Showing 27001 words to 30000 words out of 209154 words

Chapter 10 - GIDAN ARO na Sameena Aleeyou.txt

ka tashi kace ka yafe mun.. Nasan nayi maka laifuka da dama Abba, Abba dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barmu bazamu iya ba.. Maiyasa suka kad’e mun kai Abba na..”


Muryarsa ne ya katseta da da fad’in “Because they believe your father knows something shiyasa suka kashe shi Dan kar ya tona masu asiri..!”


Cak Ta tsaya da kukan nata sakamako sinkayo muryarsa da Tai... Ta d’ago rinannun idanunta ta sauk’esu tsaf akansa, zuciyarta na mata wani irin zogi take dubansa.. Take tsanansa ya ninku cikin zuciyarta..


Cikin kuka ta mik’e tana furta “This is all your fault.. Ku kuka jawo aka kashe mana Abbanmu.. Maiyasa bazaku k’yalemu ba.. Bamu San mutumin da kuke nema ba, bamu San komai akansa ba.. Mun sanar daku Iyakacin abinda muka sani.. Mahaifina Bai cancanci a kashesa mercilessly irin haka ba... Just leave us alone already.. Ka tafi Dan Allah.. Kuje can ku nemi criminals d’in da kuke nema.. And leave us in peace..!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o had’ida zubewa saman gwiwoyinta..


Dubanta kurum yake yana jin zuciyarsa na masa wani irin k’una.. Yana duban yanda hawayenta ke zubowa da sautin kukanta had’ida rok’onsa da takeyi ya tafi ya k’yalesu suji da rashin mahaifinsu da sukai.. A hankali ya soma jada baya still idanunsa akanta..


Cikin sauri Mu’azzam ya juya ya fice daga gidan gaba d’aya yana duban yanda Sadiya ta zube saman gwiwoyinta tana kuka mai tab’a zuciya..


Har ya shige su Assad dake faman tattare bayanai daga wajen mutanen unguwa basu lura dashi ba.. Sautin tashin motarsu kurum sukaji.. Assad ya saki baki yana dubansa.. Maleeka dake faman rubuce rubuce itama baki sake take duban Mu’azzam d’in..


A yanda sukaga ya kwashi motar sunsan komai ka iya faruwa..


Assad ya girgiza kai yana mai furta “Oh no..! Mu’azzam mai kake shirin aikatawa..?”


**


Ko parking mai kyau bai ida ba ya nufi ofishin Chief Inspector Jaja... A lobby ya iske Chief tareda wasu abokan aikinsu ‘yansanda suna tatauna wani matsalan.. Mu’azzam duban Chief kurum yake yana kuma sinkayo kukan yarinyar da yanda take fad’in an kashe mata mahaifi ba tareda ya aikata laifin komai ba.. Fuskar yarinyar yake hangowa cikin idanunsa yanda Ta duk’a tana zuban hawaye.. Baiyi wata wata ba yana isowa ya dunk’ule hannunsa yakai ma Chief naushi maiji da lafiya a Hanci wanda saida takai Chief har k’asa..


Ba Chief da yaji sauk’an naushin kaman a mafarki ba harta sauran ‘yansandan saida suka tsaya suna duban Mu’azzam cikin tsananin Shock Dan kaf d’insu babu wanda yaga zuwan Mu’azzam sauk’an naushin kawai suka gani..


Mu’azzam ya cakumo wuyan Chief yana fad’in “Lets end it now.. You better tell me waye kake karewa.. Ka sanar dani Manzo Jaja.. Waye kake karewa.. Do you know how many innocent lives are stake here.. Shin kasan rayuka nawa ka jefa cikin garari da gurb’atacciyan zuciyarka.. Tell me.. Tell me Chief Manzo Jaja..!!” Yanda yake jijjiga Chief dole ya baka tsoro..


