Showing 159001 words to 162000 words out of 209154 words

Chapter 54 - GIDAN ARO na Sameena Aleeyou.txt

I worn..” Ya k’arashe yana sakin murmushi mai bayyana hak’wara.


Pillow dake gefenta ta d’auka ta kai masa dukan wasa tana fad’in “That was cheating Inspector..”


Ya kuma murmusawa kafin ya janyota jikinsa yace “Inada tactics da dama da zansa kiyi abinda baki shirya ba yarinya..”


Ta kuma nitsar da kanta cikin k’irjinsa tana shak’an ni’imtaccen k’amahinsa, ta lumshe idanunta a hankali kafin tace “Because you are a detective right..?”


Murmusawa yai tana nan cikin k’irjinsa, ya fashi gefen fuskarta kad’an kafin yace “Because you are my wife and I can read your mind..”


Murmusawa tai wanda saida jikkunansu suka d’an motsa ba tareda tace komai ba.


Ya saka duka hannayensa biyu yana mai kuma manneta cikin jikinsa had’ida lumshe nasa idanun shima. Dik wani zafin kan da ya kwaso daga wajen Musaddiq sai yaji ya yaye.. Ya nema ya rasa, sai wani sanyi da annashuwa dake ratsa duk wani mahudar gashi na jikinsa. Yanayi da zaice bai tab’a tsammanin zai riske sa a rayuwarsa ta duniya ba. Tabbas yana da damuwoyinsa da kuma abubuwan da yake ya cimma na rayuwa, amma zai iya cewa shigowar Sadiya cikin rayuwarsa ya sanyashi ji kaman ya cimma wani buri na rayuwa. Sannan ta cike wani gurbi da ya jima da gib’i cikin k’irjinsa. Bai tab’a koda hasasho kansa cikin irin wann rayuwar nan kusa ba ko ba don k’alubale da matsalolin rayuwa da yake fuskanta ba.. A’a kawai dan soyayya ba abar shi bace.. Kuma baida lokacinta. Hasalima kullum fad’ansu da Assad kenan.. Sai yana ji kaman rayuwa ta basa dama ne yai experiencing abinda ya jima yana k’aryatata yana kuma gudunta Wato soyayya.. na wani d’an k’ank’anin lokaci k’ayyadadde.. Yanaji kaman rayuwar bazatayi k’argo a haka ba domin kuwa Ita duniya ba komai bace face GIDAN ARO. Bai yarda akwai Farin ciki mai d’aurewa a GIDAN ARO ba kaman dai yanda nasa ahalin basu sami irin wann Farin cikin ba.


Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin ya ware idanunsa yana duban b’angaren dining area.


“Have you eaten..?” Ya tambaya tana nan mak’ale cikin jikinsa.


A hankali ta girgiza masa kai alamun a’a.


“Oya tashi muje kici abinci you know you are a patient..” Ya k’arashe yana mik’ar da ita tsaye a hankali kaman mai tsoron kar Ta subce cikin hannunsa.


“Can you walk..? Or should I carry you to the dining table..?” Ya tambaya still yana tallafe da ita.


Marairaice fuska tai tace “Kai Inspector zan iya fah..”


Ya d’an ja hancinta kad’an kafin yace “Alright just because you insist.. Ba wai dan inaso na barki kiyi tafiya da k’afarki ba..”


“Come here zan tsaya daga bayanki dan kar ki fad’i..” Ya k’arashe yana kamota ya rik’eta a haka suka nufi dining table d’in kaman mai koya mata tafiya.


A haka har suka isa sukai kalaci mai cikeda Farin ciki. Haka yinin ranan riritata ya dingayi kaman wata jaririya d’anyar goyo, itakam abin har mamaki yake bata dan bata tab’a zaton ko a mafarki ita dashi zasu kasance haka ba.. Bata tab’a zaton he can be as sweet as yanda yake tarairayata haka ba. Abu ne da a baya ko mafarki tai yanayi zata bud’e ido tace bazai faru ba.. Allah kenan mai gudanar da al’amari yanda yaso ba tareda shawarin kowa ba.




