Showing 48001 words to 51000 words out of 59456 words
Chapter 17 - YAR LESBIAN CE COMPLETE DOCUMENT BOOK.txt
tasaka ta Zagaye Saman kanta dashi yayinda takalmin kafarta ya kasance Jane, dankunne da Sarkar wuyanta zuwa Abin hanunta suma duk jane.ga Wata kwalliya data tsantsara kamar Zata zaben sauraniyar Kyau...tsayawa Yusuf yayi yana kallonta Gani yake kamar ba kausar ba domin gaba daya ta chanza mishi. Iskar data hura mishi a Ido ita ta dawo dashi Cikin hankalinshi. Tashi yayi tsaye yana facing dinta. Kinyi Kyau my Kausar, Murmushi tayi tace Tnx my Yusuf. Zama Sukayi Atare tana mishi ya Hanya. Waye ya gayamiki masoyi na ganin Akwai tafiya Xuwa wajen masoyinshi. hakane kuma Sweetheart bakaci Komai ba. Inajiran kizo kibani, karka damu Soon. Kinsan yau gaba daya nazo da Shirina, domin ni Ayanda nake Ayanzu baki Adaura mana aure Ayau Natafi dake ba. dariya kausar tayi Sosai tace kacika Xumudi. Kece kike ganin haka yusuf ya fada Yana daukan Ayaba dake kusa dashi. Kawo na bare maka ko. No Indai kika bare kece Zaki bani dan haka kawai na hutar dake. Haka sukaciga da firarsu Cikin kulawa da Nuna Soyayya tsantsa, ta Yanda kowannesu yake ganin bazai iya rayuwa ba dayanshi ba. bari nakira maka Su Hajiya Ku gaisa, Kina nufin daddy ma Yana nan? Eh mana. Gyara Zama Yusuf yayi yace gara dana Saka manyan kaya kuma nazo da Shirina.dariya Kausar Ta fita tanayi. Ba'adau Wasu lokutaba Iyayen Kausar Suka Shigo Cikin parlon. Yusuf Na ganinsu ya Sauka kasa yana gaidasu, Cikin Nuna kulawa Suke amsa gaisuwarshi, yayinda mahaifin kausar yace yarona katashi ka Zauna daidai.kara durkusar dakanshi yusuf Yayi Kasa bekuma Tashi Ba.mahifan kausar Sunji dadin irin tarbiyarshi matuka.dan haka mahaifin kausar yafara magana kamar haka. Hakika na yaba da hankalinka Yusuf kuma Nayi matukar farin Ciki Game da Zaben miji nagari da yata tayi, dama nadade ina fatan Hakan. Allah yamuku Albarka gaba dayanku. Amin yusuf ya Amsa kasa kasa. Cigaba mahaifin kausar yayi, idan kashirya Zaka Auri yata katuro mun magabatanka Cikin Satin nan Asaka Ranar biki Zuwa Sanda yata Zata karasa karatunta. Wata Shida ya Rage ta karasa.koya ka Gani Yusuf? Baba Yanda kace nima haka Nayi tunani Zuwa jibi Zan Turo magabatana Ngd Allah yakara girma. Amin mahaifin kausar yace. Madallah da samun d'a nagari irinka ina alfahari dakai Yusuf mahaifiyar Kausar ta fada. Ngd mama. Tashi Sukai suka fita. Yusuf na ganin Sun fita yatashi tsaye Hannu yadaga Sama yana gdy ga ubangiji mai wanzar da farinciki Cikin Zukatan bayinsa. Ahaka Kausar ta Shigo ta sameshi Sanarda ita komai yayi Akan yanda sukai dasu Hajiya itama farin ciki tanuna Afili Ahaka Yusuf ya sanar da ita maganar su Yazeed kamar yanda ya Sanar da inno, Cikin ranshi yana rokan Allah ya yafe mishi game da karyar dayayi, So yake ya hada Sunnar mazon Allah S.A.W. tsakanin mutum biyu wanda yake hango babbar Alkairi cikin Al'amarin. Afili Cewa yayi Kausar mu hada guiwa mu hudu ni dake da Nazir da Leemah Mu hada