Showing 15001 words to 18000 words out of 257774 words
Chapter 6 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
*šāØMUHIBBAHāØš*
*008*
*Ā©ļøSameena Aleeyou...āš½*
Tinda ya kwanta yake wasu irin mafarkai marassa kyau, da fari mafarkin matarsa Aliya da mahaifinsa yai, bayan yayi adduāa ya sake komawa wani mafarkin ya kuma tadashi... Wannan karon akan Kāannensa guda Uku ne, abinda ya gani cikin mafarkin sosai ya tada masa hankali... Tsaye ya hangi Yazeed da Fuāad rikāe da takubba a hannayensu ko wanne takwabin dake hannunsa na dāigar da jini wanda yake jajazir.... Sunayensu ya ambata cikeda tashin hankali ganin abindake rikāe hannayensu, cikin kidāima ya nufi yanda suke a tsaye suna maida huci suna nunasa da takubban dake hannayensu lokaci guda suka fashe da dariya basu daina nunasa da takubban ba... Mamakin dariyarsu yake bayan abinda ya gani rikāe hannayensu, kāarasowar da zai kusansu sai hango wani dāaki yai a budāe cikin jerin wasu dāakuna... Basu daina dariyar da suke ba har Mahmood ya nufi cikin dāakin mai tsananin duhuwa.... Saidai yana shiga dāakin ya hango mahaifiyarsu zaune saman gadon sarautar masarautarsu... Kāirjinsa yaci gaba da bugawa sanda ya hango dāan uwansa da yakeda tabbacin ya fita zakka cikin sauran āyan uwan nasa durkāushe kan wata yarinya sai darza mata wukāar yake... Ga jini na kwarara amma da alama bata mutu ba.... Cikin zafin nama ya ambato sunan Jamal da kāarfin gaske, saidai ko gizau Jamal bai ba saima ci gaba da darza mata takwabin da yake... Tsalle Mahmood yai ya finciko Jamal don ceton yarinyar amma mai..? Yana dāagosa saiji yayi an luma masa takwabi a cikin cikinsa... Mahmood ya rikāe cikinsa yanda jini ke malala a kāasa.. Ya dāago yana duban āyan uwansa guda Uku rikeda takubban saidai bazaice ga wanda ya caka masa ba cikinsu, maida dubansaga mahaifiyarsu dake zaune saman Karagar mulkin yai saidai wannan karon matarsa Aliya ya gani ba mahaifiyarsu ba...Hannu yake mikāa mata alamun neman taimako amma inaa batai ko gizau ba tana nan zaune saman Karagar mulkin saima sakin dariyar da take mai firgitarwa... A hankali yake ji numfashinsa na dāaukewa jikinsa na zamewa har saida ya fadāo kan yarinyar da Jamal ya gama yankata da takwabi, su duka biyu jini na malala daga jikkunansu.... A daidai wannan lokaci ne ya farka daga baccin cikeda tsananin tashin hankali... Adduāoāin da sukazo bakinsa kawai yake iya karantawa hadāida jero hasbunallah wa niāimal wakil... A hankali yake jin natsuwa na saukāo masa cikin zuciyarsa... Hannu ya mikāa ya kunna side lamp kana ya dubi kāaramar agogo dake gefen bedside ya nuna kāarfe 4:30am, anata kiraye kirayen assalatu... Shafe fuskars yai da duka hannayensa biyu kana ya mikāe ya nufi bathroom ya dāauro alwala, shimfidāa abin sallah yai amma ko tsayuwar sallar saiji yai ya kasa... Ya zauna nan bakin gado abubuwan na kuma zuwa masa... Wannan wane irin mafarki ne mai cikeda rudāani da kuma tashin hankali.... Mai wannan mafarki yake nufi...? Take yaji wani bāangare na zuciyarsa na raya masa _Akasarin munanan mafarkai Daga shedāan ne ka nemi tsari da kariya daga shedan.._ Ya saukāe nannauyan ajiyan zuciya yana mai kuma shafe fuskarsa, tabbas āyan uwansa bazasu iya kashe ran wani ba koda bawa ne balle nashi.... Ya fuzar da fuci a hankali yana neman tsari daga shaidāan da kuma munanan abubuwan da ya gani a cikin baccinsa... Ya jima zaune wajen har saida ya soma jiyo kiran sallar asubahi... Ya mikāe ya dāauki cazbaha da kāaramar littafin azkar dāinsa na hisnul Muslim kana kana ya nufi masallacinsu dake nan cikin Masarautar....
