Showing 153001 words to 156000 words out of 257774 words

Chapter 52 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt

so ni nakeda alhakin zab’awa kaina macen da ta dace Tai zama matata kuma uwar yaran da zan haifa gaba.!”

“Ansaar.!!!!” Mommy ta daka matsa tsawa tana mai mik’ewa tsaye...

Ansar bai daina huci ba yake furta “Mommy Ki k’yaleni na fad’I gaskiya, wannan mutumin yazo yana poisoning zuciyarki da kalamansa na son zuciya..!”
Momy ta katsesa da fad’in “Nace kamin shiru... K’anin mahaifin Naka kake wa magana haka...? Ansar I didn’t raise you to become like this... Rashin kunya ba halinka bane kada ka fara kan wannan mak’aryaciyar yarinyar..!!”

Ansar na tsananin huci yake girgiza kai yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda yake furta “Mommy shin zaki bari son zuciya ya rufe miki ido..? Mommy Muhibbah bata miki komai ba, Mommy don’t judge her akan abinda bakida masaniya akai... Mommy ki bari nai miki bayani na tabbata zaki fahimci komai..!”

“Shut up.!! Kamin shiru nace... Bana buk’atan naji komai, kuma bana so na fahimci komai... The only abinda na sani shine bazaka auri yarinyar nan ba period.!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci..

Shima Ansar d’in huci yake idanunsa na kuma kad’awa, lokaci guda yake furta “Fine..! Haka kikace Mommy..? Kin mance same mutanen da suka k’yamaci aurenki da Daddy sabida ke tibabbiya ce same mutanen suke tunzuraki ki aikata abinda zakizo kina danasani daga baya... Mommy why can’t you open your eyes and see the truth...! Toh wllhi kinji na rantse miki.... ina mai tabbatar maku idan har baku d’aura aurena da Muhibbah ba wllhi bazan zauna da yarinyar da kukeso ba, zaku aura mata wofi ne Dan wllhi tafiyata zanyi ku nemi ni ku rasa..!!”

Marin da Mommy Ta wankesa dashi ne ya sanyashi dakatawa da magana, ya d’ago dafe da k’uncinsa yana dubanta, Baffah Yawale ya mik’e ya tsaya a tsakiya yana duban Mommy yake fad’in “Kiyi hak’uri Murja... Har yanzu dai Yakubu(Ansar) yaro ne... Baisan menene daidai da abinda ba daidai ba... Kiyi hak’uri abi abun a sannu....!”

Mommy na hawaye take nunawa Ansar k’ofa “Get out... Get out before I lost it all on you... Fita nace..!!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata....

Ansar ya aikawa Baffah Yawale wani duba kana yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa...

Ansar na ficewa Baffah Yawale ya taro ruwa a dispense ya kawowa Mommy... Babu musu Ta amsa ta kurb’a...
Bafah Yawale ya koma mazauninsa ya zauna, saida dak’ik’ai suka d’an shura kana yai gyaran murya yace “Murja ni inaga bata nan zamu b’ullowa yaron nan ba, idan har yana ganin yarinyar bazai tab’a cireta a zuciyarsa ya mance da ita ba... Idan bata gidan nan shine zai manceta gaba d’aya... Amma muddin yana ganinta Toh fah bazai mance ba....!”

Mommy ta dubesa jiki a sanyaye tace “Yawale mai kake nufi...? Kasan dai bazan iya koran Muhibbah ba, dikda abinda taimin I still love her like my own daughter... Bazan iya korinta ba..!”

Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan.. Ai nima ba abinda nake nufi ba kenan, ba korinta zakiyi ba... Aurarta zakiyi ga wani daban, kinga idan kika aurarta Ansar yasan ta haramta garesa shikenan dole ya cireta daga zuciyarsa gaba d’aya ya rungumi k’addara ya zauna da matarda Allah ya had’asa zaman aure da ita Wato ‘yar uwarsa k’anwarsa Hameeda... Kinga shikenan hankalinki kema ya kwanta..!”