Wane irin fincika Chief yai yana tsananin huci yayinda sauran ‘yansandan suka janye Mu’azzam daga jikin Chief..


Huci kurum Chief yake yana nuna Mu’azzam da ‘yar yatsa ga bakinsa dake fidda jini sabida naushin da Mu’azzam d’in yai masa “You’ll pay.. You’ll pay for this..!” Ya k’arashe yana mai shigewa ofishinsa cikin tsananin b’acin rai..


Daidai lokacin su Assad suka k’araso duk a birkice suke..


Yanda Assad ya hango Mu’azzam yasan mai aukuwa ya auku.. Saurin k’arasawa yai wajen abokin nasa dake faman yarfe hannuna wanda ya naushi Chief dashi.. Hannun Mu’azzam d’in kawai Assad ya duba da yanda yake yarfe hannun nasa ya fahimci cewa mai aukuwa ta auku..


Assad ya k’araso yana duban yanayin mutanen dake wajen yanda kowa yasha jinin jikinsa..


Dafa Mu’azzam d’in dake zaune saman kujera ya kifa kansa k’asa yai.. Ko baa ce kasan zuciyarsa ce ke tafarfasa


“Can you tell me now.. What really happened here..?” Baikai ga basa amsa ba sukaga ana mik’owa Mu’azzam d’in Doguwar takarda cikin envelop.. Saida ya dubi mai mik’o masa takardan kafin yasa hannu ya amsa takardan ba tareda ya amsa tambayar Assad ba..
Lokaci guda ya shiga warwareta.. A hankali ya lumshe idanunsa Dan yasan za’a rina haka.. Suspending d’insa akayi har na tsawon makonni biyu... Cikin sauri Assad ya amshi takardan yana karantawa..
Dafe kansa kurum Assad yai yana mai fuzar da fuci..


Cikin tsananin b’acin rai Assad ya soma fad’in “You see.. Kaga abinda nake fad’a maka Mu’azzam.. You never listen.. You’re so stubborn Mu’azzam.. Yanzu ga irinta nan kaja an dakatar dakai..”


Bai k’arasa sauraron Assad ba ya mik’e yai ficewarsa waje.. Assad ya biyo bayansa yana ci gaba da magana cikin tsananin b’acin rai..
Idan jacket d’in dake jikinsa ya amsa shima zai amsa.. Yanda motarsa ke ajiye ya isa ya shige, har lokacin Assad na masa magana yana k’ok’arin dakatar dashi suje dubawa Chief hak’uri ko rage masa tsawon wa’adin suspension d’in ne ayi amma ko ranka Assad baiba..


Tuni ya shige Mota ya fuzgeta.. Yana driving amma kukan yarinyar da rok’onsa da take su fice masu a rayuwa bai daina Yawo a kwanyarsa da dodon kunnuwarsa ba.. An kashe mata mahaifi dik akan binciken da yake na neman gaskiyar mutuwar ‘yaruwarsa.. A hankali ya lumshe idanunsa yana mai jin motar bayansa na danna masa horn.. Cikin sauri ya ware idanun nasa yana k’ok’arin saita kansa Dan k’iris ya rage baiyi causing accident ba..


Traffic ne ya tsaidasu, a daidai k’ofar wani kanti yake hango k’aton takardan Sanitary pad irin na advert d’in nan.. Lokaci guda ya tuna sanda Ta jefe shi da gidan abin.. Nan yake tina farkon had’uwarsu.. Yayi nisa duniyar tunani yaji ana masa horn motar bayansu alamun traffic light ya basu koren wuta..


Lokaci guda ya soma tafiya cikin tsanaki.. Bai zarce ko Ina ba Sai gidansa.. Saida ya iso gidan ya tina ashe su Safeenah na gidan ya kwance masu karnuka..


