Showing 102001 words to 105000 words out of 257774 words
Chapter 35 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
ta gani wuyarsa...
Yana mai sosa wuyan yake ci gaba da fad’in “Someone tried to kill me Zahra...!” Yai maganar yana mai duban cikin idanun yarinyar...
Ta zaro idanu waje “Kasheka Uncle... Waye kenan... Maiyasa ba’a kamashi ba... Whoever did this to you needs to pay Uncle..!”
Ya murmusa kad’an yace “You think so..?!”
Zahra tace “Haka ne ya kamata Uncle...”
Yazeed ya fuzar da fuci kad’an sai kuma yace “Zahra’u mai kike tunani a duniyar da babu adalci..? Mai kike tunani a Masarauta mai cikeda azzalumai wanda suka d’auki kashe rai ba komai ba...?!”
Kalamanta sunyi mata nauyi, gaba d’aya kwanyarta sai yana neman juyawa, lokaci guda tunanin mutuwar mahaifiyarta yazo mata, k’walla suka ciko idanunta.... Cikin rawar murya take furta “Uncle bana son rayuwa a irin wannan Masarautar... What if... What if this kingdom is cursed... I lost my Maama here... Bana so na sake rasa wani cikin iyayena Uncle what’s wrong with this palace...?”
Janyota yai ya rungumeta yana lallashinta lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Kar ki damu Princess, that won’t happen kinji koh... Amma inaso kisan waye yamin wannan abun Princess...”
Ta d’ago tana dubansa had’ida share hawayen idanunta “Uncle who attempted to kill you..?”
Yazeed ya tsareta da idanu lokaci guda ya furta “Your Father... My brother did this to me... Akan mulki komai za’a iyayi a Masarautar nan.... Mahaifinki kuma d’anuwana da muka fito ciki d’aya shi yayi min haka Zahra...!” Ya k’arashe babu alamun wasa a tattaredashi...
Take Zahra ta mik’e cikeda tsoro tana girgiza kai take furta “No...no Uncle You must’ve got that wrong... My Paa can never do something like that... Please Uncle tell me it isn’t true... Dan Allah kace min ba gaskiya bane.. Not my Paa please...!” Ta k’arashe cikin shesshek’an kuka..
Yazeed ya mik’e tsaye ya kamo hannunta had’ida furta “Unfortunately Zahra... It’s the truth... Your Father is not what you think he is... He’s capable of the worse akan Mulki...!” Ya k’arashe yana mai kuma jaddada kalamansa....
K’ara Zahra ta saki had’ida zubewa wajen daidai lokacinda Mahmood ya banko k’ofa ya shigo...
Hankali tashe yai kan Zahra yana ambato sunanta yana jijjigata...Lokaci guda ya mik’e ya cakumo Yazeed yana jijjigasa yake furta “What did you do to my daughter... Ka fad’a min Yazeed mai kaiwa d’iyata....Yazeeed!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigasa...
Yazeed bai daina sakin murmushi ba yake furta “I didn’t do anything to your precious princess Your Highness.. But you did.. Kai ka jefata a condition d’in da take ciki Rankaidad’e..!”
Mahmood yana tsananin huci yake furta “Yazeed don’t involve my daughter...I’m warning you...!!”
Yazeed ya murmusa yana mai furta “Zaka kasheni ne... Banji mamaki ba Your Highness tinda kayi attempting hakan....!!”
Cikin tsananin huci Mahmood ya dunk’ule hannunsa yana k’ok’arin kaiwa Yazeed naushi Zahra ta mik’e ta tare Yazeed tana mai girgiza kai take furta “Why Paa... Why...? I’m disappointed Paa... Totally disappointed..!!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje tana mai ci gaba da kuka...
Mahmood yabi bayanta yana k’walla mata kira inaa ko juyawa batayi...
Zahra bata zarce ko ina ba sai masauk’in Muhibbah....
