Showing 21001 words to 24000 words out of 54616 words

Chapter 8 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt

Advertisement

zauna bata 'boyewa Lubna komaiba seda ta fad'a mata,


Dariya Lubna tayi. "Abun naku gunin ban sha'awa kaman a Novel kinsan yawanci da fad'a ake farawa...".
Duka Mansu ta d'akawa Lubna cikin wasa Lubna tace. "Wannan alwashi haka ammafa Nadee tayi gaskiya daga baya fa reshe ze iya juyewa da mujiya....."


Hararan Lubna tayi. Kafin Lubna tace. "Qila shiyasa ma baki kula kowa har Ya Muhammad saboda kinada Secret Love dinki a 'boye......"


Pillow Mansu ta d'auka tayi kan Lubna wanda da gudu Lubna tayi ciki tana dariya, Mansu ta bita da gudu itama....




*****
Sosai Aryan ya shiga damuwa domin tun randa yama Mansu message din yana santa bata qara daukan wayan shiba yau kwana biyu kenan, kuma koya mata message ba reply duk ya shiga damuwa domin ba kad'an yakejin san Jewel a ranshi ba, Atif kam se shawara yake bashi.




Sunata shirya shiryen komawa kaduna harda Ammy da Lubna domin jibi flight dinsu ze tashi.


Anyiwa Aunty Angle lallen maiduguri me kyau da gyaran kai haka Mansu da Lubna qannin Amarya sosai suke sheqi abunku da fararen fata.




Yanzu sam bata daukan kiran Aryan hakanan takeso taja mishi aji.




""""
Gobane tafiyansu Kaduna yau sunje sunyi sallama da en uwa sunyi siyayya sunsha yawo sosai suka gaji,


Bayan magrib.


Wayan Mansu ne tayi quwa, ganin twinkle yasa Lubna da sauri tayi picking,


Mansu data fito daga bayi d'aure da towel iya cinya da sauri tace. "Wayace ki daukan min waya....? "


Da sauri Lubna ta katse wayan, tana fadin. "Yi hakuri Aunty...."


Cikin shigan lallashi Mansu tace. "Dan Allah Lubna in mukaje kaduna karki wani abu dazesa Aryan ya gane kece Lubna ko kiyi abinda zesa ya gane nice Jewel please dat's our secret...."


Cikin zolaya Lubna tace. "Ok Maa...."


Daidai lokacin kiran Aryan ya sake shigowa....


Tsaki Mansu tayi. "Miqomin wayan ya zanyi tunda kin riga kin dauka...."
Miqa mata wayan tayi tana fadin. "Yarinya er gidan miskili man kina wuta ina binki da fetir..."


Bata kula iskancin Lubna ba picking tayi tareda kai wayan kunninta,. "Helloooooo....."
Ta furta a sanyaye.


. "Hummmm....Uhmmm...Jewel have I done something wrong please tell me with inaji kaman nayi kuka...."


Cikin shagwaba tace. "Bakomai fa..."


".Jewel ko dan nace inasanki ne shine kike jin haushina....? "


Girgiza kai tayi. "Uhmmm...uhmmm..."


. "To ko baki sona ne Jewel shiyasa kikeso ki yanke alaqa dani...? "


Qara girgiza kai tayi. "Uhmmm...Uhmmm.."


Huci ya saki a marairaice yace. "To meye laifina please Jewel tell me, wat my fault dan nace inasanki tell me pleaseeee......? "


. "Twinkle...."
Ta kira sunanshi.


Bud'e idanuwanshi yayi tar ya saukesu kan qofar office dinshi.
. "Na'am...."


". Twinkle nima inasanka sosai sedai abu d'aya nake tsoro....."


Da sauri yace. "What jewel tell me mekike tsoro...? "


"Twinkle inajin tsoro kada kaganni kace ban makaba baka sona ba irina kake soba....."


Katseta yayi da sauri. "Jewel inasanki inasanki sosai zan iya rayuwa dake duk yanda kike, zan rayu dake a ko wani hali kike jewel...."


