Showing 174001 words to 177000 words out of 209154 words
sukai masu godiya kafin sukai sallama Sadiyar ma na masu godiya da fatan sauk’a lafia.
Aunty Larai ta kamo hannunta tana tsareta da idanu “Iyye irin wann haske da shek’i da kike.. Aah lallai mission yayi kyau. Tubarkallah Masha Allah.”
Sadiya ta murmusa cikeda kunya tana rufe fuskarta da mayafi.
Sosai taji dad’in ganin ahalinta cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali. Idan ka gansu duk sun canza ba kaman lokacin da suke cikin tashin hankali ba, Sai godiyar Allah.
Tana ida sallar magrib Aunty Larai ta tarbeta da wasu had’e had’en ta tasa ta gaba sai ta cinye ta shanye. Sadiya kaman zatai kuka babu yanda ta iya haka Aunty Larai ta tasa gaba da had’en had’en nan. Harda wasu turaruka na musamman ta had’a mata da shike gidanta zata tafi.
Kafin isha Aunty Larai ta sakata ta tsala wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga bak’ar abaya mai kyaun gaske wanda ya kuma bayyana kyaun fatarta. Sai zuba k’amshi take.
Ta tada sallar isha kenan ta sinkayo muryarsa da Umma suna gaisawa daga parlor.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*54*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Habeeb ya k’araso sukai handshake ya zaunar dashi gefensa saman kujeran kafin yace “Hello little Cop.. Kaje lesson d’in kuwa..? Fad’a mun mai aka koya maku..” Yai maganar yana duban Habeeb d’in dake wasa da wani silver metal shatin kwabo.
Habeeb ya girgiza kai yace “Nace masu ni Cop ne.. Chasing bad guys nake so na koya..”
Ya murmusa yana duban Metal d’in wanda ya mugun d’aukan hankalinsa. Take yaji zuciyarsa yai wani irin yankewa sanda ya soma tuna Ina yasan irin wann metal d’in.. Take yarintarsa ya soma dawo masa yana wasa da irin wann metal yana mannasa da magnet. Karb’an metal d’in yai yana juyawa, exactly babu abinda ya raba da irin wanda yake wasa dashi yana yaro.
Ya dubi Habeeb yace “Where did you get this from.?”
Habeeb dake ‘yan tsalle tsallensa yace “I don’t know.. Kawai nima na samu ne a gidanmu kafin mu dawo wann gidan..”
Mu’azzam yaci gaba da juya metal d’in.. Sai wann lokacin yake karanta abun da aka rubuta tsakiyan shatin kwabon cikin yanayin rubutu mai tsananin k’ank’anta wanda sai ka saka idanunka sosai kafin ka iya karantawa _Balck African Team_. Shine abin da aka rubuta tsakiyar metal d’in cikin rubutu mai style. Zuciyarsa ya yanke sanda ya karanta rubutun. Ya nanata a fili Black African Team...!” Ya nanata a hankali yana mai kuma juya coin d’in cikin hannunsa.
Hayaniyar Habeeb dake kallon cartoon d’in spider man yana kwaikwayonsa shi ya dawo da hankalin Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Hey little Cop.. Can you borrow me this.” Ya k’arashe yana nuna masa Coin d’in.
“Sure Mr Cop. Na baka kyauta idan kana so.”
Murmusawa yai kad’an kafin yace “Kar ka damu aro zaka bani.. Idan na gama amfani dashi zan dawo maka dashi kaji.”
Habeeb ya jinjina kansa daidai lokacin da Aunty Larai ta kirasa ciki.
Mu’azzam yaci gaba da juya coin d’in yana nanata word d’in dake jiki wanda a yarintarsa bai kula da wann word d’in ba sai yanzu.. Balck African Team” Ya kuma fad’i yana juya coin d’in.
K’amshinta ne ya soma masa sallama, Cak ya tsaya da abinda yake ya soma janye idanuns daga duban coin d’in.
Tin daga k’asa ya soma dubanta har zuwa kyakkyawan fuskarta da yai kewa.
Ya mik’e yana mai jefa coin d’in cikin aljihunsa. A hankali yake takowa har zuwa kusanta.
Suka jima a haka suna duban juna cikeda shauk’i. Hannayensa ya d’ago duka biyu ya tallafi fuskarta, kafin ya matso da nasa fuskar kusan nata. Ya manne goshinsu waje guda su duka biyun idanunsu a lumshe “I’ve missed you.. I’ve missed you so much Beautiful.!” Ya fad’i cikin murya mai tsananin sanyi.
