Showing 51001 words to 54000 words out of 209154 words

Chapter 18 - GIDAN ARO na Sameena Aleeyou.txt

Amma ni koda wasa ban zaci Wai Alhaji zai d’aura idanu kanta ba...Yayi aurensa ni bazan hanasa ba ya auri ko wacece amma kam banda Sadiya k’awar Sabeera... Ina zan Kai wannan d’imbin bak’in ciki da tashin hankali ga uwa uba Sabeera taji komai..”


Ramatu ta tab’e baki tace “Rahina zama fah bai ganki ba, tashi zakiyi muje har gidansu yarinyar nan muci uban uwarta da kyau dan itace tsararmu ba d’iyarta ba.. Ki daina wannan simi simi d’in nan naki ki tashi ki karb’a ma kanki da yaranki ‘yanci idan kuma ba haka ba ki zuba ido ki zama ‘yar kallo cikin gidanki.. Kinaji kina gani yarinya ‘yar cikinki Ta k’unsa miki bak’in ciki. Keda gidanki yafi k’arfinki.”


“Ramatu sanin kanki ne ban isa na hana namiji son mata ba dan a halittarsu ne amma damuwar shine kar ya nemi na banza, yayi auren dan shine mafi a’ala tinda Allah ya huwace masa daman auren mace sama da guda. Sannan ni idan zai auren ya auro ko wacece amma tsakani ga Allah banda Sadiya.. Idan ni zan iya jura Sabeera fah.. Sabeera bazata iya jura ba.. Ni wllhi tashin hankalin da ‘yata zata shiga nake tunani.. Yaran nan fah bacci ne ke rabasu sanda suke makaranta kafin su tafi yajin aiki har karatu tare suke..”


Ramatu Ta katse Ta da fad’in “Ni dan Allah kin isheni, kin cika ni da surutun da babu gaira babu dalili.. Dik kin San da wannan shine kika d’add’agoni ko karin kummalo banyi ma mijina ba.. Dama Kinsan wa’azi zaki kirani kimin shine baki sanar dani tin a waya ba.. Ni wllhi indai hakane kar Ki sake neman shawari daga wajena.. Kije can ki k’arata da sanyin zuciyarki aita cutanki bak’in ciki ya turaki rami.. Idan kin canza shawri kya nemeni.. Ni Kinga tafiyata..”


Bata ida rufe baki ba sukaji kukan Sabeera na tashi Babanta rik’e da Ita yana fad’in ta gama rashin kunya daga yau..


A tare Maman Sabeera da Ramatu suka nufo parlorn.


Sabeera ta fad’a bayan mahaifiyarta a guje tana kuka.. Yayinda Babanta yaci gaba da aza babbar riga yana k’ok’arin ciro igiyar decoder yake fad’in “Har ni zakije ki wulak’anta.. Kije kici wa matar da zan aura mutunci sabida bakida hankali.. Yau zakiji a jikinki..”


Ramatu kaw yab’e baki saitin kunnen Maman Sabeera Ta rad’a mata“K’awata ni na wuce kafin mijinki ya had’a dani yace ni ce uwar zigi..”


Maman Sabeera da tuni Hawaye ya wanke mata fuska Ta tare d’iyarta tai tana fad’in “Wllhi bazan Barka ka daketa ba..” Lokaci guda ta tura Sabeerar d’akinta ta maida k’ofa ta rufe.. Tare k’ofar d’akin tai tana hawaye alamun bazata barsa ya shige ya daki Sabeera ba..


Sai sakin huci yake yana duban Maman Sabeera yana fad’in “Rahina ki bani hanya na koya ma yarinyar nan tarbiya.. Tarbiyar da kika kasa bata..”


Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke dubansa, lokaci guda take furta “Wane tarbiya kake magana..? Wane tarbiya ne zaka bata wanda na gaza bata..? Tarbiyar rufeta a gida ka hanata fita Ko k’ofa dan kana tsoron kar a lalata maka Ita Ko mai..?”


Da tsananin mamaki yake dubanta “Rahina kike fad’awa magana irin haka.. Kina cikin hankalinki Rahina..? Dan kawai nazo da batun zan k’ara aure sai ki nemi ki jefeni da sharri..!”


Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke fad’in “Ni ban jefeka da sharri ba, sannan ban tab’a zarginka da aikata abu maras kyau waje ba, na sani idan kana gida Kai nawa ne amma idan ka fice zaka iya zama na kowa idan ka zab’a hakan.. Saidai ka Sani yaran nan kanadasu.. Idan ka lalata na wani ko cikin Tandu kake saka Naka ka b’oye wllhi sai an rama irin abinda kayi ma na wasu akansu..”


