Showing 1 words to 3000 words out of 67070 words

Chapter 1 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt

03 Sep 2024

9653

GAMO


*BILLY GALADANCHI*


1.


********************** ⬇ **************************
********** Arewa Novels ****************
*************************⬆ **********************
08137237071


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.arewanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


A sukwane ya fito daga ɓangaren da yake mallakin sa agidan. Kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar wannan ɗan kwalisa ne, Yana sanye da riga fara ƙal shirt ƙirar kampanin Mk, da wandon jeans blue shi ɗinma kamfanin Mk ne, agogon hannun sa Rolex ne wannan kuɗin sa zekai kimanin dalar amurika dubu goma! Akwai zoben a hannun sa wanda ya ƙarawa faratan nasa kyau. Takalmin ƙafar sa baƙaƙe ne normal shoe ƙirar kamfanin Mk. Ƙamshin turaren sa yana mamayar duk duniyar daya nufa sabida tasirin sa, Turaren Tomford the king ne ajikin sa, haɗe da wani Arabian king oud! Fuskar sa ba fara bace sam sedai bazamu kirashi baƙi ba, kyakyawan daidai kyawawan ƴaƴan hausawa, fuskar sa tana ɗauke da tsawo da ɗan faɗi kana kuma akwai zagayyayen saje wanda yake haɗe da kwantacciyar sumar kansa, yayi zagaye zuwa gemun sa. Yanada wushirya bakinsa a zagaye yake da laɓɓa masu ɗan tudu sedai ɓa cen cen ba. Yanada dogon hanci samɓal tare manya manyan dara daran idanuwa dasukeda yalwar fari, baƙin zagayen idonsa daga ciki baƙi ne amma a gefen sa yaƴi kalar bulu. Yanada tsananin cikar halitta zamu iya cewa ƙirar sa tafi kamada ƙirar samudawa madaidai ta. Kana kallon sa zakaga ƙarfafan mutum dankuwa nonuwan sa tas sun cike ƙirjin sa, ga 6 parks ruɗum ruɗum a cikin sa, ƙasan sa ya tsuke amma kafaɗunsa da faɗi cikakken mutum me kamala.
Da ɗan sauri ya isa cikin falo na ɗaya inda ya tsallake wannan falon yayi kutse zuwa falo na biyu har zuwa matakin na uku inda ya tarar ana yiwa mahaifiyar sa Makeup zataje taron ƙarawa juna sani da aka gayyace ta. Zubewa yayi ya gayar da ita cikin girmama wa, da fara'arta ta amsa masa sannan tace,


"Hakeem sai ina kuma?"
Murmushi yayi sannan ya ce


"Maganar tafiyar damuka yi ne lagos Ummi, flight namu ze tashi by 11 this morning" Ɗan ɓata fuska ta yi,


"Amma ba nace ka dena zancen tafiyar nan ba sai next week Hakeem?" Sosa kan sa yayi cikin jin nauyin abinda zai faɗa kafin yace,


"Ummi Nihal, fa tafiya zatayi yau itama, dan Allah ki barni naje, tafiyar ta aiki ce, yanada muhimmanci sosai kuma" Nisawa tayi ta zaro wayar ta cikin damuwa, 'har sai yaushe Nihal da Hakeem zasu basu haɗin kai a harkar nan?' Ta ayyana a ranta, tana me kiran wayar Babbar aminiyar ta wato Hajiya Baraka mai gwal. Da Sallama ta ɗaga call ɗin ta tana fara'a suka gaisa sannan ta ce,


"Hakeem yace Nihal bata gari?" Murmushi ta yi sannan ta ce,


"Nihal gatanan a kusa dani, tabbas tafiya takeso tayi amma Daddyn ta ya hana ta banda kuka ba abinda take" Sauke Numfashi tayi kafin ta ce,


"Hakeem ma gashinan ya kafe akan lallai seyaje Lagos, tafiyar aiki ce, ya zamuyi kenan?