Mommy tai shiru kaman mai nazari sai kuma tace “Toh amma waye mijin da za’a aura mata..? Ina zan samo mata miji da zai dace da ita wanda bazai mata gori daga baya ba..?!”

Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan... Ai samun miji ga kyakkyawar yarinya kaman Muhibbah bazai wahala ba... Ni zan tafi da hotonta wajen manyan mutane masu mutunci a haka zamu sama mata miji... Amma ita yarinyar karki sanar da ita an fasa aurenta da Yakubu shima Yakubun ki barsa akan za’a aura masa Muhibbah saidai yaji daga baya ba shi aka aura mata ba... Ina mai tabbatar miki rana guda za’a d’aura aurenta da Yakubu amma ba dashi ba da waninsa...Kinga dole yayi hak’uri ya rungumi k’addara... Ki share zancen Yakubu ki daina damun kanki ki bar min wuk’a da nama... Ni nasan duk yanda zanyi...!”

Mommy ta jinjina kai tace “Nidai idan har bazata auri Ansar ba toh shikenan, amma Yawale ka tabbata gidan mutunci ka kai Muhibbah..!”

Baffah Yawale ya Washe baki cikeda jin dad’i yace “An gama Hajjaju... Wannan ai mai sauk’i ne... Ina mai tabbatar miki yanda Yakubu ya makance da soyayyar yarinyar nan har yana sa’insa dake kika sake kika amince ya aureta Toh fah saidai Ki zuba mishi idanu Don kin haifo mata shine...!” Ya k’arashe yana mai kuma tunzura Mommy....

Mommy tace yaje yayi duk abinda ya dace... Baffah Yawale ya fice yana Washe baki...

Daga nan yanda suke tsaye suka hango ficewar mutumin daga gidan...

Turaki ya k’arasa ya tadda mutumi mai teburin kayan miya, yai masa sallama da musabaha suka gaisa... Idanunsa naga k’ofar gidan su Muhibbah da Baffah Yawale Ke k’ok’arin burka babur d’insa....

Mai Teburin kayan miya ya dubi Turaki yace “Bawan Allah na nawa za’a baka...?”

Turaki ya d’anyi gyaran murya yace “Tambaya nake dama...!”

Mai kayan lambu yace “Allah yasa na sani...!”

Turaki yai nunida gidansu Muhibbah yace “Da Allah wata yarinya nake nema a can gidan sunanta Muhibbah.. Ko ka santa...?”

Mai kayan lambu ya Washe baki yace “Aw Muhibbah... K’warai na santa... Ai d’iyar rik’o ce a gidan... Yaron gidan likita shine zai aureta...Idan ban b’ataji ba ma sati mai zagayowa za’ai bikinsu... Kaga wancan wanda yake k’ok’arin burka babur shine K’anin mai gidan, kuma a yanda naji basa so yaron gidan aure ita yarinyar... D’iyar wancan k’anin Baban nasa sukeso ya aura...!” Mai kayan lambu yaci gaba da zuba bayani kai kace tanbayrsa akai...

Turaki ya jinjina kai yace “Na gode...!” Sukai sallama mai kayan lambu yaci gaba da ‘yar wak’e wak’ensa abinka da mutane wanda bakinsu bai iya yin shiru...

Turaki na k’arasowaga Mahmood ya sanar dashi yanda duk sukaida mai kayan lambu....

Mahmood yace “What..! No Turaki dole musan abinyi... She can’t get married... Idan tayi aure komai ya lalace Turaki... Wannan yarinyar must answer to me first...Idan ta kama na janyota da kaina Ta koma cikin Masarautar nan zanyi Turaki...!!” Ya k’arashe cikeda tsanar hallaya irin nata....

