Showing 24001 words to 27000 words out of 54616 words
Chapter 9 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt
yawa na hanani sauraran dadd'an muryanki da kikeyi...."
A sanyaye ta sauke ijiyar zuciya. "Kai ana bikin kanwarka amma kai kanata soyayya ko....? "
Ware ido yayi. "Kinaso kice kina gidanmu kinzo biki...? "
Murmushi tayi. "Eh nazo d'azu....."
Cikin farin ciki yace.. "Please ki fito ina garden din gidan mu hadu yanzu am eager, I just want to see u please...."
Huci ta saki. "Ka manta agreement din mune, find me if u can...."
. "hummm Jewel zaki wahalar dani fa...."
Dariya tayi sosai. "Twinkle nazofa ka dubani zaka ganni, anjima za'ayi Wushe_Wushe a 30 request hotel kaje gurin nima zanje kaji....."
. "Hummm Jewel zanje amma saboda ke..."
Daidai lokacin Lubna ta kariso tana fadin. "Kizo Aunty Angle na nemanki... "
Hakan yasata cewa. "Twinkle se mun hadu anjima..."
Dif ta gimtse wayan.
Lubna ce tace. "Anjima zaki bayyana mishi kankine...? "
Murmushi tayi. "A'a zan gara shine seya garu sosai kaman taya..."
Hannu Lubna ta bata suka tafa dukkansu suna dariya, Lubna tace. "Bakida dama wallahi Mansu..."
Nan suka jera zuwa sama.
Karfe hud'u gaba d'aya en matan sun shirya sunyi anko iri guda,
Motocine kusan guda talatin suka d'ibesu zuwa 30 request hotel.
Motan da Angle take ciki anmai decorating da jan flowers da kyalkyali kana gani kasan motan amarya ce.
A parking lot na hotel din duka motocin sukayi parking.
Motan Amarya itace a tsakiya, da sauri wani bodyguard ya ruga ya bude motan.
Angle ce ta fito cikin shigen Lifaya marrow and golden tayi kyau sosai, hannayenta da qafafunta sunsha zane hannunta riqe da mafici da d'an karamin bag na vintage,
Lifayan har qasa yakeja tayi kyau matuqa takalminta high hill me shegen tsawo, tasha make up dan ubabsu,
Mansu ce ta fito a gefenta cikin pink and blue din Lifaya daga ganin yanda ta d'aurashi kasan tasaba dauraba ba wannan bane karon farko dan sosai dirinta ya fito, gata farar fata wow,
Tana sanye da eye glass dinta as usually, hannunta dauke da mafici me kyau da wani danqareren turare na kwalba,
Motan dake bayansu Lubna da Nadiya ne, wanda suma shigen da sukayi kenan, nan aka dingi fiffitowa a motocin wanda ko wacce kalan shigen da tayi kenan.
Tun daga parking lot carfet ne shinfid'e da jajayen fure har cikin hall din zuwa inda amarya zata zauna.
Mansu ce a gefenta se Lubna da Nadiya a baya, sannan sauran kawayen Amarya abaya bibbiyu haka suka jera,
Wasu cikakkun kanurine su biyu mata sukazo amarya na tafiya suna watsa mata kudi, wasu biyun sukazo su kuma suna fesheta da turarruka, se wasu biyun su kuma suna shashshafa mata dilka, Mansu ma se fesheta da turaren dake hannunta takeyi.
Wasu mata kuma su biyar suna bin en matan amarya suna watsa musu kud'ad'e, cool music aka sa musu wasu na rausayawa ana musu manni haka suka qarisa shiga hall din,
Wanda ya had'u ba karya, flowers ne suka zuba akan Angle, wasu mata suka riqe mata qarshen Lifayan ta dake ja da qasa, a haka ta qarisa inda zata zauna.
Nan hall ya hargitse kowa ya shigo, damqe hannun Mansu Aunty Angle tayi dan bataso tayi nisa da ita, hakan yasa dole a kusa da ita ta zauna.
Sosai Aryan yayi kwalliya cikin tsadaddiyar shaddan shi black me ratsin golden ya saka golden din hulan zanna bukar, da golden agogo Rolex se qamshi yake fiddawa tako ina.
