Showing 9001 words to 12000 words out of 54616 words

Chapter 4 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt

Advertisement

watsar shiyasa ba ruwanta da wata qawar boarding haka kuma tasha ji wai malamansu na neman wasu d'aliban shiyasa ba ruwanta da shiga harkan ko wani teacher.


To Allah dai ubangiji ya kiyaye ya tsare mana zuri'an mu amin.




Mimi queen .
2022-09-18, 6:45 a.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


13&14.


Kaman da wasa su Mansu suka fara exam yanzu gashi har sun qare weac exam dinsu suna jiran fara neco, yayinda da yawansu suka koma gida Mansu kam da Nadiya suna school din domin karatu.




Bangaren Aryan kam yanzu kam sakewanshi yake yayi abinda yakeso ganin ba wacce ya tsani gani ko ra'banta a gidan.






Lokaci bayan lokaci sukanyi waya da Mansu ta wayan aunty Ayna'u.




Kaman wasa har mun shiga watan July wanda a a watanne su Mansu suka fara zana jarabawansu na Neco wanda basuyi wasaba daga ita har Nadiya dan kar suba iyayensu kunya.




*******
Yau ne suka qare exam, mutane se murna sukeyi anayiwa juna sighing a uniform da marker, Mansu kam da yike a gajiye take yau domin ta tara bacci da yawa a idonta kwana biyu kai tsaye room dinsu ta wuce danta huta dan gobane za'ayi musu graduation gaba dayansu.


..............
Washe gari tun 10 aka fara program, sosai Mansu tayi kyau dukka mate dinsu sun saka uniform dinsu a sama sun daura graduation gown da cap sunyi kyau matuqa especially ma Mansu ba karamin kyau tayiba,


Tun 12 se kallon gate takeyi tana kallon agogo domin guest har sun fara zuwa bataga su Ayya ba,


Sosai ake programs kun dai san boarding school base na fad'aba,


Nadiya ne ta taho tana fadin. "Senior gurl kizo ana nemanki....."


huci ta saki a sanyaye ta juya, daidai lokacin aka bude gate da sauri ta juya, farin ciki tafara ganin motocin gidan sune guda biyar har suka karisa suka parking gurin da aka tanada dan paka motoci,
Da gudu ta ruga sedai bata karisaba ta tsaya ganin Aryan ya fito a mota na biyu fuskan nan a murtuke, gefenshi aka bude Farhan ne hakan yasata karisawa da gudu gunshi. "Ya Farhan..... "


Angel ne da mommy suka fito a mota na uku se Ayya da daddy a mota na hudu na daya dana biyar kuma body guard ne,


Karisawa tayi da gudu ta rungume Angel bakinta yaqi rufuwa tana fadin. "Aunty Angle yaushe kika dawo I really missed you...... "


Kankameta Angle tayi. "See my sis u look gorgeous....."
Murmushi tayi ta karisa da gudu ta rungume mommy tana fadin. "I missed you more mommyna......"


ta karishe da shagwaba kaman zatai kuka, shafa kanta mommy tayi. "Is okey baby gurl bagamu munzo ba...."


Daddyne yace. "Oya let go in anayi bamu.... "
Murmushi sukai suka nufi ciki yayinda Mansu ta lafe jikin Mommy, Aryan haushi duk ya isheshi daddy ya takura mishi yazo dole tsaki yaja ganin sunyi gaba yasa ya juya da sauri ze shiga mota ya gudu.


Daddy daya dawo bawa bodyguard umarni su shiga da kayan da sukazo dasu a boot da sauri yace. "Dikko ina zaka....? "


Juyawa yayi yana qasa da kai, hararanshi daddy yayi. "Allahsa in nemeka in rasa u will know...."


Ya karisa ya basu umarnin, ya dawo tareda nunawa Aryan hanya. "Oya let go....."