Murmushi tayi. "Kace zaka soni a yanda nike kuma ko wacece ni zaka soni....? "


Da karfi kaman wani wanda wutar santa ke cinshi yace. "Yes jewel I said it and I will always said it, inasanki a duk yanda kike kuma ko wacece ke zan rayu dake koda ko ace ke makauniyace to kam zan kasance dan jagora a gareki, idan kuma ke gurguwace to nizan dinga d'aukanki inmiki duk abinda kikeso, domin inasanki kuma na aminta dake ke kadaice 'ya macen da nake so kuma na kejin zan iya rayuwa dake fatana d'aya ki bayyana kanki a gareni nikuma a ranan zan tura magabatana gidanku a daura mana aure, burina be wuce ki zama tawa har abada ba jewel please inaso naganki I want u too be mine forever....."


Murmushi tayi. "Allah sarki Twinkle dina, niba gurguwa bace kuma niba makauniya bace inada lafiyana sannan zamu hadu very soon insha Allah zan bayyana maka kaina, nima inasanka sosai my Twinkle...."


Huci ya saki. "To when nifa na kosa please ki fad'amin...."


Murmushi tayi. "Ai zanzo bikin Angle dinku, find me inkuma ka kasa shikenan se sanda naga dama zamu had'u...."


Cizan lips din kasa yayi. "To shikenan ni kuma zanyi trying insha Allah....."


. "Twinkle lemme need my self...."
Huci ya saki. "Am not tired of hearing ur voice Jewel amma shikenan zan kiraki kafin kiyi bacci...."


. "Okey...." ta furta kafin ta cire wayan a kunninta.


Dariya Lubna tayi da takejin su tun d'azu. "Lovers....."


Mugun harara Mansu ta watsa mata.








Wani irin farin ciki Aryan yake ciki, ji yakeyi yafi kowa murna a duniya yanzu, dama haka akeji in ana soyayya.




Around 10 ya gama komai, da wuri ya shiga d'aki dan yayi waya da Mansu sedai ya kirata sosai bata d'auka ba dan tayi bacci tun 9 dan tayi mugun gajiya kuma gobe akwai hawa flight, hakan yasa ya mata messages......








Yau ne zasu juya kaduna tana tashi taci karo da message din Aryan.


"```Only my jewel I call no answer nasan kuma u want be happy 4 not hearing my voice, me too naji bacci but anyway we will talk, 2 day is chocolate dream bye and smile my jewel...."```




Murmushi tayi, kafin tamai reply....


"```And morning my Twinkle my one nd only cute, please hove u r fyn nd continue be fyn, missed ur call means I missed night happiness, nd I will continue be missing u, till d time u see my Message and call.
Nayi bacci da wuri nasa phone dina a silent dat why srry. "```




Lokacin yana shirin fita zuwa asibiti, be mata any message ko call ba, se bayan yagama duba patient.


Sukuma lokacin suna cikin mota zuwa airport, taga message dinshi.


"```I miss you like am crazzy, inasanki sosai fiyeda tunanin me tunanin and I need u to feel my love in your soul...."```


Reply ta mishi. "```I swear I feel it deep inside of me....I lose my control...."```


Kiranta yayi amma batayi picking ba, domin lokacin suka isa airport.




Basu jimaba flight dinsu ya d'aga zuwa Kaduna.....




Mimi queen ✍️.
2022-10-02, 10:04 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.




29&30.




Jirgin su Mansu na sauka lokacin motocin su Farhan, ya iso airport din burin shi d'aya yayi ido hudu da Mansun shi.


Suna fitowa daga jirgi, Angel ne ta hango Farhan da Mommy da sauri tace. "Gasu mommy....."


Da gudu Mansu tayi gaba tana karisawa ta fad'a jikin mommy tareda sakin kuka....."I missed you more mommyna....."
Qanqameta mommy tayi dan itama tayi kewan daughter dinta sosai, jikin Farhan Angle ta fad'a ta rungumeshi sosai


Janye Mansu mommy tayi tana fadin. "Is OK baby gurl...."


Karisawa tayi suka rungume juna da Ammy cikin farin ciki, nunawa Mansu tayi kaman bataga Farhan ba shima ko seya basar.....


Riqo Lubna mommy tayi suka nufi motoci.


Mommy da Ammy mota daya suka hau se Angle da Farhan, se d'ayan motan Mansu da Lubna, ahaka suka nufi gida........




Bayan sunyi parking kowa ya fito se lokacin Mansu tadubi Farhan cikin mamaki. "La Ya Farhan dama dakai akaje airport.....? "


Lubna ce tace. "Dama ke baki ganshiba se yanzu...? "


D'aga kai tayi. "Eh idona ya rufe da shauqin san ganin mommyna ita kadai na gani....."