Yazeed da Feenah aure Nasan Inno Zata Kara mana hikima shiyasa na fada Mata. tunani Kausar take ya'Akai feenah ke Soyayya da Yazeed bayan Feenah Sam Bata jituwa dashi, Kawai nasan Yusuf ne keson hada wannan Auren,toh komadai yayane nima Zanyi farin ciki da hakan Tunda ba karamin dacewa feenah tayi da yazeed ba....kikai Shiru Sweetheart! Ba Shiru Nayi ba naji dadi hakanne matuka Kuma Zamusan yanda zamuyi. Inasonki my kausar kinada fahimta. Murmushi tayi tace kamarka ba tunda kaine ka kawo zancen. Yusuff saida ya kwashi lokaci mai tsawo tukun yabar garin zariya kan Cewa jibi Zai turo iyayenshi. ππππππππ YAR LESBIAN CE ππππππππ By Nadeeya Mohd Ahmad (πWhatsapp: +2347010902548 http://arewapost.tk πWhatsapp: +2347010902548 http://arewapost.tk πNadseerπππππ) dedicated to Xaynab Ummu mahbub Page.....32 Bayan komawar Yusuf kaduna yasanar da mahaifanshi Kamar yanda Sukayi da Mahaifin kausar. Iyayen Yusuf Sunyi murna matuka dan dama farin cikinsu Ayanzu bewuce Suga Auren Yusuf ba. Dan haka Ayaune Kwana biyun da Yusuf yace ma Iyayen Kausar tacika. magabatan Yusuf Sunshirya tsaff Zuwa Zaria Ciki harda Abba Mahaifin Yazeed, dashi yazeed din kanshi har Nazir ma wanda Sakon ya isar mishi. gidan Alhji Hafis Suka yada Zango inda Aka taresu da girmamawa da Mutumci. Saida Aka tanada musu Abubuwan motsa baki daga bisani Abban yazeed yafara magana. toh kamar yanda kuka Sani munzo garin Zaria ne dumin bukatar da kuka nuna game dacewa yadace Yusuf ya tura iyayenshi, Toh Alhmdullah gamu munzo kuma Muna Shedar Yusuf mutumin kirki ne mai hankali da natsuwa. Dan haka muna nema ma Yusuf Auren Kausar la'akari dacewa ta fito daga gidan Mutumci, idan kun Amince da Hakan. Uncle din kausar ne yayi gyaran murya yafara mgn. Alhmdllh Muna matukar farin ciki daku domin munyi maraba da Yusuf tun lokacin da yazo da farko. dama ba wani Abu yasa mukaci ya turo iyayenshi ba saidan Hakan Sunnah ce kuma Al'ada ce....Sannan idan kun Aminci Za'a daura Auren Kausar da Yusuf Ayau din nan Sabida mahaifinta tafiya ta kamashi Zuwa kasar masar na tsawon Shekaru biyu, yana Son yaga daurin Auren yarshi Saikuma yanayin karatunta ya Rage da Saura, Dan haka ya yanke hukunci idan kun Aminci Adaura Auren yaran inyaso kausar din tacigaba da karatunta Amatsayin Matar Yusuf. Mahaifin Yazeed ya nisa yace Amma bamuzo da Shirin daurin Aure ba kuma Yusuf din besan haka ba. Kawun Yusuf ya kalli Abban yazeed yace Ahmad Ina ganin ba matsala tunda Shedune Ake bukata duk gamu A daura Auren kawai idan yaso lokacin dazata Kammala karatun Nata idan Sunada Ra'ayi saisuyi Shagulgulansu. toh madallah Hakanma yayi Abba ya fada. Sudai Nazir da yazeed mamaki kawai Suke wannan Wani irin Aurene lokaci daya. take Aka umarci Yazeed daya kira yusuf ya Sanar dashi domin Sadaki. Kiranshi yayi ya Sanar dashi duk yanda Akayi. Murna Awajen Yusuf bata misaltuwa, Umurtar yazeed yayi daya bada dubu50 Amatsayin Sadaki. Hakan kuwa Akayi take Aka daura Auren Yusuf da Kausar bisa Sadaki