SameenaAleeyou 📚
[8/11, 10:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*43*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Bacci ya soma d’aukanta sanda ta jiyo sautin kuka ana bubbuga mata k’ofa... Ta mik’e zumbur tana k’ok’arin danna side lamp, wayarta ta janyo ta duba time tana mamakin waye wannan mai buga mata k’ofa a daidai irin wannan lokacin gashi kuma kukan kaman k’aruwa yake... Jin muryar Zahra na ambato sunanta ya sanyata saurin mik’ewa ta janyo hijab ta zira kana ta nufo parlor... Tana bud’e k’ofar kuwa Zahra batai wata wata ba ta fad’o cikin jikinta tana kuka sosai... Mamaki had’ida tsoro suka kama Muhibbah.... Toh lafiya... Meke faruwa...? Tai tambayar cikin zuciyarta, tana nan tsaye tamkar statue ta hango Yarima Mahmood na K’arasowa cikin tafiya da yafi kama da sassarfa....
“Zahra please, sweetheart listen to me...!” Bai rufe baki ba Ta d’ago fuskarta dake jik’e sharkaf da hawaye tana girgiza kai alamun a’a take fad’in “Just go away Paa... I don’t want to see you..!” Ta k’arashe maganar tana mai fad’awa bedroom d’in Muhibbah a guje ta maida k’ofan ta kulle....
Yarima Mahmood ya lumshe gajiyayyun idanunsa a hankali had’ida fuzar da huci mai d’umin gaske....
Muhibbah dai kallon ikon Allah kurum take tana mamakin Toh mai ya had’a d’iya da mahaifin har haka.... Ta d’anyi gyaran murya ganin har wannan lokacin ya kasa bud’e idanunsa “Your Highness... Lafiya, meke faruwa...?!”
Sai sannan Mahmood ya ware idanunsa ya sauk’esu saman fusarta, ya d’an kwashi dak’ik’ai yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Please take care of my daughter...!” Daga haka bai kuma cewa komai ba saima sa kai da yai ya fice daga sashen gaba d’aya...
Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta kana Ta nufi k’ofan d’aki tana k’wank’wasawa... Da fari Zahra k’in bud’ewa tai har saida tace mata itace kuma Paa d’in ya tafi sannan Zahra ta bud’e mata....
Tana bud’ewa ta kuma komawa ta zauna bakin gado tana mai ci gaba da matsan k’walla...
Gefe da ita Muhibbah ta zauna ba tareda tace komai ba tana sauraron yanda yarinyar ke kuka a hankali, bayan shud’ewan mintoci k’alilan Muhibbah ta kaikaito tana dubanta, lokaci guda ta d’aura hannunta guda saman na Zahra... Zahra ta d’ago kod’add’un idanunta tana duban Muhibban...
Murmushi ta sakar mata mai sanyin gaske “Kina buk’atan wani abu...?”
Girgiza mata kai tai alamun a’a... Muhibbah Ta jinjina kai tace “Alright, ki kwanta ki huta haka nan is late already kinji koh...!”
Bud’e bakin Zahra sai cewa tai “I’ll never forgive him... Ever, wllhi na tsaneshi, Wannan shine abinda yake b’oye min... Na tabbata da saka hannunsa a mutuwar mahaifiyata... If he can kill his own brother da suka fito ciki guda ko shakka babu zai kashe mahaifiyata dik akan banzan Mulkin duniya da bazaka tabbata kanayi ba...!” Kuka yaci k’arfinta....
Sauk’e ajiyan zuciya Muhibbah tai a hankali tace “A duniyar da adalci yayi k’aranci babu abinda ba za’ayi ba Zahra... A duniyar da son mulki da neman dukiya tako wane irin hanya yayi k’amari babu abinda baza’ayi ba... Ana kashe rayuwa domin a cimma wani buri na duniya... Shi d’an adam mai yawan zalinci ne kuma mai yawan bijire maI yawan bijire ma rahamar Ubangijinsa ne... Amma maiyasa kike danganta mahaifinki da munanan laifuka irin wannan...?!”
