Showing 9001 words to 12000 words out of 26566 words

Chapter 4 - Miftahuzzarbil Book 2 Complete By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

ya fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Zarto amma saiya kasa.Nan da nan idanun Mozur suka wurƙile suna nuna alamun suma.Laslaiya dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawayen tausayi ba.Gashi a ƙa'idar wannan gasa ba'a raba faɗan face ɗaya daga cikin ƴan kokawar yaje ƙasa.A zahiri dai mutane suna iya ganin wutsil wutsil ɗin ƙafafun Mozur da motsin hannuwansa kamar ba suma yayi ba amma a baɗini ƙanin suma yayi,inda ya shiga tunanin irin haɗarurrukan da ya shiga a can birnin Shauƙib a lokutan da gimbiya Suhaila tasa aka yi masa dukan kawo wuƙa don a kashe shi da kuma lokacin data sa aka ɗaure shi a cikin buhu aka jefa shi cikin tsakiyar teku.Koda Mozur yazo nan a tunanin sa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa ya watstsake.Take wani sabon ƙarfin na musamman ya shige shi,kawai sai aka ji ya kwarara uban ruri lokaci guda ya ɓanɓare hannuwan Zarto daga wuyansa kuma ya sunkuci Zarto cikin zafin nama yayi sama dashi ya dinga hajijiya da shi.
****************
A wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta bushe da dariyar farin ciki tana yiwa Mozur tafi.Mozur yayi ta hajijiya da Zarto a sama saida ya fita daga haiyacinsa sannan ya kwaɗa shi da ƙasa.Gaba ɗaya filin ya ruɗe da shewa da tafi.Jama'a suka ruga kan tudun da ake gasa suka ɗaga jarumi Mozur sama suna cilla shi a cikin iska yana dawowa kan hannuwansu ana yi masa jinjina.A sannan ne Mozur da gimbiya Laslaiya suka ƙurawa juna ido yaga tana yi masa tafi fuskarta cike da annuri amma kuma ga hawaye na zuba a idanun nata.Al'amarin da yayi matuƙar jefa Mozur cikin tsananin mamaki da damuwa kenan.Nan take aka kira Azmandu yazo gaban gimbiya Laslaiya ya kwashi gaisuwa.Sannan ta sunkuya ta ɗauki ƙatuwar jaka cike da dirhami ta miƙa masa.Azmandu ya karɓi jaka ya fara tiƙar rawa cikin tsananin farin ciki.Sannan ya ruga inda jarumi Mozur ke tsaye ya rungume shi yana mai yi masa jinjina.Sarki Amzadu ya kama hannun gimbiya Laslaiya suka nufi cikin gidan sarauta dakaru na biye da su.Laslaiya tayi ta waigen jarumi Mozur suna kallon juna tana murmushi a gareshi har ta ƙule ya daina ganinta.
Lokacin da Mozur da Azmandu suka koma cikin gidan nan inda Mozur ke bauta sai suka zauna don su huta.Azmandu yasa aka kawo musu abinci iri iri da kayen shaye shaye kala kala,don suyi walimar wannan nasara da suka samu.Nan take Azmandu ya kama ciye ciye,shi kuwa Mozur saiya zubawa abincin idanu ya kasa ci,kuma ba komai yake gani ba a cikin abincin face fuskar gimbiya Laslaiya.Zuciyarsa cike da wasu wasi yana mai tambayar kansa cewa me yasa gimbiya ke yi mini murmushi haka?
Kuma mene ne dalilin zubar hawaye a idanunta?
Amsar da ya kasa samar da ita kenan a cikin ƙwaƙwalwarsa.Koda Azmandu ya lura da halin da Mozur ya shiga saiya dubeshi yace,
"Ya kai wannan jarumi tunanin me kake haka wanda ya hanaka cin abinci alhalin yau ranar farin ciki ce a gare mu ko kuwa wani abun kake da buƙata ka kasa sanar dani?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace,"ya shugabana kayi sani cewa bana buƙatar komai daga gareka kuma babu abinda nake tunani face yadda al'amuran rayuwa ta suka kasance a da da yanzu."
Da jin haka sai Azmandu ya bushe da dariya sannan yace,"ashe kuma bayi kukan shiga damuwa da tunani irin wannan?Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare."

MU HAƊU A PART F DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARIN.**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU✍️✌
PART F ❤❤
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI🧝‍♀️
TYPING AHMAD MUNNIR.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD.

MARUBUCIN YA CI GABA DA CEWA...

Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare."
Mozur yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa ita rayuwa bata da wani haƙiƙani akan kowa.Da mu daku duk ɗaya ne domin bawa na iya zama sarki,haka kuma sarki na iya zama bawa."