Katseta yai da fad’in “Anya Rahina kina cikin hankalinki.? Ni kike yab’awa magana dan nace zanyi aure.. Toh bari kiji na fad’a miki Asabar d’in mai zuwa d’aurin aurena tareda Sadiya, Idan an kawota idan Kinga dama kar ki zauna..”


Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubansa hawaye basu daina zarya saman fuskarta ba “Aure kace.. Aure wannan asabar d’in.. Yarinyar da kak’i jinin alak’arsu da Sabeera shine zaka zago kace ita zaka aura nan da kwanaki biyu rak..” Tai maganar tana mai d’ago yatsun ta guda biyu hawaye na gangaro mata..
Cikin sanyin jiki Ta nufi d’akinta ta maido k’ofa ta rufe ba tareda ta kuma cewa komai ba, amma kam kaida gani kasan da zata samu ta fidda bak’in cikin dake k’unshe cikin k’irjinta ko ta hanyar kuka ne da Ta d’an ji sanyi cikin zuciyarta.


Tsaki Alhaji Isyaku ya buga yana fad’in “Aikin banza aikin wofi.. Ni ma na tsaya Ina miki bayani.. Idan na aurota idan kinga dama kar ki zauna a gidan.. Aure kuma babu fashi.” Ya juyo ya dubi k’ofan d’akin Sabeera yace “Ke kuma k’ofa na kumaji kin lek’a balle har kije kici mutuncin matata sai na aurar dake sadaka a masallaci..” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan fuu kaman zai tashi sama yana aza babbar rigarsa.


**


Sadiya na kwance saman gado ta kasa cin komai har yamma, banda aikin kuka bata komai, harta k’annenta su Ashiru da basu wani fahimci wainar da ake toyawa ba saida suka taru suna bata hak’uri Ta tashi ta saka wani abu a cikinta.. A ‘yan kwanakin tun bayan fasa aurenta da Sagir idan kaga Sady Pretty sai ta baka tausayi musamman idan ka santa a lokutan baya lokacin da tashen kyaunta. Gaba d’aya Ta rame tayi duhu kaman ba Sady ba..


A haka Umma ta shigo ta taddata da k’annen nata sai aikin lallashinta suke. Umma ta shafa kansu tace su fita su basu waje. Babu musu Asiru ya ja hannun k’anins Habeeb suka fice. Suma yaran duk sun koma abun tausayi..


A hankali Umma ta zauna gefen kan Sadiya tana shafa kwantattun sumarta wanda suke a kwance luf ga sulb’i ga tsawo.


“Sadiya ki tashi kici wani abu kinji, zama haka bazai taimaka ba.. Ki tashi dan Allah idan nima ba so kike nak’I ci ba..” Umma tace tana kuma gyara mata sumar nata wanda ke zube saman pillown da take kwance bisa.


Bud’e baki tai da niyyar magana amma sai taji kuka na zuwa mata, da k’yar Ta iya furta “Sabeera gaskiya Ta fad’i Umma.. Nid’in tamkar macijiya ce.. An yarda dani nayi yaudara... An aminta dani naci amana.. Umma I’m nothing but a betrayal.. Tell me please Umma, am I really a bad person.?!” Tai maganar tana mai mik’ewa zaune had’ida fuskantar mahaifiyar tata.


Hannayenta Umma Ta rik’e tana mai share mata hawayenta “You are not a bad person Sadiya.. You are only human.. Dukkanmu muna kuskure, mafiya kyawun masu kuskure a cikinmu Sune wad’anda idan sun gane kuskurensu sai su tuba su gyara.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Inada tabbacin Sabeera will come to understand cewa baki ci amanan ta ba.. Da sannu lamura zasu daidaita kinji koh..” Ta k’arashe tana mai janyo Sadiyar cikin jikinta.
Sadiya bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin jikin mahaifiyarta tana mai lumshe gajiyayyun idanunta.
**


Yamma lis ana kiraye kirayen sallar magrib suka shigo gidan gonar, ko waya basuyi ba balle suce aje airport a d’aukesu dan dama tafiyar ‘yar solo ce. Motar haya suka yo shata suka taho garin. Meema sai mita take tana fad’in yau sai tayi ciwon jiki dan ita Allah ya gani bata tab’a shiga motar haya ba sai yau.. Safeenah tai gajeren tsaki tace “Toh wai da kika damen da mita nid’in na saba shiga ne.. Ni bama wannan ba Allah yasa muna shiga Inne tace duk mu tattara koma gobe gobe.. I’m sure zata goyi bayana wann karon.”