Dubanta Zahra tai hawaye na gangaro mata “Sabida yau d’in ni ganauce ba jiyau ba... Mahaifina ya tasamma kashe Uncle Yazeed akan rikicin mulki... Idan baki manta ba na tab’a sanar dake inaji a jikina yana b’oye min wani abu gameda mahaifiyata wanda baya so na sani... Ko shakka banayi abu ne da ya shafi mutuwarta.. A ido mahaifina yafi kowa kyawawan d’abi’u cikin gidan nan ashe a zuciya yafi kowa munin halayya.... Ya cuceni ya zalunceni ya rabani da mahaifiyata...!” Ta k’arashe ciki shesshek’an kuka...
Rungumeta Muhibbah tai cikeda tausayawa lokaci guda cikin kwantar da hankali take fad’in “Wasu lokutan mukanyi mummunan zato ga mutanen kirki kaman yanda wasu lokutan mukanyi kyakkyawan zato ga mutanen da ba na K’warai ba, amma a koda yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato tsakanin al’umma... Shi munana zato bazai kaika ga komai ba face tarin dana sani da kuma zunubi mai girma... Zahra shin kina zaton shi Uncle d’in naki mutumin k’warai ne...?!” Tai tambayar tana mai tsare yarinyar da idanu...
Dubanta Zahra tai had’ida jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “Da kyau da kikai masa zato mai kyau... Toh inaso kiyi haka ga mahaifinki, ki kyautata masa zato... Kince rikicin mulki suke shiyasa kike ganin mahaifinki shine bad guy a nan koh... Tsawon shekarun da kikai da mahaifinki kin tab’a shakkun kyawawan d’abi’unsa a baya...?!”
Zahra tai saurin girgiza kai alamun a’a... Muhibbah taci gaba da fad’in “Ya tab’a aibataki ko mahaifiyarki a gaban idonki kokuma kiji labari...?!”
Nanma girgiza kai Zahra tai alamun a’a... “Kin tab’a jin labarin yaci zarafin wasu mutane tun kuna k’asar Spain har kawo dawowarku Nigeria...?!”
Naman Ta girgiza kai alamun a’a cikin matuk’ar sanyin jiki...
Muhibbah Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “SARAUTA...! Sai akan sarauta kike zaton zai aikata abubuwan da ya aikata koh...?!”
Tai saurin jinjina kai alamun amincewa...
Muhibbah ma Ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh kisa a ranki cewa rikici na mulki ne tsakanin mahaifinki da d’an uwansa... Amma kar Ki tab’a kokonton k’irkin mahaifinki kinji koh...!”
Tai k’uriwa Muhibbah tana dubanta, lokaci guda Ta jinjina mata kai a hankali sai kuma tace “Toh ta yaya zan cire kokonton abinda yake b’oye min gameda mahaifiyata Tia.... I really want to know what he’s hiding...!”
Muhibbah tai mata K’uri na wasu ‘yan dak’ik’ai kana tai gajeren murmushi tace “It’s simple Zahra.... Kinaso mahaifinki ya sanar dake abinda yake b’oye miki ba tareda wani kwana kwana ba...!”
Yarinyar tai saurin jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “You ask him in public... Ki tambayesa a bainar jama’a mutanen da yake jin nauyinsu yake kuma da kima a idanunsu...”
Zahra ta dubeta cikin rashin fahimta tace “But I know Paa, bazai bani amsa direct ba... Ni nasan ko Shid’in wane irin mutum ne...!”
Muhibbah Ta murmusa kad’an sai kuma tace “Kema ba direct zaki tambayesa ba... You accuse him of something very big... Abinda kike tunanin shi yake b’oye miki... Like mutuwar mahaifiyarki... Ina mai tabbatar miki muddin baida saka hannu ciki zakiji komai dan bazai juri jin kunyan idanun duniya ba... Take zai fayyace miki duk wani Abinda ya jima yana b’oye miki...!” Ta k’arashe cikin jaddada kalamanta...