"Your Excelency ki barshi ya tafi, koda kin hanashi a yanayin yanda Nihal take bazata bamu haɗin kai ba, inyaso idan ya dawo semu zauna" Godiya tayi mata tare da sallama sannan ta ajiye wayar taci gaba da baiwa me makeup.haɗin kai batare data kuma waiwayar Hakeem ba, shikuwa yakai 40mns har aka kammala makeup bata bashi izinin tafiya ba, ta miƙe zata fice yabi bayan ta har wurin mota, seda aka buɗe mata ta zauna sannan ta rage glass ta kalle shi, duk yayi kalar tausayi


"Hakeem wai menene? Tamkar zeyi ƙwalla ya ce,


"Addu'a Ummi tafiya fa zanyi" kawar da kanta tayi gefe,


"Inada taro Allah ya kiyaye" Ta zuge glass sama ta bada izinin tafiya take convoy ya tashi. Sumar kansa ya shafa cike da damuwa, 'Ummi duk in zeyi tafiya takan dafa kanshi ta masa addu'a mesa zata masa haka yanzu kuma?' Agogon hannun sa ya kalla sannan a ƙagauce yabar wurin zuwa wurin motocin dasuka jeru sama da goma suna jiran sa, faɗawa yayi yana me addu'ar neman kariya ta barin gida.


****************
"Momy na Haɗaki da Allah ku barni.naje, dan Allah da manzan sa Momy, zamuyi Fulani's day out, zamuyi kanuri momy duk acen, Momy babu wata matsala a ƙauyen fa, inshaa Allah wannan karon da zanje baza'a samu matsala ba" Nisawa Haj Baraka tayi kafin tace,


"Nihal zan barki ki tafi saboda farin cikin ki, inaso kema ki dubi Allah ki faranta mun idan kin dawo, sannan zan gayawa Daddyn ki kinje jigawa kawai amma bazance ƙauye ba, kiyi a hankali kar kuma kizo kina wasa da azkhar ɗinki, safe da yamma" Tsalle ta daka ta faɗa ajikin Momy har tana mata kiss a kumatu,


"I love you Mom" Dariya tayi na ƙarfin hali dan harga Allah hankalin ta be kwanta da tsfiyar ba, Jiki ba ƙwari ta miƙe sannan tace,


"Bana so Excelency ta rigani isa wurin taro, zan gayawa Bouncer's huɗu suje da ke a motoci uku" Kallon Momy tayi cikin damuwa,


"Momy that will definately be too expose, ki barni inje da ƙawaye na dan Allah" A nutse ta kalle ta kafin tayi magana,


"Idan bazaki je da suba anfasa yafiyar" Ba yanda zatayi dole ta haƙura dasu ɗin momy tana fita ta kira ƙawayen ta suka hau sowa, dama 30mns ya rage subar garin kuma a shirye take tsaf dan haka ta fita tare da guads kamar yanda Momyn ta ta faɗa.


Khaleesat tana ganin guads ɗin nan gaba ɗaya ta ɓata rai, cikin jin haushi tace tana kallon Nihal,


"Niha gaba ɗaya so kike ki ɓata mana tsarin nan wallahi, me kuma waɗannsn ƙartin zasu mana anan? Dan Allah send them sway" kallon takaici Niha tayiwa guads ɗin,


"Leesat wlh Mom ce, ta kafe akan lallai sena tafi dasu sabida tsaro" Tsaki Leesat taja me tsayi,


"kinga ƙawata basu 200k suce su kama hotel na 2days ɗin da zamuyi su huta, karsu nuna kansu a gari har sai mun dawo" Shiru Nihal tayi tana nazari kafin tace


"Ohh Na fahimci me kike nufi yanzu, zan basu 300k su kama hotel da 100k 200k suci abinci for 2days" Sowa suka kuma yi sannan suka tafa, suka juya domin gudanar da ƙudirin su na korar guads ta hanyar siyesu da kuɗi.