dubu50 lakadan ba Ajalan ba. Haka kowa yatashi yana farin ciki Cikin Ranshi. Sun yake Shawara Kausar Xata cigaba da Zama A gida Har Xuwa lokacin dazata Kammala karatu koda da Sati daya ne Sai Ayi Shagalin Biki Akaita dakinta tunda Yusuf bekarasa gininshi ba. Ahaka Suka hau motocinsu Dan komawa garin kaduna. Suma Sauran mutanen yan Uwan Mahaifin Kausar Sun tashi Suna murna Ahaka babban parlon ya Rage Saura Mahaifin Kausar, tashi yayi yashiga Cikin gidan A parlo ya Samu Sara Hajiyar Kausar da murna ta tareshi. Yana Zama yamata bayanin duk yanda Akayi da yan'uwan Yusuf. kallonshi Hajiya Sara tayi Yanzu Alhji kana nufin Kausar Matar Aurece? Eh ko baki farin cikin Hakan bane? Ahhh nayi farin ciki Sosai mana Alhji kawai dai yaza'ace Aure irin wannan ba wani Sha'ani. Hakan bazai Hana idan ta gama karatu kuyi duk Abinda kukeso ba Alhji ya fada yana tashi ki kiramun Kausar din.tashi Hajiya tayi ba'afi minti3 Suka Shigo parlon da Kausar...Xama tayi Akasa kusa da Hajiya tana fadin Gani Baba. Kausar Abun farinciki ne yasamu, Abaya kinata korafi Akan munki Aurar dake Toh Alhmdllh dama Ance mahakurci mawadaci, Ayau na daura miki Aure da yusuf mijin da kika xaba Amatsayin mijin Aure Ina fatan Zaki farinciki da Hakan, domin ni bana kasar nan Zaki Kammala karatu, Shiyasa na yanke Hukuncin Nan domin Nasaki farin Cikin dana dade Ina fatan kaiwata lokacin dazan Sakaki Shi. Zaki Xauna A gida Zuwa jibi dazaku koma karatunku, idan kika kammala kika dawo Koda da Sati daya ne Sai kuyi Shagali Akaiki dakinki, da fatan Hakan ya miki? Kausar da tunda Mahaifinta yafara magana take Surutai Cikin Ranta wanda ita kadai tasan me take fada, dago Kai tayi tace Eh Baba Naji dadin Haka Allah yakara girma. Amin Alhji ya fada yakara mata da yan Nasihoyi ya tashi yabar parlon. tashi tayi takoma Kan kujiran, jikin Hajiya Sara ta kwanta tana Raira kukanta. Saida Hajiyar tata Taji Abun yayi yawa tukun tace, kin isheni da kuka ko bakya Son Yusuf dinne? Cikin kuka take mgn Mamah inason Yusuf, kawai Nasihar da Baba yamun yasani kuka, Sannan Mamah ina kara nadama Akan Abinda na Aikata Abaya, jiya danace miki Zani Asibiti Mamah kinsan mai Dr ya fada mun? girgixa kai mahaifiyarta tayi tace Aa. Mama Cemun yayi inada infection! ya kamani da yawa, Sannan ya fadamun Hanyoyin da'ake kamuwa dasu, tabbas Hanyoyin daya fadamun harda idan Kana Aikata Lesbian Kana wasa da yatsa, kuma nayi Hakan da khady, Sannan ya fadamun mace Na'iya komawa dis virgin ta hanyar Hakan. mama yacemun infection yana hana haihuwa Shine babban Abinda yafi daga mun hankali,inason yara! Mazan yanzu Suma idan baka haihuwa wulakanci Suke maka, bama hakaba Sam baka Samun kwanciyar hankali wajen yan'uwanshi da Mahaifiyarshi. Narasa yanda Zanyi mama Sam be dace yusuf ya Aureniba Domin Ni din baxan bashi farin Cikin daya dace dashiba, Naso nafada mishi Abunda na Aikata kamin na aureshi mama yanzu nasan tabbas idan yaji Sakina Zaiyi kuka mai karfi ya kwacemata takasa karasawa. Kankameta