Showing 42001 words to 45000 words out of 59456 words
Chapter 15 - YAR LESBIAN CE COMPLETE DOCUMENT BOOK.txt
*Hudallah marubuciyar* (Zainab) *Aysha Ali garkuwa* *Miss-XoXo* *Sadnaf* *Mrs JH* *Maman-Shakur* And Othersπππππππ page....28 gaba dayansu Sun Hallara Kan dining table din Suna Shirin Cin Abinci. daddy ne yace Hafsat ina yaran Nan ne? Inaga ko basu gama huta gajiya bane mum ta fada tana kokarin Serving din Nazir dake wajen... ya kamata Akirasu ko? daddy ya fada yana kallon mum. Kallonshi tayi tace da Nabari ne Saci nasu daga baya. Nazeer ne yace Ai gara kawai Aci gaba daya mum! Banza tayi dashi, ganin Haka yasa dad yace ma Mubeena ta tashi ta kirasu, tashi tayi ta tafi da gudu Zuwa Sama. ba'afi Minti5 tsakaniba Suka Sakko Atare....daddy Yana ganinsu yace duk gajiya dince Haka yarana, Murmushi Leemah tayi ta Sunkuyar da kai qasa, yayinda Feenah tace dad Akwai gajiya Wlh. Ai kun kusa gaba daya daurewa Zakuyi dad yafada. tashi feenah tayi tafara Zuba Nasu Abincin, Sunaci Suna fira banda Leemah da duk take jinta A Takure musamma data dago taga Nazir take fuskanta, Haka dai kawai ta daure tana ci gashi duk Sanda Zata dago Saisun hada ido Atare Kuma Suke Sakar ma juna Murmushi... mum ce ta dago tace Nazir Anjuma Zan Aikeka gidan "Umma" ka kaimata Sako. Shirun data jine yasa ta kalleshi, gaba daya Hankalinshi baya jikinshi magana Suke da Leemah da ido ga wani kallo dasuka tsare junansu dashi! Mumy ce ta Saki Spoon din hanunta ta dan bigi Kafadar dad tana nuna mishi Su Leemah, daga gira dad Yayi Sama yana murmushi lokaci daya Kuma yayi gyran murya Ehmmm...gaba daya Suka juyo Suka kalleshi ganin Su Ake kallo yasa Leemah taji Kamar ta nitse Awajen, durkusar da kai tayi Kasa. Nazir kuwa Inda inda yafara yace Mum maga kikai? dad ne yai Saurin cewa ba magana tayiba nine nakusa kwarewa, Hafsat tashi muje kiban Ruwa, tashi mum tayi Sukabar wajen ita da dad. feenah kuwa da dama tunda Suka Zauna ta lura da yanda Suketa mgn da ido da Hanciπitama tashi tayi tace Alhmdllh nakoshi....tashi Leemah tayi da Sauri besty jirani Nima na koshi, da Sauri Nazir yace baki koshi ba Common Xauna ki karasa,marairace Fuska tayi kamar Xatai kuka Allah yaya Nazir na...Kafin ta karasa yace Naji kin koshi Xauna muyi mgn, Xama tayi. Yace feenah dawo kema tare Zamuyi mgnr, dawowa tayi ta Xauna Nazir ya kalli Twins yace kuje Baba ladi ta Shiryaku Xankaiku gidan Su mai Kyau! Ai da Sauri Suka tashi Sukai Cikin gida. Juyowa yayi yana kallon feenah Sisto Nariga Nasan Kinsan ina matukar Son besty dinki ko? Umm ni bansaniba feenah ta fada tana yatsina face...Kara juyowa yayi yana kallonta Haba my Sis Nasan kinsan komai kuma bakya karya kigaya mun gsky. Eh Nasani Yaya Nazeer kawai Haushin boyemun dakayi Nake ta karashe mgnr harda Dan Hawayenta....haba Sis Menene Abun kuka kuma, Nifa daman Nabari ne kidawo Nagaya miki kamar Surprise Haka, kinsan bana boye miki Abu itama Leemah ban