A b’angaren Shemau kuwa waya Safeenah tai mata tana tambayarta abinda ke faruwa Fufore.


Shemau taci gaba da fad’in “Meye ma bai faru ba Safeenah.. Ai komai ya faru..”


Safeenah ta dafe k’irjinta tana fad’in “Aunty na shiga uku komai fah kikace..?”


Shemau ta yab’e baki tace “Yo komai kai.. Duk wanda yake cikin gidan gonar nan a kunnensa komai ya faru jiya da dare.. Yau na shiga da sassafe domin na tabbatar da aukuwan hakan.. Yanzu haka maganar da nake miki yini Mu’azzam yai zubur yana tarairayar yarinyar nan. Keda kin gansa yau kinga sabon ango sharr har wani annuri goshinsa yake..”


K’ara Safeenah ta saki tana fad’in “Na shiga uku na mutu na lalace..!” Ta kuma kurma wani ihun tana jifa da wayar.


Shemau tai k’wafa tace “Bakiyi ihu ba ma sai kin ganta da tumbi d’ol.” Tana ida fad’in haka ta kuma k’wafa tana mai shigewa d’aki yanda ta tadda mijin nata kaman jiran shigowarta yake.


“Da wa kika gama waya.?” Ya tambaya yana dubanta.


“Banda shahshashar d’iyar D’anuwanka Safeenah.. Wai waya tayo tana tambayata mai Mu’azzam ke ciki.. Kasan ita akan Mu’azzam Sai ta iya halak’a.. Na k’unsa mata bak’in ciki kaman yanda uwarta ta k’unsa mana ta kasa mana amfani ta samo mana documents d’in nan..”


Shiru Uncle Salman yai kaman mai nazari kafin ya murmusa ya kad’a ‘yar yatsarsa “Ahaan..! I have an idea..”


Shemau Ta dubesa da mamaki kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba mai kake nufi..?”


Gyara zama yai yana duban Shemau kafin yace “Idan uwar bata mana amfani ba ‘yar zata mana..!”


Ta kuma girgiza kai cikeda mamaki kafin tace “Hajara bata mana amfani ba sai Safeenah da kowa ya mata shaidan shashanci..”


Uncle Salman yai wata muguwar murmushi kafin yace “Ki bar mace akan kishi duk dolancinta.. Tabbas Safeenah zata mana amfani fiyeda mahaifiyarta.. Tsaya kiji..”


Shemau ta gyara zama sosai tana dubansa.






SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*








*50*








*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*










“Dama muka samu Shemau da Zamuyi amfani da ita, Kinga na farko Safeenah d’iyar Marwan ce. Kuma ni nasan D’anuwana kaf cikin ‘ya’yansa babu wacce yake matuk’ar so babu wacce ta shiga zuciyarsa irin Safeenah.. Soyayyar da yake ma Safeenah yasa ya aura mata Mu’azzam dan haka itace key d’in mu idan munaso Documents d’in nan su dawo hannunmu.. Sannan bugu da k’ari Marwan ya jima yana preparing Safeenah dan itace zata gajesa a kasuwanci ba wann mahaukacin D’an nasa ba wanda baisan ina ya saka gaba ba... Saidai dukda shirya Safeenah da ya jima yana yi shashasha ce batada wayo.. Amma kuma mu yanzu zata mana amfani dan ita Keda access da Company.. Kuma tana matuk’ar son Mu’azzam wanda zata iya aikata komai domin Ta mallakesa.”


Aunty Shemau ta d’anyi jim kafin ta girgiza kai tace “Mai kake so ayi yanzu..?”


Ya murmusa kad’an kafin yace “Zata samo miki wann takardun daga wajen Mahaifinta ke kuma zaki mata alk’awarin mallaka mata Mu’azzam..”