Hajiya tayi tana tausaya ma yar tata cikin Ranta tace tabbas nayi Sakaci, Na takema y'ata Hakkinta A baya duk dacewa Aure lokacine Amma nima na Aikata babban kuskure gashi najawo ta fada Aikata mummunan Abu ina Murna ta Bari yanxu ga Sakamakon Abinda ta aikata nan. Afili cewa tayi ya'isa Kausar kinga Shiyasa ko kadan ba'ason Asab'ama mahallici domin duk maiyin hakan watarana Saita kife dashi, Amma tunda kin tuba Allah ya gafarta miki insha Allah. Yanzu wannan kaddarace ta Sameki, kin Aikata kuskure babba kausar Amma kisani Allah SWT shi yasan Abinda ke boye Ki Saka Aranki Zaki haihu kamar kowacce mace.kuma ba Lallai kinzama dis virgin ba, Abinda nakeso dake wannan yakara Xama Horo Kan Abinda kikai Abaya. Sannan Idan kinga Zaki fada ma Yusuf dinne kifada mishi ai yaron yanada Hankali Xai fahimta.maganar Infection Ayau Xamuje Islamic-Chemist din Chan dake kusa damu ya hada mana magungunanshi. Ni matsalata yanzu gyaran jikin Ki Anje Anwani daura Aure tun yanzu. Amma Shima Bari Akwai Wasu Abubuwan daxan baki idan kinje Skul din lokacin dakike da lokacin Kanki Sai kiyi Amfani dasu Akwai nasha dana Turare duka. Gyaran jikin idan kikadawo Sai Amiki. Idan yaso tarewan Sai Akaishi Zuwa Sati biyu domin a gyara munke Sosai. kuma yusuf din Ko Zuwa Yayi dubaki Kada Kibari ya kusanceki duk da nasan ma Akwai Su feenah Adakin kinji dai na fada miki kibari har Sanda Zaki tare. Kausar magan ganun mahaifiyar ta Su Suka Sanyaya mata rai domin ta yarda dacewa Hajiyarta Xata tsaya wajen ganin ta magance mata damuwarta. toh Hajiya insha Allah nacire damuwa Araina.Allah yamiki Albarka Kausar dita.Amin hajiyata. daga Haka Kausar ta tashi tashiga Ciki. Leemah ce Rike da waya da Alama kokarin kira take....Hello! Feenah Kinji Abinda nakeji kuwa? Daga bangaren Feenah cewa tayi besty mekenan? Yanzu Naji Su Abba Suna magana wai Andaura Auren Yusuf da kausar Leemah ta fada! daga inda Feenah take Ido ta fiddo waje tace Nimafa Naji yaya Nazir yana maganar kausar da mum Amma Ni bankawo da Kausar Akeba, wai dgske Kausar Aure tayi Kenan. Leemah dariya tayi tace toh gashima Abba na maganar Aikuwa Kinsan gsky ne. Ajiyar Zuciya feenah tayi tace Wannan Aure Kamar Angaji dakai! No ba Haka bane feenah wai Babanta keson yaga Auren yanzu kuma tafiya ta kamashi, but Za'ayi bikin daga baya Sukace. Koda Naji Amma Anya lfy Kausar bata kiramu ta fada mana ba? Feenat Nasan lfy qalau Amma inaganin tana Cikin damuwa ne, mai Zai hana mushirya gobe muje Zaria dagachan Saimu huce Skul jibi. Hakan yayi Leemah bari Nafada mawa mum ko? Ok Nima Bari nasanar da Mamy Sai goben. Ok besty bay. Yusuf gaba daya yau Cikin farin Ciki yake Wanda baya misaltuwa. Godiya kawai yake ma Ubangiji Akan wannan Sabuwar Rayuwa daya shiga Ayau. Daga bisani Sashin iyayenshi yashiga Suma yamusu gdy Sosai Nasiha Sukaimishi Akan Zamantakewar Auratayya duk dacewa Tarewar bata zoba, Haka yarinka musu gdy yana farin Ciki. Dr yazeed Dr khaleed Captain Nazir da Sauran