Bata iya furta komai ba Sai wane irin sanyi da illahirin jikinta yai. Tana jin sanda ya rungumeta cikin jikinsa. Ta lumshe idanunta a hankali tana shak’an k’amshinsa da tai kewa.
Hannunta ya kamo suka zauna saman kujera ya tsareta da idanu kaman ranan ya soma ganinta.
Ta d’an muskuta tace “Ina yini..”
Bai amsa ba saima ci gaba da kallonta da yake harda yin tagumi still idanunsa akanta. Gaba d’aya sai ta jita a tsarge. Ta sadda kanta kad’an ko zai daina duban nata ya amsa mata gaisuwarta amma inaa kaman ma ba dashi take ba.
D’agowa Ta kumayi suka dubi juna still bai daina kallonta ba bai kuma canza position d’in taguminsa ba.
Ta d’an tsime kad’an tace “What.. Why are you staring at me like that.. Wait is there something on my face..?” Ta shiga shafe fuskarta tana turo baki gaba.
Jinjina mata kai yai yace “Umhum.”
Taci gaba da Shafa Fuskar nata tana neman mai yake kallo tana yi tana fad’in “Where ina yake..?”
“There.” Ya bata amsa yana d’aga mata gira da idanu alamun yana mata nuni da abinda ke bisa fuskar nata.
Ta marairaice fuska tana fad’in “Inspector Nidai banji komai ba.”
“Come here.. Zo na nuna miki..” Ya k’arashe yana janyota kusansa kad’an.
Dik ta sakankance zai cire mata abinda ke fuskar nata ne saiji tai ya manne bakinsa da nata. Daskarewa tai tanajin yanda yake sarrafa harshenta cikin bakinsa. Tai ta maza ganin yana neman fice mata daga giya ta turasa da iyaka k’arfinta.
Tallafo fuskarta yai yana dubanta da idanunsa da tuni sun k’ank’ance “Didn’t you miss me..?” Ya tambaya cikin kasaliyar murya.
Kaman zata fashe masa da kuka take fad’in “Of course I did miss you.. But.. Ba irin wann kewar ba.. And besides baka San yanda muke bane.. What if..What if..”
Bai bari Takai aya ba ya katse Ta da fad’in “Fine.. Tashi mu tafi gidanmu.. Ince kin masu sallama..”
Ta mak’e masa kafad’a tace “Ni dai dan Allah ka barni na Kwana..”
D’an shan mur yai had’ida matsawa baya kad’an “Shiga ki masu sallama ki fito mu tafi..” Ya fad’i yana duba writs watching d’insa ba tareda ya dubeta ba fuskar nan babu walwala.
Ta kuma yin narai narai da idanu tana dubansa yanda ya canza lokaci guda. Tasan tinda ya fad’i haka bazai canza ba. Jiki babu laka Ta mik’e ta nufi ciki.
Daga yanda Aunty Larai ta ganta tasan akwai wani abu “Ya na ganki haka.. Har zaku wuce ne..?”
Sadiya ta d’an turo baki gaba kad’an tace “Aunty Cewa yai Wai bazan kwana ba.”
Aunty Larai ta saki baki had’ida kame hab’a tace “Au Wai dama saida kika ce masa kwana kike son yi.. Ai ban zanci zaki fad’i haka ba da tun kafin ya zauna na koraki Kun tafi.. Au ashe da yace a fara kawoki nan bai maki ba saida kikace masa kwana kike son yi.. Toh bazaki kwanan ba.. Ko ya k’yaleki ma mu dai kam bamuda masauk’inki a nan.. Kar ma kiyi Umma taji wann batun dan Kinsan Sauran. Ungo amshi nan..” Ta k’arashe tana bata sauran had’e had’en kayan gyaran da ta mata.. Saura idan kinje kar kisha kiyi flushing nasu a toilet nida ke ne.. Natural Herbs ne duka a nan masu kyau ga lafiyar d’anadam da honey ake sha kaman tea zaki had’a maku instead of sugar ki zuba honey har shima idan yana so zai sha kinji koh.. Ta d’an turo bakinta gaba kad’an tana jinjina kai. Tana iya jiyo k’amshin cloves daga cikin jakan da yake da tabbacin dangin itace ne masu inganci da kuma kyau ga lafiya.
