Showing 1 words to 3000 words out of 26566 words

Chapter 1 - Miftahuzzarbil Book 2 Complete By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

ο»Ώ**π™Όπ™Έπ™΅πšƒπ™°π™·πš„πš‰πš‰π™°πšπ™±π™Έπ™»**
π™»π™Έπšƒπšƒπ™°π™΅π™Έ 𝙽𝙰 π™±π™Έπšˆπš„ 2
π™Ώπ™°πšπšƒ 𝙰
𝙽𝙰 π™°π™±π™³πš„π™»'π™°πš‰π™Έπš‰ πš‚π™°π™½π™Έ 𝙼𝙰𝙳𝙰𝙺𝙸𝙽 𝙢𝙸𝙽𝙸.
πšƒπšˆπ™Ώπ™Έπ™½π™Ά 𝙰𝙷𝙼𝙰𝙳 π™Όπš„π™½π™½π™Έπš.
π™Ώπ™Ύπš‚πšƒπ™Έπ™½π™Ά π™½π™°π™Ήπ™Έπ™±πš„π™»π™»π™°π™· π™Όπš„π™·π™°π™Όπ™Όπ™°π™³.

π™Ίπšžπš’πš’ πš‘πšŠπš”πšžπš›πš’ πš‹πšŠπš’πšŠπš— πšπšœπšŠπš πš˜πš— πš•πš˜πš”πšŠπšŒπš’ πš‹πšŠπš”πšž πšœπšŠπš–πšž πš™πš˜πšœπšπš’πš—πš πšπš’πš— πš•πš’πšπšπšŠπšπš’ πš‹πšŠ, 𝚝𝚘 πšŠπš–πš–πšŠ πš’πšπšŠπš— πš”πšžπš”πšŠπš’πš’ πš•πšŠ'πšŠπš”πšŠπš›πš’ 𝚍𝚊 πš’πš›πš’πš— πš›πšŠπš’πšžπš πšŠπš› 𝚍𝚊 πšŠπš”πšŽ πšŒπš’πš”πš’ 𝚠𝚊𝚍𝚍𝚊 πšπšŠπš”πšŽ πšŒπš’πš”πšŽ 𝚍𝚊 πš–πšŠπšπšœπšŠπš•πš˜πš•πš’ πš‘πšŠπš”πšŠπš— πš‹πšŠπš£πšŠπš’ πš‹πšŠπš”πšž πš–πšŠπš–πšŠπš”πš’ πš‹πšŠ.
𝚝𝚘 πšŠπš–πš–πšŠ πš’πš—πšœπš‘πšŠ π™°πš•πš•πšŠπš‘ πš’πšŠπš—πš£πšž πš£πšŠπš”πšž πšŒπš’πšπšŠπš‹πšŠ 𝚍𝚊 πš“πš’πš— πš–πšž πš”πšŠπš–πšŠπš› 𝚒𝚊𝚍𝚍𝚊 πšŠπš”πšŠ πšœπšŠπš‹πšŠ.
πš–πšžπš—πšŠ πšπšŠπšπšŠπš— π™°πš•πš•πšŠπš‘ 𝚒𝚊 πšπšŠπš’πš–πšŠπš”πšŽ πš–πšž, 𝚒𝚊 πš”πšžπš–πšŠ πš”πšŠπš›πšŽ πš–πšž 𝚍𝚊𝚐𝚊 πšπšžπš”πš”πšŠπš— πšœπš‘πšŠπš›πš›πš’ πš—πšŠ πš‘πšŠπš•πš’πšπšπšŠ.

π™Όπ™°πšπš„π™±πš„π™²π™Έπ™½ πšˆπ™°π™²π™Έ 𝙢𝙰𝙱𝙰 𝙳𝙰 π™²π™΄πš†π™°....

Lokacin da suka baro masaukinsu,asuba bata yi ba domin har ynx akwai sauran duhu a gari.Gaba daya gudajen mutane a rufe suke birnin yayi tsit kamar ba mutane a cikinsa domin ba'a jin sautin komai face haushin karnuka daidaiku.Tsoho rafkanagu,hajarul mukurus da Ruziyal ne suka biyo hanya a cikin wannan lokaci saboda suje fadar sarki Muzuluch don suji karshen hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila gaba daya Daren jiya ba suyi barci ba sbd kawai dokin gari ya waye su dawo fada.Gashi yanxun ma sun kasa hakura garin ya waye,suna tafe suna hira inda hajarul mukurus ya dubi Ruziyal yace,"Anya kuwa tun daga hikayoyin sarki Dujalu zuwa wannan ta ynx akwai wadda tafi hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila dadi"?.
