Showing 189001 words to 192000 words out of 257774 words
Chapter 64 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
cika za’a kulle k’ofar sarautun Masarautar nan akanta da ahalinta da jinin wannan yarinyar... Cikin rawar jiki na soma k’ok’arin gudu rungume da yarinyar saidai ashe bokan Izzatu tuni ya hangoni sai ganinsa nayi gaba gareni cikin wane irin yanayi maras kyan gani.... Kafin nayi wani aune ya nunani da sandar tsafinsa sai gani nayi kaman an finciki yarinyar daga hannuna ta fad’a hannunsa, naji mummunar muryarsa yana furta “Wannan tamu ce, ita d’in an d’aura mata aure da Sarauniya, Amaryarmu ce wacce sarauniya zata zuk’i jininta..!” Take naji kaman an kifar dani k’asa tin daga lokacin ban kuma sake sanin komai gameda Alfah da ahalinsa ba domin kaw farkawa kawai nayi na ganni a d’akina wannan mutumin ya d’aureni da sark’ok’i... Hakan yasa nasan Fuskar d’iyar Alfah... Kuma ko bayan shekaru da na sake ganinta sai na fahimci itace, kenan Allah bai ida nufin Izzatu da Bokanta akan d’iyar Alfah ba, ya kub’utar da ita da buwayarsa daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa... Shiyasa na k’udiri niyyan mallaka mata wannan Taswira da Wambai ya bani shekara da shekaru Ina ajiye dashi, domin kuwa jikina ya bani itace zata zamto silan tonon asirin Izzatu...!!”Tana hawaye taci gaba da basu labari har kawo zuwa yanda Muhibbah ta taimakesu itada Ja’afar da taimakon da Ubandoma yayi masu bayan duk abubuwan da yayi mata a baya wanda Muhibbah itace Ta matso masa da tsoron mahaliccinsa kusa har ya karyar masa da zuciya yayi abinda ya dace..!!
Gaba d’aya baka jin sautin komai sai ajiyan zuciya da zuban hawaye... Sosai Ja’afar yake kuka ya matso kusan Gimbiya Turai ya duk’a yace “Rankidad’e kikace budurwar data taimaka mana sunanata Muhibbah Kuma Ta ambaci sunana tace ta sanni..?!”
Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “K’warai ta ambato sunanka J’afar, kuma ta sanka, kuma wanann budurwar itace SAUDATU d’iyar d’anuwana Alfah wanda Izzatu ta halak’asa...!!”
Hawaye suka kasa daina zubowa daga idanun Ja’afar, lokaci guda yake furta “Saudah ta dawo, ta dawo cikin Masarautar nan...!!”
Gimbiya Turai ta jinjina masa kai tace “K’warai Jafar ta dawo kuma nasan duk yanda take cikin Masarautar nan tana buk’atar taimakonmu domin kuwa idan har Izzatu ta fahimci wacece ita toh rayuwarta ka iya kasancewa cikin had’ari mafi muni fiyema da wanda ta shiga a baya...! Amma ya akayi kasan SAUDATU..?!”
Ja’afar da idanunsa suka kad’a sukai jazir bayan hannunsa yasa ya share hawayen da suka zubo masa lokaci guda ya soma furta “SAUDATU wata yarinya ce da muke had’uwa da ita a k’aramar Kasuwar dake gabashin Masarautarmu, nakan shiga kasuwa duk ranan asabar domin nayi cinikin harawan dawakan Sarki na musamman, kaman yanda kuka sani ni d’in dah ne d’aya tol ga Sarkin Bargan Dawakan Sarki mai rasuwa mai suna Almu, mahaifiyata kuwa mai suna Kumbo tun lokacin data haifeni Allah yayi mata cikawa kaman yanda mahaifina ya bani labari, tun tasowata bansan komai ba face kulada dawakan Sarki kaman yanda mahaifina ya d’aurani akai, hakan yasa har bayan rasuwar mahaifina Mai Martaba bai yarda da kowa yaci gaba da kula masa da dawakansa ba sai ni dukda kuwa k’arancin shekaruna a wancan lokacin, tun ina k’arami na iya zuwa kasuwa nayi cinikayyan abincin Dawakan Sarki da kaina sabida nid’in nasan kan kalolin ciyayi abinci Dawakai wanda yafi kyau ma Dawakai... Wannan dalili na d’aya daga cikin abinda ya kuma jefa shak’uwa da Sabo tsakanina da Sarki AbdulJabbar... Toh Kasuwar da nake zuwa nakan had’u da yarinya Saudatu wasu lokutan da ‘yar jakanta Ta kayan data saye a kasuwa... Na lura yarinyar kaman tanada tsoron mutane dan ko kallo idan ka faye mata zakaga ta soma jada baya kaman zata gudu, da shike kasuwa ne k’arami hakan yasa yawancin mutanen da suke halartan kasuwan akai akai sukan iya sanin juna... Wata rana ta gama sayyayan kayan lambu dangin su tumatur ni kuma na d’auko harawata ta Dawakai na yunk’ura zan mik’e d’aukeda harawa a gadon bayana kwatsam mik’ewar da zanyi naji nayi fatali da abu ashe kayan miyanta na watsar mata... Ta durk’usa a wajen tana duban kayan miyan tana kuka...!