Da mamaki take dubansa kafin ta girgiza kai tace “Ka kuwa ji abinda kace.. Ta ina nakeda ikon mallaka mata Mu’azzam..?”


“Wani sa’in kina abu kaman marar basira Shemau.. Shin baki samu yarda da amincewar mahaifiyarta ba a lokacin da kika zab’i zaki taimaka mata Nuratu ta bar gidanta..?”


Shemau ta jinjina kai a hankali..


Ya kuma murmusawa kafin yace “Everything in life has a price. Zaki san yanda zakiyi ki raba wann yarinyar da Mu’azzam domin ya koma ga Safeenah... Ke kuma sai ta nemo miki wad’ann documents d’in in exchange.”


Shiru Aunty Shemau tai kafin tace “Wann aiki ne mai matuk’ar wahala.. Farin cikin Mu’azzam kake cewa mu tarwatsa fah.. Sann mai zance ma Safeenah yanda bazata zargi D’an uwan mahaifinta ba.. Ina nufin kai kenan..”




“I don’t give a damn idan zata zargeni muddin wad’ann takardun zasu dawo hannu na.. Kina magana kaman baki San mai duniya ke ciki ba.. Idan ta tona mana asiri kaman ta tona ma kanta ne tinda dole Mu’azzam zai San tareda ita aka had’u aka cutar da matarsa.. In fact mu sai mu jefata a ramin ma ta rufza ciki ita da mahaifiyarta da ta cutar da tasa Uwar.. Kinga Safeenah ta halak’a matarsa Hajara ta halak’a uwarsa shikenan mun zame kanmu cikin sauk’i... Just trust me Shemau wann shine kad’ai hanyar da zamu bi mu mallaki takardun nan..”


Shemau tai shiru kaman mai nazari sai kuma ta jinjina kai tace “ Wai shin yaya wann Document d’in yake.. Ya kamanninsa yake..?!”


Mik’ewa yai tsaye yana mai rungume hannayensa ta baya, saida ya bata baya kafin yace “Takarda ce doguwa cikin envelope mai ruwan k’asa.. Jikin takardan an rubuta wasu harrufa daga sama *BAT*.”. Lokaci guda ya juyo yana duban Shemau kafin yace “Ina so ta samo mun wann takardan mai d’auke da wad’ann harrufan.. Inaso Safeenah Ta samo mun BAT..!”


Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin ta jinjina kafin tace “Mai harrufan BAT ke nufi..? Kana nufin Jemage.?”


Juyowa yai yana dubanta sai kuma ya saki murmushi yace “Kalmar BAT ba Jemage yake nufi ba, yanada ma’anarsa mai zaman kansa, kawai ki saka Safeenah ta nemo mana yanda mahaifinta ya adana BAT.. Ni kad’ai nasan mai haruffan BAT ke nufi dan ko Marwan baisan mai haruffan BAT ke nufi ba. .. Saidai watak’ila yanada masaniyar had’arin dake tattareda BAT idan har ya shiga hannu na, shiyasa ya mishi ajiya mai nisa ta yanda bazan cimmasa ba.. Amma yayi kuskure dan idan har ina numfashi sai na mallaki takardan BAT.”


Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Don Allah ka fayyace mun mai BAT yake nufi..?” Ta fad’i a d’an dame.


Juyowa yai yana dubanta, murmushi saman fuskarsa, hannayensa hard’e ta baya.


Lokaci guda yake furta “B for Bet, A for Agreement, T for Transaction..” Ya k’arashe yana sakin murmushi.


Cikin rashin fahimta Aunty Shemau tace “Bet Agreement Transaction..” Ta girgiza kai kad’an kafin tace “Mai hakan yake nufi..?”