so tasaniba Nakasa daure ma Zuciya tane yasa Nagaya mata. Turo baki tayi tace Naji Amma dafatan Son tsakani da Allah kake mata? dariya tabashi yace irin Son danake miki Shi nake mata, Aa yaya Nazir nafison Nata yafi Nawa...Shiru yayi yace toh kitayani addu'a tasoni fiye da komai, toh yaya Nazir Zanyi. Leemah ce tace karfa mum tafito! bayan Sun gane komai feenah ta fada tana dariya..Atare Suka Zaro ido fada musu kikai Leemah ta tambayeta? No kune kuka tona kanku kallon juna Kamar wani Xai dauke dayanku din nan. Nazir yace Ai Hakan ma yayi kinga Sai Amana Aure da wuri! Leemah ce ta marairaice fuska Aa nifa Sai feenah tasamu miji Zamuyi Aure Rana daya...dariya Nazir yayi yace wato Ku Haryanzu yara ne, banda Abunku Ai gara daya taga auren daya Sabida idan Rana dayane daya bazatakai daya gidan Aurenta ba. Waye ya fada maka yaya Nazir? Aikoda Rana daya mukai Aure Sai Nakai Leemah gidanta kafin na wuce Nawa. Nazir ne yace kinmanta Kabeer Xaki Aura kuma yola Za'a kaiki,ba Lallai Na yarda baby taje yola Aranar Aurenmu ba...da Sauri feenah ta tashi tana cewa Ai bazaka Rabamu ba dan yanxu kasamu mun Amsheka, daga Haka tabarsu Zaune A wajen. Juyawa yayi yana kallon Leemah baby kawarki Akwai Rigima, Uhum bata Rigima Kaidinne Kake Sakata Rigima, Umm Na lura bakwason Laifin junanku Toh ya Soyayya ta yanzu Aranki??? Shiru tadanyi daga bisani tace tasamu waje babba Acikin Zuciyata, kallonta Nazir yayi kamar ba ita tayi mgnr ba ta wani fuske, Cikin Xuciyarshi yace Lallai Leemah irin macen danake muradin Aure ce, Afili cewa yayi Alhmdllh my baby Yanzu kinga kamin Ki koma Skul Sai Asaka mana Rana...Xaro ido tayi tace da wuri Haka? Eh mana bakiji Hausawa nacewa Abari ya wuce Shi ke kawo Rabon wani ba? Hakane but yaya Naz..but what? Nazir ya katseta da Sauri. Kabari lokacin daxa'a Saka Ranan feenah da kabeer Sai Asaka tare da namu. Kin kawo Shawara mai kyau baby Shiyasa nake kara Sonki,duk da kin barni Cikin tunaniki, kullum dake nake Kwana kuma dake nake tashi. Nima Haka yaya Nazir. Kin tabbata? Kallonshi tayi Suka hada ido ta kashe mai Ido daya tace Ummm, Ajiyar Zuciya Nazeer yayi Dan wani irin farin ciki yakeji wanda baya misaltuwa. "I love you So much my baby" Nazir ya fada yana Mata Murmushi. "love you more my baby" Leemah ta bashi Amsa kasa kasa. Xancire miki kunyar Nan Soon duk da Naga Alamar nama fara kokari Wajen cireta....dariya Leemah tayi ta tashi tace kada Su mum Su Sakko, tashi Shima yayi ya rakata Har kofar Room din Feenah yace kishirya Anjuma Nakaiki gida. Ok tace tashige Ciki. Inno ce tsaye Kan yazeed Tana fadin Haba tsaka ka kiramun ita Naji ko tana inane. Inno nace miki wayata Bazata iya Zama A kunanki ba dan Allah kitafi ki bani waje yazeed ya fada yana nuna mata Hanyar Sama.... tsaka! tsaka! tsaka! Sau nawa nakira ka? Oho yazeed yace ke kikasan tsaka. Kwafa Inno tayi tace yaro yarone ina tausaya maka Ranar da Zaka Shigo hannuna, Xakayi