Showing 30001 words to 33000 words out of 209154 words
dubansa.. Ita bata yarda ba tarewa zai da wancan ‘yariskar ba.. Yak’i ya tare da ita yaje zai tare da Karuwar banza.. Take taji jiri na neman kifar da ita, taji wani irin hawaye na ciko idanunta.. Cikin sauri Babu shiri ta biyo bayansa.
Sauk’owar Mommy k’asa kenan Mu’azzam ya shigo parlorn ya gaisar da ita kafin ya sanar da ita Adamawa zai tafi..
Mommy zaida taga wani walk’iya ya gifta mata dan firgici, a fili kuwa cewa tai “Toooh Fufore kuma Mu’azzam.. Lafiya inji..? Ko sun sanar dakai wani abu gameda jikin Mamyn taka ne.. Amma kuma munyi waya jiya da Daddyn naku bai sanar dani wani abu kan haka ba.. Yace ma gobe yake saka ran dawowa in sha Allah, jikin Nuratu kuma da sauk’i sosai Alhamdulillah..”
“No bamuyi waya dasu ba Mommy.. Kawai dai Zanje ne..” Muazzma ya bata amsa..
Daidai lokacin Safeenah Ta shigo tana kuka “Mommy tafiya zai ya barni ya koma zama da Ita.. Mommy I’m sure of it.. Dan Allah kar ki barsa ya tafi Mommy..”
A tare Mommy da Mu’azzam suka juyo suna duban Safeenah dake shigowa parlorn cikin kuka tana surutai..
Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “Toh Mommy ni na wuce..”
“Bazakaci wani abu ba..?” Mommy ke k’ok’arin dakatar dashi amma tuni Safeenah ta kuma fashewa da wani kukan tana fad’in Mu’azzam bai sonta..
“A’a Mommy zanci idan na fita..”
Mommy tai masa addua’an sauk’a lafiya da kuma sak’on gaisuwa..
Baibi takan Safeenah ba ya fice cikin sassarfa, yana jin yanda Mommy ke mata fad’an wauta irin nata.. Bai tsaya sauraren mai zasuce ba yayi ficewarsa.
A b’angaren Mommy ma yau ba ta shashashancin Safeenah take ba, Mu’azzam zai tafi Fufore tsoronta d’aya kar yaje ya b’ata masu shirinsu.. Ya zama dole ta kirawo Shamau ta sanar da ita cewa Mu’azzam na hanya tasan irin takan tsantsan da zasuyi kar ya fahimci wace irin mai magani aka d’aukarwa mahaifiyarsa.
Ko takan Safeenah dake zube wajen tana kuka Mommy batabi ba Ta haye sama tana dialing layin Shamau matar Uncle Salman..
Bugu biyu a na uku Shamau ta d’aga. Ko gaisuwarta Mommy bata tsaya amsawa ba ta soma fad’in “Kina jina.. Mu’azzam na tafe yau.. Anya kinaga bazai fahimci matar da aka d’aukar wa mahaifiyarsa matsayin mai magani ‘yar 419 ce ba mai maganin gaskiya bace.. Idan ya fahimci haka zai saka ayan tambaya kanki Shemau dan kece kika kawo matar.. Idan kuma ya soma bincike nasan zai iso kaina.. Shemau bana so na sami matsala da mijina kan wannan nakashesshiyar matar tasa.” Mommy Ta k’arashe tsoro fal fuskarta
Daga d’aya b’angaren Shemau ta murmusa tace “Aunty Hajara kenan.. Ni wllhi Mamaki kike bani.. Ta yaya Mu’azzam zai fahimci wani abu ba sanin kan magani yayi ba.. Mu’azzam fa D’ansanda ne ba Likita ba. Babu abinda zai fahimta koda yazo d’in.. Kyallu kuma mutane da yawa sunyi Na’am da maganinta amma ni nasan mak’aryaciya ce rufa ido kurum take wa mutane.. Idan da maganin Kyallu za’ai ma Nuratu jinya Ina mai tabbatar maki saidai ta k’arasa rub’ewa a turata rami taje ta had’e da tsohon mijinta Kinga ta fice daga rayuwarki har abada..”