A waiting centre inda boader's suke zaman jiran kira domin tashin jirgin su kuwa, Hakeem ne a kishingiɗe, yayi resting bayan shi saman seat, soyayyar Hudy tana huda sassan jinin jikin sa, tayaya Abi da Ummi zasu rabashi da farin cikin sa? Tayaya ze rayu batare da hudyn saba? Duk tsananin iko da kuma ji da kansa daya ke ace matar auren sama se an zaɓa masa? Baze taɓa cikawa Ummi da Abi wannan burin nasu ba sedai suyi haƙuri! Wayar sace tayi ringing a hankali ya janyo ta daga aljihun wandon sa ya ƙurawa screan ɗin ido har seda call ɗin ya yanke sannan ya kira back, Tana ɗaga wayar da shagwaɓa ta fara masa,


"Honey ni dan Allah haka zakamun? Na saka raina da ganin ka amma babba dakai kace wai Ummi ta hanaka zuwa, yadai dace kasan ka girmi haka" Sauke nannauyan ajiyan zuciya yayi, shida kanshi yasan Huddy ba tada tarbiya amma idan ya rabu da ita soyayyar ta fa ta kashe sa? Lumshe idon sa yayi sannan yace


"Hudy ina Airport zanzo sokoto yanzu, kina bani wahala da yawa huddy, ki sani ina miki so wanda ban taɓa yiwa wata halitta makaman cin sa ba, dan kawai inzo in ganki i had to lie to Ummi, yau ɗinnan ko addu'an datake riƙe kaina tamun idan zanyi tafiya batayi ba because batasan tafiyar kwata kwata" Ɗan gajeran tsaki taja a zuciyar ta tace 'Ko kinaso ummi ko bakya so sena zama matar ɗan president' a sarari setace,
"Kai so sad, am sorry it makes u cross the limit,na sanka sam baka ƙarya" Murmushi yaƴi,


"For the very first time in my life i lied because of you my gurl, i lied because i love you" Kafin tayi magana an soma sanarwar kiran passengers matafiya sokoto, inda da hanzari ya miƙe yabi bayan ƴan uwan tafiyar sa yana kashe wayar sa.


*******************
Ummi gaba ɗaya hankalin ta be kwanta da tafiyar nan da Hakeem ya matsa akan zeyi ba, tasan halin sa tsaf, yanayin sa kaɗai ya nuna mata cewar akwai abinda yake damun sa, Hakeem ya tsananta akan ƙiyayyar Nihal ita kuwa auren Nihal ɗin yanada matuƙar amfani agare sa take ga ko nan gaba, baya ga haka Nihal nagartacciya ce, tare suka taso da mahaifiyar ta, sun zama tamkar ƴan uwa meye abin gudu ajikin ta? A ranta tace 'Lallaɓashi zanyi tare rarrashi har yazo ya fahimci manufata'. Sanda ya isa sokoto, driver abokin sa yazo ya ɗaukeshi take awurin ya kashe wayoyin sa, kai tsaye masauki ya isa ya buƙaci cin abinci cikeda ƙyama shi yana da tsananin tsafda da tsanda iyayi ga masifaffen ji da kai! Se bayan Magrib ya buɗe wayoyin sa Ummi ya fara kira ya tabbatar mata ya shiga meeting ne yasa wayoyin sa akashe, ta masa addu'a sannan suka yi sallama. Runtse idan sa yayi haɗe da sosa kanshi cikin damuwa, shi baya ƙarya wannan halin sane da kowa ya sani me kyau, mesa yanzu yake ƙarya? Yama rasa wazai yiwa ƙaryar sai ummin sa. Huddy ya kira akan gashinan zuwa gidan su ta shiga kintse kintse da shafe shafe, duk wani turare da boka ya bata saida ta dangwala hatta kwallin idon ka ido na daya bata seda ta shafa tukunna ta zauna zaman jiran zuwan sa.


Kai tsaye ƙirjin sa ta faɗa ta kwanta lub, "Oyoyo Honey I missd you alot" Murmushi yayi ya ɗan janye jikin sa "Huddy zaki fara ko? Cikin shagwaɓa tace


"Its just a hug fa, kakuma san its bn long na ganka, plss ka barni ko 5mns ne" Janye jikin sa yayi gaba ɗaya "Wannan ma ya isa sanda zaki zama Halal ɗina komai ma zamuyi" Ba haka taso ba amma haka ta haƙura ta zauna suka ɗan taɓa hira, sannan ta gabatar masa da abincin da gaba ɗayan sa barbaɗe barbaɗe ne boka. Haka yaci wanda zaiji suka sha hirar su sannan yayi ɓarin naira agidan su ya koma masaukin sa.