Ruziyal yayi murmushi yace,"Haba Hajarul mukurus Ashe ka manta da hikayar masunci lamlas kenan da kuma attajiri kuffuru bin Aljar.Ai duk sunfi wannan hikayar ta bawa Mozur saidai kuma hikayar bawa Mozur ta fisu daukar hankali da Sosa zuciya musamman yadda sarki Muzuluch ya yanke Mana labarin a daidai haduwar sarauniya Ashikatul Ashiriya da sarki saubatul Azman a bakin kogon Baitul Husuk.Dole ne mutum yaso yaji yadda zata qarke,shin za'a yi yaki a nan wajen ko kuwa za'a shiga cikin kogon ne don a debo wannan dukiya?,Shi kansa kogon mutum zaiso yaji yadda cikinsa yake haka kuma mutum zaiso yaji abinda zai faru idan gimbiya suhaila ta gama baiwa kuyanga suzaila labari.Tsoho rafkanagu yayi gyaran murya yace,"Duk da dai baku sa dani ba a cikin hirar taku bari nayi muku karambani.Maganar gaskiya hikayar bawa Mozur tafi duk sauran hikayoyin dadi,alajabi da kuma darasi.Domin a labarin ne mutum zai gane cewa kuskure ne ka wulaqanta mutum dan uwanka don zai iya zama wani abu a nan gaba.Kamar yadda boka hazaru ya baiwa suhaila labarin cewa nan gaba Mozur zai zama sarki,haka kuma labarin na nuni da cewa tsananta gaba da mutum kuskure ne tun daga yadda suhaila ta tsani bawa Mozur amma sai gashi a karon banza ta Sami ciki da shi harma ta haifi da mai kamanninsa sak.Hajarul mukurus yace,"hakika zancen ka dutse ne nima na amince".
Haka dai su Ruziyal suka cigaba da hira har suka qofar fada.Da zuwa suka iske ba'a bude gidan sarautar ba,kuma ga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikin su.Rafkanagu ya matsa kusa da masu gadin yana dogara sanda cikin tafiya da kyar ya dube su yace,"Ya ya na ku bude mana kofa mu shiga cikin fada mu zauna mune baqin sarki wadanda yake bawa labari".
Daya daga cikin masu gadin ya dube shi yace,"Baba ai saidai kuyi haquri domin lokacin bude fada baiyi ba.Idan za ku iya jira ku zauna anan ku jira,idan kuma ba zaku iya ba to ku koma masaukinku in yaso in an jima kwa dawo".
Rafkanagu yayi ajiyar zuciya yace,"Yaro ai mun fito kenan ba zamu koma ba.Gwara dai mu zauna mu jira".
Nan dai suka zauna har lokaci yayi,sannan aka bude qofar suka shiga ciki suka zauna a gefe guda.
Sarki Muzuluch bai fito ba sai bayan sa'a uku.Da fitowarsa kowa ya miqe tsaye sai daya zauna akan karaga aka zazzauna.Sannan kuma fadawa suka fara kwasar gaisuwa har aka zo kansu Ruziyal.Koda sarki Muhucul ya dubi fuskokinsu Ruziyal sai ya bushe da dariya.Sannan yace,"Yaku wadannan baqi,menene ya hanaku yin barci jiya"?.
Cikin mamaki su Ruziyal suka dubi juansu suka kasa cewa komai.Sarki Muhucul ya sake bushewa da dariya karo na biyu yace,"Na san abinda ya hanaku yin barci,ba komai bane face dokin son jin qarshen hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila.To kusha kuruminku yanxun nan zan cigaba da baku wannan labari,kuma indai lokaci baiyi halinsa ba za kuji qarshen labarin gaba daya".
Sarki Muhucul yayi gyaran murya sannan ya fara bayani kamar haka:-

"Bayan anyi kallon kallo tsakanin gimbiya Ashikatul Ashiriya da sarki saubatul Azman sai sarauniya ta bushe da dariya tace,"Ya kai tsohon mijina kayi sani cewa duk wani shiri naka a kaina ba zaiyi tasiri ba.Ba zai yiyu ka rabani da 'yata ka rabani da dan uwana,sannan kuma kace zaka rabani da dukiyata.Kota halin qaqa saina ga bayanka,domin bani da maqiyin daya fika a doron kasa.Dukiyar da ka dade kana begenta yau zaka ganta da idanun ka,Amma saidai ka kalle ta da idanu badai ka taba ta ba ko ka mallaketa".
