Showing 15001 words to 18000 words out of 52374 words
Chapter 6 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf
tarar da ita tana goye da adil tana gyara kaya acikin wardrope,da sallama ya shiga ta amsa
tana masa maraba da dawowa ya amsa yana fadin"Momma sannunku,da gida"ta amsa da
cewa"Yauwa..Babana yawajen aikin"?ya amsa da Alhamdulillah yana tambayan Adil yayi barci
ne tace"eh..Yanzu yayi,ficewa yayi yana fadin"Momma kizo ku gaisa da Tahir yazo
gaisheku",daga haka ya fice.
Yana fitowa ya tarar da suda guda biyu Hajiya.Mama da Tahir sun kacema da hira dama
mutunintane,kan kujera ya isa yazauna yana Fadin"Hajiya ikon Allah"tace"kwarai yaro nan gani
nan bari wlh"Dr Tahir ya sheke dadariya yana Fadin"dole abar Hajiya domin bamai iyawa dake
tace"wane mutum Attahiru bawanda ya"isa ne ma"'mirmishi kawai Dr Safwan yayi yafito da
wayarsa yana latsawa,momma ta fito suka gaisa kan tashiga kichen zata zubo musu abinci,nan
fa Tahir ya gyara zama yace"Hajiya ashe abun alkhairin daya samu abokina kenan?"Haj.Mama
tace"Kamar wanne kenan Attahiru..,? yace'Na aure mana"haj.Mama ta washe baki tace'au ashe
yagaya maka dan nema ninan dana fadamasa fuskar shanu yamin tundaga ranar ina lura dashi
ko kallona baisan yi"tafada tana Nuna sa da baki Dr Tahir yayi dariya yace'ai Hajiya Allah dai ya
biyaki da aljannah abunda kikayi yayi dai dai ko Allah yasa yadace wannan karon"Haj.Mama
tace cikin jin dadi"Amin..Attahiru shiyasa nake sonka da fahimta...Nan Hajiya ta fede masa biri
har watsiya ta kareshe da cewa'Nasan wannan Auren Alheri ne shiyasama nakeso cikin satin
nan kuje ku ganta nasan zakuga abunda nake fada muku"Tahir yace"Insha Allahu zamu je
hajiya karki wani damu.
Dr Safwan ya tashi yana cewa"ubanwa zaije dakai....Karma kasa rai",Dr Tahir
yace'oho.....Haji.Mama tace"Uban wanda yayi mganan tafada tana mai dakuwa'kan tace
kagamin ja'irin yaro fitsararre to ubanka zai je dashi'Hanyar fita yayi yana Fadin"kidaina
zaganmun uba"Tace"Allah...Habule to zoka dakeni ance Ubankaneí ¾í´£í ¾í´£tafada harda mikewa
ficewa yayi yana kunkuni tace"Dawo rasa kunya in nuna maka karyan tsiya kake"tana wani rike
kugu,Dr Tahir yana ta kwasan dariya,momma takawomusu abinci ta ga ba Dr Safwan tace'Ina
babana yayi ne Haj mama tace'Rashin tarbiya yagwada min na numasa nima A ceí ¾í´£"momma
tayi mirmishi kawai nan Tahir yaci dambun zogale yayi nak kana yamasu haj.Mama sallama ya
wuce.
Shashen Sakina ya shiga yako iske hakiman zaune afalo ta hakimce ana ta zuba lissafi,adakile
suka gaisa yake tambayanta Dr Safwan dabaki tanuna masa dakinsa yako wuce yana zolayarta
da"Hajiya madam tamu"da harara ta bisa dan taga zuwansu tundazu shine sai da yagama
gulmarsa zai zoyana mata wani rawar baki to daga shi har abokin nasa dai dai take dasuí ¾í´”
Koda shigansa dakin kwance ya tarar dashi kan gado atsaye Dr Tahir ya tsaya kan yace',plz
serious mr man yaushe kake ganin zamuyi tafiyar nan?"banza yayi masa har saida ya fidda rai
da zaiyi mgana kan yace"Dis coming weeked nake sa rai daga haka yajuya baya Dr tahir ya fice
yana cewa"As u wish Sir...Nina ware,daga haka ya fice.
