Showing 9001 words to 12000 words out of 67070 words
Chapter 4 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
"HAKEEM! HAKEEM!" Ta kira sunan sa yakai so ɗari, tun tana yi tana kuka har muryan ya dushashe hawayen idan ta ya ƙafe tas! Gaba ɗaya ta dena gane komai tashiga tashin hankali mara misaltuwa. Sai da taga rana ta faɗi tukunna ta nemi hanyar tafiya inda Khaleesa, ta sani yanzu ta fara buƙatar taimakon ta, a hanya sanda ta sama mata mangoro da goba data bishiyar su ta ɗeba tare da yin bismillah kafin ta ɗeba ɗin. Dik iyakar ƙoƙarin Nihal ta rikice a hanyar nan, ta tabbatar tayi shaida amma gaba ɗaya saida ta rabo inda take rabi saita dena ganin tsinkar hakin data tara da alamar inda ta tugeshi, abinda ta fahimta musamman shine inda ta baro ba'ayi ruwan sama ba amma tabbas nan yankin an tsulala ruwa mai yawan gaske, haka ta saka aranta zata gane taci gaba dabin hanyar a sukwane tana fatan ta tarar da khaleesah lafiya.
A ɓangaren khaleesa kuwa Nihal bata haɗa mintuna 30 da tafiya ba ruwan sama ya sauka tamkar da bakin ƙwarya, tayi ƙoƙarin jan gindi taje ta laɓe ajikin bishiya amma gaba ɗaya saita kasa, dan haka anan take har ruwan ya fara harya ƙare, wani irin azababben sanyi ya kamata, nan take ta shiga makyarkyata, gaba wasu suturun kirki a jikin ta, lokaci daya khaleesa zazzaɓi ya rufe ta, wani mugun ciwon kai ya taso mata, nan take ta soma zubar da ƙwalla. Ganin ruwan ya tsagaita ya sanya ta ɗaga murya ta fara kiran "Nihal! Hakeem" Amma ita ɗinma har duhun dare ya sauka tana nan acikin taɓo da azababben sanyin dake kaɗawa babu wanda yazo ya kawo mata ɗauki. Haka tayi taimama ta dungura sallah, ga zazzaɓi tana ji kamar ta tashi sama. Wannan lokacine na tsananin damuwa awurin khaleesa, batayi zuwan rashin jin magana a ƙauyen ba, hasalima cewa tayi bazata zoba, mahaifiyar ta tace sam dole tazo tayiwa babbar ƙawarta kara ita ba mazauniya garin abuja bace, addu'a dai itace ta saka a bakinta taketa yi har sanda wani ruwan ya kuma ɓallewa, wanda atake ta samu attack na athsma, tun tana gane me ake ciki har ta shafe tatas!
Nihal kuwa gaba ɗaya bata tunanin kanta sai ƙawarta, idanta a rufe yake sosai akan khaleesah, ita da khaleesah sunsan junane ta hanyar ƙawarsu Amarya Sa'adatu, amma ba sanin yanzu ba, tuni suma suka ƙulla kawance saidai ba cencen ba. Nihal yarinya ce ƴar ƙwalisa mai asalin ji da kanta, tana da fara'a da kyau na nunawa sa'a gaba ɗayan ta ba fara bace ba baƙa ce irin baƙin nan na afurkawa mai sheƙi da santsi, fatarta sumul take kuma a murje kana kallon ta zakaga asalin ƴar hutu, yanayin zubin idan ta yanayi ne na idon ƴaƴan indiyawa, dan kuwa mashaaa Allah idan ta zube maka idan ta saikaji tamkar ka ruga, manya manya gasu farare tas zagayen baƙin baƙin wuluk, layin ƙasan idanta da kwallinsa yazo bata buƙatar yawan saka kwalli, hanci siriri dogo na usul ga ɗan jinjirin bakinta mai ɗauke da haƙwara farare tatas sedai ƙwaya biyu na gaba sunada tsayi, ilahirin jikinta shape ne mai asalin kyau tanada tsayi sosai sedai batada cikar ƙirji, a takaice dai Nihal baƙa ce sosai amma me kyau na usul. A ɓangaren halayya tanada isa, son mulki, nuna cewar ita wata ce, raini ɗagin kai uwa uba kuma ji da kai, saidai kuma tanada tausayi sosai musamman akan talakawa, tana son ƙananun yara sannan kuma tana tsananin son yin kyauta, wannan halayyar ta raina mutum ya sanya tun farko Hakeem ya tsaneta, amma fa tsanar datake masa tafi wacce yake mata dan ita ta damashi ta kuma shanye tatas a ɓangaren ƙiyayyar nan, kallo take masa na Namiji mai ji da isa, wanda baisan darajar mata ba, ita arayuwa bata burin auren mai kuɗi tana kula da yanda mahaifiyar ta ke shiga kewa duk sanda mahaifinta yayi tafiyar wata biyu ko uku, dan haka nema ta zaɓi zaid sama da Hakeem ma'aikaci a NNPC domin tasan zai samu lokaci na tattalin ta kamar yanda mazan novel sukeyi, saɓanin Hakeem dayake ɗan shugaban ƙasar su gaba ɗaya yaron da kafin zuwan mulki ya taso sosai a gidan masu hali ƴan kasuwa, tin dama cen Hakeem ɗan masu naira ne.
