa ne yaudin nan naganka kana wani annushuwane"?Dr
Safwan yanajinsa yayi masa shuru sai chan yace"Kai fa mugun dan sa"ido ne wlh Tahir"Yafada
still bai bude ido ba.



Dr Tahir ya kyalkyace da dariya kan yace"My man...ai indai kaine to momma ce kawai zata Fini
saninka common gist me "Mirmishi Dr Safwan yayi kan ya Mike Zaune yana Fadin"Zan yi
gisting dinka ammh ba yanzu ba but it only i know yau ina jin yanayi na yana canzawa i dont
know may be wani abu something zai Faru dani ne"Dr Tahir yayi galala yana kallonsa cikin
farinciki kafin yace"Ko dana ji Dr Safana Dan Allah shafamin nasan komiye yasakaka Annuri
yau iz sometin special".


Mikewa Dr Safwan yayi kan ya isa kan teburin dayama office din kwanya yana Fadin"Tsiyana
dakai wutar ciki,ba ni nace ba"yafada yana kallonsa tare da dagemai gira guda daya Dr Tahir
yace"Sure my Dr nakosa ne"Dr Safwan ya zari wani fayal yana wucewa yace"Nafasa kasan ban
san damu"Da sauri yace"Srry..Nadaina damunka but karkajamin rai"Tsaki Dr Safwan yaja kan
yace"in kafito ka rufemin office din Aku"Dariya Dr Tahir yayi kan yace"Bakomai indai za"a bani
lbr,daga haka ya fada toilet din office din shikuma Dr Safwan ya Fice.



Hmmm Su Dr Safwan tun yanzu tunma baku hadu da Safinar ba kafara zakewa

*******


*Zurmi...*



---Masha Allahu kwanansu Safeena hudu suka dawo jaharsu ayayin da jahar Zamfara tazo na

biyu,Hakika Safeena ta godema Allah dayasa iyayenta suka tsaya akanta tasamu limi yau
dalilin ilimi tasamu kujerar makka harda motar hawa golf da zunzuruntun kudi har dubu dari
biyar tayi kuka,kukan Farinciki da zamowarta wurin dabakowa ke takowa ba sai wanda Allah
yabama limi da basira,haka suka dawo cikin Farin ciki kudi dai mkrantansu ta mallakamawa
kujerar makka kuma Abbanta ayayinda motar tace Abbanta yabada adinga mishi haya,Hakika
Ummi taga Ranar Haihuwa domin makota da yan"uwa da abokan arzika sai shigowa suke
tayasu murna,suna cikin amsan baki shyasa Abbah bai samu kebewa da Safeena ba sai da
tadawo da kwana uku kana.


Cikin dakinshi yakirata bayan ya yi godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya azurtasa da
samun ya irinta,yayi mata Nasiha mai kashe jiki har sai da ta Fitar da kwallah kan ya gangaro
kan zence yace'Safeena kinsan dai bazan cutar dake bako?"Yafada yana kallonta gyada kai
tayi kawai jikinta yagama Sanyi fatanta Allah yasa bawani abu yafaru ba bayan batanan ba.


Yacigaba da cewa"to duk abunda zan Fada miki ki daukesa matsayin kaddara..Kina gabda
tafiya gasar nan na daura miki aure"Dam!dam!gabam Safina ya buga tadago da sauri cikin
Rawar murya tace'Aure kuma Abbah'...?kai tsaye yace'Kwarai Safina...Na daura miki aure sati
biyu da suka wuce da jikan Hajiyar Safana"yafada yana ciro sadakinta ya kama Hannunta ya
Damkamata,Safina taji hawaye ya wanke mata Fuska tana so tayi mgana ammh kuka yaci
karfinta mallam Aliyu ya kalleta yaji tsausayinta ya tsirgamasa yace cikin taushin murya"karki ce
komai yata Allah yayi miki albarka Safina Ubangiji ya jibanci lamarinki yakuma zaunar dake
lafiya agidan aurenki"yafada yana kauda kai kwallah tataru a idanunsa,Safina tayi karfin halin
cewa"Hakika Abbah kai yafi chanchanta daka zabamin mijin daya dace dani,na karbi auren nan
hannu bibbiyu sai dai ina rokonka dan Allah Abbah kutayani da addu'a Allah ya bani juriya da
hakuri"takareshe fada tana kara tsananta kukanta Abbah yace"tashi kije yar albarka da izinin
lahi bazaki tabe ba Safina"cikin sanyi ta mike rike da kudin tace" Abbah karike kudin"girgiza kai
yayi kan yace"A'a Safeena Hakkinki ne ki mikama Ummanki ta adana miki kan muji daga mijin
naki.Kada kai tayi kan tafice tana sharan hawaye.Runtse ido Abbah yayi yanaji har aransa
kamar bai kyauta ma Safina ba Sam.