Ya kuma murmusawa kafin yace “Bet yana nufin rantsuwar da Yayanmu Abubakar yai cewa baya buk’atar komai na daga inheritance d’in da mahaifinmu ya bari. Agreement yana nufin yarjejeniyar da mukayi nida shi cewa idan ina son nasa shares d’in zan iya had’awa da nawa kason duka na cinye. Transaction yana nufin transferring Assets d’insa kaf da yayi daga nasa sunan zuwa nawa sunan..!”


Ya kuma karkatowa yana duban Shemau kafin yace “Shemau I badly need that document.. Kafin BAT ya isa hannun Mu’azzam hannuna ya kamata ya fara isowa.. You must help me find BAT..!” Ya k’arashe cikeda zak’uwa.




Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Shikenan zan saka Safeenah ta nemo mana takarda mai d’auke da kalmar BAT.. Toh amma idan ta tambaya na menene mai zance mata..?”


“Bazata tambayeki ba muddin zata sami abinda take so Wato Mu’azzam..” Ya bata amsa kai tsaye yana dubanta.


Lokaci guda yaci gaba da furta “Aiki zaki bata Ta nemo miki BAT idan har tana so ki taimaketa Mijinta Mu’azzam ya koma gareta..!” Yana ida fad’in haka ya zauna a mazauninsa.


Shemau tai masa K’uri tana dubansa. Tunani fal zuciyarta, Anya mijinta bai zauce kan son abin duniya ba.? Bata gama warware qullin da suka had’awa mahaifiyar Mu’azzam ba itada Mommy yanzu gashi Uncle Salman ya kuma ingizata Ta k’ulla wa matar Mu’azzam d’in itada Safeenah.. Ga mahaifiyarsa ga matarsa Anya basu d’ebo da zafi ba..? Tinanin da ta dinga yi kenan har Uncle Salman d’in ya fice yana amsa waya. A hankali ta furta kalman BAT tana mai mik’ewa tsaye.


**


Kwanci tashi babu wuya wajen Allah saida su Mu’azzam suka kwashe sati garin yana tarairayar matarsa had’ida bata wani irin kula na musamman, wata rayuwa ce da suke addu’an inama su tabbata cikinta babu yankewa.
Dukda tsananin son sake kusantarta da yake bai bari yayi hakan ba, dan gani yake sam kaman bata warke ba. Saidai kusan koda yaushe suna nan mak’ale da juna tana zuba masa shagwab’a san ranta yana tarairayarta. Sannan su Umma kusan kullum sai sunyi waya taji lafiyarsu. Wayar Aunty Larai take kira dan bata faye samun na Umman ba. Tasan yanzu haka Umman ce bata son suke wayar tinda tarewarta kenan. Ta murmusa a hankali tana jinjina lamarin Ummanta.


Yau tinda ta shiga sahen Inne bata fito ba, nan ta tadda Ajidde wajen Mamy, ta taimaka ma Ajidde suka bawa Mamy magani tare.


Mama Hindu ta shigo tana tambayar idan sun gama bata maganin zata shiryata.


Sadiya ta dubi Mama Hindu tace “Mama Hindu zan so na taimaka miki da shirya Mamy koda da gyaran sumarta ne.” Tai maganar cikin tsananin son ta taimaka.


Mama Hindu ‘yaruwarsu ce sann tun auren farko da tayi mijin ya rasu nata sake aure ba take zaune nan gidan Inne hakan yasa take kulada Aunty Nuratun.


Murmusawa Mama Hindu tai tace “Allah Sarki sai kika tuna min da marigayiya Ikram.. So tari kikan tuna mun ita.. Kunada wani yanayi mai shigen kama.. Itama haka nan idan naje can Abuja gidansu Ina kula da mahaifiyar tata musamman lokutan da take makaranta bata samun lokacin kula da mahaifiyar sai ta ce mun Mama Hindu ki barni na sami albarkan Mamy koda da gyaran sumarta ne.. Sosai kika tuna mun Ikram a yau..” Ta k’arashe k’walla na ciko idanunta.