*Anitha...*
Commet
Share
Vote
Like
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*16*
"Ranar lahadi tun Safe Dr Tahir yayi ma Dr Safwan sammako,Shima Dr din yasan Halin Tahir
din da wutar ciki dat why ya shirya da wuri,Dama gashi jiya da daddare kwana sakina tayi bala'i
haka kawai yana Zaune adakinsa yana wani aiki a laptop dinsa ta shigo ta sameshi tace tana
son mgana dashi don Sakina bata da kunya wai tafaramai complain yana wulakantata yadaina
kulata kana yadaina bata Hakkinta na Aure abun haushi abun takaichi yaji wani bakinciki
yayimin shar arai yaso yamata mgama ammh sai ya tuna Neman shiri take shikuwa yayi alkwari
nuna ma Sakina shi cikakken Namiji ne _yauwa Namijina_
Kwashe laptop dinsa yayi ya fice ya barmata daki dayan bedroom din ya shige dayake 3
bedroom ne yasaka key cos yasanta yar hayaniyace sai ta samai ciwon kai,aikuwa taita bala'i
hartana Fadin dole dai Azauna da ita don babu yadda aka iya da'ita mirmishi yayi aransa yana
auna girman rainin da Sakina tayimin lalle kuwa tayi kuskure inhar take Tunanin tafi karfin shi ne
kawai kyaleta yakeyi cos darajar mahaifinta ammh shi tuni tagama Siremai da munanan
halayyanta shifa baida darajar da Sakina zata fita tafadamai sai dai yazo yaga bata gida,baida
kimar da zatayimai abinci balle sauran abunda ba'a rasa ba, ji bi yadda Adil yarasa gatan ta
ammh ko ajikinta ko nono sai taga dama in momma ta roketa ta bashi,to har wannan
macece,shiyasa yadau ma kansa Nuna mata *TA TAFKA KUSKURE*
Cikin Wata shadda gezner deep blue ya shirya jamface zanna bukar ce bisa kansa itama da
zaren blue akayita takalmin kafansa rufaffene na fatar Damisa,baki yafeshe jikinsa da turarensa
Azzaro visit Kansa yadau gyara abunka ka mai kyau sai yafito yabada wani sirrin kyau wanda
ba kowa ke ganewa ba sai wanda akayi dominshi.
Ko takan Sakina bai bi ba,tana dakinta ta kwana da takaichin wulakancin Da Dr Safwan yamata
kuma tayi alkwari kafin ya Fita sai yagayamata meye matsayinta agidan dayakemata halin ko
inkula _Topha lalle Sakina kunya bai ishe ki ba_í ¾í´”
Sashen Momma ya tarar Da Dr Tahir shima ya Shirya cikin shadda fara wagambari shima cikin
dikin muhammd shima zannah bukar din yadora kafarsa shima cikin sawu ciki bakake Sororo
yayi yana kallonsa tun shigowarsa momma Dake zaune gefe ita ta tsurama danta ido tana
kallon yadda danta yau yake Fitar dawani hasken Annuri na dabam Haj.Mama dake tsaye gefe
tasaki guda" Ayyiriri.....!!!!Masha Allahu Safiyanu lalle kanunamin kai jinin justice Habule ne,
Dr Safwan yayi mirmishi kan ya karisa ya duka yana gaida momma ta amsa tana Dafa kansa
tace cikin farinciki"Babana nadade ban ganka cikin Annuri irin na yau ba'sunkuyar dakai yayi
kan yace"Momma...Bbu komai wlh'tace"unhum...Fadamin gaskiya ko duk murnan zuwa ganin
surukar tawace?"tafada tana dago kansa da hannunta,Mirmishi kawai yamata baice komai ba
domin shima mamakin farincikin daya tsinci kansa yakeyi ayau din.