Koda jin wannan batu sai Azmandu ya furzar da abincin dake bakinsa cikin fushi yace,"wannan wace irin maganar banza kake yi?
A ina ka taɓa ganin sarki ya zama bawa?
Ai abinda ba zai taɓa yiwuwa bane,domin ko tarihin labarun da suka shuɗe ban taɓa jin haka ba."
Nan dai Azmandu ya rufe Mozur da faɗa yayi ta bambami har ya gaji.Sannan ya tashi ya fice cikin fushi ba tare da ya kammala cin abubuwan dake gabansu ba.Shi kuwa Mozur saiya kishingiɗa ya lumshe idanun sa ya cigaba da ganin hoton fuskar gimbiya Laslaiya a cikin zuciyarsa.
Kamar yadda jarumi Mozur ya kasance cikin sabon yanayi na tunani da rashin sukuni haka gimbiya Laslaiya ta kasance domin ita ma dai a wannan rana ko ruwa bata iya sha ba bare cin abinci.Idan ta kwanta sai taji kwanciyar ba daɗi don haka saita miƙe zaune.
Zaman ma saita ji ba daɗi kawai saita tayi ta kai komo a cikin harabar gidanta ta kasa zaune ko tsaye.
Duniyar gaba ɗaya ta yi mata zafi.
Tana cikin wannan hali ne mahaifiyarta Zalisha ta shigo ta risketa.
Kallo ɗaya Zalisha ta yi wa Laslaiya ta fuskanci cewa lallai tana cikin damuwa.
Nan take Zalisha ta kama hannun Laslaiya ta jata izuwa cikin ɗakinta ta zaunar da ita a gefen gado suka fuskanci juna.
Zalisha tace,"yake 'ya ta ki yi sani cewa babu abinda nake so a duniyar nan sama da ke,kuma duk abinda kike so shi nake so,haka kuma wanda kike ƙi dole na ƙi shi.
Yake 'ya ta haƙiƙa yau kina cikin damuwa don haka zuciya ta ta sosu ina umartarki da ki hanzarta sanar dani abinda ke damunki,domin na amince miki shi yanzu take."
Sa'adda Zalisha tazo nan a zancen ta sai Laslaiya tayi ajiyar zuciya.
Sannan tace,"yake ummina ki yi sani cewa babu abinda ke damuna face son ganin jarumin da yaci nasarar gasar kokawa a yau."
Koda jin haka sai mamaki ya kama Zalisha tace,"wane ne wannan jarumin?"
Haka kuma mene ne sunansa?"
Cikin yanayin damuwa Laslaiya tace,"ban san kowane ne shi ba,amma naji ana kiransa da suna Mozur,kuma sarkin gida Azmandu ne yazo da shi filin gasa."
Koda jin haka sai Zalisha tace,"ai kuwa kamar na taɓa jin sunansa a cikin gidan sarautar nan amma dai bari dai nasa a bincika...."
Nan take Zalisha ta kira wata baiwa Amaratu tace da ita ta ruga gidan sarkin gida Azmandu tace yazo yanzun.
Amaratu ta ruga da gudu don cika umarni.
Jim kaɗan sai ga ta ta dawo tare da Azmandu.
Azmandu ya ƙaraso da sauri izuwa gaban Zalisha ya faɗi ya kwashi gaisuwa cikin biyayya da sunkui da kai ƙas.
Zalisha ta dube shi tace,"ya kai Azmandu kayi sani cewa ban kira ka nan dan komai ba don sai ka yi mini cikakken bayani.
Ina son nasan wanene Mozur jarumin da yaci gasar kokawa a yau."
Azmandu ya ɗago kai ya dubi Zalisha yace,
"Ya shugaba ta Mozur ba kowa bane face bawanku wanda ke aikin niƙan hatsin gidan nan.
Kiyi sani cewa yau watansa tara cif a cikin ɗakin hatsi bai taɓa fita ba sai yau tun daga ranar da aka kawo shi daga birnin Shauƙib sa'adda aka siyo shi a matsayin sa na bawa."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zalisha da Laslaiya, saboda daɗewar Mozur a cikin gidan sarautar tasu amma ko sau ɗaya basu taɓa ganin sa ba.
Zalisha tace,"yanzu yana ina?"
"Yana cikin ɗakin aikinsa."Azmandu ya amsa.
Koda jin haka sai Zalisha ta miƙe tsaye.Sannan ta kamo hannun Laslaiya ta tashe ta tsaye,kuma ta dubi Azmandu tace,
"Na umarce ka da ka kaimu wajen Mozur yanzu-yanzu."