Mommy ta Sauk’e ajiyan zuciya hannu dafe a k’irji “Toh shikenan Shemau, ni nasan I can always count on you.. Wllhi banida burin da ya wuce Nuratu ta fice har abada daga rayuwar mijina.. Yanzu kiga yanda ya d’ibi jiki yai mata rakiya.. Ai ki gode ma Allah da wannan jarabebbiyar uwar tasu bata tura ma Salman ita ba sai ta tura ma mijina.. Koda dai nasan ma Babba za’a lik’a ba ma k’arami ba..”
Aunty Shamau tace “That’s why I’m helping you Aunty Hajara, baki cancanci haka ba.. I can feel your pain, ciwon d’iya mace ai na d’iya mace ce.. Amma Ina mai tabbatar miki Nuratu bazata sami lafiya ba balle har tayi aurattaya da mijinki.. Gidanki kuma ta barosa kenan babu kome kaman yanda wanda ya mutu baya dawowa..”
Mommy ta Washe baki cikeda jin dad’i tace “Toh yanzu hankalina ya kwanta sai munyi magana..” Daga haka sallama sukai Mommy na kuma jin zuciyarta ya mata wasai Ta yarda k’wallan mangoro ta huta da k’uda..
**
FUFORE
Tsaki yai a karo na babu adadi yana mai kuma danna kansa cikin pillow, masu buga masa k’ofan basu fasa ba. Da mugun tsaki Musaddiq ya mik’e yai zaune saman gadon, ya janyo wayarsa yana duba time.. Wani irin tsakin ya kuma bugawa yana ayyana kalan rashin mutuncin da zaima duk mai buga masa k’ofar nan.. Bai ida tinanin ba ya sinkayo muryar Kakarsa Inne tana fad’in “Toh Uban ’yan gadara, Hakimi mai Sarauta sai ka tashi garin ya waye.. Nan ba gidan Ubanka bane daka saka baccin asara, aiki zakayi a nan kuma Kowa daka gani a nan nada amfani.. Idan ka bari na shigo wajen zanci mutuncinka Gidado..”
“Goodness..! Musaddiq taka Ta k’are.!” Ya fad’i yana mai zubewa kan gadon daga zaunen da yake.
“Kai Jume Zo ka bud’e min k’ofar nan da k’arfin tsiya na shiga na samesa..!” Ta fad’i tana duban Matashin da ta kira da Jume wanda ke tsaye gefenta..
Ai Musaddiq na jin haka ya mik’e ya k’araso ya bud’e k’ofar baki a kumbure.. Harara ta rakasa dashi shid’inma a dunk’ule yake aika mata hararan k’asa k’asa..
Kafin ya samu zarafin gaisheta taceda Jume mik’a masa kayan ya saka ya fice aiki.. Ma’aikata tintinin suke Gona shi yana kwance a nan yana baccin asara..”
Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, da gaske uniform d’in ma’aikatan gidan gonar Inne ta basa tace ya saka.. Kan uba ai wllhi saidai duk abinda za’ayi ayi bazai saka wannan uniform d’in ba..
Bazawarin murmushi yai yana furta “You must be kidding.. Who’s going to wear those...?” Yai maganar yana nuna uniform d’in da Jume ke mik’a masa..
“Zaka amsa ka saka ne ko sai na tub’eka na saka maka da kaina..” Inne ta kuma fad’i a hasale.
Ya d’ago idanu ya danna mata harara.. Dungurinsa tai tana fad’in “Ka sake hararata zan tsiyayi wannan jajayen idanun naka..”
“Inne Wai dan Allah maiyasa kike mun haka ne.. Ni wllhi kawai ki fito fili kice kin tsaneni Inne, baki sona baki k’aunata..”
