Showing 237001 words to 240000 words out of 257774 words
Chapter 80 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
gaba da furta “Since the I first saw you... I felt something very special about you, like we’re connected somehow..!” Muryarta ya carke sai kuka...
Muhibbah ta kuma rungumarta tana furta “Likewise Zahra... I felt the same, mu d’in ‘yan uwa ne..!” Ta kasa ci gaba da nagana itama sai kuka... Umaima ta k’araso ta duk’a gefensu tana kuka itama, lokaci guda ta dafa hannayenta saman kafad’unsu.. Suka d’ago suna duban juna su duka ukun... Lokaci guda suka rungume juna gaba d’aya su ukun suna wane irin kuka mai tab’a zuciyar mai sauraro.. Gimbiya Turai ta taso ta had’esu gaba d’aya ta rungume tana matsan hawaye itama.. Lokaci guda take furta “Alhamdulillah..! Alhamdulillah..!! Allah na gode maka daka had’e kan ahalinmu waje guda.. Bayan duk k’ok’arin da wasu sukayi suga Sun tarwatsa kan wannan ahali sai gashi ka had’emu waje guda cikin labaru da k’addarori na rayuwa daban daban.. Wa zaiyi tunanin wad’annan ‘yanmata guda uku tsatso guda ne.. Sai gashi cikin hikimarka da buwayarka ka had’esu waje guda.. Allah na gode maka daka had’e kan ahalin Alfah waje guda..!” Kuka yaci k’arfinta ga tsananin rawa da muryarta yake...
Mommy dake gefe sai matsan k’walla take tana duban wannan al’amari mai cikeda al’ajabi ga kuma tab’a zuciya.. Allahu Akbar Allah mai iko... Ashe wannan masarauta k’unshe yake da ahalin Muhibbah shiyasa taji duk yanda zatayi sai tazo wannan Masarautar.. Ashe dai Allah ne ya dawo da ita cikin ahalinta.. Kai wanann kayan Farin ciki da yawa yake.. Ubangiji ya cika abin godiya...!
Wannan rana ta kasance wani sabon rana ne na Farin ciki ga wannan ahali, Muhibbah ta had’e kan ‘yanuwanta ta shige tsakiya ta rungumesu tamkar mai tsoron kar wani abu ya kuma gifta tsakaninsu.. Mafarkinta da mahaifinsu ta tina, ashe dai ahalinsa gaba d’aya suna a cikin wannan masarauta, yau da za’a tashi mahaifinsu ya gansu gaba d’aya su duka uku tare Tabbas da ya cika da Farin ciki... Allah ya had’e masa kan ahalinsa waje guda, duk yanda Izzatu taso Ta k’arar da zuri’ararsa a doron k’asa Allah bai nufi hakan ba.. Shiyasa Bawa baya iyayiwa d’an uwansa Bawa abinda Allah bai k’addara masa ba.. Duk abinda ya sameka ka k’addara daga Allah ne, shi ya k’addari yuwar hakan.. Wani bai isa ya maka abinda Allah bai k’addaro maka ba... Suka kasa sakin juna sai wani sabon shauk’i da k’aunar juna suke.. Sai nan nan da juna suke musamman ‘yar autarsu Zahra wacce ita d’in shalele ce a wajensu...
Zahra sai tambayar Muhibbah take ya kamannin mamansu da wa take kama, ya na babansu da waye yake kama cikinsu.. Umaima tace gaskiya zataso sanin kamannin Abbansu tinda tin tana k’arama Giwa ta rabasu bata sanshi ba.. Muhibbah ta murmusa tana dubansu gaba d’aya ukun wane irin Farin ciki maras misaltuwa yana ratsa duk wani k’ofa na zuciyarta, hannayensu ta rik’o cikin nata, ta dubi Umaima dake b’angarenta na dama tace “Well, Ke kin d’an d’auko kamannin Abbah kad’an dan kin d’auki hasken fatarsa dukda bansan ya kamannin mahaifiyarki yake ba...” Ta juyo b’angaren hagu ta dubi Zahra, ta kuma murmusawa tace “Kema kin d’an d’auko hasken fatarsa tinda kinfini haske ni Umma na biyo.. Saidai kin d’an d’auko manyan idanunmu nida Umma..!” Gaba d’aya suka murmusa cikeda jin dad’i Muhibbah ta rungumesu tana shak’an Ni’iman canjin rayuwa wanda bata samu ba a baya... Umaima tace “Giwa itace tayi sanadiyar rabuwarmu gaba d’aya..!”
Zahra ta k’ara da “Zanso na sake ganin fusakar azzulaman matar nan naji dalilinta na wanann bak’in zalunci da tayima ahalinmu..!”