Ta'be baki yayi yayi gaba, da gudu tabi bayanshi.... "Brother tsaya ka rungumeni nayi kewanka sosai....."


Be kulata ba yayi gaba, dansu mommy sunyi ciki abinsu.....


Yana gama shiga falon ta janyo hannunshi baya. "Ya Farhan ko kewata bakayiba ko....? "


Kwafa yayi. "Meyasa zanyi kewanki ni dama baki dawoba kinyi zamanki acan kawai, ki samu wani Old man ki aura kawai mu huta..."


Baya taja da sauri tareda dafe kirji cikin muryan kuka tace. "Ya Farhan ni kake cewa dama nayi zamana acan, kasan irin kewanka da nayi kuwa har Doll na siyo maka kullum senayi magananka koba hakaba Lubna....? "


Lubna dake dariya ta d'aga kai cikin dariya....


Kafin Mansu taci gaba. "Amma shine zakace in samu wani tsoho in aura kenan ka fasa aurena ko....? "
Ta had'a kai da bango ta fara kukan qarya.


Kai ya dafe dan ya gaji da shirmen Mansu hakan yasa, ya fincikota..... "Oya hug me baby gurl I really really really missed yhu alot my tiny sister...."


Da sauri ta rungumeshi tana fadin. "Nima nayi kewanka sosai my huge bro...."


Dariya sukaba Lubna sosai dan ita burgeta sukeyi.




Mommy ce ta sauko tana fadin. "Farhan barmin yarana suje su huta su fito suci abinci, Lubna maza jeki huta dena biye musu....."


Ciki Lubna tayi da sauri tana dariya.




Bayan duk sun huta suka fito dinning suka zauna sosai sukaci abinci.


Ana haka daddy ya shigo da gudu Mansu ta tashi ta fad'a jikin daddy....


Rungumeta yayi sosai. "Princess dita kin qara kyau, ruwan maid ya amsheki...."


Sinnar dakai tayi qasa tana murmushi,


Kafin yace. "Anata zuwa neman aurenki sosai princess...."


Da sauri ta d'ago, murmushi yayi. "Nidai nace suyi hakuri ba yanzu zanyiwa babyna aureba akwai lokaci...."


Cikin murna tace. "Yawwa daddyna..."
". Princess ko akwai wanda kikeso ki fad'amin se a had'a ayi tare da Angle...."


Da sauri tace. "Bakowa daddy na."


Murmushi yayi. "Yawwa kada ki kula kowa kinji akwai lokaci yanzu ban shirya miki aureba dan haka karki fara soyayya yanzu kinji ko..."


Cikin jin dadi tace. "To daddyna..."


Murmushi kawai mommy tayi domin duk abinda suke cewa dukkansu sunaji,


Seda daddy ya shige ciki bayan sun gaisa dasu Ammy, sannan Farhan ya dubi mommy. "Yanzu mommy wannan yarinyar ne daddy zece baze mata aure yanzuba kuma kinaji...? "


Cikin tsiwa Mansu tace. "Ya Farhan to meye matsalanka da aurena kai waya matsa maka qato ma dakai...."


Murmushi yayi. "Ai ni kinsan akwai wani qaton a gaba nane shiyasa amma....."


Duka Angle ta d'aka mishi. "Ya akwai mommy da Ammy kar kai rashin kunya...."


Mummy nunawa tayi kaman batasan me suke cewaba sema tashi da tayi ta nufi gurin mijinta, Ammy kam dariya kawai tayi.


. "Eh naji koma meye amma dai nasan Mansu tafara soyayya inba hakaba to ta fad'a mana waye Twinkle....."


Da sauri Mansu ta d'ago cikin mamaki jin abinda Farhan yace, kwalo ya mata.... "Lol...."


Duban Aunty Angel tayi, da sauri Angle tace. "Bani bace....."


Miqewa tayi tareda marairaice wa. "Ya Farhan please waya fadama ko Lubna ce....? "


Da sauri Lubna tace. "Bani bace wallahi. "


A fusace ta dauki qaton plate tayi kan Farhan . "Seka fad'amin waya fadama, ko in buga maka.."


Tashi yayi da gudu yayi ciki ta bishi da gudu.....


Seda ya wahalar da ita sannan yace. "Text message dinshi na gani dazu wai baki picking wayan shiba yanata kewan muryanki....." huci ta saki. "Ya Farhan please banaso ka kuma kiran sunan twinkle a gidan nan please...."
Ta marairaice.