Ba musu suka jera shida daddy, wanda suna shiga aka tarbi daddy hannu bibbiyu dan yana cikin manyan baqi, dan kujeranshi na kusa dana gwamnan kaduna,


Rungume juna sukai da gwamna sukai musabaha sannan daddy ya zauna, yana kallon iyalanshi da suke kujerun gaba.




Daidai lokacin aka kira Mansu a best student a school din wacce za'a sata a history ana nemanta a sama, gwamna ze mata kyauta.




Kara lafewa tayi jikin mommy, Angle ne tace. "Oya sis go jor....."
Kaman zatai kuka a sanyaye ta tashi ido kowa ya bita dashi yayinda camerori keta haskata wasu suna yaba kyau da tsari irin na Mansu yayinda wasu kejin ta burgesu hatta class mate dinta da burgewa suke kallonta, karisawa tayi inda gwamna ya miqa kyautan laptop daga school daganan yamata nashi kyautan na kudi masu d'inbin yawa, nan manyanmu suka dinga mata kyautuka,


Kasa ko motsi tayi ji tayi qafanta ya mata nauyi jin ana cewa anason aji wani abu daga bakinta.


Aryan dake can gefe tsaye yana danna waya, se lokacin ya d'ago kai tunda yazo gurin, murmushi me ciwo yayi yaja dogon tsaki.. "Mtssswwwww banzan makaranta sun rasa wanda zasuba best student se wannan mahaukaciyar yarinyar, aladun malamai kawai mtsswww....." ya kara jan tsaki,




(Nidai nace oho kodai jealous kakeyi lol 😂 .....)




A hankali ta amshi maik din hannunta na rawa, du'kunnar da kai tayi tayi shiru, duka kowa ido ya zuba mata, kafin a sanyaye ta d'ago da kai jikinta na rawa ga mutane fiyeda dubu kowa idanshi a kanta ga camerori na dauka tako ina,


"Am............" rawa muryanta ya fara, kafin da karfi ta fashe da kuka.


"I can't describe pleasureful am today, I will use dis opportunity to tnxs some peoples dat soo nice to my life..... "


Shiru tayi kafin taci gaba. "My guardians banda kamanku, daddy am so haply tobe with you tanks for d caring and loves u're such a sweet kind hearted loving husband and father dads u care for me more than ur children I Luv you more daddy Allah saka da alkhairy ,
Mommy u're my human angle I don't even know my real mother but u spurn me more, ure my best teacher, my comforter,
Secondly My fight partner my love my heart my Ya Farhan I Luv him more than I can do, ya girmenifa sosai but we always be fight , shout, but all dis he's my best friend he like my cartoon movie, my annoying not so annoying, sweet cutest, you've contributed alot da I can't go without shouting out to you, mad Luv bro, mad Luv am proud of you am so emotional I love yhu okey......."


Kuka ta fashe dashi sosai, jikinsu mommy yayi bala'in sanyi wani irin mugun santa da tausayinta na dad'a shigansu,


Dagowa tayi tana duban student da class mate dinsu fuskanta jage jage da hawaye. "You guys, own my heart tanks for believing in me, understanding me and always standing by my side my matured gang, my sabi womens, ni mutum ce one way or another I know during the moment I've hurt, fought someone please ayafemin duk wanda na 'batawa rai Allah barmin kuuuu........... "


Kuka ne yaci karfinta ta durkushe a gurin tana kuka sosai, share hawaye Angle tayi ta tashi da kyar taje ta taho da Mansu jikin mommy ta fad'a ta saki kuka me karfi Aryan kam yacika yayi fam se tsaki yakeyi, jikin kowa yayi sanyi a haka aka karisa graduation din, zuwa 3 an gama nan aka fara tafiya yayinda wasu keta kuka,


(Allah sarki haka school yake mutum ya qosa a gama da an gama kuka afara missing Allah sarki barinma boarding schools hummm only wanda yayi boarding school can relate)




Bangaren Mansu ma kam taci kuka ba kad'anba na rabuwa da wasu daga mate dinta da teachers yayinda kowa ke jimamin rabuwa da Mansu dan wasu teachers din da suka saba irinsu aunty Ayna'u har kuka sukayi, nan Mansu sukayi exchanging contact suka nufi gida bayan daddy ya cika school din da kyautuka,


Mansu da Nadiya sunci kuka, koda suka isa gida zazza'bi me zafi ne ya rufe Mansu hakan yasa mommy ta bata magani, amma sam taqicin abinci se kuka take,
Da kyar suka samu taci ta kwanta.