Umaima tace “Ko kad’an banji tausayinta ba, She got what she deserved after all..!”
Muhibbah ta kuma rungumosu tana fad’in “Kar mu tuna bak’in ciki, tuna wannan baiwa da rahama da Allah ya lullub’emu dashi.. Mu gode masa sai muyi Farin ciki...!”
Gaba d’aya suka murmusa Zahra na fad’in “Y la parte más asombrosa de todo es que ahora estamos todos juntos, como siempre deberíamos estar..!” (Sannan abu mafi birgewa muna tare yanzu gaba d’aya, kaman yanda ya kamata mu kasance tun daga farko..)
Hancinta Muhibbah ta d’an jawo tace “Mudai a daina mana Spanish a nan dan bamuji.. Right Umaima..?” Ta k’arashe tana mai d’agawa Umaima gira guda sama..
Umaima ta d’an kashe idanu guda tace “Ahh yaren masoyi ni na isa nace a dena yi..!”
“Au kema haka zakice..?” Muhibbah ta fad’i tana duban Umaiman sanda suka shagala da dariya daga Zahran har Umaimar.. Suna a haka Jakadiya ta nemi izinin shigowa.. Ta risina ta gaidasu kana ta k’arada “Rankidad’e.. Mai Martaba Sarkin mu na gobe mai jiran nad’i yace a sanar Gimbiya yana son ganinta..!” Ta k’arashe kanta a k’asa..
Gaban Muhibbah ya fad’i jin Mahmood yana kiranta... D’an duban Sisters d’inta tayi tace “Gaskiya nidai yau d’in gaba d’aya taku ce banson matsawa daga kusa daku..!”
Umaima Ta d’an rausayar da idanu tace “Mu mun isa mu hana Rankaidad’e ganin Queen d’insa, a’a Sistu gaskiya dai ki amsa kiran Mai Martaba.. Right Zahra..!” Ta k’arashe tana d’agawa Zahra gira guda..
Muhibbah ta tab’e baki kad’an tace “Then he wait, I’m not done catching up with my sisters..!”
Umaima tace “A’a Sistu ai ba’asan sarki da jira ba mu dai zamu jira..”
Zahra ta d’anyi gyaran murya cikin sigan zolaya tace “Kaman dai ba yanzu aka gama kuka akan Paa d’ina ba..!” Muhibbah ta janyo pillow ta jifa mata tana fad’in zaki sani ne yarinyar nan.. Zahra ta zille tana dariya ta fad’a jikin Umaima tana fad’in “Aidai gaskiya na fad’i ko Aunty Umaima, Paa d’ina is one in a million.. Kuma ma mu wajen Ummi zamuje ta bamu labarin Masarautarsu Abbah..!” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Umaima.. Umaima na jinjina kai take furta “K’warai muje muji labarin Masarautarsu Abbah..!” Daga haka suka fice rungume da juna cikeda jin dad’i.. Muhibbah tabi bayansu da kallo zuciyarta na mata wane irin sanyi.. Tunawa da tai Jakadiya na waiting room tana jiranta su tafi wajen Rankaidad’e hakan ya sanyata mik’ewa Ta soma kintsawa a nitse zuciyarta na wane irin fuzga mai gauraye da annashuwa...
Koda suka iso sashen Mahmood ita kad’ai ta shige ba tareda rakiyar Jakadiya ba.. Cikin natsuwa take takunta a hankali har ta nufi saman benensa..
Bataji alamunsa ba hakan yasa ta nufi b’angaren paint works d’insa.. Haka ta dinga takawa tana ganin baiwar da Allah yaima Sarkin nata.. Kyakyawan murmushi saman fuskarta, tai tsaye jikin wani k’aton frame tana kallo.. Kaman daga sama taji hannayen mutum saman cikinta ya rungumota ta baya daga nan yanda take a tsaye...
Zuciyarta ya tsinke ta d’an zabura kad’an Mahmood ya kuma matseta a hankali yake furta “Ina zaki gudu kije..!” Yai maganar cikin salo na d’aukan hankali...
A d’an shagwab’e tace dashi “Ba kaine ka tsoratar dani ba..!”
Ya juyo da ita suna fuskantar juna dukda cewa ita nata idanun k’asa suke duba, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Kin cika tsoro, na kula komai tsoro yake baki.. Bansan yaya akayi kika iya lek’en asiri cikin Masarautar nan da wannan tsoron naki ba..”
Murmushi mai sanyi tayi wannan karon har lokacin kanta a k’asa...