“Eh an tsaneka d’in ba’a son naka.. Ka tashi ka shirya ka fita aiki. Kar ka bari na sake maka magana..”
Ta dubi Jume dake tsaye gefe yana k’unshe dariyarsa tace “Ka tabbata ya shirya ya fito kuma ka nuna masa komai.. Sannan ka sanar da shugaban Laburorin idan Gidado yai latti ko na minti d’aya ne a hukuntasa.. Sannan koda wasa kar a basa kulawa ta musamman.. A kula dashi kaman yanda ake kula da ko Wanne ma’aikacin gidan gonar nan kaji koh..”
Jume ya risina yana jinjina kai “Toh Inne in sha Allah za’ayi kaman yanda kikace..”
Inne ta jinjina kai tana watsa wa Musaddiq da yai sakare yana dubansu mugun kallo.. Carbinta dake nad’e hannunta Ta zabga masa yana kaucewa “Jarabebbe kawai..”
Tana ficewa Musaddiq ya dawo da dubansa ga Jume, wani irin mugun kallo kawai yake watsawa Jumen musamman da yaga irin dariyar da Jume yake bayan Inne ta fice..
“Kaci gaba da biye ma wannan matar kuna shiga hakkin rayuwata.. Wannan matar na jima da sanin cewa Ta tsaneni kaf cikin jikokinta babu wanda Ta tsana irina..”
Jume yai k’ok’arin tsagaita dariyarsa yace “Wllhi Inne tana k’aunarka kuma so take ka zama good boy shiyasa ta sakaka gaba.. Gata take maka Musaddiq.. Yanzu dai ka shirya muje kai breakfast ka fice kafin kayi latti ka jaza min dan nasan nima harda ni Zata had’e tai mana d’add’aya..”
Tsaki Musaddiq yaja yana mai janyo towel d’insa, ya tsani wannan gidan Gona tamkar akan K’aya yake haka jinsa “Let her do her worse..” Ya fad’i yana shigewa bathroom..
Jume dai murmusawa kawai yana fad’in “Ka fad’a a gabanta idan ka isa..”
Jume second cousin d’in Su Musaddiq ne, Babansa cousin d’in su Daddy ne. Baban Jume kaman d’ah yake ma Inne dan D’an d’anuwanta ne.. A cikin Yola gidansu Jume yake shima bai jima da zuwa Gidan Gonar ba dan Industrial Training ne ma ya kawo sa aiki nan cikin Gidan Gonar dashike fannin da ya shafi noma da kiwo yake karantawa.. Musaddiq zai d’an girme ma Jume da shekarun da bazasu wuce biyu zuwa uku ba amma tin can dama sun saba da juna tin suna zuwa hutu Fufore hakan yasa da suka sake had’uwa yanzu abotansu na Tun baya ne yake k’ok’arin sake k’ulluwa..
Babu yanda Jume baiba Musaddiq ya saka kayan ma’aikatan gidan gonar amma fir yak’i sakawa.. Yace a haka zaije saidai Inne tayi abinda zatayi.. Aiko yana isowa k’ofar parlorn zai fice ya ganta tayi k’ebebe tsakiyar k’ofa tana aika masa mugun kallo..
Lumshe idanunsa kurum Musaddiq yai yana furta “Kai.. Kai.. Kai jama’a.. Shikenan kuma ai..!” Tin kafin ma tace ya juya ya juya d’in, d’aki ya komo ya sauya shiga cikin uniform d’in.. Ya fito yana tafiya awkwardly cikin uniform d’in kaman zai kurma ihu, shi babu abinda yafi basa takaici kaman wannan k’atoton boot d’in da ya zurma k’afafunsa ciki.. Aunty Shemau da ahigowarta section d’in kenan taci karo da Musaddiq a haka, dariyarta ta k’unshe itama tana mai k’ok’arin gaida Inne..
Zai fice Inne tace “Zo nan tsaya..”