A gidan Ayya ta tafi ta barta dan daddy yace a barta.




*****
Kwanan Mansu biyu a gidan dan taji dad'in dawowan aunty Angle wanda ta qare karatunta duka har an mata baiko 6month zatai aure a abuja wani babban barrister zata aura, Mansu se farin ciki takeyi.






..........
Yau ne Mansu zata koma gidan Ayya dan yau kwananta uku Ayya ta dameta da kira akan ta dawo.




Zaune suke itada Angle a falo suna kallon game of thrones, daddy ne ya shigo dukkansu suka zube suna gaidashi cikin qosawa yace. "Mansu maza kiramin dikko kice ina jiranshi yanzun nan a ash palo... "


A sanyaye ta tashi ta nufi room dinshi, knocking tayi jin shiru yasata ta sakai ciki bin falon tayi da kallo bakowa a ciki hakan yasa ta nufi bedroom din,


Ta murd'a handle tayi ta sakai ciki batareda tayi sallamaba, yana kwance ruf da ciki sanye da boxer na Kelvin ba shirt a jikinshi, yana kallon American film a system din dake kan gadon,


Kara kallon screen din system din tayi inda matan dake film din suke kwatan kwacin tsarara kundai san American film basena fad'aba gawasu na rungume rungume, kauda kai tayi a ranta tana cewa Allah kyauta kafin a fili tace. "Daddy na kira yace kazo yanzu yana ash falo.... "


da sauri ya d'ago danshi bemaji shigowanta ba hankalinshi nakan kallon da yakeyi da karfi yace. "Uban wayace ki shigomin daki..... "
Batareda ta bashi amsaba tayi gaba, jinjina kai yayi ya tashi ya saka Nike sport wear ya fice dan zuwa amsa kiran daddy,


Tana zaune itada Angle tana hango shigowanshi ta fara cewa. "Wallahi aunty Angle ina fad'a miki yanzu mutane sun maida kallon tsaraici ba'a komaiba kowama kallo yake da me aji da mara aji kuma ba abu bane me kyau koda se mahaukatane da basusan me sukeba suke kallo Allah dai ya baku natsuwa.... "
Yana jinta harya kariso, angel ne tace. "Ke kuma dawa Mansu.... "
Murmushi tayi tana kallon Aryan. "It's just a request nd hope it considered......"


Huci ya saki a hankali dole yaci uban yarinyar nan rainin yayi yawa, gaba yayi ya barta.




Sun jima sannan ya fito lokacin Mansu ce kadai yazo wucewa setinta ta saki dogon tsaki taci gaba da kallon TV dinta,


Around 4 bala driver yazo daukanta lokacin Angle ta tafi saloon Farhan bayanan, sosai mommy ta hada mata kayayyaki masu yawa kwalliya tayi sosai cikin atamparta tayi rolling da chiffon veil ta feshe jikinta da twilly perfume,


Ta fito kenan zata nufi inda bala yai parking din mota, se gani tayi mutum yasha gabanta kallo d'aya ta mishi ta matsa gefe zata wuce hannunta ya damqo da karfi kaman ze 'ballata har seda tayi yar quwa, idanunshi sunyi jajawur saboda tsananin tsana, idanshi ya saka cikin nata cikin kakkausar murya yace. "Get the fuck outta my heat, get the fuck out of my heart, get the fuck out of my thought kinajina, stay with in ur limit I am very very dangerous and poisonous kinaji......? "


Ya daka mata tsawa amma abun mamaki ko gezau Mansu batayiba idanta na cikin nashi ba alaman tsoro ko kadan, sema wani murmushin izgilanci da tayi.


