Showing 6001 words to 9000 words out of 67070 words
Chapter 3 - Gamo Complete Document writing Billy Galadanci.txt
nayi GAMO! Nayi gamo da aljani me siffar Sadauki Hakeem, dan Allah badan niba ki tashi mubar nan wurin kyasha ruwan daga baya" khaleesah kwata kwata ma batasan inda kanta yake ba, gaba ɗaya ta gama galabai ta, jijjigata Nihal keyi tana faman kuka har zuwa sanda ya ƙaraso wurin da suke, ganin sa akansu yasa tace "Khaleesah gashinan zai kashe mu, ki daure ki tashi mu tafi" ta ƙarashe msganar a tsaye tana shirin neman hanyar gudu, hannun ta ya riko ya janyota tazo gaban sa, hannayen sa yakai fuskarta ya waigota ta kalle sa sannan yace a hankali
"Nihal calm down mana, bawani aljani wlh nine Hakeem, badake jirginmu ya faɗi ba daga sokoto? Jin ya ambaci faɗuwar jirgi ya sanya da sauri ta kalle sa tunawa da tayi a daren da abin ya samesu tagani a facebook jirgi ya faɗi daga sokoto zuwa Abuja, tana zare ido ta ce,
"Ban fahimta ba, kaime kake anan to? Ni kidnappers ne sukaje sacemu muka bar ƙauyen damuke muka ɓata bamu gane hanya ba muka faɗo nan" Nannauyan ajiyan xuciya ya sauke sannan ya ce,
"Daga sokoto nake, muka samu plane crash kawai se farkawa nayi na ganni akan single chair na jirgin a jeji, dama ns ɗaure kaina da belt kafin faruwar abun, nayita wahala kusan 4 days ina yawo a jejin nan" A wahale ta ɗaura kanta a kafaɗar sa tana nanata kalmar,
"Alhamdulillah! Alhamdulillah, Allah mun gode maka, dan Allah Sadaukee ka kaini gun momyna wlh tsoro nake ji! A ranshi yace 'Ina fama da kaina ma bare kuma ga mata'
"ki rika addu'a kawai, inshaa Allah zamu kuɓuta, wane hanya ne kika ce ƙauyen yake? Tana share ƙwallan idan ta tace, bazamu iya ganewa ba, kwanan mu uku muna tafiya, kuma tun farko mun sake hanya ne, munso mu koma muma amma bamu gane komai ba" Shiru yayi yama rasa tunanin da zaiyi. Ruwan sama ne ya ƙwalle tamkar da bakin ƙwarya, abinda yayi saurin farkar da Khaleesah ta soma buɗe bakinta don tasamu tasha koyaya ruwan yake, hannaye Nihal ta sanya tana cikawa seta sunkuya take bata, bata damu da tsananin dukan da ruwan saman yake mata ba, Hakeem yayi tsaye kawai yana kallon ta, haka tayita bata har sanda ta nuna alamun ya isheta sannan itama tasha. Cikin tausayi Hakeem ya kalle su yace "kuyi alwala an kammala magrib tunda kukaga ruwa yazo an idar da sallah" Ba musu dukkan su sukayi alwala suka fara sallah inda suka laɓe ajikin bishiyar mangoro ys jagorance su. Dukda akwai tsananin sanyi ga dukan ruwan sama sunsha hakan be hanawa khaleesah jin wani masifaffen sanyi a ƙafar taba, sannan daga bisani se wani azababben zafi ya ziyarce ta wanda atake ya haddasa mata haɗa gumi,da ƙyar taga sun idar da sallan ta miƙe a rikice se kuma ƙafar tayi mata nauyi, cikin wata murya me nuna alamar tana shan azaba ta ce,
"Nihal wani abu ya cijeni a ƙafa me tsananin raɗaɗi, ki taimakeni ji nake tamƙar zan mutu" Duhu ya rigada ya sauka sedai ruwan ya lafa, Dukkansu har Hakeem miƙewa tsaye sukayi, ya zaro wayar daya tura a cikin wandon sa na ciki gudun karta jiƙe da ruwan sama ƴa haske torchlight, nan da nan ƙafar tayi wani girma sosai, sunkuya wa yayi yana duba ƙafar ga alama lokacin sallan isha yayi sabida ruwa ya tsagaita se kawai ya fahimci saran maciji ne, ɗagowa yayi ya kalle ta ya haske ta torchlight, tausaƴi ta bashi sosai yanda take gumi duk sanyin nan, kafin ya damu damar cewa wani abu kawai sai ihun Nihal yaji, da sauri ya kalle ta tare da haske ta a fuska,