Adil dake Hannun Dr Tahir ya amsa yana cillasa sama yana Fadin"Bawan Allah damo sarki
hakuri...Zaka bini ne"yafada kamar yana jinsa Haj.Mama tace"Bawan Allah yakusa samin uwata
gari ba wacce tambadaddiyar ba"Tafada tana nuna shashenta da Baki Dr Tahir"Yayi dariya
yace"Allah barmana Hajiyarmu"Tace"eh...Kona ga karshen tazurancinka ba" tafada harda mele
masa baki,dariya yayi kan yace"Haba Hajiyarmu verry soon za'ayi"tace"kai kasan wani vari san
ince dai ba zagina kayi ba..?í ½í¸‚í ½í¸‚í ½í¸‚Yace yana Rike baki"Wane ni Tahir"tace"Au na'aza zagina
kayi wlh in ci ubanka domin ni ban yadda da wannan gwarancin naku ba"Tafada tana harare
harare dariya sukayi gabadayansu
Har wurin mota suka rakosu Haj.Mama na jaddadamusu cewa su fara bi Safana Iyami ta
hadasu da wanda zai kaisu zurmin kar suje su bace ko yan kiddappers su sace suí ½í¸‚í ½í¸‚.
Koda tara tayi suna Safana dayake da benz din Dr akayi Tafiyan sai da suka fara biyawa gun
kawu bala suka gaishesu yayi murna da ganin Dr yayi mai Nasiha sosai kan yarike wannan
aure da hannu bibbiyu saboda yarinyace data Fito yar babba gida,Jikinsu yayi Sanyi da Nasihar
kawu kuma daman shi baija da wannan aure cos har aransa baiji Haushi ba saima wani
Annushuwa.
Iyami sai dai taga su Dr Safwan kwatsam taita ina tasaka dasu basu wani jima ba tahadasu da
dan kishiyarta manu tace yakaisu gashi anyi ta neman mallam Aliyu awaya Afadamai ba'a
sameshi ba gashi ita Ummi bata da waya balle Safina.
Karfe10:30 suka Dau hanyar Zamfara sai muyi Fatan isarsu lafiya.
*****
*Zurmi..*
Yau tun Safe Safeena taji gabanta na Faduwa bata kawo komai ba tayi addu'a taci gaba da
sabgoginta,tana kammallah aiyukanta tayi wanka ta shirya cikin bakar doguwar riga da farin
hijabinta har kasa da safa ta daura Nikabinta ta Fito tana Ma Ummi sallama kan zata Duba
Aisha bata jin dadi Ummi tamata adawo lafiya.saboda taji dakyar Abbanta yabarta fita dan
tunda tadawo bata sake fita ko'ina ba saboda akwai Hakkin wani akanta.
Tafita badadewa Ummi tana bakin kichen tana tsinkan zogale domin shi yau mallam yace yana
sha'awa wato tuwon shinkafa miyar zogale kawai taga Manu ya fado da gudu manu dai bazai
wuce shekara tara aduniya ba sa'an Usman ne Ummi ta saki tsigan zogale tana Fadin"Kai
Manu daga ina? kuma kai dawane? ajere ta jefamai tambayoyin haki yakeyi kan yace'goggo
Iyami ce tace na kawo wasu baki"Ummi tace"Baki..Kuma"Ta maimata da sigar tambaya.
Manu yace'eh...Tace mijim yaya Safeena ne"Ummi ta mike dafe da kirji tace mijin wa?"tafada
tana zaro ido yace"Mijin Yaya Safeena tace"Ummi tayi daki da Sauri tana fadin"na shiga Uku ni
zainabu zuwa ba shirií ½í¸‚í ½í¸‚Ummi ta rude taji zuwan siriki.