Ya ida shigo da motarsa yai parking a gefe Karnukan har sun koma gefe, suna ganinsa suka taso suna shinshina k’afarsa.. Yakai dubansa ga motar Safeenah, a hankali ya janyo chain d’in dake d’aure wuyan karnukan ya maidasu d’akinsu.. Lokaci guda ya isa jikin motar Safeenah..


Ta cikin glass yake dubansu yanda sukai laushi, d’an kad’an suka zube glass d’in ta d’an sama kad’an yanda iska zaike d’an shigo masu kad’an..Safeenah kam kamar ma bacci tai dan azaba, tana tak’ure jikin seat ga bushesshen hawaye kwance saman fuskarta..


Meema ce batai bacci ba amma har lokacin hawaye ne cikin idanunta.. Tana ganinsa ta mik’e wani kukan na zuwa mata.. Saman gwiwoyinta ta duk’a nan kan seat d’in, Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana fad’in “Ya Mu’azzam dan Allah kayi hak’uri.. Wllhi na tuba bazan sake ba.. Dan Allah ka k’yaleni na tafi gida na rok’eka...” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka..


Cikin ransa yace ashe k’aryar rashin kunya kike.. A fili kuwa bai furta komai ba.. Kukan Meema ya tada Safeenah.. Tana ganin Mu’azzam ta wani zabura ta mik’e zaune.. Take ta fashe masa da wani irin kuka ba tareda tace komai ba.. Saida tai mai isarta kafin ta tsagaita, cikin rawar murya take fad’in “please take us home..”. Ta fad’i tamkar zata kuma kurma wani ihun..


Basu baya yai kafin ya ciro wayarsa cikin aljihu.. Dialing layin driver d’in gidan yai ya sanar dashi ya shigo Cab yazo ya samesa..


Jim kad’an kuwa driver d’in ya iso da shike gidan nasu babu wani tafiya sosai tsakani..


Car keys d’in motar Safeenah ya mik’a masa bayan ya iso yace ya kaisu gida. Driver d’in ya amsa cikeda girmamawa kafin ya bud’e motar ya shige mazaunin driver.


Abin sosai ya sosa ran Safeenah watau bazai kaisu gida ba dikda yanda ya basu azaban nan sukai Laushi saidai ya kirawo driver ya kaisu.. Tana fama da kanta bazata iya tanka masa sannan wani sabon shakkarsa ne ya d’arsu a zuciyarta hakan yasa batace komai ba Sai mutsuke ragowar hawayen idanunta da take.. Ita dai Meema bata damu ko uban waye zai maidasu gida ba. Burinta kawai ta fice daga gidan ta ganta a gidan mahaifinta..


Suna isowa gida kai tsaye upstairs suka haye a jikace dan dama gidan ba kowa daga ma’aikata sai Mommy da Kiki. Su Daddy da Musaddiq da Inne harmada Aunty Nurah sun tafi Fufore a jiya.. Mommy ce kawai ma a gidan Sai ma’aikata dan Kiki tana WAEC Lesson zatayi trial a SS2.. Meema kuma dama jiran admission d’inta take ya fito a UK amma bayan Mommy taji yanda Safeenah ta watse da mazan turawa ta fara shakkun Barin Meema ta fita karatu waje.


Ummati Dattijuwa cikin ma’aikatan gidan ne ta had’u dasu zasu haura sama a jigace. Tana tambayansu lafiya suke ko iya amsata basayi Meema kam ma da rarrafe take k’ok’arin shigewa d’aki..


Ummati ta girgiza kai kad’an ta shige sanar da mahaifiyarsu.. Domin kuwa babu lafiya tinda har Meema da Safeenah ne zata masu magana basu darara mata tsawa ba.


Koda Mommy ta taddasu Safeenah ke labarta mata duk abinda ya faru.. Tamkar ta rufe Safeenan da duka dan takaici haka Mommy taji.. Ta rasa wace irin wauta ne kan Safeenah.. Wai har Meema ce zata bata shawari ta d’auka.