Atif ya cika da mamaki da yaji Aryan yace ya rakashi gurin kamu, Aryan dako partyn abokan sune baya zuwa saboda bayasan hayaniya balle ace na kanwarshi se gashi yau zeje har kamu wanda na zalla matane ba maza saboda ya had'u da mace,
Gaskiya ya yarda mace na canza namiji ko wanene shi, bece dashi komaiba suka fito.
Seda Aryan ya 'bata musu lokaci a hanya seda ya tabbatar an kusa tashi a gurin Kamun sannan ya nufi hanyan 30 request.
Parking yayi a parking area na hotel din, wanda tun daga nan mata ne tako ina kuma ga tashin sauti da hayaniyan mutane,
Hakan yasa a hankali yayi wining down tinted glass din motan yana lallatsa waya,
Daidai lokacin Mansu ta leqo shiga da wasu friends dinta, charaf ta hangoshi murmushi tayi ta dubesu. "Please Amira ku shiga ciki am coming...."
Ciki sukayi ita kuma da sauri ta koma gefe ta lalubi numban Aryan,
Ganin itane da sauri yayi picking.
. "Hummmm kayi kyau sosai cikin black shadda da golden hullan......."
Da sauri ya juya, qasa tayi da sauri saura kadan ya ganta,
Gimtse wayan tayi diff tana dariya, ganin bega kowaba yasa yayi murmushi, Atif da yake zaune yace. "Ka kirata mana Aryan...."
Lumshe ido yayi. "Tace in nemata da kaina bazata bayya namin kan taba, mu jira har a tashi...."
Lumshe idan shima Atif yayi.
Ciki Mansu ta koma akaci gaba da shan bidiri, Mansu tayi rawa sosai ita dasu Lubna da Nadiya, haka Angle ta dingi kuka tsaki Mansu ta dingi ja tana share mata hawaye.
Se wajen 7 sannan aka tashi bayan anyi rabon, lalli, dilka, bedsheet da sebinnias abubuwa dai da dama.
Aryan na ganin sun fara fitowa ya sake zuge glass yana kallon en matan d'aya bayan d'aya,
Atif ne yace. "Anya bata daga cikin en matan nan guda biyar na farkon nan...."
Girgiza kai Aryan yayi. "Am not think so domin kam wa'innan duk nasansu..... "
Haka suka dingi fiffitowa,
Angle duban Mansu tayi da Lubna.... "Naga kun tsaya ku fito muje mana...."
Mansu ne tace. "Kuje kawai Aunty za'a zo a dauke mune..."
Hakan yasa Nadiya da wasu en uwa da friends suka fito akabar su Mansu a ciki,
Duban Aryan yayi ganin wasu en matan na fitowa. "Dikko kodai daga cikin kanurin can take ko wancan black dince...? "
Dan karamin tsaki Aryan yaja. "Wa'inan fa duk en uwansu Daddyne ni banma san suba kuma am not thing they know me well dan ban ta'ba ganin suba before, wancan black din kuma kanwar Mukhtar ce a Niger ma take karatu...."
Daidai lokacin Angle da su Nadiya suka fito, hakan yasa Atif saurin fita. "Bari inje ga heartbeat can wow tayi kyau sosai. "
Aryan bece dashi uppan ba ya fice,
Karisawa yayi su Angle suka shiga motoci, Nadiya ne ta shagwa'be. "Tafiya zamuyi fa...."
Karisawa yayi ya amso key din d'aya daga cikin motocin, dan ya maida Nadiya da wasu su biyu, sauran motocin kuma suka fice aka bari daga motan Atif daze d'auki su Nadiya se motan Aryan.
Atif na shirin shiga mota su Mansu suka fito, cikin mamaki yace. "Ku kumafa...."
Mansu ne tace. "Na yarda eye ring dinane na tsaya nema...."
. "gashi kuma duk motoci sun tafi daga nawa wanda zan dauki su heartbeat sena DrDikko amma bari in roqeshi ya maida ku...."
Karisawa yayi gun Aryan da kanshi ke kan waya, dan bemasan abinda suke yiba,
Atif ne yace. "Dr kayi hakuri kowafa ya watse ba sauran wasu Inaga ta tafi cikin wa'inda suka tafi ne, katemaka ka dauqi wa'incan ba wasu saura se su kuma ba motoci ga magrib tayi...."
Se lokacin ya d'ago bin hannun Atif yayi da kallo, inda yake nuna su Mansu.