Cikin biyayya Azmandu yace,"an gama ya shugaba ta."

*********************************

Nan take Azmandu ya wuce gaba Zalisha da Laslaiya suka bishi a baya suka yi ta tafiya cikin gidan sarautar suna ratsawa ta saƙo-saƙo,lungu-lungu.
Sai da suka yi 'yar tafiya mai tsawo.
Sannan suka iso gidan da bawa Mozur ke ciki.
Ko ina ka duba dakaru ne a tsaitsaye riƙe da makamai suna kula da ma'aikata.Kuma sai mutum ya wuce ƙofofi goma sha biyu.
Sannan zai isa ƙaton ɗakin da bawa Mozur ke ciki.
A bakin kowace ƙofa dakarun tsaro ne a tsaitsaye guda goma sha biyu.
Duk ƙofar da aka zo sai Azmandu ya ƙwanƙwasa yayi magana.
Sannan za'a leƙo ta wata 'yar ƙaramar taga a tabbatar da cewa shine ɗin sannan a buɗe.
Duk inda suka shiga aka ga Zalisha da Laslaiya sai ayi mamakin zuwan su kuma ai yi ta gaishe su cikin girmamawa.
Ba wani abu ne yasa ake mamakin ganin su a wannan waje domin tun da aka gina wajen tsawon shekaru arba'in baya ba su taɓa kawo ziyara ba sai yau.
Shi kansa sarki Amzadu bai taɓa shigowa wajen ba.
Mozur na kishingiɗe yana tsakiyar tunanin gimbiya Laslaiya sai yaji an buɗe ƙofa an shigo.
A firgice ya ɗago kai ya dubi bakin ƙofar, domin a saninsa kullum sau ɗaya tak ake buɗe ƙofar a miƙo masa abinci kuma saida yamma gefen magriba ba kamar yanzu ba da hantsi.
Kwatsam,sai ga gimbiya Laslaiya,Zulaisha da sarkin gida Azmandu sun shigo.
Ba tare da ɓata lokaci ba Azmandu ya gabatar da Zalisha a wajen Mozur.
Sannan yace,
"Wannan kuwa gimbiya Laslaiya ce wadda na san ka ganta a yau wajen gasar kokawa."
Mozur ya risina ya kwashi gaisuwa a gare su.
Zalisha ta ƙarewa Mozur kallo sai ta ji ya kwanta mata a zuciya.Cikin murmushi ta dube shi tace,
"Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa na rako 'ya ta ne Laslaiya domin ta gana da kai,don haka yanzu zamu baku dama ku zanta."
Tana gama faɗin haka ta juya ta yiwa Azmandu inkiyar su fita.
Bada gardama ba Azmandu ya wuce gaba ta bi bayansa.
Sai da suka je bakin ƙofar ɗakin.
Sannan Zalisha ta waigo tace da Laslaiya,
"Karki daɗe sosai, domin mahaifin ki zai iya neman ki."
Laslaiya tayi murmushi tace,"ba zan daɗe ba."
Bayan fitar Zalisha da Azmandu sai Laslaiya da Mozur suka dubi juna suna murmushi aka rasa wanda zai ce ƙala har kunya ta kama Laslaiya ta kau da kai ga barin kallon sa.
Sannan tace,
"Daman can kai ɗan kokawa ne?"
Mozur yace,"A'a,amma na taɓa shiga gasar kokawa sau ɗaya sa'adda nake can birnin Shauƙib a daular Larabawa."
"Ina ne asalin garin ku?"
Laslaiya ta sake tambaya.
Mozur yace,
"A gaskiya ban sani ba,ni dai kawai na taso na tsinci kaina a birnin Shauƙib a hannun wani attajiri wai shi Abulkhairi.
A lokacin ban fi shekara bakwai ba,tun a sannan nake yi masa aikin bauta.
Wata rana sai sarki Miƙdad ya kawo masa ziyarar bazato koda ya ganni sai yaji yana sona don haka sai ya siye ni da tsada,kimanin dirhami dubu ɗari uku ya tafi da ni gidansa.
Daga wannan rana ya cigaba da kula da ni ya zamana kullum ni ke kula da turakarsa na shareta na tsaftace ta har dai ya aminta dani nake dafa masa shayi.
Kai har ta kai cewa abinci ma ni ke dafa masa kuma ni kaɗai ne zan ba shi abu yaci ko ya sha.
Hatta matarsa gimbiya Suhaila bai sakar mata al'amuran sa ba kamar yadda ya sakar mini.
Sai da ta kai ta kawo cewa babu wani sirri na sa da ban sani ba.