"Sanyi sosai wani abu ya laulayemun ƙafata" Haska ƙafar yaƴi shima saida yaja baya, wani ƙatoton maciji ne, ys naɗe mata ƙafa gaba ɗaya bakinsa alamun zekai sara yana kallon babban ɗan yatsan ta,
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un! Karki motsa Nihal macijine ɗauke numfashi zai dauka da kanshi, shine ya sari khaleesah ma" Ihu suke a tare Nihal bata motsa ba ksrya sareta amma bata fasa kuka ba, khalesah kuma tama rasa me zata ce se juyi take awurin bata ko iya ɗaga ƙafarta, gaba ɗaya Hakeem ya rasa me zaiyi, wazai kama acikin su!!!!
*Am sorry yau nayi busy ne.*
Mom Nu'aiƴm.
*✨TAURARI✨*
*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.
Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai. Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.
2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500
Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku nemi wannan lambar 07084161619.
9/11/21, 6:59 AM - Buhainat: *GAMO!*
*NA: BILLY GALADANCHI*
5.
"ki daina magana Nihal, cikin sa ne yake ciwo, yana masa sauƙi zai sake ƙafarki" Addu'a kawai ta somayi shi kuma ya sunkuya ya ɗaure ƙafar khaleesa da rigar sa daya cire, bakinsa ya saka inda akayi saran ya soma tsotse jinin dake wurin yana zubar wa. Nihal tana tsaye tamkar mutum mutumi kanta a sama idan a rufe har sanda taji macijin yana warewa a hankali a jikinta, ta bayanta ya zaga ya wuce da sauri ta dawo bayan sa tana ƙaƙƙame jikin ta a razane, "dan Allah mubar nan wurin, wlh akwai tsananin tsoro" baice komai ba har sanda ya gama tsotse iya abinda zai iya, wannan bazai manta ba a film yaga sunayi idan maciji ya sari mutum, a haka suka ja Khaleesa da gaba ɗaya ta gama shiga ɗimau ta suka soma tafiya da zummar barin wurin.
Sunyi nisa sosai sukaga dare yaƴi musu, ga Khaleesah ta galabai ta, Hakeem ne ya kalli Nihal ya ce da ita,
"Nihal wannan wurin inaga anan ya dace mu kwanta, zuwa safiya saimu kama hanya" A firgice ta kalli wurin sannan ta ce,
"A fili fallau haka, idan ruwa ya sakko fa? Nisawa yayi
"Ya zamuyi to? Yarinyar nan ta gama galabai ta, bazaki gane azabar datake ciki ba wlh, tanama da dauriya sosai, saran maciji ba wasa bane ba, kuma yanada kyau muyi sallan isha" Batace komai ba dama sam ita da Hakeem ba magana sukewa juna ba, idan akwai wutar da zasu wurga juna aciki tabbas dazasu wurga juna kawai kowa ya huta da ganin ɗan uwan sa. Taimama sukayi suka taimakawa Khaleesat tayi sannan suka sallaci isha haɗe da shafa'i dakuma wutiri, Hakeem ya dade yana jere addu'oi sannan ya ɓuge da buɗa murya yana karanto karatun alk'urani mai girma a sarari da murya sama saboda su samu su samu bacci acikin nutsuwa. Gaba ɗaya kasa bacci khaleesah tayi tsabagen azabar da ƙafarta ke mata, gumi take haɗawa na fitina, tana cikin tsananin azaba, ganin duk sunyi bacci gashi kukan ma ya gagare ta ya sanya ta miƙa hannu da ƙƴar ta bubbuga cinyar Hakeem, a hankali ya buɗe idansa dama dutsen dasuka raɓu dashi ya jingina dashi daga zaunen dayake bacci ya ɗauke sa!! Kallon ta yayi acikin hasken farin watan daya mamaye ilahirin wurin, wartsake idan sa yayi sannan ya matsa kusa da ita, har lokacin gumi take haɗawa cikin tsananin tausayi ya ce yana kallon ta,