Kallo d'aya ya musu a fusace ya maida idanshi kan Atif. "What kasan me kace kuwa....? "
Cikin tausasawa a sanyaye Atif yace. ". Ka temaka ka dauqesu kaga akwai baqi kada su fahimci halin da ake ciki kuma qilama Jewel na gefe tana kallon mu..."
Tsaki yaja ya maida kanshi kan waya. "Suyi sauri inaso in samu jam'i...."
Komawa Atif yayi gunsu Mansu da tayi wani irin pity face, yace. "Yace ku shiga...."
Riqo Lubna tayi suka nufi motan, dariya kawai Nadiya tayi.
Saboda tonon fad'a Mansu gaba ta bud'e ta shiga, dariya Lubna tayi ta bud'e baya ta shiga.
Shiru sukayi na kusan minti goma har seda su Atif suka fice sannan ya d'ago kanshi daga wayan ko kallon Mansu beyiba yaja motan ya fice daga hotel din.
Har suka kai gida daga ita har Lubna babu wanda yace uppan, a bakin gate yayi parking be shiga gidanba, bece dasu komaiba ya dauki phone hakan yasa dukkansu suka fice.
Wani irin tsanan motan yaji yanaji saboda Mansu ta shiga kuma ta zauna a gefenshi hakan yasa da gudu yaja motan ya nufi gidan Ayya dan ya ijiye motan yasa a rufe da tanfol baze sake hawantaba sedai ya dauki wata, domin ko yaya Mansu ta ta'ba abu to ya barshi kenan.....
🤔 Kai Jama'a Kunjifa wannan tsana haka, yazeyi inya gane itace jewel dinshi.....??? Ohhoooo.
Tana shiga gida ta daga waya, lokacin ya kusa gida da sauri ya taka burki yayi picking.
Cikin muryan kuka tace. "Wallahi ka bani mamaki Twinkle yanzu dama badanni kaje gurin nan ba dan wata kaje...? "
A rud'e yace. "What did yhu mean please jewel what happen....? "
. "Twinkle wacece ka dauqo a gaban motanka, nazo zan shiga naga wata sedai na koma Twinkle ka bani mamaki...."
Kai ya dafe cikin dana sani yace. "Wallahi Jewel danke naje kuma ni wannan banma ta'ba ganin taba se yau kuma roqona akayi na dauqesu...."
. "Twinkle ni kadai aka barifa...."
A rud'e yace. "Innalillahi bari in dawo in dauko ki...."
Ijiyar zuciya ta sauke. "Ai na tari napep na dawo gidanku...."
Huci ya saki. "Please jewel d'ita am sorry kinji ninaja miki...."
Itama hucin ta saki. "Hummm Twinkle nagaji sosai zamuyi waya anjima..."
'Diffff ta yanke kiran, ijiyar zuciya ya sauke gaskiya Jewel na wahalar dashi da yawa amma duk da haka yana santa sosai bayajin ze iya rayuwa babu ita, dama ance wanda baya soyayya inya fara hauka cewa yakeyi.
******
Washe gari.
Yaune za'ayi bridal shower.
Tun safe Mansu ta roqi Farhan ya kaita siyayya, da kyar ya kaita dan yanaso yaje ya dauqo Lailan shi ya kawota gidan.
Inda ake seda teddies tace ya kaita, qatowar teddy ta dauka pink color me kyau a gurin tasa aka mata kali graph, aka rubuta mata.
_ILUV YOU TWINKLE_ babba a jikin teddy din yayi kyau sosai, tasa akasa a cikin box aka mata wrapping yayi kyau sosai akasa flowers a jiki aka rubuta.
I love you so much.
Amsa tayi tana wani irin murmushi, tana karisawa ta bude baya ta saka batareda ta yarda Farhan ya ganiba, amma duk da haka seda yace. "Allah sa ba Yayana za'a yaudara ba...."
Murmushi kawai tayi, nan suka nufi gida.
Yau Aryan yana busy a hospital beje neman Jewel gurin bridal shower ba,
Inda sunyi bridal shower dinsu yayi matuqa, inda amarya taci farin weeding gown su Mansu kuma suka sha marrown din Ashobe da black head sunyi kyau matuqa sun haska.