Nan cikin masallacin ya tadda Jamal zaune yana wurdi da alama sallar nafila ya ida yana jiran kāarsowar imam a tada sallar asuba... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali natsuwa na saukāo masa, tabbas wannan mafarki nashi daga shedāan ne... Of all people bazai yuwu ma ace Jamal ne zai caka masa wukāa ba... Nan ya kāarasa hadāida zama gefen Jamal dāin... Suka sakar ma juna murmushi kana Jamal ya mikāa masa hannu alamun masabaha... Zamansa da kadāan kaw Imaam ya shigo suka tada sallah....
Bayan an ida sallah ne suka jera suna fitowa a tare suka nufi bāangaren mahaifiyarsu... Suna tafe Yarima Mahmood ya dāanyi gyaran murya kadāan kana ya dubi Jamal yace āNikam har yanzu Yazeed na nan da halinsa na kāin zuwa sallah...? Naga tinda na dawo bana ganinsa a jamāi and Fuāad ya akai yau bai fito sallah ba...?ā
Murmusawa kadāan Jamal yai wanda murmushin dāabiāarsa ce kana yace āBabu abinda ya canza da Yazeed Yaya... Fuāad kuma baijin dadāi ne shisa baka gansa ba...ā
Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali suna tafe cikin kamfacecen masarautar nasu da duk yanda suka gifta sai bayi sun risina Sun gaidasu.... A haka suka iso sashen mahaifiyar tasu...
Jakadiya ce Tai masu iso kana suka shiga suka taddata zaune saman abin sallarta da alama itama sallar Ta ida tana gabatar da wurdi...
A jere sukai zama irinta rakāumi saman Darduma dake a saitin mahaifiyar tasu wanda dama dominsu darduman yake aje wajen, dik sanda suka shigo gaisheta a nan suke zama...
Ta ida adduāoāinta suka shafa a tareda yaran nata, murmushi fal fuskarta take dubansu....Tsananin kāaunarsu na ratsa dik wani kafa na jikinta, Mahmood ne ya soma gaidata sannan Jamal... Ta amsa masu cikeda so da kāauna hadāida shi masu albarka... Daga nan ne take sanar dasu jiya Galadima ya sanar da ita cewa Yau dāin da yammaci zasuyi zama kan maganar wanda zai gaji mahaifinsu Sarki AbdulJabbar mai rasuwa...
Sosai suka natsu suna sauraren Mahaifiyar tasu sanda taci gaba da fadāin āSadauki..!ā
Yarima Mahmood ya dāago yana dubanta, Giwa taci gaba da fadāin āNa riga na zabāeke matsayin wanda ni nakeso ya gaji mahaifinku, toh amma Galadima ya tabbatar min cewa cikin masu neman sarautar nan harda Majidadāi dāan dāan uwan mahaifinku Wambai da kuma biyu daga cikin yaran Marigayi Talba mai rasuwa, sannan da shi kanshi Chiroman gari yana neman Karagar Masarautar garin nan... Dan haka ni a nawa bāangaren na tsaida kai, kuma na tabbata king makers bazasu bani kunya ba, domin kaw daga Galadima har Waziri a bāangaren mu suke, kuma sunyi Naāam cikin masu neman sarautar Masarautar nan babu wanda ya dace ya maye gurbin mahaifinku sai kai Sadauki....ā Ta kāarashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta, yayinda Jamal yaci gaba da jinjina kai yana furta āTabbas Maami, Yaya shi kadāai ya dace ya gaji Abbah... Cikin duka wadāanda kika lissafo, sannan dama ance kyaun dāa ya gaji mahaifinsa... Kuma idan har sarauta ya fice daga gidan nan haka munaji muna gani zaāa sallamemu mu bar Fada mu koma cen wani kāauye a nadāamu hakiman kāawye... Yaya youāre the rightful heir to the throne... Kai ka cancanta ka dāale wannan karaga...!ā Ya kāarashe yana duban dāan uwan nasa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa....