"Sannu khaleesa kin kasa bacci ko? Cikin tsananin zafin ciwo ta ce,
"Na kasa bacci hakeem, ku taimakeni banaso in mutu a jejin nan, idan akwai wani abu daka sani na magani ka bani, wlh ina cikin tsananin azaba mara misaltuwa" Wani ƙululun baƙin ciki ya mamaye duniyar sa, wani tausayi dabai taɓa yiwa kowa irin sa ba sai ita ya taso masa daya tilasta masa haɗa ƙwalla mai zafi, saida ya haɗiyi wani yawu mai tsananin ɗaci sannan ya ce,
"Kiyi haƙuri khaleesah, da ikon Allah bazaki mutu ba, kuma zakiji sauƙi, bari gari ya waye naga ma ya soma washe wa, zan ɗebo ganyayen dake nan zan fasa na cura miki inshaa Allah zaki dace kinji" A hankali ta gyaɗa masa kanta ta koma ta kwanta abin tausayi, matsawa yaƴi kusa da ƙafar ya soma yi mata addu'ar samun sassauci danya tabbatar ajaline kaɗai zai bada sassauci raɗaɗin azabar datake ji daga saran maciji, shi tunda yake ma bai taɓa ganin maciji irin wannan ba, kalar sa yellow shar da baƙaƙen idanuwa, shi kansa daurewa kawai yayi baiyi ta kansa ba sanda ya ganshi! A hankali yana tofe ƙafar da addu'a harta samu bacci saidai kana kallonta kasan cewar tabbas acikin baccin ma azaba take sha matuƙa, zama yayi yanata addu'a tsare da ita baiko yi tunanin runtsawa ba tunda ya farka bai kums bar side ɗinta ba har gari ya soma haske, ya tashi yaƴi sallan asuba sannan yaci gaba da Azkhar yana tsare da ita bayaso ko kaɗan ya tashe ta. Sanda Nihal ta farka ƙura musu ido tayi na wani lokaci kafin ta taso ta maso kusada Khaleesah, ƙafar ta kalla taga yanda yayi wani suntum takai hannu zata tashe ta cikin tausayi da sauri ya riƙe hannun ta suka kalli juna, ɓata fuska yayi ita kuwa ta buɗi baki ta ce,
"Lokacin..... Yatsansa ya dauka ya ɗaura akan lips nashi tare da yin sautin shshhhh alamar tayi shiru, da mamaki ta kuma buɗe baki zata tambayi dalili cikin tsawa yace "Ke bakyaji ne wai, karki tashe ta mana" Khaleesah ɗan matashin ihun dayaƴi shine ya tashe ta cikin jimami ta farka sannan tayi salati, harara Nihal ta wurga masa cikin takaici sannan taja gajeran tsaki ta miƙe batare data koda kalle ta ba ta soma shirin yin taimamar ta, matsawa da sauri yayi kusa da khaleesa, tausayin ta yakeji kamar me, yana kallon ta da tausayi ɗauke a fuskar sa ya ce,
"kiyi hakuri ta tasheki ba haka naso ba, naso ki samu bacci koda awa uku ne, wannan sudar da bata iya shiru ta tayar da ke, yanzu ya ƙafar? Kinji sauƙi kuwa? A hankali ta gyaɗa kanta sannan ta koma kwanciya zazzafan zazzaɓi takeji, ga jiri, a zaune ta samu tayi salla. Nihal kuwa sai cika take tana batsewa! Shidai shiryawa yayi abinshi ya kalli Khaleesa ya ce,
"Bara na dubo abubuwan danake ga zasu taimaka wa ciwon dukda bawai nasan su bane, amma dai ganyaye da itatuwa magunguna ne masu amfani" Batare daya kalli Nihal ba yace "Ki kula da ita" Ita ɗinma bata tanka shi ba harya bar wurin ya shiga jeji.