Mommy tai k’wafa tana duban Safeenar cikeda takaici “Ya miki kyau ai.. Ki godema Allah da bai baki takardanki tin a titi kafin ki tare gidansa ba.. Banda shashanci da dolanci irin naki ta yaya zaki bisa har wajen aikinsa kici masa mutunci kici ma abokiyar aikinsa mutunci without any solid evidence..”


Cikin kuka Safeenah ta katseta da fad’in “Mommy I’ve proof... Sanitary pad d’in is enough evidence.. And Mommy you should have seen her face sanda nake cin mutuncinta ita karuwar.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba cin amanata yake da Ita...”


Dak’uwa Mommy ta dunk’ula mata tana fad’in “Kimin shiru kafin na tashi na tattakaki a wajen nan.. Banda ke shashasha ce sokuwa, idan ma da gaske cin amanar naki yake ta haka ne zaki samu gaskiyan lamarin..? Ta haka ne zaki kare auren naki..? Wannan dolancin da kikayi bashi zai hana ya fasa abinda yake ba idan ma yanayi d’in..Kusanci ma zaki K’ara masa da ita.. Yanzu haka zaije ya lalasheta bayan ya gama cin k’aniyarki.. Kinga wa gari ta waya..”


Safeenah tai shiru tana duban mahaifiyarta tana jin zuciyarta na mata k’una. “Mommy yanzu ya zanyi..?”


“Ya kuwa zakiyi banda ki k’yaleshi har ya sauk’o kafin ki basa hak’uri kan abinda kikai..”


A zabure take duban Mommy “Mommy shi fa ya mun laifi amma kike cewa na basa hak’uri..” Ta shiga bubbuga k’afafu tana turo baki tana kuka take fad’in “Wllhi dama an jima ana nuna wariya gidan nan.. Daga ke har Daddy bakwa tab’a ganin laifin Mu’azzam, dik abinda yayi daidai ne wajenku.. Wllhi Mommy this is not fair..!” Tana maganganun tana kuka ta shige bathroom..


Tsaki Mommy tai cikeda takaicin ‘yar nata.. Ita batasan ba dan komai take so Ta auri Mu’azzam ba sai dan watarana Fortune d’in Mu’azzam d’in wanda Mahaifinsa ya mutu ya bar masu ya dawo hannunsu.. Mahaifin Mu’azzam shike Babba cikin yaran mahaifinsa.. Su Uku ne yaran Jauro Gamji, Abubakar wanda shine Babba kuma shine mahaifin Mu’azzam da marigayiya Ikram, sai Marwan Wanda shine mahaifin Safeenah Musaddiq Maryam(Meema) da kuma Karimatu (Kiki). Sai Salman wanda shine autan Inne kuma shine cikon na ukunsu.. Shi yana zaune ne a can Fufore dan kula da gidan gonar su dake Fufore d’in da kuma Kampaninsu na GAMJI MEAT FACTORY dake Adamawa.. Kaman yanda Daddy ke kula da Kampaninsu na GAMJI DIARY DISTRIBUTION FACTORY dake a birnin tarayya Abuja.. Gidan Gonar da kakansu Jauro Gamji ya mutu ya bar masu shine yake samar da nama da kuma madaran da companies d’insu ke producing.. A halin yanzu Uncle Salman shike kulada Gamji Meat Factory dake Adamawa wanda a baya mahaifin Mu’azzam shike kula dashi. Sannan shi Uncle Salman d’in shi ke kula da Babban gidan gonar nasu dake garin Fufore. A can gidan gonar suke zaune gaba d’aya dan mahaifinsu saida ya k’era gini maiji da lafiya a cikin gidan Gonar wanda tafiya mai d’an nisa zakai kafin ka isa ginin sabida tsaban girman da gidan gonar kedashi bama zakai tunanin a gidan gona kake ba idan ka shige cikin Mansion d’in.. Shuka da shanu suna cen gefe yanda ake kula dasu..