Hijabi ta yaya tasanya kan tajawo tabarma ta Shimfida kan shararran simintin dake tsakar gidan
tana Fadin",Maza manu ce su shigo.Yako ruga da gudu ya fice yana murna yasha dadin mota.
Suna tsaye ajikin motar Dr Safwan yana bin dan gidan su Safeena da kallo aransa yana
fadin"wai daman akwai masu rayuwa a irin gidan nan" _Tab...Lallenema Dr to dankai kana gida
mai kyau sai yazamana kowama hakane_
Shiko Dr Tahir anguwan yake bi da kallo dagani dai anguwan ta masu rufin asiri ce ba'a fadi
dayan ba kofar gidansu Safeenar agyare tsaf dashi aransa yace"Tab....Nan gidan kuma Hajiya
mama takawomu" _Kaniyarka Tahir Gidansu Safeenar kake zagewa_í ½í¸›
Suna zencen zucci ne manu yafito da gudu yana fadin"ance ku shigo"Dr Tahir yakalli D Safwan
yace"to bismillah...Kaine maigidan aie"yafada yana dariya kasa kasa Harara ya wurgamasa
kafin ya wuce ya rufamasa baya da sallama suka shiga abakinsu Ummi dake kofar daki ta amsa
kanta na kasa tana masu maraba dukkansu zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa Ummi ta
amsa tana tambayan su Hajiya Dr Tahir ya amsa da "Suna gaisheku"
Shuru ya biyo baya Ummi kunya yahanata daga kai shikuma Dr Safwan tagefen ido yake bin
gidan da kallon duk da dai talakawane ammh suna da tsafta ko'ina ashare shima Dr Tahir
hakane ammh aransa fadi yake"Kar dai ace Wannan babar itace Safeenarí ½í¸‚í ½í¸‚í ½í¸‚,cikin kunya
Ummi tace"Ku zauna kan tabarma bari insa asiyo muku ruwan sanyi' ciccire takalmansu Sukayi
suka zazzauna kai aduke Dr Tahir sai dariya yakema Dr Safwan kasakasa shikuwa yanajinsa
yama sa banza.
Ummi ta shga daki takwalama Manu kira yazo tabashi kudi tana fadin"Kasan gidan su
Gaddafi...?ya amsa da eh tace to maza hanzarta kaje yaya Safeena na gidan kace ta yi hanzari
tadawo inzaka dawo ka biya shagon basiru kasiyo min ruwan gora guda biyu.
*Shakira...*
Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
_*Dedicated to my wattpadians Fans and my Whatsappians Fans ina ganin sakonnin Fatan
alheri da Addu"o'inku Allah ya saka da Alheri Tanque so much Allah ya bar Kauna da zaman
Tare Ameen..*_
*17*
Yako zura da gudu ya fita Ummi tace"'oh ni Zainabu Allah dai yakai lpy...",gashi tana so
tamusu bayanin Safeenar tadan fita zuwa gaida kawarta,ammh kunya ya hanata Fita,uwa uba
kuma tana son komawa kichen domin tadora miya aranta tace bari Safeenar ta shigo su dawo
daki inba haka ba Takurani zasuyi oh ni Ummi kunyaí ¾í´”
Manu kuwa da gudu ya shiga gidansu Aisha mamansu Aisha tace'kai daga ina?"yace"Ummi ce
tace Yaya Safeena tazo yanzu"Maman Aisha tace"Tom gatanan zuwa kara fice yayi yanufi
shago siyan ruwa,itakuwa maman Aisha lekawa tayi dakin da su Aishan ke ciki tace"To iyayan
daka kufito kusha iska ke Safeena Ummi ta aiko kije yanzu"Safeena ta mike da sauri tana
Fadin"To lafiya...Dan Ummi bata taba aikomin ba"Maman Aisha tace"Nima dai..Ki hanzarta
komeye mai mahimmacine kam"Hijabinta ta sanya saboda sauri Nikabin ahannu ta rikoshi.