Jiki a sanyaye ta isa taima Umma sallama ta fito ta taddashi. Sanda ta iso waya ne manne kunnensa yana amsa kira. Yana mik’ewa taga bayan navy blue polo d’in dake jikinsa an rubuta FCID da manyan haruffa.. Ko ba’a ce ba kasan rigar Office ne. Ta d’an tab’e baki kad’an a ranta tace k’ila daga Office ko gida baije ba kenan.. Watak’la ya tsaya wani wajen ne.
Har suka shige Mota waya yake, ita har mamaki take shin kunnensa bai gajiya ne. Har suka kusan isa gida waya yake wanda zata ce bata fahimci komai ba dan aikinsa ya shafa.. Yo itakam ma window take ta duba abinta tana kallon tangama tangaman titunan birnin tarayya da aka k’awatasu da security lights ta ko Ina.
Koda ya gama wayan bai ce mata komai ba, ta saci kallonsa taga hankalinsa kacaukam naga tuk’a mota. Sai itama ta maida nata kan b’angarenta. Ta kuma jingina kanta tana kallan gari.
Har suka iso gida bai ce mata komai ba, dik sai taji jikinta yayi sanyi saikace ba shine ya gama cewa yayi kewarta ba ya wani k’i kulata yanata minding business d’insa. Tai k’wafa cikin zuciyarta.
Har dai Patrick ya k’araso yana musu sannu da zuwa welcome sir, welcome ma..” Still Mu’azzam bai kulata ba saima umartan Patrick da yake ya k’arasa da suitcase d’in nata k’ofar parlor.
Ko zarafin amsa Patrick dake gaisheta bata samu ba. Toh kardai fushi yai da ita.. Shin meye laifin dan tace ya barta ta kwana d’aya wajen Ummanta da ‘yanuwanta.. Kawai dai mai hali ne da bai fasawa amma itakam bataga wani abu cikin hakan ba.
Baibi takanta ba yai shigewarsa, tai k’wafa cikin zuciyarta tana jin zafin yanda yake ta wani basarwa yana shareta saikace ba yau ta dawo ba.. Dama k’ila babu wani missing d’inta da yai.. Da yayi kewarta bazai banza da ita haka ba. Ta K’araso parlorn jikinta dik a mace. D’ago kan da zatai taga gidan an canza masa tsari gaba d’aya. Kaf kayan dake cikin gidan an canza an zuba sabbi.. Taci gaba da takowa a hankali tana kallon tsarin gidan.. Gidan da tai zaton bazata kuma dawowa cikinsa ba. Gidan da tai masa lak’abi da GIDAN ARO. Zuciyarta ne ya yanke sanda ta tuna tangamemen hotonsa da Safeenah da ake soma hangowa idan ka nufi staircase. Ta d’ago idanu tana duban spot d’in da hoton yake.. K’irjinta ya kuma bugawa sakamakon ganin nasu hoton da tai.. Hoton da aka masu suna zaune a park farkon fitarsu mission da sukai tare. Ya matso da bakinsa kusan kennenta yana fad’a mata dik abinda suke acting ne cikin mission ne Ita kuma Ta saki murmushi wanda tasan yak’e ne kawai amma sai gashi a hoton baiyi kama da acting ba. Komai looks real kaman dai soyayya ce ta gaskiya. Ta saki murmushi a hankali still idanunta na kan hoton.
Juyowar da zatai ta gansa tsaye bayanta fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai ta d’an sha jinin jikinta ta sadda idanunta kad’an.
Ta soma takowa a hankali ta K’araso gaba gareshi. Still idanunta a k’asa take furta “Fushi kake dani.?”
Bai ce mata komai ba Sai dubanta da yake.
“I’m sorry.. Bansan maganar zai b’ata maka rai ba.. Kai hak’uri kaji..” Ta k’arashe muryarta na rawa kaman zatayi kuka.
D’an takowa yai ya matso dab da ita sosai kafin ya kamo hannayenta, ta d’ago idanunta kwantattun k’walla tab cikinsu tana dubansa. Murmushi ta hango saman fuskarsa wanda ba lallai ka fahimci hakan ba sai idan domin kai akayi.
Ya juyar da ita had’ida rungumarta ta baya ya d’aura hannayensa saman cikinta, su duka biyun suna fuskantar hoton nasu.
“Did you like my surprise..? Tsarin gidan ya miki..?” Ya tambaya yana rank’wafo da kansa kad’an zuwa wuyanta.
