Showing 3001 words to 6000 words out of 25328 words

Chapter 2 - MIJIN KWAILA Book Complete .txt

bayaga zahra banta'ba 'kaunar wata d'iya mace kanartaba."
Sadiq ya kwashe da dariya"gaskiya abokina koda banga girl dinnanba nasan mai zafice,don nasan bakayi da 'kwaila."
Isha'q ya murmusa...
Maganarshi ta ma'kale cik,
Sakamakon hango zahra dayayi da bataliyar yara suna dambe,zahra har 'kara over acting takeyi.
Sadi'q dake duban yaran yace"kai yarinyarcan badai masifa ba,allah tsine ranar da zata fito takoma ga allah batare da anrabata fad'a da yaraba.
Yarinya saikace shed'aniya,
Wannan zanga wandanzai kwasheta yakwashi bala'i.
Isha'q yaji 'kirjinshi yabuga dam.
muje zuwa guy's
September 21, 2017 at 12:05pm ·










������������
*Anty 'yar charas*��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA* ����‍♀










Chapter 4.




Isha'q yaji 'kirjinshi yabada dam,
Amma dayake jarumine saiya fuske gami da janye hannun sadi'q dafad'in "kayi abinda yadameka malam",
Sadi'q yasake kyal'kyalewa da dariya yana fad'in"allah yarinyar ce so funny"
Isha'q yaja tsoki bai tankashi ba,
Sai gab da isha'i zahra tanufo gida,'kirjinta yana bugun uku-uku aranta tana addu'ar "Allah yasaka umma bata tsakar gida,
Talala'bo tana sand'a lokacin datashigo gidan takalma a hannu bayan tafara zuro kanta taga gidan babu kowa.
Tafara tafiya sad'af-sad'af danufin fad'awa d'akinta sai dai batayi auneba taji umma tacafketa caraf ,
Ta waigo fuskarta da alamun tsoro,
Kafin tayi wata magana umma takifa mata mari.
Da tambayar "daga gidan ubanwa kike?"
Zahra idanu suka raina fata,
Tafara ro'kon umma"wayyo ummana kiyi ha'kuri bazan sakeba."
Umma tace"rufemun baki shashashar banza,bazan 'kara d'inkiba datana tasiri dayanzu namance dawata aba wai ita damuwa.meyasa kikeson sakamun hawan jinine zahra,abinda duka y'an uwanki basuyiba."
Umma ta'kare maganar kamar zatayi hawaye.
Zahra dai kuka take tana"allah umma nadena."
Umma bata bartaba saida tayimata ligi-ligi tasaketa,tafara haramar alwalar isha'i.
Zahra ta 'kyalla idanu taga umma tashige d'aki,
Hakan yabata damar sake ficewa gidan da saurin gaske,
Bazata mance kirarin dasukeyima kansuba wai *abuga asaki bata maganin d'an iska sai dai ta'kara taurin fata*.
Azauren su ummilolo tala'be,tana 'kwalama ummilolon kiran,
Hajara kishiyar innar ummilolo tafito tana masifa don tasan zahrace"kewai wacce irin ballagazar yarinyace,halan kekam uwarki bata kwa'ba maki.duka yaushe kuka shigo gidan amma dayake bakida tarbiyya harkin sake fitowa,to oya maza fice anan ummi babu inda zataje."
Shegiyar yarinyar yarinya mai kama da d'inya,ke ba'ka halinki ba'ki.
Zahra ta murgud'a baki dacewa "badai niba."
Inna hajara tace"sai ubanwa"
Zahra cikin rashin tsoro tace "ubanki"
Aiko inna hajara tayo kanta zahra tajuya da niyyar rugawa amma tuni inna hajara ta cafketa.
Mari biyu 'kwarara tayi mata, taci gaba dafad'in"duka iskancin dakikeyi 'kyaleki akayi.wlh kinshigo gonata ubanki zakici."