"You are too smart, actually I thought something was wrong with you cos u seems off, u deserve to be examine and admitted in the asylum ka! the dumose head don lose notice fa........... "


Bata rufe bakiba taji ya zuba mata wasu marika guda uku da seda kanta ya juya jin ta kirashi da mahaukaciya.
Yana huci yace. "Ke ni zaki cewa I need to be examine in asylum to bari in miki dukan tsiya se a kaini gidan mahaukatan da gayya..... "


Hannu yasa yafara zare belt ganin da gaske yake yasata cewa. "Eh din naji but am so done with you like...... "


da gudu tayi cikin gidan ya bita,


Bayan mommy dake kitchen ta boye tana fadin. "Mommy u see dis mugu want to bite me ko..... "


Mommy ganin Aryan ya taho da belt yasata fadin. "A'a meye haka what is dis Aryan meke damunka Mansu zaka daka to zoka daketa tunda kaika haifeta sannu ubanta tunda jaka aka haifan maka..... "


Shiru yayi ya tsaya yanaji zuciyanshi na mishi quna Mansu kadai yakeso yaga yana nad'a ko zeji sanyi, a zuciye ya juya yayi dakinshi cikin zuciya,


Janyota gaba mommy tayi. "Dama baki tafiba. "?
. "shiya tsareni mommy.... "
"okey baby let me ex court u out naga wanda ya isa ya dukanmin baby....."


Seda mommy ta rakata har mota sannan ta koma, se lokacin Mansu takejin zafin marin daya mata, kunci ta riqe tana hawaye. "Allah ya isa mugu azzalumi wallahi bazan wani jira se nanda bayan bikin aunty Angle ba as Nadiya said yau zan fara aikina......"




Suna isa gida, lokacin Ayya na bacci me mata aiki tun safe sukai sallama ta tafi hakan yasa bayan ta natsa kitchen ta shiga mock tail chicken wings ta musu warming,


Wayan Ayya ta dauka ta lalubo numban Aryan inda ta rubuta Dikko, wayanta ta dauka ta kwafe numban tayi saving da ```Maddest``` tana wani irin murmushi da ita kadai tasan na meye se kuma ni me rubutun.


Daidai lokacin ruwan alqalamina ya kare, se gobe Abban zarah zemin refiling......


Taku Mimi queen ✍️.


```Alkalami🖊️yafi takobi```⚔️
2022-09-19, 12:11 a.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


15&16.


Zaune yake a falonshi yana kallon match na Argentina a frence,
Sanye yake cikin marrown hoodie yadi dawowanshi daga hospital kenan yayi bala'in kyau,


Wayan shine dake ijiye kan center table tayi quwa alamun shigowan message,


Da kaman baze duba ba se kuma yajanyo wayan, message akayi mishi da baqon number duba message din yayi inda yaga an rubuta
```"Assalamu alaika```
Shiru yayi kafin a hankali yaja tsaki ya ijiye wayan ko wayema shi baya daukan baqon number ko chat ne bayayi dasu balle message, wa'inda ma yasani din bakowa yake kulawaba a online balle ya dau kiransu,


Ci gaba yayi da kallonshi yana sipping hot coffee a hankali,


Bangaren Mansu kam zaune suke ita da Ayya da aunty Angle fira suke yi sosai,
Aunty angel ne tace. "Wallahi Mansu da bakinan everything looks dull....."


Sallaman Nadiya sukaji da gudu Mansu ta tashi ta fad'a jikin Nadiya, tana fadin. "Oyoyo my zuma rock.... "
Tureta Nadiya tayi tana fadin. "Ni seki 'ballani Mansu kinsan kin fini qiba....."