Abokanshi Kasa hakuri Sukai Saida Suka hada yar walima na taya Abokinsu murna da farin Ciki. Bayan Sun gama ne kowa ya koma gida. Kwance Yusuf yake yana Kara gdy ga Allah yana farin Ciki mara misaltuwa. daga bisani ya dauko wayarshi yashiga Kiran Kausar ba'a wani bata lokaciba ta daga Cikin Sanyayyiyar Muryarta wanda tasha kukanta ta gaji. My wife lfy najiki so silent? Lfy qalau Sweetheart Kaina kedan Ciwo. Oh Sorry wifey! Tnx sweet. Ajiyar Zuciya yusuf yayi "How do you feel same's Happiness today my Kausar?" Shiru tadanyi daga bisani tace inajin farin Ciki better than you feel my yusuf. murmushi Yusuf Yayi yace dandai kowa kanshi yasani danace miki bantaba Shiga farinciki irin na yauba. I love you my Kausar jina nake Kamar na daukoki mukasance tare Ayau din nan. Wata Kunya yaba Kausar Rufe Ido tayi tace Nidai kabari.dariya yayi yace yau kuma kunyan ta karu kenan, ina nan Zuwa gobe Zancireta gaba daya. Nidai kada kazo fita Zamuyi da Hajiya. Lallaibaki isaba ai baki tambayeni Zaki fita ba dan haka kishirya ina nan Zuwa maybe ma na daukeki A goben! Marairaice fuska kausar tayi Cikin Ranta tace fitama Saika tambaya wannan duk yana Cikin biyayya Aure tabe baki tayi tace toh yanzu bashine Nake fada maka ba. dariya yanayin yanda tayi maganar yaba Yusuf yace ok na Amince kije but nine Zan maidaki Skul jibi kinyarda? da Sauri kausar tace na yarda Sweetheart. Haka sukaci gaba da zuba Soyayyarsu Awaya Inda kausar keta faman xuba ma yusuf shagwama Shikuma yana biye mata, Ahaka damuwar da take ciki tadan kara raguwar mata. daga bisani Suka kashe kowannesu da farinciki Cikin Zuciyarshi. bangaren Yazeed yau kawance yake duk Ji yake inama Ace Shine yayi Auren nan Ayau babu Abinda zai hanashi daukar matarshi. Ai illan kananan yara kenan kayi aure kamata yayi kaima ka kasance da matarka kamar yanda kowani Ango ke kasancewa Amma ina Gashinchan Zaiyi bacci kamar yanda kowani mara mata keyi, Allah ya kara mishi ma ai.maybe harnazo nayi aurena Shi be tare da matarshi ba. Ni yazeed wace macece ta dace da Rayuwata? wacece wadda zata iya daukan Nauyina gaba daya, Allah kabani mata ta gari mai sona kona huta da zaman gidan Nan da wannan fitinanniyar tshohuwar. Haka tacigaba da tunaninshi Har bacci yayi gaba dashi. Hakan take Awajen Nazir shima gaba daya tunanin ya lullbeshi inama shi da leemah ne aka daura ma aure Ayau. Kai danayi farin ciki wannan Al'amari, Amma nima very Soon. Haka yacigaba da tunani daga karshe ya kira Leemah Sukasha Soyewarsu. [15/12, 19:42] Hussaini Atk: ππππππππ YAR LESBIAN CE ππππππππ By Nadeeya Muhammad Ahmad (πWhatsapp: +2347010902548 http://arewapost.tk πNadseerπππ) dedicated to Xaynab Ummu mahbub *this page is for you pretty Salma Abbas thanks for Love nd Sport* Page....33 Washe gari tunda Safe Su feenah Suka Shirya domin Zuwa Zaria. Yazeed Mamy tasaka Zai kaisu Dan haka Tunda ya tashi yake Cika yana batsewa Dan ya gane Inno ce duk tasaka Akace Shi Zai kaisu. Karfi8 Na safe Feenah tagama