Zahra dayake ruwa ruwace tuni ta 'barke da kuka tayi waje aguje,
Takuwa koma 'kofar gida ta tara duwatsu tadinga yima gidansu ummilolo ruwan duwatsu,
Duk da haka bakinta bai sassauta da zagin datake d'urama hajaraba.
A tsotsayi d'an hajara yafito zashi kicin d'aukar abinci dutsen ya sauka akanshi jini sosai ya tsinke ganin hakan yasaka hajara kama hannunshi suka nufi gidansu zahra tanata masifa.
Zahra daganan zugar yaranta sukaja,suka la'be lungu ilai kuwa saiga inna hajara tadawo da abbalo ansaka mashi bandage,
Zahra da sauran 'kawayenta sukayi masu ature da 'kasa har cikin bakin hajara da idanuwanta.
Zahra data du'ka tana 'kyalkyala dariya tace"kuma wlh kisake dukana saina kama wannan d'an naki a islamiyya saina fasamai baki."
Inna hajara tace"tsinanniya kije zaki samu dai daike."
Zahra dake wani gantsarewa tace"tsinanniya tana bayan uwarta tanashan nono,"
Sauran yaran suka kwashe da dariya.
'karshe dai inna hajara ganin zasu kunyatata gaban mutane yasakata sulalewa tayi gida,acan tad'ora sabon bala'i tana sauke kwandon zagi akan zahra da iyayenta.
A filin gad'a ma zahra saida suka dambace da yara kusan uku,
Daganan tace ayi zuga atafi jan fad'a.
Suna tafe duk wanda suka gani saisun tsokana,wani ya 'kyalesu wani yabisu a guje amma baya iya kamosu.
Dai dai wani lungu suka hango saurayi da budurwa na tad'i,
Zahra tace "yauwa alhmdlh dama waccen habibar dake fira prefect d'in makarantar muce gata muguwa tayita dukanmu,
Kuzo muje"
Yara suka bita d'uuuu,tana gaba.
Dayake garin akwai hasken nepa dakuma na farin wata,
Habiba na tsaye gefen saurayin nata can gefe wasu samarine data gama yima wula'kanci taga mai mota yazo.
Bata saka hijabiba sai d'an gyale daya tsaya iyakar kafad'unta.
Gefe dasu teburin masu shayine damasu tsire antara majalisa ana cafta.
Zahra tana isa kusa da habiba batayi wata wataba tasaka iyakar 'karfinta ta fincike zanin habiba,
Habiba gashi sam bata saka undey ba.
Saiga 'kafafun habiba tsaye zalo .
Zahra kuwa tace 'kafa menaci ban bakiba.
Takwasa aguje,yayinda saurayin habiban ya rufa masu baya
Tsabar kunya habiba saita du'ke inda take.
Sauran samarin data yan'kwana kuwa har fad'uwa sukeyi suna burgima saboda dariya .
Majalisar masu tea ma dariya suke suna 'karawa.
'karshe habiba d'an gyalen dake kafad'arta ta yafa a kafafunta.
Da rarrafe ta shige gida .
Su zahra sunyi gudun da yakai nisan inaa.sannan suka yarda zanen saurayin ya tsintoshi bayan ya du'ka yanata hakin wahala
Dafad'in "shegun yara saigudu kamar zomaye."
Daga tonon wannan fad'an kowa ya ware gida,
Kanshi tsaye banda zahra dake faman ra'be ra'be.
Tamakure a lungu,
Abba yadawo daga nemanta har yagaji yanufo gida yaci karo da mutum...
Matsalar nepa.
Ayi ha'kuri da wannan
September 22, 2017 at 7:44pm ·




��������


by yar charas��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*����‍♀






Chapter 5.