Murmusawa kad’an Sadiya tai k’walla na ciko idanunta itama, a hankali Ta furta “Allah sarki.. Allah yasa tana Aljannah.. Ubangiji yasa ladar jinyar mahaifiyarta da tayi ya risketa har cikin makwancinta..”


Mama Hindu ta amsa da Ameen tana duban Mamyn. Lokaci guda take ci gaba da furta “Bata sani ba.. Bata San cewa d’iyarta ta rasu ba.. Zata farka ne ta tadda babu Ikram idan Allah ya nufa jinyar bana tafiya bane..” Ta k’arashe tana goge hawayenta.


Sadiya daketa duban Mamyn itama goge nata hawayen tai kafin Ta jinjina kai tace “In sha Allah Mamy zata sami lafiya.. Kuma Allah zai d’agata... Allah zai sanya mata hak’uri da dangana cikin zuciyarta.. Zataima Ikram addu’a wanda zai bita har makwancinta.” Ta k’arashe tana mai dafa hannun Mamyn.


Mama Hindu ta murmusa kad’an kafin tace “Allahu yashaa Sadiya.. A lokacin da Aunty Nuratu zata farka zata tadda babu d’iyarta Ikram amma zata tadda sabuwar d’iya Allah ya bata bayan ya amshe Ikram daga gareta.. Shi d’in shine mafi kyawun kyauta da kuma jin k’ai..”


Sadiya ta murmusa tana dubanta daidai sanda Ajidde ta k’araso da ruwa da towel Sadiya na warware dogon gashin Aunty Nuratu da yake bak’ik’irin mai sulb’i da shek’i.. Wani ikon Allah duk tsawon lokacin nan da tai tana jinya sam sumarta bai cinye ba, yana nan da tsawonsa saidai abinda baza’a rasa ba.


A tare suke gyara mata sumar itada Ajidde gwanin ban sha’awa Sadiya na nuna ma Ajidde abinda zata taimaka mata dashi, Yai tsaye daga bakin k’ofa yana dubansu yanda suke gyara mahaifiyarsa. Sai yaji wani abu can k’asar zuciyarsa na tsargar masa.. For the first time da yaji tsanar da yake ma Ajidde cikin zuciyarsa ya ragu.. Bai shiga ba haka nan bai tankasu ba sai gudanar da al’amaransu suke kaman wani Sun jima da sanin juna.


Ya tuna kalaman Musaddiq cewa Wai yana son yarinyar kuma zai aureta.. A hankali ya janye idanunsa yana jin wayarsa dake aljihu tana vibrating.


Abokinsa Assad ne mai kira. Saidai kafin ya d’aga kiran yaji Ta katse..


Yai tunanin ko network hakan yasa ya kuma danna kiran layin Assad d’in.


Har saida wayar ta kusan tsinkewa kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga cikin yanayi na rashin kuzari.


Daga yanayin da Mu’azzam ya jisa ciki ya fahimci akwai matsala, snn a ‘yan kwanakin ya kula Assad yana avoiding wayarsa, dan tinda yazo garin zai iya k’irga sau nawa sukai waya ba kaman da ba da ko yaushe suna nan suna waya da juna yana bawa Mu’azzam d’in updates.. Toh amma wnn karon gaba d’aya abokin nasa ya canza amma sai ya alak’anta hakan da cewar Assad d’in space yake basa yaci angwancinsa da kyau..Yasan tsiyar Assad yanzu haka wnn dalilin na iya Sa ya d’an janye masa k’afa har ya gama kwanakinsa a garin.


“Ina jinka Wai meke damunka ne..?” Mu’azzam d’in ya tambaya yana ficewa waje.


Assad ya d’an tamke idanunsa yana k’ok’arin daidaita bugun zuciyarsa. Lokaci guda ya d’an kuma fuzar da fuci kad’an kafin yace “It’s nothing.. Kayi enjoying hutunka kuma ka kula da Amarya.. Zan kashe wayar banjin dad’i ne..”