*Shakira..*




Commet
Share
And
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�




*15*



----Tana isa daki tafada jikin Ummi dake zaune gefen gado,tafashe da kuka Ummi tariketa tana
fadin"Ya isa Safina kidaina kuka haka Allah ya kaddara kinsan bawa bai isa ya gujema
kaddararsa ba"


Safina tadago tana kallon fuskar Ummi da dan hasken makarfin daya dan haske dakin fuskarta
shabe shabe da hawaye ta hade da majina,cikin dashashiyar murya tace"Ummi...Yazanyi da
Mallam yahuza,da sonsa yafara samun gurbi azuciyata?


Ummi tace"Hakuri zakiyi Safina shine mafita kawai"Tsuru mata ido tayi tana kallonta hawaye
suna kwaranya tace"Ummi taya zaku auramin wanda baku sani ba,bakusan addinin saba balle
al'adansa ba,Ummi meyasa? takareshe tana kara fashewa da kuka.


Ajiyar Zuciya Ummi ta Sauke kan tazaunar da Safina kan gadon tamike tana
cewa"Hakane...Ammh bakin alkalami yariga ya bushe Allah yaga zukatanmu Badon komai
muka bada ke garesu ba sai dan Amanar dake tsakaninmu da Hajiya mama shekara da
shekaru bazamu iya ture bukatarta ba"Safina takara jan majina tace"Ummi....Dakata"Ummi
tafada tana tsaidata da Hannu kan tacigaba da cewa"Kada fa bacin rai yasa ki manta

matsayinmu agareki,munada daman zaba miki mijin daya dace dake...Ki dawo cikin Hayyacin ki
Safina ki mika lamarinki ga Allah shine zai taimakeki.



Daga haka tasakai tafice cikin tsausayin yarta mafi soyuwa aranta,tana Fita Safina tafashe da
kuka mai cinrai ta sulale kan gadon tana kara volume din kukan,ashe ashe shiyasa mallam
yahuza ranar da suka dawo yana mata murna yaki kallon cikin idanunta in baza ta manta ba har
kwallah tagani kwance cikin idanunsa,Allah sarki mallam yahuza ashe an rabamu ne wayyo Ni
Safina ina zansa kaina"tafada tana kara fashewa da kuka kara dunkulewa tayi tana cigaba da
kukan rashin madafa.




Haka Ummi ta tarar da Abbah cikin alhini dataga yadamu ita tadinga kwantar mai da hankali har
yadan ware kadan.





Koda gari ya waye Har Abbah yafita kasuwa Safina bata Fito ba yasan zataji badadi shiyasa
yace Ummi tabita Ahankali haka yasakai yafice cike da tsausayin yarshi aransa,sai wajen goma
Safina tatashi idanunta sun kumbura kanta yamata Nauyi dayake tana Fashin sallah wanka tayi
tashirya cikin wani jan material dinkin doguwar riga fuskarta ko hoda bata sanya ba ta fito ta
tarar da Ummi A kichen tana gyaran wake tasanya Hannu zata karba Ummi tahanata tadago
idanuwanta dasuka kumbura tace"Ummi...Ki.."Bani zaki ba hakuri ba Safina mune zamu baki
hakuri dan mun bata miki"Tafada kanta tsaye daga gani ranta abace yake Safeena ta durkusa
tace"Dan Allah Ummi ki yafemin wlh baran karaba"tafada hawaye suna zubo mata Ummi ta ijiye
waken ta riketa ta data ita tsaye tasa hannu tana share mata hawaye tace"Shikenan Safeena
kar ki kara irin wannan...Abbanki da damuwarki yafita inbaki bashi gwarin gwiwa ba yakike so
yayi ehe?