Bayan isha ya shigo gidan, Mansu da suke fira a compound din gidan sunada yawa akan carfet, ganin ya shigo attension dinshi nakan waya yasa da sauri ta miqe tayi ciki da gudu.
Da gudu ta fito da wannan gift din teddy a hannunta, ta karisa.... "An ban saqo in baka.."
Chakkk ya tsaya jin muryan yayi kaman a mafarki da sauri ya juya, qara had'e fuska yayi ganin Mansu da sauri ya kauda tunanin da zuciyanshi ke mishi akan murya,
Juyawa yayi rai 'bace da sauri tasha gabanshi. "Wata budurwace tace in baka wannan...."
Kallon qaton gift din yayi, kafin ta kuma wani magana ya fizga ya wuce.
Murmushi tayi kawai ta koma akaci gaba da fira.
Yana shiga d'aki ya ijiye kan table beso bud'e waba, ganin an rubuta I love you so much a jiki, yasa da sauri ya bud'e, murmushine ya bayyana a fuskarshi ganin daga Jewel dinshi gift din yake, rungume teddyn yayi yanaji inama jewel ce dataga soyayya,
Da sauri ya had'e rai tuna wacce taba saqon ta bashi da yayi.
Da sauri ya janyo waya ya lalubi numbanta.
Da sauri ta tashi cikin hayaniya ta koma can gefe tayi picking, kan ta gaidashi yace....."Naga saqo nagode, amma banso kikaba wannan yarinyar ta bani ba banasan yarinyar ko kadan batamin ba..."
Lumshe ido tayi tanajin d'acin abinda yace a ranta tace. "Waya fad'a ma nima kamin ne mtsssww nima banasanka...? "
Amma a fili cewa tayi. "Calm down baby yarinyar da kacemin ranan Kamu kafara ganinta taya zakace bata makaba...? "
Huci ya saki. "Aini tunda na ganta at all naji bataminba na tsaneta...."
. "Kayi hakuri twinkle dina nayi kuskure amma insha Allah zan kiyaye, amma am sorry to say ba hujja bane ka tsani mutum hakanan dole akwai abinda ya maka, yanzu ita yarinyar please kayi tunani meta maka da kaji ka tsaneta..? "
Shiru yayi shidai gaskiya ba abinda Mansu ta mishi hakanan yaji tun tana yarinya baya santa, hakan yasa yace.
. "Bakomai gaskiya kawai dai ninaji batamin ba..."
. "Hummm Twinkle you're wrong babu kyau mutum ba abinda ya maka kaji ka tsaneshi please think and correct...."
Shiru yayi bayajin ze iya dena tsanan Mansu, yanzuma daga magananta har kanshi ya fara ciwo hakan yasa yace. "Jewel I wanna sleep we talk letter, I love the teddy so much yanzuma tana rungume a qirjina..."
Murmushi tayi. "Sleep well darling I love yhu..."
Janyo teddyn yayi ya rungume a kirjinshi tarede katse wayan yana tunani sosai.
Washe gari ranar jajibarin d'aura aure kuma ranan ne za'ayi dinner anjima da daddare dan su Ya Barrister da abokanshi duk sunzo suna guest house.
Sanye take da doguwar riga sun fito itada Nadiya zasuje amso mawa Angle saqo,
Dikko da yake tsaye jikin mota ganin sun kariso yasa ya d'ago kai ya kalleta, karo na farko kenan daya ta'ba kallon Mansu harya hango kyanta, da kaman bazeyi maganaba se kuma yace.
..."I want to talk to you...."
Nadiya ce kadai ta juya, yace. "Not yhu..."
Hakan yasa Mansu juyawa cikin mamaki, cikin isa da ko in kula yace. "Please wannan wacce ta baki saqon jiya ko zaki iya min bayanin yanda take..."
Itama cikin nuna ko in kula tace. "Doguwar budurwace kyakykyawa bazata wuce 21 to above ba..."
Juya ido yayi. "Amma in kika ganta zaki iya ganeta...? ."
. "Uhmmm am not think so domin gaskiya da niqaf a fuskarta, muryanta kawai naji tace please sister kiba DrDikko wannan......
Da sauri yace. "Thanks that all...."
Gaba yayi yana kad'a key yanajin qunan dama be tambayeta ba zejawa kanshi yarinya ta rainashi, amma ko meye jewel taja mishi.