Karisawa sukayi Nadiya ta gaida Ayya tareda yiwa aunty angle murnan baiko da murnar qare karatu,


Dakin Mansu suka nufa su ukun suka bar Ayya ita kadai a falo,
Suna shiga gadon Angle ta fad'a tana fadin. "Nadee ya Atif.? "


Murmushi tayi. "Tare mukazo aunty Angle shiyana gun Dr Dikko..... "


Daidai lokacin Mansu ta shigo dauke da tray ta kawowa Nadeeya abinci, gyalen dake kanta ta cire ta ijiye gefen bed nan dogon gashinta da aka mata kalaba kanana ya bayyana sai lilo suke, fuskarnan tai fayau idanun sunyi zuru zuru dan shegen kyau, batasa glass a idanuntaba,


Kwanciya tayi ta daura kanta kan cinyan aunty angel tana fadin. "Aunty nayi kewan mummyna sosai. "
Nadiya dake cin sand which tace. "sorry kinji yar Mummy kema ai kwana nawane dazaran miji yafito aure zamuyi miki. " dungure mata kai tayi tana hararan ta


Tace. "Ke komi aure aure, to dan kiji saina zama babbar yar jarida data amsa a duniya sannan zanyi aure. " tabe baki Nadiya tayi tace. "Kya ru'be agida bokoko. " itama tabe baki tayi tace .
"Ru'ba'ben tumatir yafi dadi. " kama baki Nadiya tayi tace. "Laaaa Mansu yar air ce kefa, rotten tomatoe. "


Hararanta tayi zatai magana
Aunty Angle tace. "dalla nidai ku rabu dani da wannan musun naku muyi firan duniya. " hararan Mansu Nadiya tayi tace. "Rotten tomatoe kawai. " dariya kawai Mansu tayi bata karace mata komiba.




Nan suka dingi fira, sunjima sannan Atif yama Nadiya message akan ta fito su tafi, nan tayiwa Ayya sallama ta fito,




Bayan Atif ya tafi still yaga an kara mishi message din sallama ta wannan numban ignoring ya karayi sema tashi da yayi ya shirya dan zuwa sallama da daddy dan gobe ze tafi seminar qasar Russia.






***
Mansu tafi kwana uku tanayiwa Aryan message ko sau d'aya beyi reply ba bata gajiba dan tasan akwai abinda takeso tayi achieving.




Zaune take tana sanye da glass idanunta nakan novel din da take karantawa na the noisy neighbor,


Techno dinta ta janyo tashiga numban mahaukaci kaman yanda yai saving tayi typing ```"Salaam```.
Ta tura mishi, ganin bataga reply ba yasa cikin sigan shagwaba ta rubuta,


```"Please Ya answer me pleaseeeee.....```
taja please d'in


Yana zaune a cikin motanshi driving yakeyi saqon ya shigo, tsaki yaja gaskiya an dameshi be sake kallon wayanba harya isa gida,


Fitowa yayi ya nufi part dinshi lokacin Mansu ta fito tana waya da mommy harara suka sakarwa juna yayi gaba,


Zama yayi akan kujera se lokacin ya karanta saqonta na qarshe
```"Please in bazaka amsaba ka tsaya ka saurareni please ko kadanne"```


Tsaki yaja ganin saqon yayi yawa yasa yayi typing din. ```"who am I speaking with?" ```


Mansu da suke waya da mommy ganin message yasata cewa mommy zata kirata, ganin reply din daga Dikko ne yasata yin wani juyi tareda fadin. "Yes.... "


Da gudu ta koma daki ta fad'a gado kafin ta rubuta. ```"One of ur fans..... "``` ta tura


Huci ya saki ganin reply dinta ya rubuta
```"One of my fanss! Oh really.? "```


Ya tura kafin yasake rubuta. ```"Who give you my number? "```


Murmushi tasaki kafin ta rubuta.
```"Goggle```


Murmushin izgili yayi kafin ya tura mata ```". Oh goggle fa to me kikeso..?```


```". I want to be ur friends```


Tsaki yaja kafin ya rubuta
```. "Now a days they are some about the kidnapping so I will not trust you.....```


Murmushi tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login