Girgiza kai Mu’azzam yai yace “Wait Assad don’t hang up.. Wai meye ne ke faruwa.. Meke damunka ne..?”


“I told you Babu komai... Stress ne kawai, zamuyi magana later ka gaida Amarya..” Yana ida fad’in haka ya datse wayar yana shafe goshinsa had’ida tattaro naman goshin.


Wallet d’insa ya bud’e hoton d’iyarsa mai shekaru biyu a duniya ya bayyana. Take yaji wasu irin k‘walla na ciko idanunsa. Ya lumshe idanu ya sumbaci hoton, lokaci guda yake furta “Zaki girma cikin mutunci da muntatawa.. Bazan tab’a shafawa rayuwarki bak’in fenti ba bayan wanda mahaifiyarki ta Shafa miki.. Nayi alk’awarin b’oye miki dalilin rabuwata da mahaifiyarki cewa na kamata ne da wani.. Maiyasa zan bari wad’ann hotunan su watsu a duniya wanda za’a ajiye miki har girmanki.. Tarihi Ta kuma nuna miki cewa ga abinda mahaifinki ya aikata.. Tabbas ka girma ka tadda iyayenka mutanen kirki ne Dattawan K’warai ba k’aramin rahama bane da Allah zaiwa Bawa. Ban taso na tadda d’aya daga cikin iyayena mutumin banza ba bazanso ke ki taso ana nunaki ana fad’in ga abinda mahaifinki ya aikata ba. Idan har zan rufe miki abinda mahaifiyarki ta aikata Tabbas zan rufe miki wann.. Sweetheart inada zab’i ne guda biyu.. Kodai ki girma ki tadda mahaifinki na kurkuku kan laifin da bai aikata ba.. Ko kuma ki girma ki riski bak’in labari da zai shafi martabarki da sunan ki kan kuskuren da mahaifinki sam shima bai aikata ba..” Muryarsa yaci gaba da rawa yana jinjina kai yake duban hoton d’iyar tasa “Tsakani biyu dole na zab’i d’aya.. Dole na zab’i d’aya..!” Ya k’arashe yana kuma lumshe idanu a hankali.
**


A b’angaren Mu’azzam kaw koda yai ta kiran Assad d’in bai d’aga ba yasan dole akwai abinda ke faruwa. Sann yanayin da ya masa magana ciki ya kuma tabbatar masa akwai abinda ke damun Assad d’in.


Fuzar da fuci yai kad’an yana tunanin kiran layin Yusuf ya tambayesa abinda ke faruwa. Bai ida tinanin ba wayar Assad ya kuma shigo masa. Cikin sauri ya d’aga cikeda zak’uwa yana son jin meke wakana da Assad d’in.


Daga d’aya b’angaren Assad yace “Mu’azzam.. There’s something I need to tell you..”


Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ehen go ahead ina sauraronka..”


Assad ya kuma shafe fuskarsa yana mai fuzar da fuci a hankali “You see.. Bana so na b’ata maka wann lokaci mai mahimmanci na rayuwarka.. But I guess banida zab’i Mu’azzam..!” Ya kuma fuzar da fuci a hankali.


Mu’azzam da yai shiru yana sauraronsa ya girgiza kai yace “Tell me Brother.. Meke faruwa, kar ka damu you can just tell me..”


Ya d’an rintse idanunsa kad’an kafin ya bud’e yace “It’s... You see maganar bata waya bace.. I think zaifi kyau idan muka had’u.. But kar ka katse tafiyarka.. Idan ka dawo sai mu tattauna..”


Girgiza kai Mu’azzam yai yace “No.. You sound serious Assad.. Zan dawo sai muyi maganar.”


Assad yai k’ok’arin dakatar dashi amma Mu’azzam d’in bai saurari hakan ba, Assad d’in yasan bazai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login