Wannan shine iyakar labarin asali na wanda zan iya baki."
Laslaiya tace,
"To yaya aka yi kuma aka siyo ka a matsayin bawa har aka kawo ka wannan nahiyar tamu ta baƙaƙen fata alhalin tafiya ce mai tsawo?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace,
"Ya shugabata kiyi sani cewa amsar wannan tambaya taki daidai yake da na baki gaba ɗayan tarihin rayuwa ta.
Idan kuwa nace zan baki wannan labari sai mu kwana anan ban gama ba."
Laslaiya tayi murmushi tace,
"Ai kuwa ko ba yau ba sai naji wannan labari daga bakin ka.
Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa a iya rayuwa ta ban taɓa ganin mutumin dana ji ya burgeni ba face kai.
Ka sani cewa tun rabuwa ta da kai ɗazu a filin gasa na kasa samun sukuni, domin zuciya ta ta cika maƙil da begen ka,idanu na kuwa suka cika maƙil da hawayen rashin ganin ka.
Gaba jikina ya kama karkarwa saboda rashin jinka a kusa.
Ina mai sanar da kai cewa a halin yanzu ina ji a cikin raina cewa ba zan iya yin rayuwa ba muddin babu kai.
Lallai kaine zaka zamo abokin rayuwa ta.
Shin zaka iya gaya mini yadda kake ji a zuciyar ka dangane da ni?"
Yayin da gimbiya Laslaiya tazo nan a zancenta sai mamaki ya ƙara turnuƙe jarumi Mozur kuma hankalin sa ya dugunzuma domin ya san cewa Laslaiya ta naɗa gammo don ɗaukar dutsen da yafi kowane dutse girma a duniya,haka kuma tana shirin jefa rayuwar sa ne a cikin bala'in da bai taɓa shiga ba,don sai ya gwammace mutuwa da rayuwar sa.
Cikin alamun karayar zuciya Mozur ya dubi gimbiya Laslaiya yace,
"Yake wannan 'yar sarki kiyi sani cewa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa,don haka tafi ƙarfin taɓawar yaro.
Ina bawa ina 'yar sarki?
Haƙiƙa nima na kasance a cikin irin halin da kika tsinci kanki na yawan tunani da bege to amma fa dole ne mu haƙura da juna in ba haka ba kuwa zamu jefa kanmu cikin rayuwar ƙunci,wataƙila ma ta zama sanadin nadama ga ɗaya daga cikin mu."
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa gimbiya Laslaiya tace,
"Ya kai Mozur kayi sani cewa in dai a kanka ne ba zan taɓa yin nadama ba koda kuwa zan rasa rayuwa ta.
Kayi sani cewa daga yau na ɗaura ɗamarar yaƙi da duk wanda ke son rabani da kai.
Idan har kana sona da gaskiya kaima ka ɗora taka ɗamarar.
Na barka lafiya sai nazo ganin ka a karo na biyu."
Laslaiya na gama faɗin haka ta juya ta fita ta bar Mozur a tsaye ƙiƙam kawai sai ya bita da kallo cikin tsananin damuwa zuciyarsa cike da fargaba.
****************************

Sa'adda Zalisha da Laslaiya suka koma gida suna shiga cikin turakar Laslaiya suka tsaya cak a razane sakamakon ganin sarki Amzadu zaune a bisa gado ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan ɗaya fuskarsa a murtuke babu alamar annuri.
Zalisha da Laslaiya suka yi ƙerere ido ya raina fata.
Sarki Amzadu ya dubi Zalisha yace,
"Amma dai kin bani kunya.
Ban taɓa zaton cewa tunani da hankalin uwa zai zo ɗaya dana 'ya ba.
Ya kamata ace kin fita basira da hango abin da ita ba zata iya hangowa ba.
Ya za'a yi ace a matsayina na sarki mai daraja da ɗaukaka 'ya ta tace tana son bawa.
Bawan ma baƙo,kuma maƙasƙanci mai aikin niƙan abincin mu.
Haba!!
Haba 'yata ki tuna cewa 'ya'yan sarakai kyawawa sun zo sun biɗi auren ki,amma duk kin ƙi su.
Saboda son da nake miki ne na ƙyale ki da zaɓin zuciyarki kuma yanzu saiki rasa wanda zaki zaɓa sai maƙasƙancin bawa.
Na rantse da darajar abin bauta babbar wuta saina datse wannan soyayya dake tsakaninki da bawa Mozur ta kowanne hali."
Koda sarki Amzadu yazo nan a zancen sa sai gimbiya Laslaiya ta fashe da kuka.