Turaki yace “Alright your Highness... Bamuda time muyi sauri mubi bayan mutumin kafin ya b’ace mana...!”

Cikin sauri suka nufi mota Turaki ya tada sukabi bayan Babur d’in Baffah Yawale....




SameenaAleeyou *MUHIBBAH*



*60*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Daga cen nesa da k’ofar gidan da Yawale ya shige sukai parking, suka k’araso k’ofar gidan Turaki ya bud’e murya yai sallama, saidai basuji an amsa masu daga ciki ba... Sun kusan minti biyu tsaye wajen babu wanda ya lek’o daga cikin gidan har kaman zasu juya saiga wani yaro ya fito rik’eda allon karantu Ta ‘yan makarantar zaure... Turaki yai saurin taresa da fad’in “Kai Yaro gidan nan kake...?!”

Yaron ya jinjina kai yace Eh... Turaki yace “Shiga ciki kace ana sallama da mai gidan...”

Yaron ya dubesu da mamaki sai kuma yace “Ai masu gidan sunada yawa, k’ofofi kashi kashi ne cikin gidan... Wanne zan kirawo maku...?!”

Turaki ya d’an shafi kansa yace “Toh..! Bakaga wani mutumi da ya shige yanzu ba da Babur..?”

Yaron yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Kodai Baffah Yawale kuke nufi shine naji k’aran babur d’insa yanzu...”

Turaki yaji sunan kaman wanda mai kayan lambun can na k’ofar gidansu Muhibbah ya fad’a masa, saurin jinjina kai yai yace “Yauwa shi dai... Shiga kace ana sallama dashi..!”

Yaron ya jinjina ya koma cikin gidan... Jim kad’an ya fito yace dasu Wai yana zuwa....

Bayan shigewar yaron da wasu mintoci Yawale ya fito yana mamakin Ina ya samu bakin buzaye shida babu kowa nasa k’asashen hamada..

Iso yai masu cikin Zauren yanda tabarma ke shimfid’e, yai masu sannu da zuwa suka gaisa gaba d’aya, Yawale ya bud’e murya yace “Saidai kuma ban gane daga ina bane..?”

Turaki ya d’an murmusa yace “Eh Toh daga k’asashen can arewacin hamada muke, dama tambaya mukazo gameda d’iyarku mai suna Muhibbah...!”

Ai Tun kafin Turaki ya rufe baki Yawale ya soma fad’in “Fad’uwa tazo daidai da zama, dama mun rasa mijin da zamu aura mata, Allah yasa idan kun aureta kuyi nesa da ita da garin nan... Ku tafi can k’asarku da ita yanda bazata kuma dawo mana ba, bazamu kuma cin karo da mai irin fuskarta ba..!”

Turaki da Mahmood suka dubi juna da mamaki, Baffah Yawale yaci gaba da fad’in “Kar Kuji komai ba’a mata miji ba, dama uwar goyon nata tace duk wanda ma samu na aura mata, ko kuturu ko makaho kai ko wane irin mutum ne... Toh Alhamdulillah tinda ta samu mutumin da zai ketara da ita wata Nahiyar ai abin ai godiya ne... Dama mu kasancewarta kusa damu ne bamu fata... Wata sati ake bukin d’aura mata aure... Bayin Allah sadaki kawai zaku kawo ni ko yanzu zan kirawo shaidu a d’aura auren...!”

Turaki yai murmushi wanda yafi kamada yak’e yace “Oh haka ne Baba..! Toh ai inaga zamu koma dai muyi shawari da magabata...”

Turaki bai rufe baki ba suka sinkayo muryar Mahmood daga cikin nad’insa ta buzaye yana fad’in “Babu shawari Baba... Mune nan magabatan wanda mukazo nemawa auren... D’an uwana k’anina zan nemawa aurenta... Yanzu basai anjima ba zan damk’a maka sadaki...!”
Ya k’arashe yana mai zira hannu cikin aljihun babban rigarsa Ta buzaye, ya ciro wata ‘yar jaka ta fata ya mik’awa Baffah Yawale...