Mr Inspector kenan komai nasa burgeta yake. Wato bazai amsa mata ba saidai ya nuna mata a aikace. Ta lumshe idanunta kad’an kafin ta jinjina masa kai ba tareda Ta iya furta koda kalma ba.
Ya murmusa kafin yaci gaba da fad’in “Nan gidanki ne.. Everything here is yours.. Komai da komai dake cikin gidan naki ne.. Including me..” Ya k’arashe cikin wane irin siga mai kashe mata jiki.
Hawayen da suka jima mak’ale cikin idanunta suka gangaro.. Ba komai ta tuna ba face farkon zuwanta gidan da ya jaddada mata cewa gidan tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta wanda za’a iya sallamanta ko yaushe.. ta zauna cikin shiri sann kar ta baje kolinta dan ga duk mai hankali da hangen nesa ba’a baje koli a GIDAN ARO. Sannan dik abinda aka ce maka na aro ne akwai ranan da za’a karb’i wann abun. Hausawa sunce Kayan aro baya rufe katara.. Sann dik daren dad’ewa zaka mayar da abinda aka ara maka..
Juyo da ita yai suna fuskantar juna, ya saka yatsarsa guda yana goge mata hawayen dake gangaro mata.
“Baki son gidan ne.. Ko tsarin ne bai miki ba..?”
Ta Ware idanunta tana dubansa “Komai yayi mun... Thank you for this wonderful surprise.. But do you know something..” Ya tsareta da idanu, yayinda taci gaba da fad’in “Kaid’in kafi mun duk abinda ka zuba cikin gidan nan.. Soyayyarka da k’aunarka a gareni sun isheni..” Ta jinjina kai kad’an hawaye naci gaba da gangaro mata “A baya wad’ann k’yale k’yaleni sune mafarki na kuma sune burin Sadiya.. Nayi zaton Sune kad’ai suke haifar da soyayya.. Nayi zaton idan babu su babu wata kalma da ake kira So.. Saidai bayan had’uwata da kai na yarda akwai wann kalma da ake kira So koda babu k’yale k’yale na rayuwar duniya wacce za’a tafi a barta a nan duniya.. Ba kaman mutane guda biyu da suka rayu domin Allah suka so juna dan Allah.. A ranan k’iyama Allah ya tadasu tare.. Shin akwai soyayyar da tafi wann..?” Murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta. Yayinda Mu’azzam ya k’ura mata idanu yana jin kalaman nata har cikin b’argo da tsokarsa.
Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “Akwai abubuwa da dama da Allah zai baka a duniyar nan kasan cewa ya gama maka arziki.. Kaman dai arziki na lafiya wacce babu arzikin da ya kaita bayan kaancewarka musulmi mai kad’aita Ubangiji.. Bayan naga Mamy da halin da ta tsinci kanta ciki na jarabawa Tabbas na yarda k’yale k’yale na duniya ba komai bane face rud’i ne na d’an wani lokaci da yake k’ayadadde.. Mafarki na ne a baya na kasance cikin daula da tarin arziki... Amma a halin yanzu na shafe wann mafarkin.. Kaine mafarki na.. Kuma kaine cikan burina Mr Inspector... Ina fata na rayu dakai a nan gidan Duniya wanda yake GIDAN ARO ne.. Sannan a rayuwa na gaba Ina fata Allah ya kuma tadani da kai k’ark’ashin Inuwa guda a gidan Gaskiya.. I love you so much my Detective..” Ta k’arashe tana mai rungumarsa.
Rungumeta yai yana mai lumshe idanunsa shid’inma siririyar Hawaye ta gangaro masa “I love you.. I love you more my Beautiful Stubborn head.” Ya k’arashe yana mai kuma matseta jikinsa.
Soyayya suka dinga nuna ma junansu wanda ya tabbatar masu cewa sud’in sunyi kewan juna sosai da sosai. Babu kaman Mu’azzam wanda har saida Sadiyar Ta tausaya masa taga wautanta da tace zata kwana gida bayan shafe kusan sati da yai baya tare da ita.