Akaita bata hak’uri tak’i tayi shiru, nima da naji haushi nayi zuciya nace kar Allah Sa kiyi hak’uri Ke wannan yarinyar dama haka kike ko yaushe kina yawan zuwa kasuwa amma kaman akwai abinda kike b’oyewa, wasu irin iyaye ne gareki ma da bazasu Zo kasuwa da kansu ba sai su turo k’aramar yarinya kaman ke...!! Haka nayita mata masifa a wajen har ta tsagaita da kukan da take ta tsaya tana dubana... Ashe itama taji haushi matuk’a ai kuwa tuni naga ta daka tsalle ta finciko harawana ya tsinke gaba d’aya k’ullun dakai masa ya watse a wajen... Sai faman sakin huci take tana hararata... K’arshe jama’an dake wajen suka shiga bamu hak’uri da ni ita, aka tattara mata kayan miyanta nima aka tattara min nawa harawan..! Sosai rashin tsoronta ya bani mamaki... Ni kuwa nace wannan yarinyar batada tsoro kuma ban santa a fad’in yankin ba, bansan su waye iyayenta ba, amma wannan rashin tsoro nata yayi min kamada d’iyar manyan mutane ko masu mulki, nace sai nabi yarinyar naga inane gidansu... Tana tafe ina biye da ita har ta fahimci Ina biye da ita... Taja ta tsaya ta rik’e kunkumi tanaci gaba da sakin huci, lokaci guda kuma naga Ta auna a guje tana k’ok’arin canza hanya.. Nayi saurin shan gabanta nace “Ki tafi a hankali kada ki kuma zubar da kayan miyanki, ni babu abinda zan miki...!”
Sai naga taja Ta tsaya amma dai tsoro bai rabu da ita ba... Na aje harawana gefe nace “Ke kuwa yarinya menene sunanki kuma daga ina kike dan ni ban tab’a ganinki a yankin nan ba sai tsakanin kwanakin nan..!”
Ta kauda kanta gefe kaman bazata min magana ba sai kuma tace “Abbah na ya hanani magana da kowa a garin nan..!”
Mamaki ya kamani nace “Ya hanaki magana da kowa kuma shine yake turoki Kasuwa kiyi sayayya..?!”
Ta jinjina kai tace “Eh ya hanani magana da kowa yace akwai dalilin da ya kawo mu garin nan da zaran mun sami dalilin zamu tafi mu bar garin nan, Abbah na baya fitowa daga gida sai dare sabida yace akwai wasu mugaye a garin nan da zasu iya cutar dashi shiyasa baya iya zuwa kasuwa saidai ya turani...!”
“Sosai mamaki ya kamani jin irin kalaman da take fad’i, na jinjina kai nace “Toh Ummanki fah.. Maiyasa bazata miki rakiya zuwa Kasuwar ba..?!”
Ta d’an dubeni kad’an sai kuma tace “Ummah ta batada lafiya, ta kusa haifa min k’aramin k’ani bazata jure fitowa kasuwa ba..!”
“Na jinjina kai nace toh inane gidanku..?! Daga yanda muke tsaye tamin nuni da wani gida can da yake arewa da yanda muke tsaye, gidan shi kad’ai ne a wajen tol ko mak’ota basu dashi..! Na jinjina kai nace ni kuma cikin Masarauta ne gidanmu kuma sunana Ja’afar...! Ni ba mugu bane kaman yanda kikayi zato, kiyi hak’uri da zubar miki kayan miya da nayi..! Wani ikon Allah sai gani nayi ta murmusa tace “Shikenan Babu komai nima kayi hak’uri da zubar maka harawarka da nayi..!”
“Na kuma murmusawa Ina dubanta sai kuma nace “Basai kin bani hak’uri ba ni na hak’ura... Ki tafi gida kar a soma nemanki..! Ki wuce har ki shige gida ina kallonki bazan bari wani ya cutar dake ba..! Ta murmusa tace min na gode, zan iya kiranka Yaya Ja’afar tunda banida kowa a garin nan kuma ba’a barina na fita ko ina sai kasuwa kasuwan ma sai ranakun sati..!”