*************
Villa kam yasha baƙi ƴan ta'aziyya, gaba ɗaya Nigeria ta gama ɗauka akan Abdulhakeem ya mutu yaron president, our great youngest pilot in Nigeria, ansha kuwa da Mahaifinsa da mahaifiyar sa ƙaramar hauka sukayi, Mr president ana zaman karɓar gaisuwa yana sharar ƙwalla da majina shaɓe shaɓe tamkar wani ƙaramin yaro, Her Excelency the wife of the president gaba ɗaya ciwo ta faɗa, dik a cikin yaranta tafison Hakeem, mutuwa tayi mata babban yankan ƙauna, tana roƙon Allah ya bata dangana akan wannan babban rashin.
A gidan su Khaleesa ma datake ƴar governor na Jigawa state da kuma gidan sh Nihal an shiga karɓar gaisuwa anyi amanna da cewar tabbas kashe su akayi ba amfanin neman su, sai dai kam iyayen su sun shiga tsananin tashin hankali!
Hakeem duk iyakar ƙoƙarin shi na ganin cewar ya gane hanyar dayabi yazo neman ganyayen nan gaba ɗaya abin cin tura yaƴi! Tun safiyar nan har la'asar bai dawo ba, hankalin su ya tashi suka shiga neman sa musamman Nihal sabida gaba ɗaya ta gagara ɗaukar Khaleesa ita kuma bazata iya tafiya ba,ga yunwa haka suka sha tsamiyar dasuka ga bishiyar ta a wahale, sannan Nihal tana kuka ta ce tana kallon Khaleesah dake cikin tsananin azaba,
"khaleesah zan sakaki a bayana in goyeki, semu tafi, Hakeem dama ba mutumin kirki bane ba, mutumin dake zuwa gidan mu fin awa 2 baya iya cewa dani cikanki tsabar girman kai da jin kai shine zai bauta mana, yaga alamar zamu zame masa kayan nauyi shine yayi mana na ƴan duniya ya gujemu! A wahale khaleesa tace
"Idan ya gujemu mun shiga uku, taya zamu rayu a wannan jejin muna mata mumu biyu ga wannan lalurar data sameni, na sani kinsha faɗamun rashin kirkin sa amma haɗuwar nan tamu sai nake ga tamkar yanada tausayi, ashe bashida kirki" Bayan hannu Nihal takai ta share ƙwallan ta,
"Allah yanaji kuma yana gani ƴar uwa, tashi ki hau bayana zan goyaki muyi gaba ko Allah zai sa mu dace" Saukar da kai ƙasa khaleesah tayi cikin jimami sannan tace "Wlh Nihal kodaga cen zuwa nan bazan iya tashi ba, ni kaɗai nasan irin abin da nskeji, wani ɗaci ne har cikin raina, bansan ya zan kwatanta miki ba" Haka da ƙyar da dabara Nihal ta ɗagata ta goya a wahale suka kama hanyar dabasu san inda ƙaddara zata kuma cilli dasu ba.