Yawale hannu na rawa ya amshi ‘yar jakar Ta fata, ya shiga warwareta yana ganin abin mamaki.. Silallala ne zallan zinari wanda darajarsu zai iya kaiwa dubu d’arurruka....

Yawale ya kuma murtsuka idanu yana ganin wannan ikon Allah, a ina mutane irin wad’annan suka sami wannan dukiya shidai bai gansu da wata babbar Mota ba hasalima bai gansu da abin hawa ba, daga su sai suturan jikinsu ya gansu...

Kaman Mahmood yasan tunanin da yake ya soma fad’in “Kar kaji mamaki Baba sabida mu haka al’adarmu take, mace Tanada matuk’ar daraja, duk mutum yakaiga talauci sai ya nemo silalla na zinari kafin a basa mata, iyayenmu sukan bar mana gadon Rak’uman da muke kiwo Dan muyi kud’in aure dasu....”

Yawale ya jinjina kai har lokacin jikinsa rawa yake yana juya coins na zallan gold a hannunsa... Lokaci guda yace “Ai..Toh... Toh ai shikenan, kasan kowa da al’adarsu... Babu komai sati mai zuwa kuzo ku amshi auren d’an uwanku...!”

Mahmood ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba saima k’ok’arin mik’ewa da yake da zimmar tafiya... Yawale ya tsare fararen k’afafunsa da kallo wanda da gani kasan hutu da jin dad’i ya zauna a wajen babu wani alamun tafiya cikin hamada a k’afafun balle har ace makiyayi ne mai kiwon Rak’uma cikin Hamada...Anya wannan ba manyan mutane bane suke son b’adda kama... Wad’annan basuyi kamanceceniya da gajiyayyu ba... Shifa baya fata yarinyar nan ta samu wajen maik’o yafi so ta tagayyara, kardai ya kaita yanda zata huta... Toh amma ai shi dama so yake ta fice daga rayuwarsu dan idan har tana tareda Murja da kuma Ansar sam bazata tab’a bari ya cimma burinsa akan dukiyar D’an uwansa da ya mutu ya barwa Ansar da Murja gado, kuma dukiyar Murja ma harinta yake tinda batada magaji bayan Ansar d’in... Idan kuma Ansar ya mutu baida Magajiya face d’iyarsa Hameedah wacce zata zamto matarsa , komai ya dawo hannunsa a sauk’ak’e....

Sallaman Matarsace rik’eda ruwa a faranti ya dawo da Yawale daga duniyar tunanin da ya tafi, da alama baima San bak’in nasa sun fice ba har sun tafi....

Matarsa ta tambayesa Ina bak’in...? Yace Ai har sun tafi Ta koma da ruwan... Ya k’arashe yana mai b’oye silallan zinarin cikin aljihunsa.... Bai isa kowa yaga wannan dukiya ba, ko Murjah bazata gani ba... Kasuwa zai tafi ya saida guda d’aya tak ya kaiwa Murja a matsayin kud’in auren Muhibbah... Sauran kuma ya dafe Allah ya kashe ya basa, shikenan ya samu kud’ad’en da zai kayan d’aki wa Hameedah a sauk’ak’e...

**
Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin abinda Mahmood yai ba, shi tsananin mamaki ma ya hanasa furta koda kalma.... Da alama shi kuwa Mahmood d’in ko a jikinsa...

Turaki ya nusa kad’an yace “Your Highness, ka tabbata da abinda kayi..? Shin waima cikin k’annenka waye ka nema masa auren Muhibbah, Yazeed ne ko Jamal ne kokuwa Fu’ad ne..?!”

Ba tareda ya dubesa ba yace “Maiyasa ka faye gaggawa Turaki..?!”