“Na kuma murmusawa nace “Toh ai ban wani girmeki sosai ba ni kar ki tsufar dani ki kirani Yaya..! Ta kuma murmusawa tace “Amma ai ka girmeni, kuma nasan k’anwarka ce tsarata kaga ni banida wani Yaya banida kowa sai Ummah na da Abbah na saiko k’aramin k’anin da zata haifo min..!”
“Tayi maganan cikeda yarinta, na murmusa nace “Toh shikenan tinda bakida Yaya Ki kirani Yaya nima tinda banida k’anwa kin zamto k’anwata...Hakan yayi miki..!?”
“Ta jinjina kai tana kuma murmusawa tace yayi min.. Yaya Ja’afar..! Daga haka d’aga min hannu tayi ta shige tana waigowa har ta kusan isa gida Ina nan tsaye Ina dubanta, sai kuma na dakatar da ita nace “Gashi kuma Yaya baisan sunan k’awarsa ba har zata shige..!” Ta murmusa kad’an tace “Sunana SAUDATU..!”
“Na jinina kai nace “K’anwata Saudatu..! Tai gajeren murmushi Ta kuma d’ago min hannu tace sai anjima...! Har saida naga shigarta gida kafin nasa kai nima na d’auki ciyawata na shige...! Toh tin daga wanann lokacin Sabo ya shiga tsakaninmu da Saudatu, nakan mata rakiya har zuwa gida, a haka bukin sallah ya k’arato na kula tana son zuwa taga hawan Dawakai amma baza’a barta ba a gida tinda ba’a barinta taje ko ina... Nayita bata labarin yanda hawan bukin sallah yake kasancewa, sosai yake sakata nishad’i yanda kasan ta had’a jini da sarauta... Kullum bata da labari da ya wuce na Dawakai da gidan sarauta... Tace min tana son ta shigo Masarautar nan wata ran taga yanda ginin gidan sarauta yake.. sabida idan tanama Abbanta labarin sarauta da abinda ya shafi gidan sarauta sai yayita mata fad’a yace koda wasa babu abinda ya had’ata da sarauta, babu komai cikin gidan sarauta sai zalunci... Dukda kuwa tsananin son kasancewa gidan sarauta da Saudatu keyi... Wata Rana Nace ta biyoni na shiga da ita taga yanda gidan sarauta yake ko sau d’aya ne a rayuwarta...haka kuwa akayi wani rana ta biyoni a tsorace na nuna mata cikin Masarauta, tayita mamakin girman gidan sarauta da yanda ake gudanar da al’amaran cikin Masarauta.. Naga yanda take matuk’ar son gidan sarauta da abinda ya shafi sarauta... Nace tinda ga k’aramar Sallah ta gabato ta fita taga yanda ake wasan Dawakai masu mulki suna hawa dawaki kuma suyi wasan saman dawaki su nuna bajintarsu.. Tace dani Aiko duk yanda za’ayi zata nemi hanya ta fito dukda ba sanin gari tayi ba, amma tana matuk’ar son ganin wasan doki... Nace zanso nayi mata rakiya tinda batasan kan gari ba amma saidai nid’in Bawa ne banida iko sai abinda Iyayen gidana sukace.. Na bata hak’uri nace bazan samu mata rakiya ba domin kuwa ni ne nake jan linzamin dokin D’an Sarki k’arami Wato Yarima Fu’ad sabida bai iya rik’e linzami..! A haka dai tace toh shikenan amma tabbas zata fita taga yanda wasan Doki yake kasancewa...!”
J’afar ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya hawaye naci gaba da gangaro masa yake furta “A ranan bukin wannan sallan tabbas wani al’amari ya faru... A hanyarmu ta komawa dani da yaran Sarki gaba d’aya wanda mune mukai dare sabida wasan doki da yaran sarki suka tsaya yi... A hanyarmu muka tsinci Saudatu ta b’ata sabida batasan kan gari ba... Yarima Mahmood wanda duk cikin yaran Sarki yafisu jin k’an mutane shi yayi umarni mu d’auketa mu maidota gida dan na sanar dashi na santa kuma har gidansu na sani.. Hakan yasa muka d’aukota muka nufo Masarauta... Na tafi na barta tareda yaran Sarki..!!” Muryarsa ya carke hawaye naci gaba da zubo masa...! Lokaci guda ya kuma d’agowa yana duban Gimbiya Turai wacce itama hawayen take... Cikin rawar murya yake furta “Kenan sun lalata rayuwar Saudatu..! Sunci zarfinta.. Sun tarwatsa ahalinta..!!! Tabbas daga baya na daina ganinta a kasuwa na kuma tadda gidansu su Saudatu ya k’one babu kowa cikinsa ya zama kango... Kuma babu wanda ya sansu balle naji labarun ina suka koma.! Ashe abinda Giwa da ‘ya’yanta suka aikata ma Saudatu kenan..!!” Ya k’arashe cikin wane irin huci lokaci guda ya mik’e yana furta “Wllhi sai na d’au fansa akan abinda suka mata..! Sai nayi ajalinsu d’aya bayan d’aya koda nima za’a d’auki nawa a matsayina na k’ask’antaccen Bawa..!!” Ya k’arashe cikin wane irin karaji...