nadamar yimun wannan Abun Dan Ubanka,yanzu namaka Uzuri dan nagane dalilin dayasa kakemun wannan Abun...Amma muje Zuwa ni inno jikar Saluhu da balaraba Nakusa Na dana maka tarkon da bazaka iya tsallakeshiba. Kallonta yazeed yayi yace iyaka kice idan Abba ya dawo Xaki fada mishi, Toh Sai me? Haka kace ko? Eh Haka nace mtsww kizo kitafi koma ma huta. Fatima kayimawa tsaki bani ba...muxuba ni dakai. Tashi yayi yana toshe kunanshi...daidai nan Abba yayi Sallama Cikin parlon. Suman tsaye Yazeed yayi dan yasan yau Inno Sharri Xataimishi ba kadan ba. da karfi Inno tace Ayirirerere yau Ga dana Ya dawo huta Roro. ...da fara'a Abba ya karaso kusa da ita ya gaidata amsawa tayi Cikin walwala da Sakin fuska, Abba ya kalli yazeed my Son lfy kuwa? Sannu da dawowa Abba! Yawwa Son duk kuna lfy ko? Alhmdllh Abba. Ya katsaya Haka kamar wani police? da Sauri Inno tace Nakirashi ne ya kiramun Halimatu A waya Shine yake kokarin kiranta Saikuma ka Shigo. da mamaki yazeed yake kallonta Suka hada Ido ta watsa mishi Harara, Shi kuwa cikin Ranshi yace Tabbas wannan tsohuwar Akwai Abinda ta Shirya Mun. Abba ne ya katseshi toh kakirata mana, toh Abba. Kiran Leemah yayi ta dauka ya mika ma Inno! Allo Halimatu. daga bangaren Leemah tace Na'am Inno ta. Kina inane munata jiranki Shiru Har Abbanku ya dawo. Inno Naje gidan Uncle Umar ne, yanxu gani Ahanya tare da feenah da Twins. Har Naji dadi Halimatu chanake kokin fasa Xuwa ne. Aa Inno Gani nan,me kika dafa mana? Saidai kinxo Yar nan.Toh Inno gani nan. Anshi tsaka kashe ban iyaba....Amsa yayi da Sauri yabar parlon danshi tsoro yake kada tamai Sharri wajen Abba. Mamy ce ta Sakko daga Sama Cikin Adonta, barka da dawowa Abban Leemah,yawwa barka Maman Leemah.tashi inno tayi tace bari nabarku Ku gaisa, Kuma Amadi gobe Xaka maidani inda ka daukoni, bata jira amsarshiba ta bar wajen. Yazeed na fita yaci karo da Yusuf dake Shigowa Yanzu...Aa Dr Ashe kana ciki? Ina ciki Yusuf Zomu karasa Akwai matsala fa. Karasawa bangaren yazeed Sukayi, Yusuf yace Matsalar Menene Aboki? Yusuf mamaki nake Abba ya dawo inno batace mishi komai ba, kasan Halin Inno da Rashin hakuri gani Nake Anya ba Wani Abun ta Shirya ba? Gyara Zama Yusuf Yayi yace banajin Akwai Abunda ta Shirya, Inaga kawai dan tasan Za'a Maka fada Shine tadan kauda Zancen. Shiru yazeed yayi daga bisani ya girgixa kai, Anya Kuwa yusuf? nasan Halin Inno Sarai wlh Amma mubar mgnr ni bawani tsoroma nakeji ba taje tayita fada. dariya Yusuf yayi wanda shi kadai yasan Ma'anarta yace Aikuwa Abar mgnr kawai. yawwa yazeed haryau baka samo Wacce kakesoba? bansamo ba Yusuf ni banga wacce tamunba! Kallonshi Yusuf yayi yace duk Matan dake fadin garin kaduna babu wacce tamaka? Eh Yazeed yace Atakaice danshi gabanshi ma dan faduwa yake.. Ok Yusuf ya fada Amma Kana nan kan idan kasamu yarinyar data kalle Cikin idonka tayi magana Xaka Aureta ko? daga Kafada yazeed yayi yace yes. Atare Suka Sakko daga