Turaki ya girgiza kai yace “Your Highness zarginta kawai kake baka tabbatar ba, bakada k’wakk’waran shaida da zai tabbatar maka da hakan...!”

Idanunsa da suka kad’a sukai jazir naga kwalta yake furta “Bayan k’aryar da tayi mana, Iyayenta ma neman kai sukeda ita... Ai kai shaida ne tinda gabanka akayi komai... Wannan kawai ya isa na kuma aminta da cewa ita d’in ba mutumiyar K’warai bace..!”

Turaki ya girgiza kai yace “Mugaye sunyi yawa a duniyar nan, wasu idan har basu suka haifi yaro ba toh basu damu da duk halin k’uncin da zasu jefasa ciki ba, your Highness ya kamata kayi tunani akan hukuncin da kake k’ok’arin zartarwa... Nasan kana son yarinyar nan, kar kayi abinda daga baya zaizo ya dameka ...!”

Katsesa yai da fad’in “Bana sonta ban tab’a sonta ba kuma bazan sota ba..!!”

Turaki ya murmusa kad’an yace “Idan da baka sonta bazaka tab’a damuwa da al’amranta ba... Your Highness case d’in Muhibbah da Raheema ya banbanta, Raheema ka kamata dumu dumu ita kuwa Muhibbah zarginta kake wanda ni nayi imani can k’asan zuciyarka baka yarda zatayi duka wad’annan abubuwan ba... Nasan baka yarda ba Mahmood..!” Turaki ya k’arshe cikin sanyin murya..

Window kurum Mahmood yake duba Dan baiso ya yarda da kalaman Turaki... Shi hukuncin da ya yanke shine daidai... Idan har yana so Muhibbah Ta dawo cikin masarauta toh hanyar kenan ya aura mata wani cikin Masarautar kafin iyayenta su aurarta ga wani tinda idan tayi aure babu hali ta dawo cikin Masarautar, dole duk yanda zai ya nemama wani cikin Masarautar aurenta...! Ya k’arashe tinanin yana mai dunk’ule hannunsa sabida tsananin b’acin rai...
Muryar Turaki ya sinkayo yana fad’in “Toh idan ka aura mata d’aya cikin ‘yan uwanka ita kuma Raheemar fah... Wa zaka aura mata..?!”

Ba tareda ya dubesa ba yace “Idan Allah ya kaimu lokacin zakaji ko wanene mijin nata...!”

Turaki yai shiru yana duban abokin nasa ba tareda ya kuma cewa komai ba saima maida hankalinsa ga tuk’i da yayi....
**

MASARUTA

Giwa da mamaki take duban yanda halitta Jakadiya ya jirkid’e lokaci guda... Ko iya d’ago kanta batayi, Gata nan dai d’aure saman kujera iyaka jin jiki tayisa kam...
Ko Iya d’aga kanta Jakadiya batayi, Giwa kanta saida ta firgita da ganin yanda halittan Jakadiya ya sauya lokaci guda, bata tab’a tsammanin muguntan Jamal yakai wannan mataki ba... Jiki na rawa Giwa ta isaga Jakadiya tana k’ok’arin dungurinta take fad’in “Anya tanada rai..?!”

Jamal ya jinjina kai yace “Tanada rai Maami kawai alluran hutu tasha, nanda wasu sa’o’i zata farka...!”

Giwa tai mata K’uri tana duban yanda fuskar Jakadiya ya kumbura ga wata akwati d’aukeda tools a gefe... Dank’ari mak’ari, wannan wane irin azaba Jamal ya baiwa matar nan...

Giwa Ta dubesa tace “Jamal mai Jakadiya tai maka..?!”

“Amanata taci... Kuma kema taci amanarki don na tabbata ita ta taimakawa Ja’afar ya gudu...!” Ya k’arashe cikin huci...