Shiri tayi kasa inda Su Mum ke Zaune. Tana karasawa ta gaidasu mum Na Shirya Haruna Zai kaini gidansu Leemah daga Chan Zamu wuce. Kallonta mum tayi da fara'a my feenah ku kula da kanku kunje. Insha Allah mum. dad ne yace Ummi daga Chan Zaku wuce Skul ne naganki da kaya Haka? Eh dad Sabida gobe ne Zamu koma Shiyasa mukace Xamuhuce daga Chan. Toh Allah ya tsare Ku gaba daya. Amin daddy. Aunty feenah Nima Zanje Zaria din! Mubeena ta fada tana marairaice face Alamar kuka. My Mubeena Sorry wajen Mai Allura ne kuma ba'a zuwa da yara Zan Siya miki Abun dadi. Mubeen ne yayi Saurin cewa nima Aunty feenah kisiyamun. Ok big boy I will buy for you. Yaya Nazir ne ya kalleta yace Tashi na kaiki gidan Su Leemah din. Oh yaya Nazir Nazata Haruna ne Zai kaini? Idan ba kyason na kaiki Shikenan, dama danna aiki Haruna yasa nace kizo na kaiki. Kokuma dan Wata manufa taka ta daban ba mum ta fada tana Harararshi. Sosa kai yayi yana fadin Aa fa Mum. Tashi kutafi dad ya fada yana murmushi. Atare Suka jera Xuwa inda motar Nazir take. Shiga Sukayi yayi hanyar gidan su Leemah. Sister kinason da Ki hanani ganin baby na ko? Kai yaya Nazir Nifa bansan ganinta kake son yi ba. Kokuma dai kinajin Haushi bakida Saurayi ba! Tamke fuska feenah tayi tace Habaa yaya Nazir saikace bakasan iya Adadin Samarina ba, Kawai nidai Dan yanzu na tsayar da Wanda Nakesone Shiyasa bana kula kowa. Oh Sister Sorry wayema kika tsayar dashi? Kabeer mana Feenah ta fada tana chuno baki. dariya Nazir yayi Cikin Ranshi yace wannan Sun Rainamu da yawa Suna Soyayya A boye yanzu kuma ta kawo Xancen wani daban. Afili Cewa yayi Sister kamar fa bakwason juna keda Kabeer tunda banga kuna waya ba hasalima ban taba ganin yazo wajenki ba. Tabe baki feenah tayi yaya Nazir ba Lallai Sai munyi waya dashi ba ai, Kawai Xamuyi dai Aure. kallonta Nazir yayi Sister Kenan Aurenshi kawai Zaki badon kina Sonshi ba? dafe kai feenah tayi Alamar ya isheta, yaya Nazir Cikin Zuciyata Ina Sonshi mana. Tunani Nazir yayi yasan idan ya kureta yanzu Saita mishi kuka dan haka yace Toh Shikenan Sister Allah ya Kaimu lokacin musha Biki. Amin yaya Nazir Na my besty. Murmushi Nazir yayi yace Sister Jiya din nan Sainaji dama Nida Leemah ne Mukai Aure na kosa na mallaketa Amatsayin mata. Toh yaya Nazir ba haryanzu kaki Sanar dasu mum ba maza dai wani yaje yaimaka Shigar Sauri. Kai sister kamar ya Shigar Sauri bayan Leemah ni take So? Yaya Nazeer misali wani yaje Yanzu yayima Abbanta magana yanasonta idan Abba yayi la'akari da yaron nada tarbiyya Zai iya ya Aura ma Leemah Shi, domin last time Naji yace idan bamu kawo miji Nida itaba Zai bamu Zabinshi. Tunani Nazir yadanyi Azuciyarshi gaskiyafa Feenah ke fadi yazama dole na Sanar da bukatata. Kayi Shiru yaya Nazir. Yes Sister Gaskiya kika fada, da nayi tunanin Nabari Sai kun karasa karatunne but yanzu Zan Sanar da dad kamin ya koma. Yawwa Hakan Shine daidai Feenah ta fada.daidai Sanda Suka karaso gidan Su Leemah.fita Sukayi Atare Sukashiga