Yaja ya tsaya fuska a tamke
Irin hular fulani makiyaya mai kaman malfar sak’a ta d’auko ta d’aura masa akansa tace “Toh maza aje ayi aiki.. Ayi noma ayi kiwo Allah ya bada sa’a..”
Jume da Aunty Shemau ne suka amsa da Ameen shikam Musaddiq tuni ya fice cikin k’unan zuciya..
Sai sannan Inne ta dawo da hankalinta ga Shemau.. Suka kuma gaisawa Shemaun na tambayarta jikin Aunty Nurah..
Inne ta amsa mata da fad’in “Jiki Alhamdulillah, Hindatu na ciki tana kula da ita..” (Hindatu ma’aikaciyar Inne ce dake tayata kula da Nuratun)
Aunty Shemau Ta d’an murmusa tana kuma sanne kanta k’asa had’ida gyara zaman mayafinta, Ta d’an muskuta tace “Nace ko mai maganin ta iso, ko yau batazo ba..?”
“Ai yaushe garin ya waye Shemau, zatazo ne k’ila zuwa anjima..” Inne ta bata amsa..
Aunty Shemau ta jinjina kai tace “Haka ne.. Bara na lek’a na dubata..”
Inne ta amsa mata da fad’in “Toh madallah.. Ki shiga tana ciki..”
Shemau ta mik’e cikeda girmamawa kafin Ta nufi d’akin Aunty Nurah.
**
Gaban madubi ta tsaya tana kuma zana gazal da janbaki saman fuskar nata da sunan kwalliya.. Lokaci guda take fari da idanu tana juyi gaban madubin.. Ita da kanta take kirari ma kanta “Yarinya mai kyau.. Had’uwa iya had’uwa.. Ba farar k’afa kike dashi ba kaman yanda Inne Kyallu ke fad’i.. Tsaban had’uwarki ne shiyasa samarin garin nan basa iya tunk’ararki.. Albarka na gaba gareki ko Inne Kyallu bata furta miki ba...” Ta k’arashe tana kuma juyi hannayenta saman kunkuminta ga uwar d’amara da tayi kaman zata tashe... Lokaci guda ta d’auko d’ankwalinta ta nannad’e kafin ta d’aura saman goshinta, ta turo kallabin gaban goshi, ta zubo da kitsonta guda biyu b’angaren dama da hagu.. Ta kuma duban kanta tana sakin murmushi.. “Wo ni.. Gaskiya kin had’u Ajidde..” Dundun da Kyallu Ta d’und’uma mata a gadon bayanta ya sanyata mik’ewa babu shiri tana sakin ihu had’ida sosa bayanta.
“Uwar mi kika tsaya yi a nan da bazaki tafi ba..?”
Ajidde Ta turo baki gaba kad’an tace “Inna Kwalliya fah na tsaya ko Allah zaisa ki sami Sirki a hanya..”
Kyallu ta janyota waje ta jefa mata buhun maganin tana fad’in “Kinajina ki bud’e kunnuwanki da kyau ki saurareni.. Idan kikaje kice a fita a baki waje keda majinyaciyar zaki had’a mata magninta ki bata.. Idan an watse an barku ku biyu tinda babu abinda take iyawa bama zata fahimci kin d’auko wani abu ba.. Ki bincika d’akin taro da sisi da duk wani abinda zaki samu na arziki ki k’unso cikin buhunki ki kawo man Kinji koh.. Idan kika dawo min gidan nan babu abin arziki a turke zan d’aureki ki kwana.. Maza Tashi ki shige..”
Ajidde ta jinjina kai a hankali baki a ture tana kuma sosa dundun da Kyallu tai mata wanda take ji kaman ta rabe mata k’ashin baya ne..
Lokaci guda ta mik’e ta d’au jakan buhu na maganin Ta rataye saman kafad’arta..
Kyallu ta zuba mata jajayen idanunta tana huci “Babu uban da zai tab’a sonki Ajidde dan ked’in Anno ba ce mai farar k’afa nima dan inada makarinki ne da tuni kin gama dani da mugun farar k’afarki..!”