Koda Ashikatul Ashiriya tazo nan a zancenta sai sarki saubatul Azman yayi murmushi yace,"Yake Ashikatul Ashiriya kiyi sani cewa yar da kike tutiyar cewa taki ce ba jinin ki bace,domin kuwa inda jinin ki ce ba zata guje ki ba ta taho wajena.Haka kuma dan uwan da kike tutiyar cewa dan uwanki ne yau ya zabi ya bar gidanku ya tafi wata duniyar ya zauna da dukiya ba da sarauta ba saboda kishin karagar da kike kai.Kinga kuwa ashe bai kamata kiyi gaba dani ba akan yarki da dan uwan ki,saidai kiyi gaba dani akan dukiyar ki".
Koda jin wannan batu sai itama Ashikatul Ashiriya tayi murmushi tace,"Ya kai saubatul Azman kayi sani cewa shi dan uwa rabin jiki ne ko ya guje ka dole ne ka so shi,tunda hannunka baya rubewa ka yanke.Batun 'yata daka ce ba jinina ba ce,mene ne hujjarka"?.
Shaubatul Azman ya bushe da dariya.Sannan ya bata labarin lokacin data haihu tare da kuyangarsa.Sannan yayi rantsuwa da darajar abin bautarsa yace,"Wannan labari gaskiya ne".
Koda fadin haka sai idanun Ashikatul Ashiriya suka ciko da kwalla ta dubi shaubatul Azman tace,"Hakika ka cuce ni da ka bani 'yar wata na shayar da ita a matsayin tawa ta cikina.Na rantse da girman birnin Kisra saina dandana maka azabobi bisa wannan laifi".
Kafin Shaubatul Azman yayi wani yunquri tuni dakarun Ashikatul Ashiriya sun yanyame shi da dakarun nasa aka daddaure su da sarqa.Ashikatul Ashiriya tasa aka gurfanar da Suhaila a gabanta tace,"Yake Suhaila kiyi sani cewa na rene ki da zuciya a matsayin 'yar cikina kuma kin tsotsi nonona.Na kula da rayuwar ki da lafiyar ki tun kina jaririya har izuwa girmanki,yanxu da butulci zaki saka mini kenan?,ya kamata ace kin mini kara ko dan saboda halaccin dana miki a rayuwa.Tabbas kema kin cancanci sakamako kwatankwacin abinda kika aikata".
Nan take sarauniya ta bada umarnin a daure gimbiya suhaila cikin sarqa.Dakaru kuwa suka bi umarni da gaggawa.Daga nan saita kirawo jarumi Haiman ta dora hannunta guda a kafadarsa tana mai murmushi a gareshi tace,"Ya kai dan uwana kayi sani cewa kai jinina ne,kuma komai zaka yi min dole ne dauki haquri don haka na yafe maka wannan laifi daka yi a gareni,kuma ina roqonka daka bini zan sauka daka kan karaga na baka".
Yayin da jarumi Haiman yaji wannan batu sai idanun sa suka ciko da kwalla take yayi nadamar abinda yayi,ya nemi gafarar Ashikatul Ashiriya.Kawai saita rungume shi tana kuka.Ba zato ba tsammani sai Ashikatul Ashiriya ta zaro wuqa cikin shammace ta cakawa jarumi Haiman a ciki.Haiman ya sulale kasa ya fara shure shuren mutuwa.Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan.Koda jarumi Miqdad yaga abinda ya faru ga abokinsa Haiman,saiya kwalla ihu yayi ya rusa kuka a cikin ragar qarfen da aka sa shi.
Ashikatul Ashiriya taxo kan Haiman Wanda yake magagin mutuwa ta tsaya tana mai zubda hawaye tace,"Ya kai dan uwana kayi mini gafara na kasheka da hannuna.Ka sani cewa rayuwar ka hadari ce ga tawa.Ina son mulki fiye da komai a rayuwa ta.Tabbas in dai kana raye wata ran saika rabani da shi saidai zan kasance mai matuqar bakin ciki tun da yanzu bani da sauran dan uwa na jini a duniya".