Meema ta danna mata harara cikeda takaici tace “Malama returning flight zuwa Abuja sai an shiga next week.. Zamuyi weekend mu kwashe kwanaki kawai kiyi shirin zaman garin nan..” Tai tsuka tana kuma jan suitcase d’inta “Ni wllhi Adda Feenah kin gama dani dan banyi niyyan zuwa ba ga jaraban wannan masifaffiyar tsohuwar na jiranmu..”


Feenah tabi bayanta cikin sauri tana kiran sunanta tana jan nata jakan da k’yar gashi babu kowa da alama ma’aikatan dik sun tafi sallah da alama. Safeenah Ta kuma sakin tsuka tana jan jakan.


A daidai mashigar da zai sadaka da k’ofar babban parlorn Ajidde dake rik’eda bak’in ruwa mai kaman black ink cikin kwano sukai karo itada Safeenah wacce shigowarta kenan tana kokawa da Jakarta, ai kuwa bak’in ruwan nan bai shek’e ko Ina ba Sai fuskar Safeenah da yake fari tas Wanda lokaci guda bak’in ruwan nan ya maidasa bak’ik’irin kaman tayi wanka da ruwan da aka wanke bayan tukunya..


Meema dake gefe baki sake take duban fuskar Safeenah da yai bak’ik’irin yayinda Ajidde ma ta saki baki da hanci rik’e da kwanon tana duban matar data wanke mata fuska da maganin Kyallu.




“Wow.! What a nice welcome gift you’ve received Addah Feenah.” Meema tace tana mai tintsirewa da dariya.


Ajidde kaw tuni Ta arce a guje tana fad’in “Kai wllhi Allah bazanyi dariya ni kad’ai ba.. Kuran tashe dole yaga wannan.”


Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsawa da tsananin mamaki take duban yarinyar kafin ta maidoda dubanta ga Meema da ke ta faman k’yalk’yala dariya harda ciro waya tana fad’in Ta tsaya tai mata video..




A daidai exit d’in da sukai zasu had’u ta taddasa, da alaman isowar Ta yake jira..
Musaddiq na hangota ya kuma duba agogon dake d’aure hannunsa yana girgiza kai “Ya na ganki haka.. Ina maganin..?”


Ajidde bata amsa sa ba sai dariya da take har tana zama a k’asa.


Takaici ya cika Musaddiq jin har an kusa sallamewa a masallaci “Ke Crazy Dove ki tashi kimin magana kafin su fito daga masallaci su samemu a nan.. Ina maganin yake..?”


Ta kuma tintsirewa da dariya tana fad’in “Ka tab’a ganin dodanniya..?”


Mu Sadiq ya girgiza kai yace “Dodanniya kuma..”


Ajidde ta mik’e tana fad’in “Kai sauri ka biyoni kar ta b’ace..”


Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, sai kuma ya girgiza kai yana furta “Crazy Dove, you truly are crazy..” Lokaci guda ya take mata baya.












SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*








*19*








*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*








Cikin tsananin b’acin rai Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsa ‘yar yatsar k’afarta take duban Meema da har lokacin dariya take tana mata video sa waya “Meema you know I’m a very sensitive person, and I don’t take things lightly...Don’t make me take it out on you..!” Tai maganar tana bud’e hannayenta cikin tsananin b’acin rai da huci.


Daidai lokacin Ajidde ta k’araso hannu biyu aka tana dariya. Cikin tsananin mamaki Safeenah Ta karkato tana duban mahaukaciyar yarinyar wacce tai mata wannan aika aikan sannan bama tasan ta aikata ba balle Tai tinanin bada hak’uri waima dariyarta take tana duban fuskar tata..


Wani irin wawan birki Musaddiq yai ganin wacce Ajidde ta wanke da ruwan maganin nan ba kowa bace face Safeenah, dikda bai ganeta daga fari ba har saida yaji tana fad’in Meema ta damk’o mata shegiyar mai aikin nan taci uwarta ta koya mata manners.


Baki sake Musaddiq yake duban Safeenah da sam baisan da zuwansu ba yana duban yanda Ajidde ke dariya kaman sabuwar Kamu.


Meema ta yatsina fuska tace “Ni ce zan tab’a jikin wnn mahaukaciyar Adda Feenah.. Chabd’i God forbid.! You know I’ve a very sensitive skin. I might easily catch infection.. Kawai ki rungumi k’addara kizo muje ki wanke.