Hakeem yanda yaga ake tsula ruwa ya tabbatar wa kansa cewar matan nan suna cikin matsala, ga duhu sosai shima kenan dayake da torchlight ta waya inata gasu da gaba ɗaya suke ɗif, hankalin sa ya tashi sosai ya shiga ruɗu, inda ana ruwan ya tsingo ganyen bishiya masu faɗi ya nannaɗe wayoyin sa ya musu maɓoya a kunkurun sa ya fito neman su acikin ruwan.
A gida an kammala zaman makokin su duka uku, iyayen su har yau suna ɓaƙin ciki da rashin samun koda gwarsu ne, haka suka haƙura suka ɗauki abin a matsayin ƙaddara, danshi mahaifin Nihal baiko tuna akan basu sanar masa labarin tafiyar taba, tsananin baƙin cikin daya shiga a rayuwa!
A hankali Nihal take tafiya jin taku a bayanta bayan tsagaitawar ruwan, bataso ta waigo sabida batasan dame zatayi karo ba, babu namun jeji ko ɗaya a jejin tana mamakin wannan wane irin mugun jeji ne! Tsit daga kai ne sai halinka, addu'a takeyi taga hanyar dazata sadata da ƙawarta ko zata samun nutsuwar zuciya, tabbas abokin tafiya ma rahama ne babba, dan kuwa ji take tamkar tayi fukafiki ta tashi a sama kowa ya huta! Takun sosai yake matsowa kusa da ita wannan ya matuƙar gigitar da ita, walƙiya akayi me hasken gaske, ji tayi an cirgo ta bayan rigarta ta faɗa jikin abu, lokaci ɗaya tare da wata iriyar tsawa dats gigita duniyar ta fiye da jan da akayi mata, wata razananniya ƙara da ƙwalla tare da ambatar "Wayyo momy!!!"
Mom Nu'aiym.
*✨TAURARI✨*
*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.
Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai. Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.
2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500
Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku tura kuɗin ku ta wannan lambar Acc ɗin.
2029764071.
First Bank
Nafisa Nuhu.
Shaidar biya ta wannan lambar
08033719070.
Idan kuma katin waya zaki tura,seki tura katin mtn ts wannan lambar wayar.
07084161619
Shaidar biya ta
07084161619
Muna maraba daku.
Mungode💃🏻💃🏻💃🏻 .
9/11/21, 7:00 AM - Buhainat: GAMO!*
*NA: BILLY GALADANCHI*!
7.