Tana gama fadin haka ne idanun Haiman suka rufe komai na jikinsa ya daina motsi.Nan take tasa aka dauko gawarsa aka dunguma izuwa gaban qofar kogon Baitul Husuk.Sarki Shaubatul Azman,Jarumi Miqdad da gimbiya suhaila kuwa aka taho da su a daddaure har bakin kogon.Da zuwa sai Ashikatul Ashiriya ta kama hannun Haiman ta soka dan yatsansa a cikin rami guda dake jikin qofar.Sannan ta soka nata dan yatsan a cikin rami na biyu.Yin hakan ke da wuya sai hayaqin nan da kuma walqiyar nan dake sararin sama bisa ganuwar Baitul Husuk suka bace bat.Wani zagayayyen qarfe mulmulalle dake cikin qofar ya zagaya da gudu.Sannan wasu manyan sakatu daga ciki suka zare kansu.Take qofar kogon Baitul Husuk ta fara budewa a hankali.Shi kansa budewar katuwar qofar ya isa abin al'ajabi.Tsaitsaye a bakin qofar wasu dakarun yaki ne na aljanu gasu nan birjik sunyi dogon layi ba adadi.Gaba dayansu a qame suke kamar gumaka,ko motsi basa yi amma fa idan ka dubesu sau daya ba zaka sake kallon su ba saboda kwarjinin su da ban tsoro.Cikin kogon kuwa babu kasa ko ina dutsen lu'u lu'u ne a shimfide kamar dama can haka aka halicci wajen.Kafin Ashikatul Ashiriya ta shiga cikin kogon saida tayi wurgi da gawar dan uwanta Haiman.Sannan ta shiga cikin kogon Baitul Husuk aka bi ta a baya duu gaba daya.
Kogon Baitul Husuk a haskake yake da wani irin haske na musamman Wanda ko allura ce ta fadi kasa sai an ganta.Duk da cewa kogon yakai shekaru dubu a kulle babu kura a ciki,kuma babu yana.Ko ina ka duba fes fes yake banda qamshi babu abinda ke tashi.Duk inda mutum ya duba dukiya ce baja-baja mai tsananin tarin yawa kuma duk dangin Zinare, lu'u lu'u,yaqutu,jauhar,zubardaji,murjani da sauransu.Kai inda za'a Kai shekara daya ana diban wannan dukiya ba zata qare ba.Kayan qawa gasu nan iri-iri harda Wanda mutum bai taba gani ba.Saida kowa ya shiga kogon sannan kofar ta rufe kanta da kanta.
Nan fa aka zazzaro idanu cikin rudewa da mamaki.Nan fa jama'a suka dasawa dukiya wawa suna ihu kamar mahaukata.Saida Ashikatul Ashiriya ta daka tsawa sannan kowa ya shiga taitayinsa.Nan take ta bada umarnin kowa ya cika jaka da dukiya.Nan fa aiki ya samu,wasu ma saisu cika yadda baza su iya dauka ba,dole sai sun rage.Haka dai miliyoyin jama'a suka yi ta facakarsu kai ka ce kasuwar duniya ce a wajen.
It's kuwa Ashikatul Ashiriya sai ta sami wuri ta zauna fadawanta suka kewaye ta ana fadanci sai kyalkyala dariya take da farin ciki da ta dubi tarin dukiyar da aka diba ta tuna cewa duk tata ce,kuma in an koma gida a baitul malinta za'a zuba wannan dukiya.Haka kuma duk sa'ar data buqatar qari sai a dawo a diba.Abinda ta mance shine ynx fa kofar kogon ta rufe kuma ba zata taba buduwa ba sai an sake zura dan yatsan ta guda dana dan uwanta Haiman Wanda tuni ta kashe shi tayi wurgi da gawarsa a kofar kogon kafin a shigo.Duk wannan buduri da mutanen Ashikatul Ashiriya ke yi Jarumi Miqdad da sarki saubatul Azman da gimbiya suhaila na kallo amma basu da ikon diban komai kasancewar a daure suke.Shi kuwa littafin nan na sihirin shiga kogon Baitul Husuk na tare da gimbiya suhaila ta boye shi a cikin rigarta.
Saida aka shafe kwana uku cur miliyoyin jama'ar na dura dukiya cikin jakunkuna.Sannan kowa ya gama cika jakarsa.Nan take Ashikatul Ashiriya tasa aka zo da sarki Shaubatul Azman, Jarumi Miqdad da gimbiya suhaila aka kwance su,sannan aka sake daure su a jikin wasu manyan dirkoki na cikin kogon.Ashikatul Ashiriya ta dube su daya bayan daya ta bushe da dariya tace,"Ya ku maqiyana kuyi sani cewa anan zamu barku cikin wannan kogo kuyi ta zama a haka har yunwa da qishirwa su kashe ku.Da wannan kalami nake muku bankwana da taya ku murnar mutuwa a sauqaqe".