Ita kuwa Zalisha sai ta matsa gabansa cikin ɓacin rai ta dube shi tace,
"Ya kai mijina yanzu kenan ka zaɓi kare martabar Mulkin ka fiye da farin cikin 'yarka guda ɗaya kacal a duniya?"
Cikin fushi Amzadu ya miƙe tsaye yace,
"Ƙwarai kuwa,daga yau ku sani cewa ina kishin daraja da darajar mulkina fiye da yadda nake kishin ku."
Yana gama faɗin haka ya nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Har yasa ƙafarsa ɗaya waje sai ya waigo ya dubi Laslaiya yace,
"Zan sa kyawawan matakan tsaro akan ki don kada kije inda Mozur yake idan kuwa kika matsa har kuka sadu saina kashe shi."
Amzadu ya juya ya fice daga ɗakin.
Yana fita Laslaiya ta ruga ga Zalisha ta rungume ta tana kuka,ita kuma ta shiga rarrashin ta.
A wannan rana dai yadda Laslaiya taga rana haka taga dare, domin kwana tayi tana kuka.
Sai da ya zamana kullum bata da aikin yi face zama da tunanin jarumi Mozur.
Abinci kuwa sai Zalisha tayi matuƙar takura mata sannan take cin ƙanƙani.
Koda ta sami kwana bakwai a cikin wannan hali sai ta rame ta fita hayyacin ta.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Zalisha kenan ta kirawo sarki Amzadu don yaga halin da Laslaiya ta shiga.
Yayin da sarki Amzadu yaga yadda Laslaiya ta zamo wato a rame,kuma a firgice.
Sai ya ƙyaƙyale da dariya.
Sannan ya dubi Laslaiya yace,
"Yake 'yata kiyi sani cewa ko zaki zamo ƙwarangol ba zan amince kiyi soyayya da bawa Mozur ba bare har kuyi aure."
Sa'adda Laslaiya taji wannan batu sai tayi murmushi tace,
"Ya kai Abba na kayi sani cewa bana fatan ka tausaya mini bisa duk irin halin da zan shiga,amma ina da burin ka sanya ni cikin kabarina da hannun ka idan ciwon son Mozur ya zamo ajali na."
Koda jin wannan batu sai sarki Amzadu yayi shiru ya kasa cewa komai.
Cikin sanyin jiki ya nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Zalisha ta ruga da gudu ta sha gabansa tana mai fashewa da kuka tace,
"Ya kai mijina kayi tunani mai kyau bisa wannan al'amari.
Ya kamata ka hanzarta ceto rayuwar wannan 'ya tamu guda ɗaya kacal a duniya tun gabanin lokacin nadama bai zo ba."
Maimakon sarki Amzadu yace wani abu sai ya hankaɗe Zalisha ta faɗi ƙasa.
Nan yasa ƙafa ya shallake ta ya tafi abinsa.
Zalisha da Laslaiya suka ƙara fashewa da kuka a tare lokaci ɗaya.
Daga wannan rana al'amura suka ƙara dagulewa har ta kai cewa Laslaiya ta kwanta cuta aka yi ta magani amma a banza.
Shi kuwa sarki Amzadu wannan al'amari na ta nuƙurƙusar zuciyarsa amma ya rasa hanyar da zaibi ya magance matsalar domin ko zai mutu ba zai iya bari Laslaiya ta auri bawa Mozur ba.
Al'amarin jarumi Mozur kuwa shima duk ya rame ya ƙara baƙi,kuma ya tara gashi a fuskar sa saboda baƙin cikin rashin ganin Laslaiya da kuma yawan tunanin ta.
A koda yaushe a cikin tunaninta yake dare da rana koda kuwa yana kan aiki ne.
Sau tari sai ayi tayi masa magana amma baya jin mai maganar face an taɓa jikinsa saboda tsananin tunani.
Duk wanda ya dubi jarumi Mozur a wannan lokaci dole ne yaji tausayinsa.
Babu abinda yake ƙara ɗaga masa hankali face jin labarin irin halin da gimbiya Laslaiya ke ciki na rashin lafiya duk saboda shi.
Ba wani ne ke kawo masa wannan labari ba face Zalisha da kanta.
Bisa wannan dalili ne Mozur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya gudu daga cikin wannan gida inda aka tsare shi,amma sai yaga cewa babu dama domin akwai cikakken tsaro.
Babu yadda za'a yi ya wuce ta ƙofofin nan guda goma sha biyu waɗanda ke ɗauke da zaratan dakaru sha bibbiyu dukkanin su na riƙe da muggan makamai.
Haka dai Mozur ya cigaba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login