Ajidde dake lab’e jikin k’ofa dik kalaman Kyallu a kunnuwarta ne, cikin sanyin jiki ta soma tafiya rataye da jakan maganinta dan Idan da Sabo Ta saba da jin wad’annan kalamai daga bakin Inna Kyallu..
**
Koda ya iso motar da zai kaisa garin Fufore ya shiga, dan dama bai sanar dasu yana tafe ba balle ya sanar dasu isowarsa azo a d’aukesa..
Da shike Gidan Gonar wajen gari take hakan yasa shi ya soma sauk’a cikin motar tasu.. Yai tsaye yana k’are ma gidan gonar kallo, abubuwa da dama na ziyartan zuciyarsa.. Wajen da yafi so yafi k’auna a rayuwarsa.. Wajen da yake jefa zuciyarsa cikin nishadi da annashuwa.. Garin da aka haifesa ya kuma taso cikinta.. Gari mai tarin albarka da kwanciyar hankali.. Babu fitintunun da ya baro babu komai sai kukan tsintsaye da dabbobi dake sanyasa nishad’i.. Ya lumshe idanunsa yana shak’an iskan dake kad’awa.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*12*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali yake takowa yana kuma k’arema wajen kallo, memories d’in baya suna dawo masa.. Daidai jikin wata bishiyar mangoro ya tsaya ya d’aga kai yana duban bishiyar, lokaci guda yake tuna zamanin yarintarsa, sukanyi wasa da mahaifinsa wasan Corps da Bad guys, dama tin yana k’arami yake mafarkin zama D’ansanda domin ya kama masu laifi.. Ya tina wasu lokutan yakan d’ale bishiyar yayi kwanton b’auna Babansa na k’asa yana nemansa.. Sai ya bari Babansa yazo daidai jikin bishiyar Sai ya d’ago bindigar robarsa ta wasa yana pointing Baban nasa dashi yana fad’in ‘Na kamaka.. Freeze or I’ll shoot..’ Ya saki murmushi yana tuna moments masu dad’i da suka kasance ciki shida mahaifinsa.. A hankali ya aje jakarsa jikin bishiyar kafin ya dafa bishiyar ya d’ale.. Sai yana ganin hoton abubuwan cikin idanunsa kaman yanzu suke faruwa, komai yana nan yanda yake babu abinda ya canza Sai rayuwarsu data canza..
Akwai wani d’an hole jikin bishiyar yanda yake b’oye k’aramar bindigar robar tasa dik sanda zasuyi wasan hide and seek da Dad d’insa, ai kuwa nan ya hangota ciki tana nan a wajen har wannan lokacin.. Mu’azzam ya saki murmushi mai bayyana hak’wara yasa hannu ya d’ago bindigar yana juyawa, lokaci guda yake kuma tuno abubuwa da dama murmushin bai bar saman fuskarsa ba.. Yana nan zaune saman bishiyar yana tinani rayuwar baya ya hango wata yarinya Ta nufo wajen.. Tana tafe tana cillo da jakan dake hannunta tana ‘yan wak’e wak’e.. _”Mangoro.. Mai Mangoro kawo musha.. Idan da kud’i ma zamu sha idan babu kud’i ma zamusha.. Balle ma mu na bati zamu sha..”_
Mu’azzam ya mik’e daga kishingid’en da yake nan saman bishiyar yana kuma duban yarinyar dake nufo bishiyar tana wak’e Mangoro..
Cak Ajidde ta tsaya sakamakon hango bak’in jaka da tai aje k’asan bishiya..
Ajidde ta shiga wage baki tana furta “Allah ya kashe ya baki Ajidde, tsuntsu daga sama gasasshe.. Wannan jaka da gani Kud’i ne a cikinki..Idan nayi nasaran bud’eki na d’ibi kud’in ciki na kaima Inna Kyallu ko shakka babu zata yabeni za kuma Ta saka mun albarka..” Taci gaba da Washe baki tana kuma nufo jakan...