Koda gama fadin haka sai kowa ya bushe da dariya.Nan take sarauniya ta bada umarnin a tashi a fita daga cikin kogon don a koma birnin Kisra.Kamar tururuwa na fitowa daga cikin raminta haka mutane su kayi ta tafiya suka nufi bakin qofar.Saida aka shafe awa bakwai ana tafiya sannan kowa ya isa bakin qofar aka tsaya akayi cincirindo domin qofa a rufe take.A sannan ne Ashikatul Ashiriya ta tuna cewa dole saida dan yatsan dan uwanta Haiman kofa zata budu.Nan fa hankalinta ya dugunzuma ta kwarara uban ihu Wanda ya firgita kowa.Ashikatul Ashiriya ta dubi fadawanta ta sanar da su halin da ake ciki.Nan fa ido ya raina fata kowa yayi tsuru tsuru murna ta koma ciki.Ashikatul Ashiriya tasa dan yatsan ta ita kadai da nufin kofa ta bude amma sai kogon ya cika da wata irin qara mai cika kunne.Nan take sandararrun Aljanun nan suka bude idanuwansu wato dubunnan masu tsaron Baitul Husuk.Babu wanda ya lura da hakan.

π™Όπš„ π™·π™°π™³πš„ 𝙰 π™Ώπ™°πšπšƒ 𝙱 𝙳𝙾𝙽 𝙹𝙸𝙽 𝙲𝙸𝙢𝙰𝙱𝙰𝙽 πš†π™°π™½π™½π™°π™½ π™Ίπ™°πšˆπ™°πšƒπ™°π™²π™²π™΄π™½ π™»π™°π™±π™°πšπ™Έ.

π™½πšŠπš“πš’πš‹πšžπš•πš•πšŠπš‘ π™Όπšžπš‘πšŠπš–πš–πšŠπšπŸ˜ŽπŸ˜**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU.
PART B
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI.
TYPING AHMAD MUNNIR.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD β€οΈπŸ™πŸ˜„

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..

Koda Ashikatul Ashiriya taga babu abinda ya faru sai ta sake sa dan yatsan nata a karo na biyu.Nan fa Aljanun suka motsa hannanayensu dake ruqe da makamai.Sai da kowa yaji wannan motsi amma ba'a gane ko na mene ba.Ashikatul Ashiriya ta sake zura dan yatsan ta a karo na uku.Faruwar hakan ke da wuya sai Aljanun nan suka zama rayayyu gaba dayansu.Kawai sai suka afkawa mutane da sara.
****************
Nan da nan kogon ya hargitse da ihu,masu gudu na yi,masu faduwa a mace na yi.Gimbiya suhaila da jarumi Miqdad kuwa na daure a jikin sarqoqin gini haka ma Shaubatul Azman.Kiri-Kiri suna ganin halaka,amma babu damar su gudu su ceci kansu.Sarauniya Ashikatul Ashiriya kuwa da rarrafe ta shiga cikin wani saqo na kogon,ai kuwa sai wasu daga cikin fadawanta suka bi ta da gudu suna tunanin cewa wata hanyar ce daban ta tsira.Abin da basu sani va shine sun sake kai kansu cikin wata babbar masifar ne wacce za su gwammace gwara su tsaya a baya Aljanun su kashe su.
Haka dai Aljanun suka dinga ragargazar jama'a kafin kace wani abu tuni fadar ta cika da jini male-male.Wasu daga cikin dakarun sun yi qoqarin su yaki wadannan Aljanun amma ko kadan basu sami nasara ba,domin Sara da Suka baya tasiri a jikin su.Sai dai kaga mayaki ya yarda makaminsa ya take da gudu amma sai Aljanun su cafko shi da hannu daya su tsarge shi da takobi su yar da gawarsa.Kai a wannan rana mun ga tashin hankali domin munga yadda aljanu ke daukan rayukan miliyoyin mutane kamar suna zubar da kwayoyin hatsi.