Muryar Ubandoma suka sinkaya cikin zuban hawaye yana furta “Kai ba k’ask’antacce bane Ranakaidad’e..! Kai d’in Mai Martaba ne jinin mai Martaba..! Kai d’in D’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa kuma mahaifiyarka tana nan a wajen nan tareda Kai...!!!”
K’irajai suka shiga bugawa..!! Gaba d’aya idanu suka koma kan Ubandoma....
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*72*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ubandoma ya d’an tsagaita da kukan da yake ya d’ago ya dubi Gimbiya Turai ya kuma duban Ja’afar wanda su duka biyun hawaye ne Ke gangarowa daga idanunsu ya kuma saita dubansaga Gimbiya Turai ya duk’a gabanta had’ida risinar da kansa “Rankidad’e Jaririn da Giwa ko ince Izzatu ta canza da naki shine jaririn Malam Almu Sarkin Barga... Izzatu itace Ta kashe matar Malam Almu ta kuma kashe jaririn, tazo da da wani jariri rayayye ta canza da jaririn matar Almu, ni....!” Muryarsa ta soma rawa sosai sanda Ja’afar da tuni jikinsa ya soma rawa sosai ya duk’a gaban Ubandoma yana mai furta “Da wani jariri ka canza..! Kayi magana, ka sanar damu wanene jaririn..!!?”
Ubandoma yaci gaba da hawaye yana mai furta “Gaba d’aya cikin laifukan da nayi a baya bisaga umarnin Izzatu babu wanda ya tsaya min a rai irin wannan sabida ya k’unshi jariri wanda baida hakkin kowa... Bansan daga yanda ta samo rayayyen jariri a wancan lokacin ba Ta bani nayi musayen jaririn da na matar Malam Almu wanda tuni tayi tsafi ta kashesu daga shi har uwarsa...!” Ya kuma d’agowa yana duban Ja’afar da Gimbiya Turai kana yaci gaba da fad’in “Rankidad’e wannan jaririn da aka kai miki matsayin naki tabbas ba naki bane kaman yanda Fattu Ta gani kuma ta fad’i maki... Jaririnki yana nan da raye..! Rankidad’e jaririnki ba kowa bane face JA’AFARU..!!!” Ya k’arashe cikin wani irin kuka yana mai zama dirshan a dandamalin k’asa...!
Innalillahi wa inna’ilaihi ilaihi raji’un..! Kalaman da zukatansu Ke iya nanatawa kenan...! Ja’afar da yaji batun a wane irin ba zata d’ago gajiyyayun idanunsa yai yana kuma duban matar da Ubandoma ya gama sanar dasu cewa itace mahaifiyarsa kuma shid’in ba Bawa bane d’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Giwa itace ta rabasa da mahaifiyarsa ta kuma maidasa Bawa k’ask’antacce a gidan Mahaifinsa... Ya rayu a matsayin Bawa a cikin Masarautarsa..! Shin wannan zalunci da mai yayi kama...!! Sosai jikinsa yake rawa gumi na kuma karyo masa dukda iskan damuna dake hurawa, ji yake kaman numfashinsa na neman d’aukewa ya bar jikinsa.... Bai kuma fahimtar meke faruwa ba saida yaji hannun matar nan tana shafa fuskarsa cikin rawar murya take furta “Kaid’in d’ahna ne..! Tabbas kai d’in d’ah na ne... Domin kuwa jikina ya bani akwai abuna mai mahimmanci a gefen d’akinda Ubandoma ya rufe ni.. Ban fasa kankare jikin ginin ba, ban kuma amince na tafi na barka hannun azzaluman nan ba har saida na tabbatar Allah ya kub’utar damu tare...! D’anah.! Jaririna..!!!” Wane irin kuka mai k’arfi ya kufce mata tana mai janyo Ja’afar d’in cikin jikinta da tuni ya koma tamkar wanda yayi sumar tsaye..! Jijiyoyin jikinsa sai mimmik’ewa yake ba komai yake tunawa ba face irin wulak’ancin da yaran Giwa sukai masa musamman Yazeed da Jamal, Yazeed akan tsananin son Mulki da izza shi kuwa Jamal akan Umaima ne... Ya tuna akwai wani rana da Yazeed ya take gadon bayansa