Kāuri Mahmood yai masu yana dubansu kana ya saukāe ajiyan zuciya a hankali yana mai shafe fsuksrsa da tafukan hannunsa, ta yaya zai sanar dasu ba abinda ya dawo dashi Masarautar nan ba kenan.. Ta yaya zai sanar dasu ba neman mulki bane gabansa, ta yaya zai sanar dasu abinda ya dawo dashi yasha bambam da abinda suke tinanin shi ya dawo dashi.... Muryar Giwa ya sinkayo tana ci gaba da fadāin āKai nake sauraro dāah na nasan bazaka bani kunya ba...!ā
Kāakāaro gajeren murmushi yai irinta masu mulki kana ya soma fadāin āAllah shi taimaki Giwar Sarki AbdulJabbar, Allah shi taimaki Mai babban dāaki... Allah shi taimaki Gimbiya Turai dāiyaga Sarki Jamaludden na kāasar Benin, La princesa de benin (the Princess of Benin), La reina de jos (the Queen of Jos)... Mi hermosa madre (Kyakkyawan mahaifiyata) Allah yaja zamaninki...!!ā
Tinda ya soma mata kirari take dubansa da murmushi saman fuskarta, hannu tasa ta shafi fuskarsa kadāan kāwalla tab idanunta... Tana matukāar kāaunar Mahmood, akwai wani abinda ya banbanta dashi cikin āyan uwansa...
Yarima Mahmood ya dāan kamo hannunta ya sumbata su duka biyu dāin suna sakarwa juna murmushi kana ya soma fadāin āMaami, bawai na banbanta da raāayinki bane... Bawai bana son amsar tayinki bane... Ke duk kin wuce haka a wajena... Umarni kawai zaki bani nabi.... But Maami, sarauta ba layina bane... Almost 14 years bana Masarautar nan saidai nazo lokaci zuwa lokaci, da yawan wasu abubuwan ban saba dasu ba, ban San ya ake gudanar dasu ba... Maami idan nace zan amshi sarautar Masarautar nan hakan na nufin tamkar sabon karatu zan fara, dole na koyi abubuwa da dama.... Inaga zaifi kyau Idan aka nadāa wanda yafini cancanta da dacewa da rikāon Masarautar...ā
Cikin saurin Yarima Jamal Ke girgiza kai yana fadāin āNo, no Yaya... Babu wanda ya dace ya kuma cancanta face kai, Yaya kana so mun fice daga Masarautar nan ne cikin kāaskāanci da tozarci...? Yaya kana sona fidda matan mahaifinmu a dāakunansu akaisu wani kāauye ne..? Yaya so kake mu fice daga cikin gidan da aka haifemu aka renemu cikinsa...? Yaya so kake mu bar asalinmu da abinda muka gada... Nasan duk bazaka so abubuwanda lissafo su faru ba....!ā Ya kāarashe cikeda kulawa...
Giwa kam kāuri taiwa Mahmuda tana kallon sarautar Allah...