Bai janye idanunsa daga dubanta ya kamo hannayenta ya sakale yatsun cikin nasa lokaci guda yake furta “Gashi kuma na saka Ki kuka, yanzu kuma na baki tsoro.. Duk ni kad’ai..?!”Ya k’arashe murya a hankali
Ta kwantar da kanta cikin k’irjinsa cikeda kunyan abinda tayi...
Ta d’an mak’e kafad’a tana nan kwance cikin k’irjin nasa, tamkar wacce zata kuma wani kukan tace “Nifa ba kuka nayi ba Rankaidad’e..!”
Ya murmusa kad’an yana mai kuma shigar da ita cikin jikinsa “Oh na mance ashe sakamakon jarabawar ne bai miki ba.. Kodai a sake wani jarabawar ne..?”
Ta d’ago a d’an zabure tana dubansa wannan karon sai kuma taji kunyar kanta da kanta Ta kuma bama kanta dariya.. Rufe fuskarta da tafukan hannayenta tai tana mai murmusawa a hankali..
Lokaci guda Mahmood wanda shima sihirtaccen murmushi ne saman fuskarsa ya kuma janyota cikin jikinsa yana mai furtawa a hankali “Karki damu ni da ke auren zobe mukayi.. Mutuwa ce kawai zata rabamu kinji koh..!” Ya k’arashe yana mai aika mata wasu salonsa masu sanyawa taji duniyar tamkar su biyu ne kad’ai suka rage a ciki... Hannunta ya kamo yana mai furta “Come let’s talk..!” Ya k’arashe yana mai masu masauk’i saman Yalwataccen Darduma ta alfarma mai d’aukeda manyan cushions irinta gidajen masu sarauta.. An k’awata saman darduman da kayan marmari sai wanda zuciya ta zab’a...
Zaune suke suna fuskantar juna, idanunsa akanta yayinda ita kuma Muhibbah ta sadda nata idanun k’asa...
Dak’ik’ai sukad’an gifta kafin yai gyaran murya ya soma fad’in “I believe by now keda Zahra kunsan cewa kud’in ‘yanuwan juna ne.. Harma da Umaima..!”
Ta jinjina masa kai a hankali ba tareda Ta amsa ba.. Lokaci guda yaci gaba da furta “Abubuwa da dama Sun faru ko nace suna kan faruwa..! Ban tab’a tsammanin rana irin wannan zatazo ba, ranan da zan sanar da Zahra cewa bani na haifeta ba.. But as they say No secret remains hidden forever... Duk daren dad’ewa dole wata rana zata sani..!” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “I don’t know, bansan ta yaya zan soma sanar da matata da kuma yarinyar da na raineta like my own cewa I was the one who ran over their Mom, ni ne nayi sanadiyan rasa mahaifiyarku da kukayi Hibbah.. Bansan yaya zaku d’auki al’amarin ba, it was hard for me to confess, but I had no choice ya zama dole na sanar daku koda bazaku Iya yafe min ba.. Muhibbah ni Mahmood ni na buge mahaifiyarku da Mota wanda yayi sanadiyar barinta duniya.. Zafin wannan abin yasa naji Eh gwara na swwak’a miki dan kar abin ya maku yawa nima kuma bazan iya rayuwa da hakan cikin zuciya na ba.. But then I realize I couldn’t... I can’t let you go... Because I love you...!” Cak ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa jin abinda yake fad’i, lokaci guda Mahmood da idanunsa tar suke kanta yaci gaba da fad’in “So much...!” Ya d’an had’iyi throat d’insa yanda kana iya hango motsawar wuyan nasa ta waje kana yaci gaba da fad’in “I’ve always loved you since the day I first saw you, when you were little...!” Ya d’anyi fasali yana daidaita numfashinsa, idanunsa wanda babu komai cikinsu face tsantsan gaskiya suna dubanta yaci gaba da furta “Bayan na sake had’uwa dake a cikin Masarautar nan a karo na biyu as a full grown woman, I can admit I feel something... Something very special... Te amo demasiado Muhibbah..!” (Ina matuk’ar k’aunarki Muhibbah)
Tinda ya soma magana take duban cikin k’wayan idanunsa hawaye na gangaro mata... A hankali ta lumshe idanunta hawaye naci gaba da gangaro mata... Hannayensa taji saman nata ya rik’o nata hannayen.. Cikin rawar murya yake furta “Will you still accept me, after learning that I was the one who ran your mom over..! Hibbah will still accept me.. Talk to me please Hibbah...!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai kuma matse yatsun hannunta cikin nasa..
A hankali yaji tana janye hannayenta... Yayi tsam ya rik’e yatsun nata, lokaci guda yake furta “Bazaki tab’a yafe min ba koh...?”