Tsaki yaja. "Munafuka meyasa kika 'boyemin..."


. "Zan fadama komai Yayana amma sekamin alqawari kaji please...."


."Okey nayi fad'amin..."
. "ba yauba...."
Ta fad'a tareda ficewa da gudu, murmushi kawai yayi yabi bayanta.




Ranan kwana sukayi fira su duka barinma yau ga Farhan uban surutu, mommy tacewa Ayya se bayan biki Mansu zata koma, Unin ranan Aryan be leqa gidanba amma sunyi waya da daddare da Jewel.....




******
Yau itada Lubna da Nadiya sukaje suka amso dinkin ankunan su gaba daya kusan kala takwas da mommy ta bada d'inki nasu su ukun, dan yanzu an hana Angle fita.


Tuni Ya barrister ya turo da Invitation card (Sunan da Mansu take kiranshi dashi kenan hakan yasa kowama yake kiranshi da hakan, dan har ita kanta Angle takan kirashi da Ya barrister, amma asalin sunanshi Barrister Fu'ad Nasir...)




Tun a mota suketa faman waya da Twinkle, har suka iso


Driver na ijiye su dukkansu en matan suka fito, gaba Mansu tayi tana wayan tana dariya ta barsu Lubna zasu dauko d'inkunan.


Daidai lokacin da yake tambayanta, yaushe zatazo biki dan an fara zuwa.


Ta bud'e baki zata bashi amsa kenan taji ta bangaje mutum,


Wayan dake kunnin shine ta fad'i kasa, a firgice ta d'ago
Yana sanye da sky blue din hoodie yadi yayi kyau matuqa Mansu bata ta'ba ganin kyanshi irin rananba.....


Wani irin kallon tsana yake jefa mata da sauri a rud'e ta duqa ta dauko wayan nashi tamiqa mishi...


Tsaye yayi yana jefa mata wani mugun kallo, a hankali yasa hannunshi ya zaro sim card dinshi dan tunda Mansu ta ta'ba wayan yaji ya tsani wayan gaba d'aya....


Yana zare sim card din yayi gaba yabar mata wayan a hannunta, jujjuya wayan tayi iPhone 14 ce sabuwar shigowa wayan data tasamma miliyan biyu, wani irin mugun haushin shine ya kamata, fad'in ranshi da jiji dakai d'inshi da nuna isa sunyi yawa,
Hakan yasa tana shiga falo ta ijiye wayan kan center table tayi sama abinta, domin ita kam ba abinda zatayi da tsiyar Aryan.




Ranshi 'bace ya nufi parking lot, daidai lokacin Nadiya ke cewa. "Lubna kiyi sauri kinsan anjima zamuje raba IV...."


Chakkkkkkk......
Aryan ya tsaya jin sunan da Nadiya ta kira wato Lubna, tunani ya farayi,


Ra'bawa su Nadiya sukayi suka wuce ta gefenshi ido ya bishi dasu har suka shige.


Da sauri wata zuciyan tace mishi. "Ina hakan baze yiwuba wannan ba Lubnan Jewel bace, ai suna linzamine, sunan sune iri d'aya..."


Kad'a kai yayi yama motanshi key, ya shiga.




Kasancewan Angle batada wasu qawaye a Nigeria, dan ita karatunta duk a waje tayisu yasa komai Mansu keyi se su Nadiya da Lubna dake tayata, dan Nadiya ma ta dawo gidan se bayan biki zata koma.


Haka Ayya itama ta dawo gidan.


Tuni en uwa daga ko wani 'bangare sun fara zuwa, gida ya cika maqil se bidiri akeyi......




Zaune Mansu take a haraban gidan suna waya da Twinkle se dariya takeyi sosai, Farhan ne ya fito tsaki yaja.


. "Yarinyar nan ta kwance akan Twinkle dinnan..."


Gaba yayi, yana zuwa parking space yaga Aryan tsaye bakin mota se bude qofan motan yakeyi yana rufewa,


Se dariya yakeyi yana wani irin annashuwa da ba koda yaushe kake ganinshi a cikiba dan da alama soyayya yakeyi,


Ta'be baki Farhan yayi..."Shima wannan ya kwance akan wata...."