Yarima Mahmood ya kamo hannayen Yarima Jamal su duka biyu dāin suna duban juna sanda Mahmood Ke fadāin āDik ba wannan nake nufi ba Jamal, kuma bana fatan dāaya daga cikin abubuwanda ka lissafo su faru, sannan Allah ya albarkaci mahaifinmu da yara maza dāai dāai dāai har guda hudāu and we are all entitled to the throne.... Ga Yazeed gaka nan, even Fuāad zai iya zama sarki ba wani abu bane.. Ba lallai sai Babba ba kāaramin cikinmu ka iya zama kan Karagar mulkin nan hardai yanada damar data mallaka masa hakan... So Maami why not a tsaida dāaya daga cikin āyan uwana....ā Wata kakkausar murya ce da ko shakka babu sun San mai ita ta katsesu da fadāin āBabu wanda ya isa, babu mahalukāin da ya isa ya fitar da mulkin Masarautar nan daga hannun ahalinmu... Babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan mahaifina, Mu kadāai ne jinin sarauta, mu kadāaine muka gaji sarautar... And yes Yaya, youāre absolutely right... Naji dadāi daka dāauki shawarina... For the first time weāre on the same page, kai kanka ka amince babu wanda ya cancanta ya zama sarki face ni Yazeed..!!!Dāaddāaya yake maganar yana takowa cikin katafaren dāakin hannayensa guda biyu hardāe ta baya, cikin taku mai cikeda kāasaita yake tafiyar nasa tamkar wani Amale... saida ya iso dadai tsakiyar dāakin kana ya karkato yana fuskantar Mahmood, lokaci guda yake furta āAnd now that we are on the same page, inaso ka jaddadawa wadāannan masu sarautun Gargajiyan kar wani daga cikinsu yayi gigin shiga gonata, ina rantsuwa da mahallicina idan dāayansu yayi kuskuren jayayya dani da sarauta ta, ba rawaninsa kawai da mukāaminsa zai rasa ba, zai iya rasa abinda yafi wadāann mahimmanci a wajensa... Ina nufin zai iya rasa ransa..!!ā Ya kāarashe cikin tsananin huci...
Girgiza kai kadāan Mahmood yai kana yace āAnd kana tunanin kaine wanda ya dace da kujerar..?ā
Saida ya kuma takowa kadāan murmushin bai bar saman fuskarsa ba kana yace āIām far better than right... I am perfect... Yeah Perfect..!ā Ya kāarashe cikeda pride
Kāuri Mahmood yai masa yana dubansa , lokaci guda ya mikāe tsaye suna fuskantar juna shida Yazeed, idanu cikin idanu suke duban juna kana Mahmood ya soma fadāi cikin dakewar murya āWanda duk yace shine toh ba shi bane, sannan baāa shugaba mai zafin zuciya wanda baida jarumtar kwantar da zuciyarsa idan rai ya bāaci, baāa shugaba maras dāaāa da ganin girman na gaba, baāa shugaba maras tsaida dokokin Ubangijinsa... Shi shugaba ya kamata ya kasance mai taushin zuciya sannan Jarumi, taushin zuciya domin ya tausasawa alāummansa yaji kāansu sannan ya kwantata adalci a tsakaninsu, Jarumi domin ya zamto sulke wajen kare alāummansa da tsaresu daga abokan gaba... Mai bin dokokin Ubangijinsa domin ya zamto abin koyi ga Alāummarsa... Mai girmama na gaba domin wadāanda suke kāasa dashi su girmama shi.... Ta yaya nake tunanin zaka iya zamtowa shugaba bayan baka aikata dāaya daga cikin abinda na lissafo... Nayi kuskure da nai zaton zaka iya maye gurbin mahaifinmu.... Yanzu na tabbata baka cancanta ba Yarima Yazeed....!!ā Ya kāarashe yana mai kuma matso da fuskarsa dab na Yazeed cikin muryarsa mai cikeda amo....