Murmushi Zahra Ta saki kana tace “Kai amma na gode Tia... Perfecto, wannan shine kawai hanyar da Paa zai sanar dani abinda yake b’oye min.. Thank you thank you Tia... Gracias..!” Ta k’arashe tana mai rungumarta...
Murmushi Muhibbah keyi tana shafa kan yarinyar lokaci guda tana hango fuskar Mahmood yanda zai falling gaban d’inbin jama’an Masarautar nan... Zai sha kunya zai fad’i k’asa warwas kuma abinda zaifi masa ciwo shine d’iyarsa itace downfall d’insa... He’d definitely get what’s coming for him.... Finally zata gama da Mahmood da martabansa cikin Masarautar...! Ta k’arashe hawaye mai ciwo na gangaro mata, lokaci guda tinanin k’uncin rayuwa da uk’uban da ta shiga ansanadiyan yaran Sarkin na zuwa mata daki daki... Ta lumshe idanunta tana k’ok’arin saita kanta dan kar Zahra ta fahimci wani abu... A tare sukai bacci nan d’akin Muhibban tana mai kuma calming Zahra harda bedtime stories tai mata Zahra na dariya take fad’in Ta tuna mata lokutan baya haka Maa d’inta da Paa sukan sakata tsakiyan gado suyita bata tatsuniyoyi da labarai masu dad’i har bacci yayi gaba da ita kafin su tafi nasu d’akin.. Wasu lokutan ma haka gaba d’aya bacci yakan d’aukesu gaba d’aya.... Muhibbah saidai tai murmushi tana jin Zahra na labarin wasu kyawawan d’abi’u na mahaifinta.. Ba tareda tasan cewa cikin zuciyar Muhibbar babu komai sai tsanar Mahaifin nata da k’yamatarsa.... A haka bacci b’arawo ya sacesu...
**
Washe gari Fada ta cika fam da masu sarautun gargajiya, yaran Sarkin kaf suna nan idan ka d’auke Mahmood wanda tun safe yai ficewarsa daga Masarautar... Yazeed sai famkam famkam yake za’a tabbatar dashi matsayin sarki mai jiran Gado sannan Juma’a mai zuwa a nad’asa... Sautin algaita da tambura sai tashi suke cikin masarauta... Yazeed yasha gayu cikin kayan sarauta tamkar wani d’awisu haka yake taka k’asa Hadiminsa na biye dashi yana masa kirari da yabo irina gidan sarauta....
Babban Zauren taro ya cika fam da masu sarauta... Yazeed ya k’araso gaban Fu’ad dake binsa da muguwar kallo tun shigowarsa, murmushin nan nasa ya saki da gefen baki, yayi tsayuwa irinta masu ji a Mulki gaban Fu’ad, hannayensa hard’e yake dubansa kana yai gyaran murya kad’an yace “Aren’t you gonna congratulate me little brother... Ko har yanzu kana shakkun ni ne nan zan zama Sarki...?!”
Fu’ad ya d’an murmusa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannunsa biyu wanda yin hakan d’abi’arsa ce, ya k’arewa Yazeed kallo daga sama zuwa k’asa ya d’an kauda kai gefe yana kuma sakin murmushi yace “Ai banga Sarkin ba balle nai maka murna... B’ata lokacinka kawai kake don na tabbata kai d’in har abada bazaka tab’a zama Sarki ba muddin za’a bi cancanta da kuma dacewa...!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya...
Yazeed ya kai k’ololuwar b’acin rai... Sai faman sakin huci yake yana tururi yake duban Fu’ad ji yake tamkar ya kai masa naushi sai faman dunk’ule hannunsa yake... Bazai iya jure kalaman Fu’ad ba... Ya yunk’ura zai kai mai naushi Jamal dake gefe yai saurin rik’esa a hankali yake furta “Don’t make a scene here please Yazeed..!”