motar gaba daya Suka Shiga gidan. Da gudu Twins Suka karasa Ciki Suna kiran mai Kyau! Suma Shiga Su leemah Sukai ba kowa a parlon dan Haka Sukai Xamansu Anan. Nazir yace bari Naje Wajen Yazeed da Sauri Twins Sukace Suma Zasuje, fita Sukai Atare Sukai part din yazeed. Feenah tace ina mamy da Inno Suke ne? Leemah tace kya tambayeni nida mukazo tare, Kinsan Abba yadawo maybe mamy Taje mishi wlcm Sunyi missing juna kinsan, itakuma inno Inaga Wani Abun takeyi duka feenah takaima Leemah ke bakida Kunya ko? Toh Menene Ai gsky na fada, yawwa Feenah dazun baby kecemun Wai Asakamana Rana kamin nakoma Nace Nooo Saikin tashi Naki Auren. Toh waye kuma baby!? dan Rufe ido leemah tayi tace yaya Nazir mana. Tabe baki Feenat tayi tace Umm. Saiki bashi phone number dinki Kada mukoma Skul kina tunani. dariya Leemah tayi tace baki lura ba Amota ya amsa? Ina Xanlura fa kunshige gaban mota kuna Xancen love, Amma harda kukan munafurci ni feenah ina tsoro waye waye mtsww magulmata daga Ke har Shi. Inno ce ta Sakko daga Sama tana A'uzubillah wake tsaki irin na tsaka? Tashi Leemah tayi takarasa gunta tana dariya. Inno ta ya gida? Lfy Halimatu ta Shine kika fara Xuwa gidan Su Naziru baki Xomunba. Sorry Inno ba gashi yanzu Munzo tare da feenah ba. Kallon feenah Inno tayi tace Nafisatu yan makaranta... ina yini Inno? Lfy Nafisatu ya karatu? Yasu Hafsat?ya garin kuma? Ya Ummaru? Kallonta feenah tayi ta kauda kai don idan Akwai Abinda tafi tsana Shine yawan tambayoyi irin ya kaza ya kaza. daga gira Inno tayi Sama Ahhh Wlh kwarai Halinku daya da tsaka....kallonta feenah tayi tace waike kowa Saikin bata mishi Suna ne? bude baki inno tayi tace Laaa aisaiki fadamun bakyason Ina tsokanar yazeedu bawai ki rinka mun Kwana kwana ba. tsaki feenah tadanja Kadan. Inno tabe baki tayi tace Ummm gaskiyar Yusufa. Kallonta leemah tayi tace inno mai yusuf din yace miki? Zomuje daga Chan na fada miki Inno taja Hannun Leemah Suka bar Wajen. Kinsan me Yusuf ya fada mun kuwa? Aa inno fadamun! Kasa kasa tayi da murya, yace mun yazeedu da Nafeesatu Sun dade Suna Son junansu, Amma Sabida gaba dayansu Sarakan miskilanci ne yasa Suka Ki tsayawa Su Sanar da junansu, Amma yazeedu ya fada ma Yusuf yana Son Nafeesatu, kuma yazeedu Aure yakeso Sosai Sabida RANAR dana kori Kafurar yarinyar nan naje amsar kudi gunshi ya rufe kofa da Sauri ya Hanani Shiga, daga baya da idona Naga yarinyar ta fito daga bangarenshi tana Sanda, Toh ke Halimatu Kawar taki bata taba gaya miki tanason yazeedu ba? Leemah datunda Inno tafara maganar ta daskare Awajen tace, inno bata gayamun ba, Kuma inaga yusuf Wasa yake miki Feenah bazata boyemun komaiba,inno ke bakiga basa Shiriba ma da bro? Ke da alla Sakarya Yusuf yace irin tasu Soyayyar Kenan kedai Kada kifada Mata kibari muga gudun Ruwansu. Ajiyar Zuciya Leemah tayi tace Toh Inno.Amma kasan Xuciyarta Sam bata gasgata maganar ba. fitowa Sukai parlon Leemah jikinta duk