Da sauri wata zuciyan tace. "Ko tare suke waya....? "


Dafe kirji yayi yana girgiza kai..."Ina it's impossible baze yiwuba..."


Wata zuciyan ne tace. "To ka bincika kagani...."


Cikin sand'a ya karisa ya 'boye bayan wata mota inda yana jiyo muryan, Aryan yana fadin. "Saying I love you can't explain irin kaunar da nake miki, I don't know how to explain but alhamdulillah u can understand more I love yhu more Jewel...."


Riqe baki Farhan yayi. "Yaushe miskilin nan ya fara soyayya haka?..."


Da gudu ya rarrafa ya koma gun Mansu ya la'be a bayan flower yanda ze jiyota.


Murmushi tayi me sauti. "Twinkle kenan naka kadai ka sani ko, bakasan nawaba I love you kaman nayi hauka...."


Cikin mamaki yana tunanin, To meya canza wa'innan dutsunan lokaci daya kowa ya fara soyayya?.


Kowama yayi daidai lokacin, Aryan ke fadin. "Inasanki sosai fiyeda tunanin me tunani and zan cigaba da hakuri zan jira har lokaci yayi in ganki, in rungumeki sosai sannan naita miki waqa, ke kuma kiyita min shagwa'ba and u be calling me ur Twinkle, I love you plenty plenty Jewel...."


Qafan Farhan ne ya fara rawa, kenan dama Aryan ne twinkle?, dama soyayya sukeyi suke raina musu wayau da tsanan karya?.


Ganin bashida amsoshin tambayan yasa ya nufi gun Mansu, tana ganin ya taho tayi sallama da Aryan ta miqe zata shige gida.


Ya fizgota da sauri. "Ke 'yar rainin wayau dama Ya Dikko shine Twinkle....? "


Zaro ido tayi. "Waya fad'ama...? "


Hararanta yayi. "Karki rainamin wayau yanzu naji kuna waya kuma dagaji da juna kukeyi, ki fad'amin komai kona je na fad'a mawa daddy ya muku aure..."


Da sauri ta riqoshi. "Dan Allah Ya Farhan kar kaje zan fadama komai..."


Zama tayi shima ya zauna, nan ta fad'a mishi komai ,ta qara da fad'in..."Kasan u're my best friend to please hide our secret karka fadawa kowa dis is ours...."


Katseta yayi. "Hummm ba wani our secret it's urs, amma dai ki kula karkizo ki fara bacci kina kiran sunanshi...."


Murmushi tayi, shikuma yayi gaba.


Aryan na shirin fita a mota, Farhan yayi saurin katseshi tareda qarisawa.


Dubanshi Dikko yayi. "Meya faru Farhan...? "


Huci yayi. "Bro nazo dazu inama magana naga kana waya baka jiba da alama kafara soyayya ne...."


Wani qasaitaccen murmushi Aryan yayi, hakan yasa Farhan cewa. "Yaya wacece auntyn nawa me sunanta...? "


. "Jewel...."
Ya ba Farhan amsa.
Murmushi yayi. "To Ya yaushe zaka kawo mana ita mu ganta...."


". Very soon Farhan zatazo bikin Angle...."


Farhan na shirin magana ya katseshi. "Farhan kasan banasan tambayoyi jirana ake yi a asibiti..."


Murmushi Farhan yayi
Yace. "A dawo lafiya...."


Horn yayi me gadi ya bude mishi ya fice.


Binshi da ido Farhan yayi yanajin wani irin tausayin yayanshi domin ya kamu da yawa, gaskiya salon daukan fansan da Mansu tabi , yayi matuqar tsauri sosai kuma yasan zata cutar da yayanshi sosai.


Amma yazeyi bakin alqalami ya riga ya bushe dan Aryan ya kamu sosai.




Matar Abdul ce ✍️.
2022-10-06, 4:25 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.




31&32.


Biki nata matsowa sun shirya event kala da kala, tuni qawayen Angle daga kasashe da dama sunzo gida ya cika maqil ba masaka tsinke......




Yau za'a fara event.
Inda za'a fara da Kamu wanda a yarensu na Kanuri suke kiranshi da (wushe_wushe) a 30 request za'ayi Karfe hudu na yamma.


Yau Mansu tana busy amma se faman kiranta Aryan yakeyi,
Gefe ta koma ta d'auki wayan,


Ijiyar zuciya ya sauke.... "Jewel kina wahalar dani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login