**
Coin d’in ya dinga juyawa yana tuna lokacin da yake k’arami cikin stuff d’in mahaifinsa ya sami exactly irin wann coin d’in wanda tsakiya an rubuta _Black African Team_ mai hakan yake nufi.. Ya akai ya sami exactly irin wann coin d’in a wajen Habeeb k’anin Sadiya..? Kodai su Danger ne suka yasar da Coin d’in a gidansu Sadiya Habeeb ya tsinta..? Toh kenan wann coin d’in ta iya yuwa nada alak’a da su Danger kenan..? Toh amma idan wann coin d’in nada alak’a dasu Danger ya akai ya sami irinta a cikin kayan mahaifinsa..? Gaba d’aya kansa ya k’ulle.. Anya coin d’in iri guda ne..? Babu abinda zai had’a mahaifinsa dasu Danger.. Ya dafe kansa kad’an kafin ya furta a fili “Su waye su Danger.?” Ya bama kansa amsa da fad’in “Sune mutanen da suka kashe mun k’anwa Ikram..” “Toh idan wann coin d’in nada alak’a da mutuwar Ikram kenan ta iya yuwa mutuwar mahaifinsa ba accident bane..? What if shiryawa akai..? What if su Danger Sun jima suna bibiyan ahalinsa..? What if mutuwar Daddynsa shiryayya ne..? Zuciyarsa yai wani irin yankewa. Ya shiga girgiza kai yana dafe kansa wanda gaba d’aya ya masa nauyi komai ya cunkushe masa. Tunanin yanda ya aje wancan coin d’in ya soma.. Ya zama dole yai comparing coins d’in ya tabbata idan sunada kamanceceniya. Da wann tinanin ya aje coin d’in gefen bedside ya janyo sadiya dake bacci zuwa cikin jikinsa, ya lumshe idanu yana shak’an k’anshinta mai sanyi wanda ya sauk’ar masa da natsuwa cikin zuciyarsa.
**
A can Fufore kaw Shemau k’arfe shad’aya na dare ta soma bugun k’ofar gidan k’awarta Baddo.
Da k’yar Baddo ta k’araso ta bud’e k’ofa cikeda tsoro dan dama mijinta baya nan yayi tafiya ga yanda duniyar ta zama kowa kaffa kaffa yake da rayuwarsa.
A razane Baddo take k’ok’arin tura k’ofa tana karanto addu’o’i dan Ta zaci mahaukaciya ce ko gamo tai cikin daren.
“Baddo nice Shemau dan Allah kar ki rufe k’ofar.. Ki ceceni Baddo banida yanda zanje. A cikin uku nake..!”
Baddo ta dafe k’irji tana duban Shemau cikeda tsoro dan bata ma ganeta ba saida Shemaun tai magana “Shemau kece haka..? Mai zan gani ni Baddo..”
Kuka Shemau Ta fashe mata dashi tana fad’in “Baddo ki taimakeni.. Wllhi cikin tara nake bama uku ba..”
Baddo ta shiga salallami tana tafe hannaye tana duban Shemau cikeda tsoron duniya..
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*55*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Baddo ta canza position d’in taguminta yafi sau abinda yafi “Ni babu abu guda dana fahimta Shemau. Kinaso kice mun tin jiya da dare abin ya faru.. Toh a ina kika kwana..?”
Gajeren tsuka Shemau tai “Duk wann ba lallai kiji ba Baddo tinda Allah ya taimaka na wayi gari.. Da ace jiya kika ganni nayi imani Bazaki ganeni ba.”
Baddo tace “Yanzun ma da k’yar na ganeki wllhi saida kikai magana.” Ta ida maganar tana aje mata plate d’in indomie da ta dafa mata.
Shemau ta janyo plate d’in ta soma nad’an abincin hannu baka hannu k’warya.
Baddo ta rapka uban tagumi tai zaune gefe tana kallon Shemau matar Alhaji Salman Gamji yanda ta fice a hayyacinta cikin lokaci k’ank’ani. Ta gyara zama tana kuma canza position d’in taguminta “Wai ni mi ya faru dake ne.. Mai ya jefaki cikin wann ukun..?”
Shemau ta dubeta sai kuma tace “Safeenah ce ta jefani cikin wann bala’in.”
Baddo ta girgiza kai tace “Safeenah kuma..?”
Shemau ta janyo ledar pure water ta huda tana zuk’a saida ta shanye tas kafin ta dubi Baddo tace “Yo Safeenah Ta jazamin da na d’auki shawarinta..”
“Kika d’auki shawarinta kaman yaya..?”
“Kinga Baddo ke k’awata ce kuma rugarmu d’aya tare muka taso.. Kin sanni na sanki babu wata ‘yar b’oyo a tsakaninmu dan haka zan fayyace miki dik abinda ya faru.” Ta gyara zamanta tana karanto ma Baddo duk