yayi Sanyi So take Abunda Inno tafada yazama Gaskiya da tafi Kowa farin Cikin hakan kuwa. Su mubeen ne Suka Shigo tare da Nazir Wajen inno Suka nufa Suna dariya. Yusuf Naga ya Aje Wata mage kofar yazeed ya nufo Cikin gidan Shima. Kiran feenah Akai Awaya tace laaaa Leemah Kausar ce, bari Naje Waje na'amsa karfa kibiyoni. Toh Leemah tace Hakan ba Karamin dadi yama yusuf ba. Tana fita yace inno inaga wajen yazeed Zataje bakiji tana kada Leemah ta betaba. Ai ita Sakaryar Halimatu din nan bata yardaba inno tafada. Kallon leemah yusuf yayi yace barta inno yanxu zata yarda ai. Fitan Feenah yayi daidai da lokacin da Yazeed ya fito daga daki da Sanda A Hannu,dama ganin magen da yayi yasa yakoma ya dauko Sada dan yakoreta dan idan tana wajen bazai iya wucewaba tsoronta yake. Sandar yasaka yana dan ture magen itakuwa taki tashi. Feenah ce ta hango Abunda yake tace Kausar dan kashe kadan, bro din Feenah Kema mage mugunta Bari naje namishi ta tassss. *Gud nyt loversππ Ina typing Ina gyangyadi duk because inasonku kamar yanda kuke Sona yasa na daure nai muku wannan* ππππππππ YAR LESBIAN CE ππππππππ By Nadeeya mohd Ahmad (πWhatsapp: +2347010902548 http://arewapost.tk πNadseerπππ) dedicated to Xaynab Ummu mahbub Page....29/30 Karasawa tayi Cikin tafiyarta wacce kamar bata Son taka kasa. daidai gaban yazeed taja ta tsaya Kai Malan! dagowa yazeed yayi daga durkusan da yake ya Zuba ma kaykyawar fuskar feenah ido take gabanshi ya fadi Rasss. Itama feenah Ido ta Saka Cikin Nashi yayin da itama gabanta ke faduwa wani irin kwarjini taga yamata,jitake kamar ta juya ta koma Amma takasa motsin Arziki, daurewa tayi ta k'ara Saka idonta Cikin Nashi still takasa mgn, durkusar da kai kasa tayi tafara motse da dankaramin bakinta, Kai Anamaka Kallon mai tausayi Ashe Kai mugu ne! Yusuf ne ya karaso wajen yace Ahh feenah yazeed fa mai tausayi ne tsoronta yake Ji kawai, Amma idan kin isa ki kalli Cikin idonshi kifada mai bashida tausayi mana. kallon Yusuf Feenah tayi ta yatsina fuska tace, Kan mai Xan kasa?? Toh idan Zaki iya Kiyimana. d'aga kanta tayi tasaka idonta Cikin Na yazeed yayin data daga Dan yatsanta tana nunashi kai yazeed Sam bakada..... ai da Sauri Yusuf yabar wajen yana fadin Wlh itace matarshi. Feenah itakam mgn take mai bako iftawa bare inda inda,,,,,Kai dama duk wannan fadin Ran naka barinshi kayi domin Sam baya maka kyau, yanzu kazo kana ma mage mugunta katuna itama Hallitace kamar ka! kuma Sai Allah ya muku hisabi kan muguntar dakai mata, kana ganin kaidin kamar kafi kowa ne Toh kasan wa'inda Zaka rinka mawa mugunta,kada Abun ya kasance Har kan bayin Allah. daga Haka feenah ta bar wajen....da Sauri Su inno dasu Leemah dake lekensu Suka koma Ciki ganin ta tawo, Ashe Yusuf daya koma yace musu Suzo Suga su feenah na Soyayya, bayan Sunma Nazir bayani kuma Sunci Shima kada yamusu magana Shine Suka Leko Suna kallonsu Amma Sam basajin Abinda Suke cewa, Leemah har