Hannun sa yakai ya rufe mata baki sannan a hankali Kunnenta ya raɗa "Daina magana Nihal, a gabanki akwai karen jeji kinji" Jin muryan Hakeem ya ƙara rikitar da ita, dukda yake ta tabbatar shiɗin ne saidai ta fara tunanin anya ba aljani bane yake mata gizo kamar hakeem? Yaushe yazo nan ɗin? Da sauri sauri take sauke numfashi har zuwa sanda ya saketa da kanshi.... Zabura tayi zata ruga da gudu ya kuma riƙota ta dawo jikin sa, har lokacin ta bayan sa take,
"ki nutsu idan baso kike ki ƙara ɓacewa a jejin nan ba, gaya mun yanzu ina Khaleesah, tunda na kasa mayar da kaina inda kuke yarinyar tayi tsaye a raina, na tabbatar tana shan wuya" Sauke nannauyan ajiyan zuciya tayi cikeda samun sassauci kafin tace
"Mutuwa taketa cewa zatayi, kai na fito nema, dan Allah karka bari ta mutu, wlh inason mu koma gida atare" Hannunta ya riƙe yana mejin zafin zuciyar sa fiye da da,
"Ɓata nayi Nihal, na rasa hanyan komawa agareku, wlh da ƙyar na sameku a yanzu, ita tana ina yanzu?
"Nayita neman hanyar komawa gareta ban samu ba, na ɓata nima a jejin nan wlh, gaba ɗaya nashiga matsala banda nutsuwa, khaleesah tana tsananin buƙata na a kusa da ita" Cikin damuwa ya ce,
"To yanzu ina mafita? Muje neman ta kawai" Haka suka rings bi inda suke tsammanin zasu ɓullo amma tafiyar harta kaisu asuba basuga koda mai kamada khaleesah ba, saima burguna da wasu ƙananun namun jeji dake tabbatar musu da cewar sun faɗo wani jejin mai namun jeji ba wancen ba!
Khaleesat tana kwance acikin taɓo tajiyo wasu muryoyi a saman kanta dabata gane wanne iri bane, ga dai magana rangaɗaɗam amma sam ba hausa bace ba kuma turanci bane kai gaba ɗaya ma ba yarurrukan damuka saba ji bane, da ƙyar ta iya ɗaga ido ta kalle su, mutanen datake yawan gani a film, ana cewa dasu ƴan zindirawa, masu yawi tsirara da ganye kaɗai suke rufe al'aurarsu ta gaba baya ko oho, lumshe idanta tayi bayan ta ƙare musu kallo sannan a ranta ta ayyana
"Lallai ni khaleesa na haukace, yanzu kuma gizo abubuwa suke mun" Tana nan lumshe da ido har suka ɗagata sunata wasu waƙe waƙe suna kiɗa sukayi gaba da ita, gaba ɗaya bata iya koda guttun motsi, tafiya mai nisa sukayi da ita, batasan inda zasuje da ita, ga bakunan su basu gajiya da waƙe waƙen ba.
Da sauri Hakeem ya riƙo hannun Nihal ya mayar da ita bayan sa, tare yi mata alama akan tayi shiru, ganin ƴan zindirawan nan ɗauke da khaleesah suna iface iface suna tsalle tsalle, cikin sanyin jiki ya ce a hankali
"Karkiyi magana dan Allah, wlh mutanen jeji ne sam basuda hankali, zasu iya kisa kai tsaye" Idon tane ya kawo ruwa a hankali ta ce,
"To me zasuwa khaleesah? Kaddai kashe ta zasuyi? Dan Allah kazo muje mu karɓo ta karsu kashe ta Hakeem" Da ssuri yace "Shshhhhhh, ki daina ɗaga murya, sannan kina haukane? Tayaya zamu tinkare su ai yankamu kawai zasuyi" A bayansa ta lafe haka suka ci gaba dabin bayansu cikin sanɗa har suka isa wani wuri mai kamada gari, gari ne ma tunda gashi nan akwai bukkoki da ɗakuna irin kara ba ginar laka ko bulo, agaban wani mutum aka ajiye khaleesa, tana kwance komai jinsa take tamkar a mafarki. Ana ajiye ta mutumin dake kan kujerar nan ya faɗo ya mata sujjada yana wasu surutai dabasu gane kan surutan nasa ba! Nihal da Hakeem kallon juna sukayi suna mamakin wannan al'amarin? Basu gama shan mamaki ba saida sukaga duk mutanen wurin sun taru sun zube suna sujjada! Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, Hakeem yace da Nihal