Bud’e idanunta tai masu zuban ruwa Ta ware su tsaf saman kyakkyawan fuskarsa wanda ya cika da rauni a yanzu saikace ba Sarkin nata ba..
A hankali Ta soma furta “Rankaidad’e Maiyasa zaka ce haka, bayan bada ganganci ka aikata hakan ba.. Maiyasa zakace haka bayan kaid’in Allah ne ya k’addari had’uwarku da ita don ka zamto garkuwa ma jaririyarta wanda azzalumai suke neman ganin bayan ahalinmu a wancan lokacin.. Allah ya maido da Zahra cikin ahalinta ne shiyasa ya k’addari rik’onta a hannunka..! You’re like an Angel Your Highness..Ka bayyana a rayuwar Zahra kuma ka haskaka rayuwarta, ka bata dukkan kulawa da ya dace.. Rankaidad’e ka mance cewa buge Umma da kayi ko k’warzani bata samu ba, kawai kaid’in ka bayyana ne domin ka kula da Zahra..! Sannan Bawa baya shige ajalinsa, kowa ajalinsa a rubuce yake Rankaidad’e.. Kuma Idan akwai wad’anda zamuce sunyi sanadin mutuwar Umma toh ba kowa bane face Giwa da ‘ya’yanta domin kuwa tun bayan abinda ya sameni da mahaifina, zuciyar Umma yayi rauni bata kuma lafiya ba ga juna biyu da take d’aukedashi.. Koda Ta haifi Zahra cikin jinya take batayi lafiya ba.. Idan baka manta ba kaman yanda kace Likita yace her heart was weak toh haka d’in ne zuciyarta tayi matuk’ar rauni tun bayan wad’ancan iftila’i da suka auku mana.. Baka kashe Umma ba Rankaidad’e.. Lokacinta ne yayi sannan Giwa da ‘ya’yanta sune sanadi..!” Cikin tsananin rawar murya take ci gaba da fad’in “You gave my sister a life Rankaidad’e..! Thank you, thank you for taking care of my sister..? Thank you your Highness..!” Muryarta ya sark’e sabida kuka...Lokaci guda Mahmood ya janyota cikin jikinta cikin jikinsa kaman jira take nan kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro... Ya matseta cikin jikinsa sosai yana lallashinta.. Haka yayita riritata yana bata baki had’ida jero mata kalaman k’auna masu sanyaya zuciya wanda har saida tayi mamakin Wai Dama ya iya fad’in kalmomi haka... Kaman dai ba Rankaidad’e d’in data sani ba...
Rayuwa ta kumayin dad’i abubuwa Sun kuma warwarewa, ahalin sun cika da Farin ciki maras misaltuwa... Tuni an soma gudanar da shirye shiryen bukin tarewar Muhibbah da Mahmood.. Shi Mahmood kam ma da anbi Ta nashi ne baza’a tsayawa wani biye wa al’ada ba zai tare da amaryarsa amma Ummi tak’i amincewa tace sai nan da sati guda bayan an ida yiwa Muhibbah duk wasu tanadi da ake na al’ada an kuma yi bukin yanda yake a al’adance.. Tuni ta killace Muhibbah yanda ko samun ganinta Mahmood baiyi, gaba d’aya ji yake wannan al’ada da sarautar ba k’aramin tak’urasa sukai ba... Mommy ma ta koma gida dan gudanar da ‘yan kintse kintse, a zaton Muhibbah mommy ta tafi kenan bazatazo Bikin ba, haka taita magiya tana cewa Mommy ta taya ayi da ita, Mommy tace bayan abubuwan da sukai musamman Yawale da Gudidi ita har kunyar Muhibbar take balle ahalinta, uwa uba kuma ga abinda Ansar yazo yayi daga baya... Da k’yar dai ta amince watak’ila ta dawo ayi da ita...
Zahra da Umaima basu sama basu k’asa, hidimar tasu ce ta ko ina... Ranan alhamis ake saka ran Amarya Muhibbah zata tare yayinda juma’a ake bukin nad’in sarki Mahmood..