ya d’ale doki, ya tuna akwai wata rana da Jamal ya sakasa ya sumbaci takalminsa dan ya gansu da Umaima kawai don ya nuna masa cewa shid’in k’ask’antacce ne bai dace da basarakiya jinin sarauta kaman Umaima ba....Dan ma shid’in Allah yayisa mai taurin kai da kafiya ne tun a baya lokacin yana matsayin Bawa, yakanyi abu tamkar ba Bawa ba musamman idan ka tasamma tab’a mutuncinsa sam bazai barka ka k’ask’antashi ba a matsayinsa na d’anAdam wanda Ubangijin talikai gaba d’aya ya d’aga darajan d’an adam kan sauran halittun duniya..! Shi mutum ko yaya ka gansa ba abun wulak’antawa bane, baka San kalan Baiwar da Ubangijinsa yai masa ba, kuma bakasan koma ya fika daraja a wajen mahaliccinku ba, idan yafika tsoron Allah sai ya fika daraja..! Sam Shari’a bata bama kowa daman kaci zarafin wani wanda yake k’arashinka ba koda kuwa bawanka ne...!
Ya dinga tuna ire iren cin mutunci da wulak’anci da ya fuskanta daga wajen wannan ahali... Sai yanzu komai yake dawo masa daki daki, watak’ila Mai Martaba ya fahimci shine mahaifinsa na asali da Giwa ta fahimci hakan shine ta kashe mai Martaba shima kuma Ta nemesa zata kashesa.. Wannan mata takai mak’ura wajen zalunci... Shi ko a labarun hikayoyi da ake karanto masu da cikin Fada bai tab’a cin karo da labarin azzaluman Baiwa irin Izzatu ba...! Amma zuluncinta yazo k’arshe da izinin Allah, sai ta girbi duk abinda ta shuka daga ita har yaranta guda biyu...! Yana mamakin yanda Yarima Mahmood ya kasance daga cikin ahalin wannan azzalumar mata domin kuwa shid’in ya banbanta da muguwar ahali irin wannan.. Kodashike Allah yakan fidda rayayye daga cikin macecce sannan ya kan fidda macecce daga rayeyye... Domin kuwa babu abinda yafi k’arfin buwayarsa...! Ja’afar ya lumshe idanunsa a hankali sanda yaji hannun Gimbiya Turai tana shafe fuskarsa da ruwa dan su duk a zatonsu suma yayi...! Yaja wane irin dogon numfashi had’ida sauk’e idanunsa kan matar, yai mata K’uri bayanan kalan azabtarwa da muzgunawa had’ida mummunan cin amanan da Baiwar ta tai mata na kuma yawo a kwanyarsa...!
Hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa wanda tuni Sun kad’a sunyi jazir.... Ji yayi yakai hannunsa dake tsananin rawa saman fuskarta yana share mata hawayen dake kuma gangaro mata. Cikin rawar murya yake furta “Ta cutar dake..! Ta miki zalunci mafi muni Ummi tah... Ta maidaki Baiwa cikin gidan Mijinki sannan Ta maida d’anki Bawa cikin gidan mahaifinsa... Daga k’arshe ta haukataki ta kuma salwantar da sauran ahalinki..! Wannan matar bata cancanci yafiya ba domin idan na yafe mata ni kaina bazan iya yafewa kaina ba sabida abubuwan da tai miki Mahaifiyata..!!” Ya k’arashe cikin wane irin cazgan kuka..! Tuni Gimbiya ma kukan ya kufce mata suka had’e goshinsu itada d’anta Ja’afar waje guda suna yin mai isarsu...!!
Tirk’ashi..! Rayuwa mai bud’e ma Bawa shafuka daban daban, ko wanne da yanda yake zuwa maka, wad’annan bayin Allah rayuwa ta kuma bud’e masu sabbin shafuka.. Bayan tsawon shekarun nan gashi Allah ya had’a fuskokinsu, tabbas tsanani yana tareda sauk’i mai hak’uri shikeda riba...!
Bayan komai ya tsagaita Baba Nomau ya nusa had’ida furta “Alhamdulillahi..! Alhamdulillah...! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da babu wani bayan shi, mai mulkin Sammai da k’assai da abinda ke cikinsu da abinda ke tsakaninsu, tsira da amincinsa su