Ana haka Hindu ta k’araso jin hayaniya daga parlorn.




Musaddiq ya dafe goshinsa kad’an yana jinjina rashin hankalin Ajidde wacce taima Meema gwalo tana rataye jakarta tana fad’in “Ni kuma sai na tsaya ki kamani. Tab lallai kina ruwa.. Ko banza naci dariya wllhi.. Allah bamu Alheri dodanniya.” Tana ida fad’in haka Ta kuma arcowa a guje tana ma Meema gwalo.


Daga Meema har Safeenah da tsananin mamaki suka bita da kallo yanzu kam sun gama yarda Tanada tab’in hankali.




Saida tazo daidai yanda Musaddiq ke lab’e ya janyo jakanta da k’arfi ta dawo da baya.


Ihu ta saki tana fad’in “Dan Allah Dodanniya kiyi hak’uri.” Dik a zatonta Safeenah ce ta biyota.


“Ke Crazy Dove.!” Musaddiq ya fad’i cikin daka tsawa.


Jin Musaddiq ne ya sanyata sauk’e ajiyan zuciya ta bud’e idanu tana fad’in “Wllhi kallo ya shige ka.. Kaga..”


Katseta yai da fad’in “Waike lafiyarki kuwa.. Kinsan abinda kika aikata kuwa.. Yanzu idan ‘yanmatan nan suka biyoki suka lakad’a miki duka waye zai ceceki..?”


Ta sakar masa murmushi tana kashe masa idanu guda, abindake mugun basa dariya idan tai. Lokaci guda tace “Toh ba gaka nan ba.. Na San zaka tsare min kaman yanda ka tsare min sanda mugun abokin nan Naka mai bindiga ya biyoni wanda baya dariyar nan.. Mutum kullum kaman shed’an kasan d’azu ma na gansa ya fito wancan k’ofar fuskar nan babu annuri..”


Ya tsareta da idanu kafin yana mamakin halin Ajidde, lokaci guda ya girgiza kai yace “Watau sabida ina nan shine kike taro masifa ki gudu kice zan tsare miki koh.. Toh randa banzo aiki ba fah..”


“Zan jiraka har kazo ai..” Ta bashi amsa kai tsaye kayanta.


D’an girgiza kai yai yace “Kina jina idan baki daina shiga abinda babu ruwanki ba wataran zaki taro abinda yafi k’arfinmu daga ni har ke..” Yai maganar cikin yanayin b’acin rai.


Ta d’an dubesa da kulawa wannan karon “Kayi fushi ne..?”


“Banyi ba.. Inaso kimin alk’awari gobe zaki bama matar nan da kika b’ata mata fuska hak’uri.”


Tsuke fuska tai ba tareda tace komai ba.


Musaddiq ya tsareta da idanu babu walwala wann karon.


“Tau naji ince Dodanniya.. Anji anji.. Anji d’in.. Za’a bata hak’urin.. Hankalinka ya kwanta.”


Tsareta da idanu yai yana duban yanda take maganar tana duban wani b’angare. Harga Allah mugun nishad’i take saka sa, shirmenta da shiriritar ta mugun nishad’i yake saka Sa.


Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro kud’ad’en ya mik’a mata ”Oya take this..”


Bata karb’a ba sai dubansa da take a kaikaice alamun tana fushi dashi yace sai ta bawa Dodanniyar cen hak’uri wanda bama tasan ‘yanuwansa bane.


“Karb’a mana ya kuma fad’i yana dubanta.. Ko sai na baki hak’uri nima..?”


Wannan karon murmushi tai tana wani kad’a kai dan sosai take jin dad’in yanda yake damuwa da damuwarta abu ne da ba’a tab’a nuna mata ba a rayuwarta sai akansa tasan hakan.


Ta girgiza masa kai tace “Ai yau Inna Kyallu batace na sato mata wani abu ba, wanda ka bani jiya kace na bata kuma na bata..”


Tsayuwarsa ya gyara yace “Ke baki gane ba, Idan kika kai mata a jere kwana biyu a matsayin sato mata kike zata rage duk wasu abubuwan da take miki tinda imaninta kenan..”


Ajidde ta tsaresa da idanu tana dubansa “Toh randa bakadashi fah..?”


“Kar ki damu badai ina aiki ba.. Zan tara mana na baki ki kai mata..”