Fu’ad na murmushi yake fad’in “Barshi... Please do it... Go ahead, do it Yazeed... Ka nuna musu asalin kaid’in ba wanda kake faking ba... Just do it...!” Ya k’arashe cikin huci....
Jamal ya janye Fu’ad yana fad’in “Ya isa haka Fu’ad, karku bamu kunya dan Allah... Martaban gidanmu zaku tab’a...!” Fu’ad ya d’an dubi Jamal had’ida fincike hannunsa ya koma gefe ya zauna yana sakin huci dan dukansu biyu da Yazeed d’in har Jamal d’in haushi suke basa idan ya tuna tilasta masa da sukai ya aikata laifin da har yau yake danasanin aikatawa tsawon rayuwarsa.. Laifin da ya zama silan rugujewar rayuwarsa da Farin cikinsa....
Yazeed kaw k’arasawa yai yana ci gaba da taku cikin babban Zauren masu muk’amin cikin Fada na kawo masa caffa (Gaisuwa irinta masu mulki) kai kace an riga an nad’asa... Shi kad’ai sai wani cika yake yana ayyana hukunci mai tsauri da zai yanke wa Mahmood da zaran an nad’Asa Sarki.... Tabbas Mahmood zai zama abin kwatance cikin Masarautar, sai ya d’and’ani kud’ansa Ta yanda sunan Sarki Yazeed kawai yaji an ambata zai daburce hankalinsa ya gushe... Ya murmusa kad’an yanajin badon Shid’in yanzu sarki bane da tuni ya fashe da dariya tsaban tsananin munin horon da ya tanadarwa Mahmood d’in.... Yana tsaka da tinanin ne yaji cak sautin algaita da tambura sun tsaya kaman daga sama ya hango Majidad’i ya shigo cikin Zauren kai kace jeho sa akai... Doguwar takobinsa rik’e a hannunsa sai faman huci yake tamkar wani zaki....
A d’ari Yazeed ya mik’e tsaye yana ware idanu tabbas wannan mahaukacin ne rik’eda takobi....
Majidad’i na dariya yake fad’in “Wow wow wow..! King Yazeed AbdulJabbar ai ban zanci har munyi wasan Takobin har kaci har an nad’aka ba.... Ka mance ne na tuna maka...? Agreement d’in namu ba haka bane Dark Prince... Bayan mun kai Mahmood k’asa Wasa za’ai d’aya ya fille kan d’aya wanda yai nasara shine zai zama Sarki..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji yana mai zaro Takobin daga cikin gidanta...
Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka mik’e tsaye suna kallon kayan Al’ajabi wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan....
Ana tsaka da wannan yanayi kururuwa da hayaniya had’ida ihu ya gauraye cikin Fada ana fad’in bayyanar Mahaukaciya... Dogarai sai faman guje guje suke ana kokawan Kamata amma sun kasa....
Giwa Alkyabba a hannu ta nufo k’asa dan ita kanta kururuwan da hayaniyar har tsakan kanta takeji ga hannunta dake tsananin mata k’aik’ayi wanda bata tab’a jin irinsa ba.... Tafiya kurum Giwa take ba tareda sanin yanda take jefa k’afafunta ba... Bayi sai k’amewa suke suna bata hanya ... lokaci guda take doka kiran Jakadiya a hargitse...
Masarauta babu lafiya...
*Toh fah yau akeyinta ga Izzatu ta bayyana....Ga kuma Yazeed da Majidadi ko yaya wasan zata kaya.....???
SameenaAleeyou📚
[8/13, 7:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*44*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A daidai mashigar sashen nata suka had’uda Jakadiya jikinta sai karmami yake, illahirin jikinta rawa yake... Cikin tsananin tashin hankali Giwa taceda Jakadiya “Jakadiya mai nakeji... Shin da gaske Izzatuce ta bayyana...?!”