Fadah ta kacame gaba d’aya, matan masu mulki daga ta ko ina Zuwa suke, kama daga matan Su Talba Galadima Matawalle da dai sauran Hakimai, harta matar Baba Wambai tazo, Majidad’i kansa ya samu Mahmood ya risina gaba garesa ya basa hak’uri dan ya yarda idan Rana ta fito tafin hannu bata kareta, Zakaran da Allah ya nufa da cara ko Ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi... Hassada taki ne ga mai rabo inji masu iya magana... Nan ya sanar da Mahmood d’in duk abubuwan da suka k’ulla masa shida Yazeed.. Ya kuma nemi gafara.. Mahmood yace bai tab’a rik’esa cikin zuciyarsa ba Allah yasa ya amfana da darasin rayuwa da ya d’auka bisa abubuwan da suka aikata.. Shi kuwa Ja’afar tsaresa da idanu yai yana fad’i a hankali daidai kunnen Majidad’in “Fadah bata marhaban da munafukai balle azzalumai, dan haka ka tabbata tuban gaske kayi ba tuban d’an muzuru ba dan idan na fahimci tuban d’an muzuru kayi.. Zaka amshi sakamako irin wanda ya dace dakai..!” Majidad’i ya d’an d’ago yana duban Ja’afar dake tsume da fuska yana dubansa shima.. Ubandoma ya dubguri k’eyar Majidad’i yace “Yarima yana magana amsa masa ake..! Hattara Majidad’i..!”
Majidad’i ya jinjina kai a hankali yace “In sha Allah Masarauta zata sameni da cika alk’awari.. Tuban k’warai nayi Yarima Ja’afar..!”
Ja’afar ya jinjina kai a hankali ba tareda ya furta komai ba...
Manyan masu sarautun gargajiya sai sanyawa ‘ya’yan Sarkin Albarka suke.. Tun ana sauran sati Tambura da algaita suke guguwa a masarautar... Ga duk wanda yasan Masarautar shekaru k’alilan baya ya kuma ganta yanzu yasan abubuwa da dama Sun sauya.. Wani ni’iman kwanciyar hankali da annashuwa ne zalla cikin d’inbin Masarautar...
A can b’angaren mata ma kowa ya hallara idan ka d’auke matan Waziri wanda abin kunyar da mijin su ya jaza masu ya hanasu shiga cikin mutane...
Yau ta kama laraba Washe gari ake saka ran gudanar da bukin aurensu itada Rankaidad’e... Tana zaune ana shafe tafin k’afafunta da lalle kaman yanda yake a al’ada, Umaima da Zahra suka shigo murmushi saman fuskokinsu... Zahra ta Ware idanu tana duban yanda ‘yaruwar tata ta k’ara shek’i da kyau a ‘yan kwanaki biyun da tayi a killace, tace “Kai Tia Wai Dama haka kikeda fitanennen kyau ne.. Black is gold, Kinga fuskarki kuwa.. Gaskiya Paa dole ya k’ara sadaki..!”
Umaima ta kai mata bugun wasa tana fad’in “Ja’irar yarinyar matar Baban naki ne abokiyar wasanki..”
Zahra ta d’anyi k’ara kad’an tana furta “Ouchh Aunty Umaima daga wasa.. Kuma ma ai Paa Yaya na ne ta wane b’angaren.. Ni daga yanzu ma Yaya Rankaidad’e Paapa angon Tia zanke kiransa..!” Harta da dattab’an matan dake zaune wajen saida suka nurmusa Umaima na kuma janyo kunnen Zahra guda.. Ita kaw Muhibbah shiru ta b’ace wajen tana jin wani bak’on al’amari tattareda ita, Wai bukin aurensu ake da Rankaidad’e... A tare Umaima da Zahra suka k’arasa gabanta suka duk’a, tausayinta sai ya kamasu... Umaima ta sanya hannu a robar lallen ta d’an lakata ta shafa mata a hanci tana mai furta “Be happy sister.. Coz you deserve all the happiness in the world..!” Muhibbah ta murmusa kad’an tana duban ‘yar uwar tata cikeda shauk’i... Zahra ma ta lakata lallen kad’an a yatsarta ta shafa mata a goshi tana furta “ Sé feliz hermana...!” (Ki kasance cikin Farin ciki ‘yar uwata.)
Murmushi take tana dubansu lokaci guda itama ta lakaci lallen tana k’ok’arin shafa masu suka mik’e suna zagaye kampacecen d’akin suna cewa su ba amare bane bazata shafa masu lalle ba.. Aiko nan taita binsu tana fad’in saita shafa masu suma.. Haka saida suka sa Muhibbah taita ‘yar dariya kafin suka k’yaleta.. Zahra da Umaima suka dubi juna suna ‘yar murmushi...
Muhibbah ta dubesu tana Ware idanu “I know you two are up to something again..!”
Suka murmusa a tare kana Umaima tace “Manyan bak’i muke tafe miki dasu..”
Ta d’anyi Jim tace “Manyan bak’i..”
Zahra ta jinjina kai tace “K’warai kuwa.. Wait..!” Ta