picture ta daukesu Dan ba karamin kyau Sukayi Ayanda Suka tsaya ba.....yazeed a inda tabarshi ya daskare pic din bakinta kawai yake kallo lokacin da take motsashi da irin yanda take nunashi da Hannu Sam babu tsoro ko fargaba Atare da ita lokacin da take maganar.....Yusuf ne ya karaso yadan bangaji kafadar yazeed firgitgit yayi yadawo Cikin Hankalinshi, Janshi Yusuf yayi Zasubar wajen Saiga feenah ta fito da Ruwa A wani Cup na plastic ta Aje gaban magen ko kallonsu bataiba ta kara komawa Ciki. daki Yusuf yaja Yazeed Kan bed Suka Zauna, yusuf Ya kalleshi ya daga mai gira yaaa tayi ko? Ajiyar Zuciya yazeed yayi ya yatsina face wace? Yusuf ne ya kalleshi yace wace kake tambayana, yarinyar nan mana. Aini koda Nace maka nasaka gasa tsakanina dakai bance maka harda yarinyar nan Ackiba, wannan yarinyar Abinda yafi hakama Zata iya, Dan dama batada kunya yazeed ya fada yana kara kauda kai. gyara Xama Yusuf yayi yace Wlh Malan baka isaba Ai Kaine Kace Mun koma wacece, Kuma Ai Wannan tacika kowani Sharadi dakace kafison mace ta kasance tana dasu. Yusuf Sharuddana Uku ne dan tayi daya Ai batai Sauran biyunba. Karya kake duka tacika yazeed. Na1. kace wacce kakeson ka Aura ta kasance mai tausayi! Agabanka yanzu ta dibo Ruwa taba mage, Kuma kana gani magen tasha Ruwan Sosai Sannan tabar wajen Kenan dama k'ishi take ji yasa tazo kofarka. Na2. Kace ta Kasance mai kuzari tahaka Xata iya kula da gidanka da kai kanka da kuma yaranka! So Ayanda feenah tamaka mgn tana Nuna maka yatsa bakinta na furta Abinda takeso ya'isa kaa gane cewa ita din Mai kuzari ce. Sai Abu na3. Kace wacce Xata iya kallon Cikin idonka tayi magana, Naga feenah tunda tafara magana bata kifta ido ba, gashi ta Sumar dakai Atsaye Sabida Xakin muryarta. Toh me kuma kakeso ka fadamun yazeed??? Numfashi yazeed ya Saukar Ahankali yace Abinda nakeso yanzu ka kyaleni Yusuf tunda kai kacika naci kabari Zanyi Shawara. "Alright" Yusuf yafada yace kasan gobe Xani Zaria ko Zaka Rakani? Allah ya kyauta na raka ka wajen Mace yazeed ya fada yayi Hanyar Cikin gida. Tashi Yusuf yayi yabi bayanshi Suka Shiga parlon Atare. Yanzu hatta Mamy da Abba Suna parlon fira kawai Suke Suna dariya. Inno Naganin yazeed Sun Shigo tafara waka....."Namiji kuchaki Ahadashi da kuchaka Kamarshi, Na miji miskilalle Ahadashi da Miskila Kamarshi" gaba daya parlon Suka Saka dariya Abba yace Inno keda waye haka? Kallon gefen idon yazeed tayi tace Amadi wakar mu muna yara na tuna kawai...tabe baki feenah tayi Aranta tace tshohuwar Nan bazata Rasa Aljanu ba bakinta Sam baya Shiru. Shima yazeed Cikin Xuciyarshi Cewa yayi ai gara dai goben tazo kitafi muhuta. Inno kamar tasan mai suke fada cikin Zuciyarsu tace Wanda ya Zageni Cikin Ranshi Allah ya hadashi da daidai Shi. dariya Suka kara kwashewa dashi. yayinda yusuf yatashi yace nidai Zan tafi Saida Safenku. Inno tace yusufa Agaida gida, Abba da mamy ma Sukamai Saida Safe. tashi Nazir