Jakadiya tai saurin jinjina kai tana mai zubewa saman gwiwoyinta “Allah shi taimakeki gaskiya ne Izzatu...Izzatu itace Ta bayyana cikin Fada...!”
Giwa ta zaro idanu waje tana dafe da k’irji take fad’in “Jakadiya hakan ba mai yuwa bane... Sanin kanki ne bayyanar matar nan tashin hankali ne tsantsa da musiba cikinta... Bayyanar Izzatu yana nufin za’ai babban rashi cikin Masarauta... Jakadiya ina Ubandoma... Shi kad’ai yake iyawa da Izzatu ta k’arashe cikin wane irin yanayi mai gauraye da d’imauta....
Jakadiya Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Allah shi taimakeki kin mance cewa Ubandoma yana tsare hannun Masarauta... Bamuda hurumin tunk’aransa a halinda ake ciki...!”
“Jakadiyaa!!” Giwa ta darara mata wani irin gigitaccen tsawa wanda ya sanyata mik’ewa tsaye zumbur ba tareda tasan tayi hakan ba...
Giwa taci gaba da fad’in “Mune Masarauta, mune Fada Jakadiya babu Uban da ya isa ya hanani aiwatar da dik abinda naga dama cikin Masarautar nan, ba’a haifa ba kuma baza’a haifesa ba... Badon mahimmanci da rayuwar Izzatu kedashi a gareni ba da yau d’in Ta bak’unci lahira kowa ya huta...!! Jakadiya inaso Ki nemomin Ubandoma yanda ya shiga ya fita..!!”
Cikeda risinawa Jakadiya tace “An gama rankishidad’e..!!” Daga haka sa kai tai Ta famtsama cikin Masarauta tana tinanin Ta yanda zata soma neman Ubandoma gashi babu Waziri babu dalilinsa, duk tulin kiran da Giwa Ke masa sam bai d’aga ko guda d’aya ba... K’irjin Giwa yaci gaba da bugawa ba tareda tasan dalili ba... Hankalinta bazai kwanta ba muddin bataga Izzatu a hannunta ba... Ya zama tilas Ta canza ma Izzatu ma’ajiya idan ba haka ba tabbas duk wasu abubuwan da ta jima tana ginawa tsaf zasu rushe, sadaukarwar data jima tanayi zai tashi a aikin banza ita kuwa sam bazata tab’a barin hakan ya kasance ba...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai fitowa daga sashen nata...
Ganin Masarautar a cike mak’il yasata tina cewa ashe akwai taron cikin Masarautar sam sabgogin gabanta sun sa ta mance hakan... K’irjinta ya kuma bugawa tamkar an sauk’e mata guduma... Lallai kuwa Izzatu bata zab’i rana mai kyau ba... Bazai yuwu yau d’in tayi shawagi cikin Masarauta ba hakan barazana ne Babba gareta... Babu shiri ta koma sashenta yanda ta umarci Hadimanta guda biyu su fiddo mata sutura na mulki da k’asaita dole ta nufi babban Zauren taro zama a fadarta bai ganta ba yau d’in....
Muhibbah da fitowarta kenan daga b’angaren su Umaima tayi rakiyawa Zahra ta barota tareda Umaiman bayan taceda Umaiman ta kula da ita dan har lokacin Zahra bata wani dawo dai dai ba nan ta hangi wilk’awan Giwa tamkar giftawan walk’iya... Koda ganin irin tafiyar da Giwa take kasan babu lafiya... Tai d’an jim tana mamakin meke faruwa dan su sam basuji duk hayaniyar da ake cikin Masarautar ba...
Wasu bayi dake kakkab’e babban parlorn Giwa na k’asa ta sinkayo suna fad’in tashin hankalin dake cikin Fada na bayyanar mahaukaciya... Gabanta ya