"Safeena tarike Hannu Ummi tace"Naji Ummi kuma insha Allahu zaku sameni mai biyayyah
agareku"Ummi tace'ko kefa diyar albarka kisaki ranki kinji...Ubangiji yasa albarka Arayuwarki
kinji yata"Tafada tana matsa kumatunta Dariya Safeena tayi har hakoranta suka bayyana
tace"Nagode Ummi nagode daya kasance kika zama uwa agareni"Ummi tace"Nima haka
Safeena na.


Daga haka suka cigaba da aiki suna hirarsu har lokacin da Usman yadawo daga mkranta,koda
Abbah yadawo yaga yadda Safeena tasaki ranta ransa yamasa dadi yaji kaso dayawa na

damuwarsa yaragu yadinga sa mata albarka har sai da tafitar da kwallah na tsausayin iyayenta
hakika in bata musu biyayyah ba data tabe duniya wa lahira.






•••••••••••••••••




*Kaduna...*




Haka Dr Safwan yadinga janma Dr Tahir rai shikuma yaki Hakura ranar dai suna cikin mota Dr
Safwan ke tukawa zasu koma gida Dr Tahir yabiyosa zai gaidasu momma Dr Tahir ya kallesa
yana driving ammh hankalinsa na wani wuri,Dr Tahir ya tabasa yana cewa"mr man...Wannan
dogon Nazarin naka wai yaushe zai kare ne?"Mirmishi Dr Safwan yayi hankalinsa na kan titi
yace"har Abada Tahir...Bansan yaushene zandinga hango kaina amatsayin cikakken Namiji
ba"Yafada muryansa na bayyana Rauninsa.


Dr Tahir ya kallesa cikin tsausaya kan yace"verry soon Abokina...Allah nasane dakai kuma inaji
ajikina kamar komai yazo karshe"Dr Safwan yayi mirmishin gefen baki yace"Kaji wata
chakwakiyar da Haj.Mama takara jefani wai Aure tamin"Zuru Dr Tahir yayi masa yana kallonsa
shikuwa yasan yana kallonsa dat why yaki kallonsa.

Cikin mamaki Dr Tahir ya maimata"Aure...Wai Aure na gaske kona wasa?"wai na gaske"kai
tsaye ya basa Amsa kan yacigaba da cewa"shine mganar danace zamuyi tun last week
aie...Yatabe baki yace"Kasan ma har an daura auren wai" wani uban ihu Dr Tahir yasa har saida
Dr Safwan yaci burki yana binsa da kallo.


Cikin matukar murna Dr Tahir yace"Ehyyyyyyye.....Dis iz juz d begining abokina,Wlh wannan
mganar kara aure tuni ke Raina kawai saninka ne yasa nakasa kawo maka wannan
shawaran.Kai Haj.Mama tagama min komai wlh"Yafada harda buga kafa Dr Safwan yabuga
tsaki yace"Mtewwww...Kai fa wlh dan juju ne to meye nawani ihu"Dr Tahir yace'eh naji...Nidai

yanzu ina amaryan take infact ma ya'akayi duk wannan abun cikin gaggawa,Dr Safwan ya
zabgamasa harara yace"Gata goye abayana uban yan tsegumi.." Dr Tahir ya sheke da dariyar
shedanci yace"Kace komai abokina lokacinka ne nawa nanan zuwa wlh sai ka raina kanka
yaro"Yafada yana zunguran kafadansa,Banza yayi dashi yacigaba da tukinsa.





Suna isa sai da Dr Tahir yakara kular da Dr Safwan chan ya barshi gun Habu mai gadi yana
tsinannan surutunsa ya isa shashen su momma,Hajiya ya tarar afalon tazuba ido tana kallon
talabijin a tashar Arewa 24 sallama yayi bata ji ba kawai ya girgiza kai ya wuce dakin momma
ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login