Nihal kuwa sun isa ƙauye lafiya anan aka shiga hidimar duniya ana zagayen ƙauyen ana dariya, ɓarin naira ake tayi a garin kuwa. Nihal shanaye goma ta siya ta bayar kiwo tare da bada kuɗaɗen abincin shanayen ga wani kawun ƙawar ta akan amata kiwo tana tsananin son kiwo. Sanda suke zagayen kasuwa Nihal da ƙawayen ta ƴaƴan masu naira sai sadaka sukeyi da kuɗi, haɗuwar su da Barde shine babban kuskuren su a rayuwa! Leesat ta kalle sa tana dariyar shaƙiyan ci sannan tace


"Tabb sena tuna wani labari da ada muna ƴara muke karantawa a school, labarin ƙurungu sarkin kawuna, ashe dama akwai irin su a duniyar zahiri! Gaba ɗaya suka saka masa dariya, abinda ya basu mamaki suma se suka dara, Nihal tace "Leesah wai mesa bakida kirki ne, halittar Allah ne fa, kai ɗan ƙauye ungo zoka karɓa" kallon Nihal yayi data kirashi da ɗan ƙauye ya matsa ya karɓa kyautar dubu ɗaya datake miƙo masa yaƴi godiya, tana kallon sa tace


"Malam ƙurungu dan Allah makiɗa muke so, masu ƙidan fulani zamuyi biki acikin jejin cen" Kallon sosai yayi mata kafin ya ce,


"Wanne jejin? Leesah ce tace


"Jejin ɗan sadau" Murmushi yaƴi


"Nasan da shagalin bikin, ai kuna matsawa wurin masu kalangun cen shikenan angama magana" Godiya sukai masa suka nufi wurin. Barde da sauri yaje ma ɓoyar su a kusada Oga ya zube yace


"Yallaɓai tasamu, inaga aiki biyu zamuyi gobe" Oga mahe yana busar sigarin bakin sa ya ce,
"Ya ake ciki ne?


"Oga baƙi ne agarin nan ƴaƴan manya damuke nema ido rufe, ko fyaɗe mukayiwa shegu mun huce haushin iyayen su" Dariya Oga yayi yace


"Nasan dasu Barde, duk kashe su zanyi, idan munje kwasar shanu gaba ɗaya harbesu zanyi, iyayen su suyi abinda zasuyi" Nan suka hau sowa aka shiga tsara yanda kisan ze kasan ce, Barde yace "Wayaga yaran manya a hannun mu, zanso ganin iyayen su suna kukan mutuwar su a TV ni kuma ina dariya" Haka suka zauna tsare tsaren mugun abu har kusan isha.


*****************


Washe gari Hakeem ya shirya dawowa gida Abuja, yaga Hudaisa hankalin sa ys kwanta, ya zama dole ya dawo gida ko hankalin mahaufiyar sa ze kwanta, ya fahimci sam bata cikin nutsuwar ta akan tafiyar sa. A sukwane ya ɗale matattakalar jirgin, mutanen dasuka san yaron president ne sai bibiyar sa suke da gaisuwa, 'Yan jarida kuwa suka masa caa inda saida ya tsaya suka ɗan gaisa suka masa tambayoyi wannan ziyarar ta ba zata daya kawo a sokoto, yake shaida musu personal abu daban ya kawo shi.