Ta murmusa kad’an tana mai rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shima kafeta da idanu yai yana mai sakin murmushin. Harga Allah Ajidde na d’aya daga cikin dalilin da yasa garin ke masa dad’i baya fatan abinda zaisa ya daina ganinta a gidan gonar.. Zaiyi dik yanda zai ya taimaka mata Ta daina mummunan d’abi’a na sata da Innarta ke koya mata koda hakan na nufin yayi aikin k’arfi ne ya samu Kud’i ya bata Ta fanshi kanta wajen Kyallu.


“Maza Jeki kar dare yayi.” Ya fad’i yana dubanta.


Ta jinjina masa kai a hankali kafin tai masa sallama. Yana nan tsaye yana dubanta tana tafiya tana cilla Jakarta. Murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda itama take juyowa tana sakar masa murmushi, har saida Musaddiq yaga shigewarta kafin ya nufi masallacin dake nan cikin Gidan Gonar da zummar gabatar da nasa sallar dan already sun sallame.


**


A can cikin gida kaw Inne ce ta tsaresu tanai masu d’add’aya dan babu wanda yasan da zuwansu sai ganinsu akai kaman sauk’an aradu dikda cewa Meema tace da sanin Mommy da Daddy suka zo.


Inne tai k’wafa tana mai kuma furta “Idan da sanin iyayenku kuka taho ke Safeenah mijinki yasan kina tafe ne.. Ko kuma saran da kuka d’auko kenan, shi yazo ke kin biyosa.. Zai shigo ne ya sameni, dukkanku Ina dai dai daku nikam..”


Meema ta mik’e tana fad’in “Nidai na gaji d’aki nake son zuwa na huta.. And I’m starving already.. Hindu..! Hindu.. An gyara mana d’akin..”


Inne da Ta saki baki tana duban Meema dak’uwa tai mata tana fad’in “Kinci gidanku.. Baza’a gyara maku d’akin ba, idan baku da hannaye kuna iya kwanciya a haka.” Ta dubi Hindu da k’arasowarta kenan tana fad’in “Ummilo tana can tana gyarawa..”
Lokaci guda Inne tace kije kice mata ta bar d’akin mata ne, zasu gyara da kansu..”


Baki sake Meema ke dubanta kaman zata kurma ihu “Haba Inne Haba Inne.. Dan Allah fah we just arrived here, and I’m pretty tired wllhi Ko hanuna ban iya d’agawa.. Please mana Inne, I can’t do any house chores wllhi..”


“Ni kike ce ma kin gaji baki iya ba idan ban tashi na jefaki cikin turmi na dakaki ba, sangartacciyar banza a rasa da wa za’a mun takwara sai ke.. Matsa min a nan kafin na tashi na daddakeki.. Kuna mata kuce komai sai an maku saikace ba gidan wani zaku ba.. Ba dai kunzo nan ba, toh har girki sai kunyi ni bazan lamunci goyon sangarci da iyayenku sukai maku ba.. Kun sanni sarai ba a nan zakuyi iya shegenku ba..”


Meema ta shige tana bud’e murya kaman mai kuka “Wayyo Wayyo na shiga uku.. Wllhi this is all your fault Adda Feenah.. I shouldn’t have followed you here.. Wayyo Allah na..” Haka Meema ta dingayi kaman wacce ake bugunta, ta shige tana tafiya tana jefa k’afafu tana fad’in dik Safeena ce ta jawo mata.


Ana haka Musaddiq yai sallama ya shigo.


Kallo d’aya yaima Inne ya fahimci a d’ane take yau ko ba’ace ba su Safeenah suka kunnata.. Ya nufo parlorn yanda Inne ke zaune tana girgiza k’afafu.


Musaddiq da ya hango Safeenah zaune da bak’in fuska tana yatsina fuska dariya ya soma yana fad’in “OMG! Who do we have here.. Hey yaushe kikazo..? And what’s that on face..?” Ya k’arashe yana kuma k’unshe dariyarsa.


Harara Feenah ta watsa masa “Kaga babu ruwanka dani.. Mind your own business..”


Musaddiq ya kame bakinsa yana fad’in “Allah baki hak’uri Dodanniya..”


“What..? Mai kace.. What did you just call me..?”


“Abinda kunnenki yaji..” Ya bata amsa kai tsaye.


“Inne Kinga kice ya fita hark’ata..” Safeenah tace tana kuma turo baki.


“Ke rufewa mutane baki ank’i ace d’in..” Sakaryar banza.


Musaddiq ya k’unshe dariyarsa yana k’ok’arin k’arasowa kusan Inne dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login