Tana tafe ahanya tana zencen zucci Allah yasa lafiya domin yadda gabanta ke faduwa tun safe
nan da nan ta kawo dayake babu tazara Daga gidansu zuwa gidansu Aisha, taga mota akofar
gidansu ammh ko alama bata kawo gidansu tazo ba tasan dai bawani mai zuwa amota balle
tasa rai _Allah sarki Safeena to yau gashi mai motarma mallakinkine_
Da siririyar muryanta tayi sallama tasawo kai cikin gidan,kanta na duke shiyaasa bata lura dasu
ba ammh kamshin Turaren Dr Safwan ya cika tsakar gidan,da hadaddun takalmansu tafara cin
karo binsu da kallo take cikin Mamaki,har zuwa mamallakan takalman idonta yafara Sauka
kan wani hadadden Namiji fari mai cikar zati da kamala da haiba mai dauke da doguwar fuskar
sajensa ya zagayen bakinsa wanda yakaramasa kwarjini hakiki Allah yayi Halitta Anan gurin sai
akayi sa'a tun lokacin da Dr Safwan yaji muryan Safeena cikin sanyi da natsuwa tayi sallama
yaji muryan tadakesa yayi saurin dagowa ya zuramata ido yana binta da kallo daga sama har
kasa yakasa dauke idanunsa daga kanta duk da babu abunda zai dora da kamanninta ammh
zuciyarsa da gangar jikinsa sun Fada masa cewa wanna ce _*SAFEENARSA_ kaji Dr S S
Safana wai Safeenarsaí ¾í´”
lokacin da idanuwansu suka hadu wani marganet ne yajasu dukkansu Safeena ta tsinci kanta
awani yanayi na mutuwar jiki da sauri ta sadda kanta kasa jikinta ya cigaba da rawa kafafunta
Sun kasa daukanta Dr Tahir ne yayi gyaran murya saboda yaga yadda Safinar ke gabda
faduwa.
Waskewa Dr Safwan yayi yacigaba da latsa wayarsa ammh zuciyarsa na fat Fat kamar wanda
yayi gudun famfalaki DrTahir yayi karfin halin cewa"kari so mana malama Safeena"cikin rashin
kuzari Safeena tadaga kafa ta kariso sai data danganta da kofar dakin Ummi kana tace cikin
rawar murya"Sa....sannunku da....Da zuwa"Yauwa Sannu Dr Tahir ya bata amsa yana kara
kallonta yadda Hijabin yake wani zumbudede dashi harda Safa duk da kanta na duke adan
kallon dayamata yafahimci yarinta karara atare da ita.
Tana cewa haka tafada daki da gudu tana Haki Ummi tayi Saurin mikewa tajawo hannunta suka
shige kuryan daki tace"Safeena mijinkine fa suka zo"sororo Safeena tayi gabanta na tsananta
Faduwa tace"mi...Mi...Mijina kuma Ummi..?"Ummi tace"Eh....Nima kwatsam na gansu kinga
bbu lokaci na aiki Manu siyo ruwa shuru bai dawo ba bari ni in je inji da abinci da za"a
musu,kekuma ki koma gurinsu"Safeena tace"Ammh..Ummi"Ke wai wata irin shashashace ko
bakiji menace miki bane,"Ummi tafada ranta ya baci"Safeena tace"yi Hakuri Ummi zanyi yadda
kikace daga haka tafice tayi tsaye afalo hannunta dafe da kirji tanajin zuciyarta nawani
harbawa.