Tana isowa ta soma ‘yan waige waige dan ta tabbatar babu mai ganinta.. Saida Ta tabbata babu kowa wajen kafin ta duk’a ta soma kiciniyar bud’e jakan...
Mamaki ya cika Mu’azzam Ganin k’amar yarinya na k’ok’arin sata..
Ajidde bata fasa kiciniyar bud’e jakar ba tana fad’in “Dik taurin kanki sai na bud’eki jaka..!” Ta k’arashe tana mai daddage k’arfinta tana kiciniyar bud’ewa harda wani bada balance tai..
Tana kiciniyar bud’e jakan taji mangoro guda ya fad’o mata akai timm..
“Kai Kai Kai..” Ta fad’i tana dafe kanta.. Ta d’auki mangoron da ya fad’o ta shiga nunasa da yatsa tana fad’in “Tind kika buga min Kai zan miki shan azaba Alk’ur’an.”
Lokaci guda kuma ta saki Tsaki tana mai furta “Ke mangoro yau bata taki nake ba.. Ki bari na samu abinda zan samu cikin jakan nan kafin na dawo kanki, nidake akwai amana ai..” Ta k’arashe tana mai kuma janyo jakan..
Fad’owar wani mangoron ne data kumaji ya sanyata tsagaitawa.. Ta soma k’ok’arin mik’ewa tana tinanin kodai mai jakan na saman bishiyar ne..
A hankali ta soma k’ok’arin d’ago kanta.. Ai a zabure ta saki wani irin k’ara sakamon hango mutumin datai saman bishiyar rik’eda bindiga “Bindiga.. Bindiga..” Kalman data iya furtawa kenan jikinta na k’yarma.
Ajidde batai wata wata bata ta suri takalmanta da jakan maganinta a hannu ta soma gudu.
Mu’azzam dake rik’e da bindigarsa tin na yarinta dirk’owa yai daga saman bishiyar ya soma k’ok’arin bin bayan b’arauniyar yarinya wacce bai tab’a ganin ko mai kamanninta a Gidan gonar ba dik zuwansa..
Gudu take tana waige waige tana hango alamun mutumin na nufota.. Rumbun da ake aje abincin dababbobin tai wuf ta shige had’ida turo k’ofar..
Musaddiq dake cikin d’akin aje abincin an basa aikin gyaran d’akin yanayi yana turb’une fuska kaman daga sama yaji an turo k’ofa an shigo.. Ya dakata da abinda yake yana dubanta da mamaki yanda take lek’en mutumin dake casing d’inta..
Motsin da taji bayanta ya sanyata juyawa babu shiri.. Razana tai da ganin yanda fuskar Musaddiq ya b’aci da k’ura shima ya razana da kwalliyar dake fuskarta da yanda duk ta dame kwalliyar ya b’ata mata fuska sakamakon gudun famfalak’i da tai.. Suka saki k’ara a tare kowa na tsoron juna.. Kowa gani yake gamo yayi..
Sai kuma Ajidde ta soma matsowa kusansa tana kuma zuru zuru da idanu, Musaddiq bai daina binta da kallon tsoro da mamaki ba.. Kan ya ankara ta duk’a ta soma k’ok’arin janye boot d’in da k’afafunsa ke rufe ciki.. Musaddiq yana janye k’afarsa yake furta “Hey what are you doing.. Who are you.. Ke ki sakar min k’afata..”
Ajidde bata fasa janye takalmin cikin k’afar Musaddiq ba, harga Allah tsoro ya kamasa sosai ganin yanda wannan halittar ke janye masa k’afa.. Bata fasa janye Boot d’in ba har saida ta cireta gaba d’aya.. K’afar Musaddiq ya bayyana.. Ajidde na ganin k’afar Musaddiq ta sauk’e ajiyan zuciya hannu a k’irji tana fad’in “Wai Allah na.. Ashe mutum ne..!”
Mamaki bai saki Musaddiq ba ganin itace ya kamata yace ashe