Shuāumin murmushin ne nasa saman fuskarsa, lokaci guda ya lankāwasa Kai kadāan yana mai kāarewa Mahmood dāin kallo kana yace āToh waye ya cancanta..? Kai...?!ā Yai murmushi mai sauti irinta masu mulki kana yaci ya a da fadāin āIdan duk kanada qualities dāin daka kāirgosu abu guda dāaya tak da ka aikata ya rushesu... Yarima Mahmood... Makāaryaci yafi dacewa da shugabanci irinta siyasa amma ba shugabanci irinta Babban Gida ba..!!!ā
Cikin zafin nama Mahmood dake tsananin huci yake furta āDonāt Yazeed... Donāt you dare cross the line...!!!ā
Yazeed da ko a jikinsa Murmusawa ya kumayi kana yace āOh really now... Your Royal highness..! Baka so a fadāi naka aibun, bayan Kai ka iya fadāin na wasu cikeda kāwarin gwiwa... Ai baāa sarki matsoraci mai tsoron Ta kife... Kāaryar Jarumta kake...Yarima Mahmood..!!!ā
āYazeeeedddd!!!!ā Ya daka masa uban tsawa hadāida dāaga hannunsa da niya watsa masa mari... Saidai tuni Jamal ya shige tsakaninsu yana tausan Mahmood āYaya please donāt... Kar ka mareshi... Kayi hakāuri dan Allah....Allah ya huci zuciyarka..!ā
Idanuwansa da suka kadāa sukai jazir yake duban Yazeed dasu, abinda da wanda bai iya bāacin rai ba sai abin ya zama abin ban tsoro... Kana iya hango yanda kāirjin Mahmood Ke hawa yana saukāa alamun tsananin bugun zuciya da bāacin rai....
Lokaci guda yake nuna Yazeed da dāan yatsa kana yaci gaba da fadāin āIāll warn you for the last time Yazeed.... Do...not..try..me!!! Do..not..cross..the line..!!!ā Daga haka sa kai yai ya fice cikin sassarfa da tsananin bāacin rai...
Yazeed ya rakasa da muguwar kallo kana ya kuma sakin shuāumin murmushinsa, gyara zaman rigarsa yai hadāida kuma hardāe hannayensa ta baya dāabiāar masu mulki, ya maido da dubansanga mahaifiyarsu data cika tai fam, ta tsaresa da idanu cikin tsananin bāacin rai....
Dukda ya hango tsananin bāacin rai a idon mahaifiyarsu hakan bai hanasa sakin murmushi da gefen bakinsa ba, kana ya isa kusan kāafafunta ya zauna yana mai gaidata, ya kāarashe yana fadāin āA saka min albarka Maami na...!ā
Daga Giwa da Yazeed ya dāauko hannunta guda ya dāaura saman kansa alamun saka albarka har Jamal dake tsaye tamkar statue kallon mamaki suke bin Yazeed dashi... Shifa ko a jikinsa da alama, baima san yayi laifi ba... Yazeed bazai tabāa canzawa ba, Ta zaci aure zai canza Yazeed gashi yayi yara har biyu amma halinsa na nan babu abinda ya ragu saima wandake kāaruwa... Har kullum adduāan shiriya takewa Yazeed amma kaman dadāa tabāarbāarewa yake... Tana ji ya gama fadāin iyaka abinda zai fadāi tamkar wani mai bata sakāo kana ya mikāe yai ficewarsa cikeda kāasaita wanda Ke matukāar masa kyau...
Jamal ya bisa da kallo har ya bāacewa ganinsa kana ya maidoda dubansaga mahaifiyarsu da ko shakka babu kāwalla yake hangowa cikin idanunta, dukda kāokāarin dannesu da takeyi, shidāin yafi kowa sanin mahaifiyarsu yasani idan abu na matukāar damunta... Bai wata wata ba ya isa yanda magungunata Ke aje ya dāauko da kansa yana bāalla mata dan bazai iya jiran wata kuyanga tazo bata magani ba... Sai faman sannu yake mata yana tausanta... Jinjina masa kai kurum take abubuwa da dama kāunshe cikin zuciyarta... Idanma aka ce an bar karagan mulkin nan tsakanin yaranta kadāai tasan wani yakāi ne mai zaman kansa... Sai yanzu maganan Talāudu ke kuma dawo mata da yace yaga kāura mai duhuwan gaske da dandatson mayakāa... Amma koda zaāa tashi wannan masarauta bazata tabāa bari dai sarautar ya kufce masu ba... āWambaiā sunan da zuciyarta ta ambata...