Giwa Ta lumshe idanunta a hankali dan tasan tsanar Jafar ne ya shafi Jakadiya, Jamal zai iya yin komai akan yarinyar nan Umaima...
“Toh amma ya akai ka Sani....?!” Giwa ta tambaya tana mai tsaresa da idanu...

Mayafin Jakadiya dake aje gefe ya nuna mata yace “Kin gani wannan ne shaida...!” Take ya labartawa Giwa duk yanda abin yake...

Giwa Ta d’aga mayafin tana juyawa... Ko shakka babu bai kamada mayafin bayi ba, duk yanda akai wannan ba na Jakadiya bane... Akwai wata k’ulleliya, amma bazatace komai ba har sai Jakadiya ta farka.... Da k’yar ta shawo kan Jamal ya sassautawa Jakadiya da irin uk’ubar da yake mata, Kwanceta yayi ya ajeta a nan d’akin had’ida treating duk wasu wounds dake jikinta... Giwa kanta saida ta tausayawa Jakadiya Dan ko motsi bata iya yi... Haka suka fice suka barta rufe nan cikin d’akin kafin alluran su saketa ta farfad’o....

**

Sharkaf da zufa tamkar babu AC cikin d’akin haka ya farka daga baccin nasa, mafarki yayi wata Murya da baisan daga ina bane tana fad’i masa Maiyasa zai zamto mai munana zato da mummunan zargi ga mutanen kirki... Da yawa daga cikin zato zunubi ne, kuma sashenta ba gaskiya bane..!

Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa mafarkin na dawo masa daki daki... Wasu mutanen kirki ne ya munana masu zato..? Tambayar da zuciyarsa tai masa... Toh kodai Yazeed ne..? Ko Raheema ce..! Toh amma ya kamasu red handed ba zato yake masu ba.... Take yaji zuciyarsa Ta ambato masa MUHIBBAH...

Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai kuma shafe fuskarsa, Toh idan sashen zaton nasa ya zamto gaskiya fah...?
Wata b’angare na zuciyarsa ta basa amsa da fad’in Kai da kanka ka kasa aminta cewa zatai abinda kake zaton ta aikata...!

Ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi tunanin na kuma damunsa, duk yanda yaso ya yakishe tinaninta cikin zuciyarsa ya kasa... Dik yanda yaso ya amince cewa ita d’in mutuniyar kirkice ji yake bazai iya hakan ba musamman da Zahra ta sanar dashi duk wasu shawarwari da Muhibbah taita bata tin daga fari, har cewa da tai ta tambayesa a cikin mutanen da yake jin nauyinsu... Kenan Muhibbah itace Ta tunzuro Zahra tai masa abinda tai... Gaba d’aya sai yana jin bazai iya aminta da ita ba bayan all that he learned about her... Da k’yar ya iya mik’ewa ya nufi bayi Don d’auro alwala....

**

Giwa sai faman safa da Marwa take a k’uryar d’aki Jamal na gefe yana juya mayafin, kenan Zahra itace Ta baiwa Jakadiya...!

Jamal ya dubi Giwa yace “Maami amma Zahra bazata iya lek’en asiri cikin d’akina ba... Maiyasa ma zatayi haka...? What could be her reason..?!”

Giwa tai shiru tana nazari sai kuma tace “K’warai Zahra bazatayi duk abinda ka zayyano mai wannan mayafin tayi ba, duk yanda akai akwaita a k’asa... Kodai akwai wata ‘yar lek’en asiri cikin Masarautar nan ko kuma bata cikin Masarautar amma tana amfani da Zahra...!”

Jamal yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maami karki damu, I’ll talk to my niece a nitse nasan zata sanar dani komai... Kinsan na k’ware a iya shan cikin mutane Dan naji labari...!”

Giwa ta murmusa tace “Hakan yayi Gwarzo na... K’warai na yarda dakai.... Idan muka sami wacece wannan ‘yar lek’en asirin...”

Jamal ya katseta da fad’in “Horon da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login