"Waɗan nan mutanen nasan labarin su, shekarun baya a Nigeria an taɓa samun mutane irin su, indai har labarin danaji gaskia ne toko tabbas muna cikin tsaka mai wuya, Abi ne da kansa ya gayamun an samu mutanen dake rayuwa a jeji su abu mai tai suke bautawa indai yakai girman akuya! Abi ya sanar dani idan suka zo abin bautar su ya mutu za'a zauna anata kuka na kwana bakwai, daga nan se a shiga jeji duk abu mai rai da aka haɗu dashi na fsrko yana motsi shine sabon abin bauta. Nayi tunanin irin su ne saboda yace haka suke yi sunata sujjada wa koma miye, wanka da komai yi suke masa koda dabba ne kuwa, hatta sarki abun yake bautawa. Idan har ba kuskure nayi ba tabbas wancen sarkin ne kuma kinga ya zube yana mata sujjada" Zufa ce t tsatsafowa Nihal a hankali tana kallon sa tace
"Yanzu ya zamuyi? Idan labarin ka hakane suma haka al'adar tasu yake kuma khaleesah ta faɗa hannun su, kenan dawo da ita hannun mu abune mai matuƙar wahala, bayan haka ko ƙoƙarin guduwa mukayi da ita tabbas zasu kamamu tunda sun fimu sanin kan jejin nan" Shi ɗinma zufa ya sharce a goshin sa sannan ya ce,
"Yanzu dai mu ƙara laɓewa mu barwa zuwan dare komai, yanzu ke ki adana kanki anan, niko zanbi bayan su duk inda suka kaita zan nemota inyaso cikin dare saimu sace ta mu gudu da ita" Jinjina kanta taƴi alamun gamsuwa sannan ta ce,
"You have to be very very carefull, mutanen nan wlh basuda hankali" Murmushi yayi mata baice komai ba kawai sai gani sukayi an saka wuƙa an fasa ƙafar Khaleesah dake ciwo, take wani jini ya tartse a firgice Nihal ta ƙwalla ƙara abinda ya janyo hankalin ɗaukacin mutan garin dake wurin zuwa ga inda suka jiyo sautin muryar mace, ita ma kanta Khaleesa wata uwar ƙara ta ƙwallah jin anyi mata wannan yankan! Sarki ne cikin yaren su ya ce a duba meyayi ƙara!!!!
*Manage zan sauke wani da yamma, ina typing ya goge wannan kaɗanne karku jini shiru.*
9/11/21, 7:00 AM - Buhainat: *GAMO!*
*NA: BILLY GALADANCHI*
*Iittafin GAMO da HUDA na kuɗi ne, dan Allah idan kina buƙatar saya ki tuntuɓi wannan lambar 07084161619.*
8.
Hannu yakai ya rufe mata baki, sannan ya danƙwarar da kanta sukayi ƙasa, kallon ta yayi yanda take zarar ido a firgice ya girgiza mata kai a hankali alamun karta yi motsi ma, suna nan a duƙe manyan gwarazan maza suka riƙa tsallake kansu suna wucewa da gudu haka ta haɗe jikinta da nasa cikeda tsoro, hannunsa ya ɗaura saman kanta, zuciyar ta sai harbawa take sairi da sauri, tausayin Nihal sosai yake fiƴe da tunanin mai tunani. Haka suka takure saida taku ya ɗauke sannan ya jata da rarrafe suka lafe bayan wata bukkar wacce saida dare ya raba sannan suka shige ciki ganin hadari ya gangamo. Tsugunawa sukayi har gari ya waye basu rintsa ba suna nan a tsirace dukkan su, bamaiyin magana acikin su.