Uncle Salman da iyalansa harma da Inne a nan gidan Gonar suke zaune.. Uncle Salman yanada mata guda d’aya mai suna Shema’u tareda yaransu guda uku duka mata. Babbar zatai tsara da Meema sai sauran k’annenta guda biyu wanda Twins ne...
A lokacin da mahaifinsu Mu’azzam ya rasu Uncle Salman yaso a cire kason Su Mu’azzam da k’anwarsa Ikram a basu tinda dole sunada kaso a both companies d’in.. Kason mahaifinsu.. Ya zaman babu sauran kason mahaifinsu cikin dukiyar.. Babu yanda Uncle Salman baiba Daddy yak’i amincewa da hakan.. Yace wannan kasuwanci ta ahalinsu bazai tab’a yuwa a cire kason Su Mu’azzam a basu ba dole za’a ci gaba da juya musu dukiyarsu ba tareda an bari dukiyar ta salwanta ba, idan shi Salman bazai iya kulada dukiyar ‘ya’yan d’anuwansu ba Wato Mu’azzam da Ikram shi Daddy zai kular masu dashi zaici gaba da juya masu har lokacin da zasu buk’ata.. Koda Mu’azzam ya girma Uncle Salman baisan Ina Daddy ke kai kud’ad’en Mu’azzam d’in ba amma yasan duk budget da za’ai sai an cire nasu.. Yasan har wannan lokacin Mu’azzam da ‘yaruwarsa harma da mahaifiyarsu sunada kaso cikin dukiyarsu.. Wannan kenan..


**
A b’angaren Mu’azzam kusan kwana yai yana tinanin Abinda ya samu mahaifin Sadiya. Baisan dalili ba amma tinanin nasa mahaifin ne ya fad’o masa..Mahaifinsa da ya rasa a Meat cold Room wanda ya shiga inspecting freezer d’in tsautsayi da ajali ya ritsa dashi a can Meat Distribution Factory d’insu dake Adamawa.. Mahaifinsa yayi stucking a cikin meat cold room wanda har yayi ahalinsa sai gawarsa aka cire.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna irin mutuwar da mahaifinsa yayi, lokaci guda ya tina jarabawa na cuta da mahaifiyarsa ta had’u dashi ya kuma tuna rasa ‘yaruwarsa Ikram da yayi... A hankali ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa biyu.. Babu abinda yake so a halin yanzu kaman ya kasance da mahaifiyarsa.. Sosai yaji yana so ya tafi Fufore.
Bazai mance sanda aka ciro gawan mahaifinsa da ya sandare da k’ank’ara ba, kwanciya yai saman gawan mahaifin nasa yana kuka kaman dai yanda Sadiya ta kwanta bisa gawan mahaifin nata itama tana kuka..


Bazai tab’a mance kalaman lallashi da mahaifiyarsa ta fara furta masa ba ‘Kai hak’uri Mu’azzam, Duniya GIDAN ARO ce yanda mukazo cikinta kaman bak’i haka wataran zamu tafi mu barta.. Kayi hak’uri kayima Daddynka addu’a muma duka ma tafiya ne idan lokaci yayi’


A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kafin ya mik’e ya nufi motarsa..


Wajajen k’arfe shabiyu da rabi na dare ya shigo gidan. Baibi takan kowa ba ya nufi side d’insa ya soma shirya kayansa jirgin Washe gari yake so yabi zuwa Adamawa.






SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*








*11*










*©️Sameena Aleeyou...*












Tin farar safiya Safeenah ke kitchen, duk abinda tasan Mu’azzam naso shi take instructing ma’aikatan kitchen d’in su girka.. Su kansu sunyi mamakin ganin Safeenah a kitchen dan kitchen ba wajen zuwanta bane.. Ko mi Suka dafa sai ta tasting, idan ya mata tace yayi idan bai mata ba tayi fatali dashi tace su sake girka wani.. Gaba d’aya sun gundura da kasancewarta a kitchen d’in.. Saida ta tabbata komai ya kamata kafin ta haura sama sauri sauri ta shirya dan bataso ta makara har Mu’azzam ya fice aiki basu had’u ba. Tasan shi da respecting time musamman lokacin aikinsa sam bai wasa da abinda ya shafi aikinsa, hardly kaga ya makara saidai dan ajizancin d’anadam.


Tasha kwalliyarta sai watsa k’amshi take ta nufo k’asa, ta kuma duba dinging area ta tabbatar an jera komai yanda ya kamata kafin ta zauna saman kujera guda tana mai juya k’afafu d’aya bisa d’aya..Lokaci zuwa lokaci take duban agogon bango dake manne cikin parlorn tana mamakin rashin fitowar Mu’azzam d’in.. D’an mik’ewa tai ta lek’a window tana tinanin kodai bai dawo gida jiya bane.. Amma ganin motarsa da tai a parking lot ya tabbatar mata ya dawo gidan.. Ta d’an fuzar da fuci a hankali tana mai kuma duban agogo.. Toh kodai ta dubasa a d’akinsa ne..? Ta tambayi kanta tana mai d’an tsuke fuska.. Lokaci guda kuma ta tina yanayin da suka rabu jiyan.. Anya ita ya kamata ta fara dubasa.? Toh amma idan bataje ba tasan yana iya ficewarsa without checking on her.. Ta kuma fuzar da huci kafin ta yanke shawrin dubasa a d’akinsa.


Ta d’auki lokaci tsaye bakin k’ofarsa tana tinanin yanda zasu kwashe.. Sai tazo kaman zatai knocking sai kuma ta fasa.. Ji tai kaman Ta juya Ta koma amma sai taji bazata iya ba, tana tsananin son Mu’azzam kuma abinda take k’ok’arin Yi kare aurensu take.. Tai k’ok’arin saita kanta had’ida d’ago hannunta da zummar knocking, saidai kafin takaiga k’onk’osa k’ofar taga ya bud’e k’ofar.. Tai tsaye tana dubansa, Shima d’in Ita yake duba saidai sam babu walwala saman fuskarsa.. Kallon mamaki take masa dan gashi dai cikin shiri da alama fita zai amma ba shirin da ya saba Fita office ta gansa ciki ba, bai faye saka Tshirt ba idan zaije aiki saidai lokutan zafi. Most of the time suit yafi sakawa.. Red Armani shirt ne jikinsa da ya fito da yanayin suffar jikinsa sai wando cream chinos.. Tana cikin k’are masa kallon ne taga luggage d’insa gefensa.. Tai saurin d’agowa tana dubansa da mamaki..


“Where are you heading to.. And why are you with your suitcases.?” Ta tambaya cikin tsananin mamaki


“To the airport.” Ya bata amsa kai tsaye hannayensa duka biyu sakale cikin aljihu ya d’an turo k’irjinsa kad’an.


“Ban.. Ban gane ba..”


“Meye baki gane ba..”


“Airport fah kace.. Mai zakajeyi airport.. Wait idan akan abinda na maka jiya ne I’m here to apologize.. You can’t just leave..!”


Agogon dake d’aure tsinstiyar hannunsa ya duba kafin yace “Safeenah bani hanya, I want to catch my flight..”


Unbelievably take rolling idanunta, murmushin da za’a iya kiransa da murmushin takaici saman fuskarta “Seriously.. Are you leaving us to go live with her..”


Wannan karon cikin tsnanin b’acin rai yake dubanta “Don’t start.. Don’t even start Feenah..!” Yai maganar cikin rarrabewar kalamai. Lokaci guda ya janyo jakarsa ya matsar da ita gefe da hannunsa guda kafin yai shigewarsa..


Mutuwar tsaye tai tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login