Dariya Nadiya ta fashe dashi. "Gaskiya Mansu ke muguwace jubi yanda kika rud'a miskilin mutumin daba ruwanshi da mata, yau shine yayima Mansu maganan kirki, harda yi mata godiya saboda Jewel gaskiya mace, mace bala'i ce wallahi......."
Mansu dariya kawai tayi......
Kuyi hakuri kwana biyu am busy shiyasa amma insha Allah inna samu tym zan dinga muku typing da yawa, kuna raina Luv yhu all 💋.
Mimi queen ✍️.
2022-10-08, 10:57 a.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)
Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa
_____________________________________
Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.
Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.
Bismillahir rahmanir raheem.
33&34.
Yau ta kama Friday.
Kuma yaune za'a daura auren Aunty Angle.
Tun safe ake walima a cikin gidan, Mansu nacan se kuka takeyi domin zata rabu da Auntynta wanda itama Angle kuka takeyi kaman ranta ze fita, da kyar mommy ta lalla'basu suka tashi suka fara shiryawa.
Aryan kam nacan cikeda baqin ciki domin yasan daga gobe za'a kai Angle, kuma shikenan Jewel d'inshi zata tafi batareda ya gantaba.
Sosai Mansu tayi kyau kaman itace Amarya dan haka ta dingi shige kala da kala, an mata heavy makeup tayi kyau kaman a sace, sedai bata cikin walwala daka cika ta'ba ta zata fashe maka da kuka dan a wuya take, tana tunanin rabuwa da Auntynta wacce suka taso tare tun suna qananu dan shekaru uku Angle ta bata.
Karfe biyu aka daura aure,
Lokacin su Ya barrister suka nufo gidan,
Wayan Mansu ya kira, d'auka tayi yace. "Ki kawomin amaryata muna compound muna jiranku...."
Tashi tayi tareda duban su Lubna. "Angwaye suna jiranmu kuzo muje...Aunty Angle angonki na kiranki...."
Tashi sukayi, sukasa aunty Angle a tsakiya wacce tayi kyau kaman me,
Suka nufi waje.
Tun daga nesa Mansu ke jefawa Ya barrister harara dan haushin shi takeyi ze rabata da Yar uwarta.
Har suka karisa, duk suka gaidasu amma badda Mansu data koma gefe ta tsaya dan abokan Ya barrister akwai d'an banzan kallon jaraba.
'Daya daga cikin abokan Barr. Fu'ad da Mansu take mugun burgeshi yace. "Mansu ya kuma kika tsaya a baya matso mana mu gaisa..."
Fu'ad ne yace. "Rabu da ita Ma'abub ai tun jiya naga Mansu se harara ta akeyi...."
Cikin muryan shagwa'ba tana shirin sakin kuka tace. "Bakai bane zaka rabani da Auntyna....."
ta ruga da gudu tareda fashewa da kuka,
Dariya tabasu dan har Angle seda abun ya bata dariya kowa yana jinjina shagwa'ba irin na Mansu.
Aryan ne ya taho yana waya yasa shaddanshi sholley fari yayi mugun kyau, batareda Mansu ta luraba ta bangaje Aryan ta tafi luuuu zata fad'i dan har glass dinta seda ya zame yai qasa, Aryan besan sanda yayi saurin tarbota ba tafad'a jikinshi.
Ido ya zuba mata itama cikin kwayan idan shi ta zubawa ido tanajin wani irin abu, da sauri ya kauda idanshi daga nata ya saketa timmm ta fad'i a kasa yayi gaba.
Kai ta had'a da gwiwwa ta fara rusan kuka,
Ranar haka Aryan yaita neman numban Jewel be sameta ba duk ya shiga damuwa.
Washe gari.
Karfe hudu aka wuce da Angle, inda Angel taci kuka mommyma seda ta zubda kwalla,
Bayan an gama mata nasiha aka nufi parking lot da ita, kuka takeyi sosai Farhan ma kuka yakeyi yakasa daurewa Aryan kam na saman staircase ta window yake hangosu ko zega Jewel.
Amma yana ganin Mansu ta fito tana kuka sosai yaja tsaki ya zuge labulan window din, ya koma ya zauna kan siter ya lumshe ido yanajin wani mugun rad'ad'i a ranshi, waya ya janyo ya kuma kiranta.
Sedai a kashe hakan yasa ya rubuta saqo ya tura