Khaleesah har gari ya waye ana mata cure cure a ƙafa, bayan an fasa an tsatse jinin aka bata wasu ruwa tayita aman jini sannan aka rufe ƙafar da wasu ganyaye da mata suka daka! Tabbas ta samu tsananin sassaucin abinda takeji daya danganci azaba amma shin me suke nufi? Waɗan nan mutanen sukuma su waye? Me suke nufi da ita? Addu'ar tane Allah ya amsa tanaga! Ƴaɓ zindirawa basa salla basa salati, basu masan annabi ya kafu ba, haka aka fito da ita da sanyin asuba aka ɗauko wani dutse aka ajiye ta akai. Wadu maza ne suka shiga rabata da kayan jikinta, inda ta fara kokawa tana kakkare jikin ta amma haka ta ƙsrfin tuwo suka rabata da rigar ta da wando suka mata zigidir! Wannan safiyar ma su Hakeem fitowa sukayi daga bukkar nan suka dawo maɓoyar su cikin sanɗa, sedai me suna fitowa suka hango an shiga ciki an fito da wasu kayan dasuka gani a bukkar ajiye an nufi wurin da khaleesah take a zaune tana makyarkyatar tsoro da kuma sanyi! Hakeem ɗauke idanshi yayi daga duban khaleesa yana tsoro idan ba sacrifice zasuyi da itaba, zakara suka ɗakko fari fat suka tsaya asaman kanta suka yankashi jinin yana tsiyaya a saman sumar kanta har zuwa jikinta, bakinta ta buɗe ta soma karato duk wata addu'a datazo bakinta a sarari cikin murya ƙasa ƙasa. Cikin ƙatuwar tukunya tana tafasa agefe aka wurga zakaran nan sannan aka ɗakko akuya aka wurga ta ciki da ranta! Haka matasa maza da mata suka zagaye ta wasu suna kiɗa wasu kuma rawa ana zagayar ta ciki hadda sarki. Wata ƙwarya aka ɗakko aka miƙawa sarki ya karɓa ya kurɓa, sannan ya baiwa wata mace itama tasha haka aka riƙa zagaye da ƙwaryar a tsakanin mutanen wurin sanda kowa yasha sannan aka miƙawa khaleesa, kallon ƙwaryar tayi jinine aciki tabbas tayaya zata iya shan jini? Ɓata fuska tayi sannan ta kawar da kanta daga duban ƙwaryar dama mai miƙa mata, sukayi sukayi taƙi karɓa dan haka suka sanya wani ƙato ya riƙe kanta wani ya kafa mata ƙwaryar a baki, tana turjewa yana tirsasa ta.
Hakeem bindon daya ɗakko acikin bukkar nan ya janyo sannan ya rarumo dutse madaidaici ya saita ƙwaryar ya harba! Take ta suɓuce a hannun wanda take hannun sa kuma ta tarwatse a ƙasa jinin ya watse, wani irin razana yayi cikin tsananin tsoro ya zube a ƙasa yana wani surutu da basa ganewa kuma basaji danya musu nisa. Zabgegen takobi wanda suke tunanin shine sarki ya zaro a fusace ya fille masa kai, sannan wanda yake riƙe da kanta ma ya fille kansa, jikin khaleesah ne ya ɗauki ƙyarma, lokaci guda ta saki fitsari a jikinta, gashi an mata tsirara haka sarki yayi wata magana aka zare ta zuwa wannan bukkar da suke ɓuya kowane dare. Cikin ɗoki Hakeem yace da Nihal
"Yau da dare zamu saceta mu gudu" Tana murmushi tace
"Allah yasa su barta aciki, nizan goyata idan muka sace ta" Batare daya ce komai ba ya ƙura mata ido , a ranshi yace dama Nihal tana dariya, dama kyakkayawa ce haka? Narke fuska tayi a shagwaɓe tamkar zatayi kuka sannan tace tana langwaɓar da kanta
"kanata kallo na meye ne to?" Hannun sa yasa yakai hancinta yaja "A jejin nan idan kikamun rashin kunya miƙaki zanyi awurin maguzawan cen suyi peppersoup dake su cinye" Kallon juna suke har lokacin a narke ta ce,
"Da wannan yunwar daka barni dashi ai gwanda kawai ka miƙa ni a gunsu" Hannunta ya riƙo cikin tausayi "kiyi haƙuri Nihal inshaa Allah yau zan sama miki abinda zakici" Sauke kanta da ƙwayar idanta tayi a ƙasa cikeda jin yunwa
"wasa nake dama, ta yaya zaka samomun tunda yake babu abincin ne" Motsi sukaji kusa dasu da sauri suka waiga atare, wata macece da Namiji suke maƙale ajikin bishiya suna aikata masha'a basu masan dasu Nihal a wurin ba, sai yare suke ƙasa ƙasa cikin sambatu kuma ga alama laɓewa ne sukayi. Hakeem