Take ta sanar da Jakadiya Tai mata kiran Ubandoma...
***
Tsaf ta shirya cikin jan leshi dāinkin doguwar riga da yai matukāar amsarta, ta dāaura alkyabba fara kāal wanda Umaima ta Aiko mata da safen nan... Tsaye tai gaban full length mirror tana duban Wai ita SAUDATU ke sanye da kaya ta mulki da sarauta yau dāin... Ta tina sanda ta fice daga Masarautar cikin kāaskāanci da tozarci yau sai gashi ta dawo cikin karamci da girmamawa... Tabbas Saudatu ta mutu Muhibbah ce a raye yanzu...Ta saki murmushi mai ciwo a hankali kumatunta suka lotsa... A fili take furta āYou better be ready, cos my revenge is action...!!ā Ta kāarashe cikin tsananin karaji tana mai duban fuskarta cikin madubi.....
(Anya bakiyi kuskure ba Muhibbah...? Muje zuwa..)
SameenaAleeyouš
[5/29, 9:41 PM] +234 703 453 9908: *šāØMUHIBBAHāØš*
*009*
*Ā©ļøSameena Aleeyou...āš½*
Zama yai gefen bedside yana jiran fitowarta dan yaji alamunta a closet, ya sani bazai wuce shirin school take ba...
Idanunsa suka saukāa kan picture dake aje gefen bedside dāinta, ya jima yana duban picture dāin... Lokaci guda ya saki murmushi a hankali dan bazai tabāa mance ranan da sukai hoton ba a cen kāasar Spain, lokacin family dāinsa na cikeda Farin ciki, inama abubuwa zaku koma kaman yanda suke before.... Yasa hannu ya dāauki hoton yana shafawa a hankali... Zahra da fitowarta kenan daga closet sanye cikin shiga irinta āyanmakaranta tsaye tayi tana duban mahaifin nata yanda yai kāurima picture dāinsu, lokaci guda tausayinsu gaba dāaya na kuma kamata.... Ta dāan tako kadāan kana ta zauna gefensa...
āGood morning Paa...ā Ta fadāi sanda take zama...
Gyara zamansa ya dāanyi yana mai aje picture dāin kana yace āGood morning my love... Da fatan kin tashi lafia..?ā
Jinjina masa kai tai kana tace āLafia Paa... How about you Paa..? You seemed worried... Is something bordering you..?ā
Kāakāaro murmushi yai hadāida shafa kanta kadāan āBabu komai Princess, do you want me to take you to school by myself...?ā
Dāan dubansa tai da mamaki kana ta murmusa āCāmon Paa, kai da kanka kake ce min nan ba Spain bane, things are different here...Well, Iām starting to get used to it... Nasan bazamu tabāa komawa kaman yanda muke a baya ba... It hurts tho..!ā Ta kāarashe tana mai zura safar kāafanta....
Dubanta yake da wasu irin idanu, shi kadāai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa, yanada good relationship da dāiyarsa, bazaiso wani ko wani abu ya bāata wannan alakāa mai kyau da yakedashi shida dāiyarsa ba, Amsar socks dāin da take kāokāarin sakawa yai lokaci guda ya saukāo daga saman gado yana zira mata safar a kāafarta... Zahra tai masa Kāuri tana dubansa hadāida tunanin anya ba wani abin Ke damun Paa dāinta ba... Kāokāarin amsar safan take tana furta āPaa you donāt need to do this... Zan iya