Jirgin su Hakeem ya nutsa sosai akan gajimare sanda matuƙin jirgin ya fahimci cewar jirgi fa babu lafiya!! Yayi iyakar yinshi amma gaba ɗaya seya zaman control ya ƙwache masa, abokanan aikin sa sukazo amma jirgi sai shawagi yake a yamutse. Dole suka yi anouncing kowa ya ɗaura rigar iska ya zama acikin shiri dan jirgi yana shirin tarwatse wa! Innalillahi wa inna ilaihiraji'un itace kalmar dayake ta nanata wa. Ɗaukacin mutanen jirgin se kuka suke suna saka rigunan domin fita daga jirgin amma banda Hakeem. Ya runtse idan sa gagam yana hango mutuwar sa ayau. Be shiryawa rayuwar sa ƙarewa a yanzu ba, beyi tanadin tadda mahaliccin saba, ya gina abubuwan more rayuwa iri iri a rayuwar sa ta gaba, ya shirya ƙyale ƙyalen more rayuwa bila adadin sabida sabunta ingancin jin daɗin sa!! Tabbas mutuwa tayi masa shigar sauri, babu amfani shiga acikin jerin masu kokawar ceton rayukan su, tabbas idan yana daga cikin ƙaddarar rsyuwar sa mutuwa a jirgin nan baze tsira ba komai son sa da rayuwar sa, mutuwa ita kaɗai ce aba dabaza ka iya faɗar yaushe kakeso kayi ta ba, kaico inama yasan idan ya shigo jirgin nan tabbas ta shi ta ƙare da babu wata ilar dazata kaishi waha jirgin ajalin sa!! Duk irin addu'ar dayake sabida kawai ya samu tsira hakan be hanawa Jirgin tarwatse ba ji kake tassss!!! Tamkar tashin Bomb!


*KADA KU MANTA ƘITTAFIN GAMO NA KUƊI NE, ME BUƘATAR CI GABAN SA SEYA NEMENU TA WANNAN HANYAR.*




*✨TAURARI✨*


*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼‍♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩‍🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.


Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai. Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.


Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.


2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500


Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.


Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku tura kuɗin ku ta wannan lambar Acc ɗin.
2029764071.
First Bank
Nafisa Nuhu.
Shaidar biya ta wannan lambar
08033719070.
Idan kuma katin waya zaki tura,seki tura katin mtn ts wannan lambar wayar.
07084161619
Shaidar biya ta
07084161619


Muna maraba daku.
Mungode💃🏻💃🏻💃🏻.
9/11/21, 6:58 AM - Buhainat: *GAMO!*

*BILLY GALADANCHI*






2.


Ummi tana zaune kawai taji wani mummunan faɗuwar gaba ya ziyar ce ta! "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un itace kalmar data furta a hankali, wayar salular ta ta janƴo ta kira His Excelency the president, sedai kamar ta sani bazata shiga a matsayin call ba sedai voice mail later when he is less busy ze kirata. Akalar kiranta ta mayar ta zuwa Hakeem wanda tayita faman kiran wayar sa arufe gaba ɗaya. Dik abinsa akwai layin da sam baya taɓa rufe sa shine layin sa na Family, lokaci yayi daya kamata ace sunyi landing daga lokacin da ƴakira akan zasuyi boading, meye Lagos zuwa Abuja? Tsaki taja a hankali dannan ta tabar cikin falon tana addu'a Allah ya dawo da Hakeem lafiƴa dan gwara Abi sunyi waya kuma tasan shida Nigeria sae Next month!


Dayawa daga cikin mutanen dasuka fara fita a jirgin suna cen suna yawo a saman iska sanda ya tarwatse, matuƙan jirgin sunso sosai su faɗa a ruwa amma kafin sukai ga isa acikin ruwan jirgin yaƴi watsewa mafi muni, Hakeem be ƙara tuna kansa a ko'ina ba, ya sare dama yayi imanin shida rayuwa sedai a lahira idan anayi, shikenan Ummi, Abbi, Yaa mamu, Zuhar ƙanwar sa gaba ɗaya bazai ƙara ganin su ba har abada, Huddyn sa ma wani zata aurah shikenan be bar koda ƙadangaren dazai masa addu'a ba sai ummin sa, Daddy ayƴuka sun masa yawa wataƙila baze wuce shekara ba zai manta dashi, tun yana wannan tunanin har numfashi ya ajiye masa!!!!

Ƙarar saukar bundiga shine abinda ya tashi ɗaukacin matan dasuke je biki daga bacci suka soma neman tseratar da rayuwar su ta hanyar shirin gudu, Nihal dake a ranaze ta kalli Khaleesat tace,


"Munshiga uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login