Da ƙarfi yake ɗaga murya wurin kiran Khaleesah! Tako ina jejin amsa kuwwar kiran dayake wa khaleesah yakeyi, tun yanayi da ƙarfi harya gagara ɗaga muryar, ga yunwa damma yankunan dayake zagaye ruwa ne, yakan sha kuma yayi alwala, gaba ɗaya ya shiga ruɗu duk inda ya juya hanya iri ɗaya take dawo masa a jejin, tunanin sa tas yana kan matancen guda biyu musamman Khaleesah, Allah kaɗai yasan halin datake ciki. Damuwar tunanin su yafiye masa zafi akan wannan jejin dayake cikin sa, yayi imani da Allah idan har ajalin sa a jejin yake saiya tafi dashi, damuwar sa wahala ne, har akayi magrib yana yawo a jejin neman hanya amma sam bai gane komai ba, haka har duhu sosai ya gama sauka. Yanzunma dutse ya nema ya zauna akusa dashi yana faman addu'o'i wayarsa saura masa 87% a babbar, me binta 56% bayaso gaba ɗaya yau ace wai sun ɗauke dan sune hasken sa, so yaga ya samu signal koyaya ne yayi amfani da GPS ya nemi hanyar fita a jejin acikin sauƙi.
Tun Nihal tana daurewa goyon harta gagara daurewa, atare suka faɗi ragwaf a kife, da ƙyar da siɗin goshi suka mirgina, khaleesa tana ɗaukar numfashi da ƙyar ta ce da Nihal,
"Nihal da zakibi ta tawa dakin tafi kin barni, wlh na tabbatar dawuya na kai safiya da rayuwa ta a jejin nan, gaba ɗaya jikina nini kaɗai nasan abinda nake ji, zaku biyeni a rasamu duka, gwanda ki koma ki ƙarar da abinda ya sameni, akan ace an rasa labarin mu har abada" Kuka Nihal ta fashe dashi
"Bakida hankali ne kike faɗamun irin wannan maganar? Tayaya zan rayu a farin ciki idan na tafi na barki, ohh na tafi na barki ki mutu kenan? Dan Allah ki dena faɗa ma" Anan suka zauna sunata kuka atare.
Mom Nu'aiym.
*✨TAURARI✨*
*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.
Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai. Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.
2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500
Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku tura kuɗin ku ta wannan lambar Acc ɗin.
2029764071.
First Bank
Nafisa Nuhu.
Shaidar biya ta wannan lambar
08033719070.
Idan kuma katin waya zaki tura,seki tura katin mtn ts wannan lambar wayar.
07084161619
Shaidar biya ta
07084161619
Muna maraba daku.
Mungode💃🏻💃🏻💃🏻
9/11/21, 7:00 AM - Buhainat: *GAMO!*
*NA: BILLƳ GALADANCHi*
6.
"Bazan taɓa iya tafiya na barki ba khaleesah, duke abinda zai samemu saidai ya samemu a tare, idan ma mutuwar ce khaleesa gwanda mu mutu a tare!"
"Amma Nihal kina kallon fa ƙafar nan, kiwane wucewar daƙiƙa ɗaya da tsananin azaba yake wucewa a duniya ta, na tabbatar yau akwai azaba, idan har abinda nakeji ba zafin ɗiban rai bane ba toko tabbas ina tausaya ranar da zan ja in kuma sauke numfashi na na ƙarshe, wlh Nihal ina cin azaba dabansan yaya zan misalta miki ita ba" Hawayen idanta ta share sannan cikin ƙarfin hali tace
"Banaji zamu iya tafiyar nan babu Hakeem acikin ta, ya zamar mana dole mu neme sa, Allah ne garkuwar mu shine makamin mu, gwanda na neme sa akan na barki a wahale, zanyi alama hanyar nan zanɗan zago inga koda zamu haɗu dashi" Cikeda hope ta gyaɗa mata kai kawai ita kuwa gyara mata kwanciya tayi ta nufi jejin, da hannu take alama ta hanyar tuge hakin dake ko ina a zube, idan ta tuke saita wurgar gefe taci gaba da tafiya, a nata hikimar zata gane idan zata juyo. A haka ta kutsa cikin jejin tayi nisa sanda ta fara kiran sunan sa da ƙarfi