Sukuwa tana shigewa Dr Tahir ya zunguri Dr Safwan yana Fadin"Kai mijin malama kako ga
malamartaka i think fa itace Safeenar"Banza dashi Dr Safwan yayi sai dannan wayansa
yakeyi,ganin haka yasa Dr Tahir kama kansa agurguje Safeena tadan kara gyara falon ta
shimfida musu darduma kan ledar dake tsakar dakin,cikin sanyin jiki ta leko da kanta tace"ku
shigo ciki kuna zaune awaje"Dr Tahir yace"a"a ayi Haka ranki yadade"mirmishi tayi kawai atare
suka mike Dr Tahir ne yafara shiga da sallama kana Dr Safwan wanda Safeena ke tsaye akofar
dakin har yanzu suka zauna,ita dai Safina kanta aduke takasa motsi Dr Tahir yazauna yana
Fadin"Masha Allahu..Amarya baki tambayi wanene angon naki ba"yafada yana kallon Dr
Safwan dashima yawani sadda kai
Wuf ta fice tana Rufe fuska dukkansu suka bita da kallo Safwan yanajin wani iri aransa kunya
tab to shi ina ma Sakina takeda kunya balle ayi mgana taji kunya,mirmishin gefen baki yayi
yana bin inda tabi da kallo.Dr Tahir sai kallonshi yake yana mai dariya kasa kasa.
Ummi ta fito itama cikin kunya suka kara gaisawa kana tafice ta tararda Safeena zaune a kichen
tayi tagumi Ummi ta kalleta tace"Ke kam Allah yayi miki Sauki...'Safeena tayi saurin mikewa
tana rufe fuskar Ummi tayi dariya kan tace"Allah ya shiryeki..Kinga nifa tuwon shinkafa nakeyi
miyar zogale ya kike gani za'a sake yi musu wani Abun ne..?Safeena tace"Ki barshi Ummi wlh
sai kiga sunfi son tuwon ma "Ummi tace"ok sai na musu zobe su hada dashi,maza ki koma
gurinsu niban ma gane surikin nawa ba duka yaran masha Allah.
Ummi tafada tana dariya mirmishi Safeena tayi kan tafice tana fita manu yakawo ruwan swan
din guda biyu ta amsa ta sanya cikin faranti tahado da kofuna da sallama tashiga suka amsa,ta
durkusa ta ijiye Tahir na mata sannu da aiki tadauki kofi tana tsiyaya musu Dr Safwan yana
kallon ta ta wutsiyar idanunsa aransa yana jinjinama Hajiya mama ita aganinta wanna ficilar
yarinya ne zata iya dauke Nauyinshi tab shi atunaninshi duk randa ya haikemata zata iya
Mutuwa _see dis guy to ka gwadane_í ¾í´’
Gefe takoma bayan ta zuba musu ta zauna akasa kanta a duke tana wasa da yatsun hannunta
kowani dakika na mintina zuciyarta na bugawa,Dr Tahir yasha ruwa yana fadin"Munsha ruwan
Amarya.."Yafada yana mirmishi kan ya cigaba da cewa"an dawo lpy kuma nanawa aka ciyo
mana...?"ta gefen ido take kallon Tahir kan tace cikin sanyin muryanta"Na biyu nayi...Lafiya
kalau"Yace"Wow..Masha Allahu lallai kin cika Hafiza"Mirmishi kawai tayi Tahir ne keta janta da
mgana tana bashi amsa da umh a"a shikuwa Dr Safwan yana ta danne danne awayarsa ammh
hankalinshi kaf akansu yake lokaci kankani yaji yarinyar ta burgesa yadda takeda aji da kamun
kai.
Mikewa DR Tahir yayi yana Fadin"Bari na baku guri ku zanta.."yafada yana ficewa Safwan
yarakasa da Harara,yana waigowa karaf suka hada ido tayi saurin sadda kai kasa mirmishi yayi
yasamu kansa da kuramata ido kur yana kallonta jikinta yabata ana kallonta tana dagowa
idanunwansu suka sarke ma juna,wani miracle ne ke aiki atare dasu kamar ansa super glue an
manne musu sun kasa daina kallon juna.
Safeena taji jikinta na saki da wannan azababban kalon da Dr Safwan ke binta dashi ita tayi
saurin jaye idanunta saboda bazata jure wannan kallon daga Dr ba,jikinta yana rawa takara
dukar dakai tana kara jin bugawar zuciya.