Ana cikin wannan badaqala ne takobin wani aljani ta sare sarqar da aka daure jarumi Miqdad.Ai kuwa nan take sarqar ta tsinke.Ko da Miqdad yaga ya kubuta sai ya daka tsalle sama ya doki wani aljani dake shirin sare sarki Shaubatul Azman da kafa biyu.Aljanin ya bugu da dirkar gini takobinsa ta su6uce kasa.Cikin zafin nama Miqdad ya dauki takobin ya hau Aljanun da sara.Bisa mamaki sai muka ga duk aljanin da ya sara sai ya kama da wuta,ya kone qurmus ya zama toka.Nan take Miqdad ya gano cewa sirrin na jikin takobin Aljanun.Cikin zafin nama Miqdad ya sare sarqoqin da suka daure Shaubatul Azman da wadanda suka daure ni muka ku6uta.Da karfin tsiya Miqdad ya qwato wadansu takubban guda biyu daga hannun Aljanun ya bamu ni da Shaubatul Azman yace mu kare kanmu.Nan fa muma muka shiga ragargazar Aljanun.In ka dauke mu ukun babu wani mahaluqi mai iya ta6uka komai a wajen.A haka dai muka kutsa ta cikin Aljanun muna saransu suna saranmu har muka sami damar shiga saqonnan inda su Ashikatul Ashiriya suka bi.
Wani irin saqo ne mai zururun lungu,kuma mai dubu ba don muna riqe da takubban Aljanun nan ba da baza mu iya wucewa ba.Hasken takubban ne ya ringa haska mana hanya.Tun da muka shiga wannan saqo muka tsira daga wadancan aljanu,amma muna ta jiyo ihun mutane da karar takubban Aljanun alamun cewa har ynx Aljanun kisa kawai suke ba sassauci.Sai da muka yi tafiyar sa'a guda a cikin wannan saqo.Sannan muka iso wata babbar haraba inda muka iske wani wawakeken rami mai cike da tafasashshiyar dalma tana za6al6ala.Hucin zafi na fesowa daga cikinta tare da hayaki.A cikin ruwan dalmar akwai wasu manyan sandunan karfe da yawa da suka yi tsiri sama.Fadin saman nasu na da fadi kadan.Dole ne mutum ya tattaka wadannan sandunan karfe idan yana son ya tsallake wannnan kogin darma.Sannan ya cigaba da tafiya akan turba.
A cikin kogin darmar ne muka ga gawar mutum biyar daga cikin fadawan Ashikatul Ashiriya suna nutsewa.Nan fa muka tsaya muka dubi juna cikin shakka da tsoro.Jarumi Miqdad ya dubi kogin darmar nan da kuma sandunan dake cikinsa a tsaitsaye yayi nazarin su sosai.Sannan yace,
"Kuyi sani cewa bamu da wani za6i face mu bi ta cikin kogin darmar nan muna masu taka kan sandunan nan.Amma fa ku sani cewa ba kowace sanda ake takawa ba,domin wata idan aka takata nutsewa kasa zata yi da mutum ya fada cikin kogin darmar nan ya narke.Babu mamaki Ashikatul Ashiriya ta san sirrin Baitul Husuk shi yasa ta iya wucewa ta nan,amma da sai mun iske gawarta a cikin kogin darmar nan."
Koda fadin haka sai na girgiza kaina nace,"Ko shakka babu sarauniya ta san sirrin kogon nan,domin ta taba bani labarin cewa ta haddace duk abinda da ke rubuce a cikin wannan littafi da ake kira Mabudin arzikin Kisra."
Koda nazo nan a zancena sai jarumi Miqdad ya dube ni yace,"Ina wannan littafin shin ba yana tare dake ba?"
Koda jin haka saina tuno da littafin da yake cikin rigata.Cikin sauri na laluba aljihunan rigar tawa.Ai kuwa sai gashi na fiddo littafin.Miqdad ya karbi littafin ya bude har izuwa shafi na uku,saiga hoton wannan kogin darma.A kasan hoton anyi bayani kamar haka:
"Ya kai bakon wannan kogo kayi sani cewa baza ka iya shallake wannan kogin darma ba face ka bi takan wadannan sanduna na cikinsa.Dole ne ka rufe idanun ka yayin da zaka taka sandunan kuma ka tabbata cewa idan ka taka sandar farko ka tsallake ta biyu kafarka ta dira akan ta uku.Haka zaka yi tayi harka fita daga cikin wannan kogi na darma mai tsawon kamu dari uku.Kuskure daya na nufin ajalinka."
Koda jarumi Miqdad ya gama karanta wannan jawabi sai muka dubi juna muka yi ajiyar zuciya.Cikin karayar zuciya na dubi jarumi Miqdad nace,"Ni kam bazan iya hawa wadannan itatuwan ba idanu na a rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login