Da touch light ya haske mata fuska ta d'ago fuskarta da alamar tsorata don sarai tasan abba bayada wasa.
Da 'karfi yakira sunanta"zahra,mekikeyi anan daga ina kije.?"
Kanta tsaye tace"wasa naje yi",
Abba ya gyad'a kai,"dakyau".
Kawai yafad'a yayi cikin gida abinshi,yayinda zahra ta rufa mashi baya.
Umma tana tsakar gida hankali a tashe abba yashigo zahra nabin bayanshi,
Umma tana ganin sundawo tawuce d'aki abinta ranta a dagule yake.
Bai tanka zahranba ya kutsa dakin da umma take,tahad'a kai da gwuiwa idanunta daf da hawaye.
Abba yadafa kafad'arta dakiran sunanta"amina,kiyi hakuri kifidda damuwar zahra acikin ranki,kisani kowacce rayuwa akwai jarabta mu tamu jarabtar kenan,don haka kima dena zancen wai kiyita dukanta.kitattara kici gaba da addu'a amma ni sam lamarin zahra yadena bani mamaki yakoma bani tsoro."
Umma tasauke numfashi,"to yaya zan'iya cire damuwa abban zahra,damuwa ai ita keyin kanta.ace babu rana ta ubangiji dazata fito takoma ga allah ba'azo ancedani zahra ta'aikata wani abuba.saikace tafi sauran y'ay'ane."
Abba yace"kul dakiyima yarinyar nan baki,mudaici gaba da addu'a,jiyama liman yazo hargida yanamun kashedi wai tajefashi kwata zashi sallar isha'i."
Umma tazaro idanu dafad'in "liman d'in dakanshi,,?
Abba ya gyad'akai"'kwarai kuwa,waisuna wasa anrufe idanunta toyazo 'ketare kwata tazata yarinyace shinefa ta cakumeshi,shikuma wai yana addu'ar zuwa masallaci bazaiyi maganaba.
Nana kokuwa ta sar'ke tajefashi kwata."
Umma duk da 'bacin ran datake ciki saida ta dara,
Data tuna yanda liman yake saka malummalum idan zashi masallaci.
Ta girgiza kai,"Allah ya shirya,"
Abba yace "ameen."
Zahra kam tuni ta kwanta abinta, bata tsaya neman abincin dareba don dama ba ma'abociyar cin abinci dayawa bace.
Barta dai ga 'kwalama wannan fa ogace.
**********
Bayan kwana biyu....
Zaune yake a tsakiyar grass carpet d'in daya gewaye tsakiyar 'katon falon,
Gabanshi laptop ce yana 'kara nazarin banbancin dake tsakanin zahransi da little zahra kamar yanda yasaka mata suna,
Gefe guda 'kanwarshice hanan wacce bazata shige tsaran zahraba,
Doctor ru'kayya ta tako ahankali daga stairs cikin dakakken leshinta mai tsadar gaske,jikinta akoda yaushe yana fitar da siririn kamshin turarenta mai tsada.
'yar kyakyawar fuskarta dabata tsufa tana manne da glass din daje kuma kayatata.
Isha'q da hanan atare suka mi'ke dukansu suna sakarmata murmushi
Tazare wayar dake kunnenta tana sakarma kyawawan yayan nata murmushi,
Ta kalli isha'q dafad'in"yayankane muke maganar yarinyar dakake bani labari,yace kamata yayi mushirya muje muganta ayi komai da lissafi,sannan yakira wayarka tana a kashe."
Isha'q yasaki dariya yace"nakashetane nasaka charge mum".
Yami'ke da sauri yana fad'in"mum kice kawai inshirya yau saigidansu pretty,yawani dun'kule hannuwa da naushin iska,wlh mum saikin ganta she's very beautiful nd younger."
Mum tace "kome kakeso isha'q aibaka ganin muninshi,haka kake tun kana yaro.sa'banin yayanka dayakeda a'kida dakuma ra'ayinshi na santseni."
Ya shafi gefen fuskarshi yana murmushi,"Allah mum tanada kyau,iluv zahra very much mum."
Zaunawa tayi tana canja channel''idan kagama surutunka inajiranka,haka zakaje kana rawar jiki ai yarinyar saita raina class dinka,ya murmusa yana tafiyarshi ta 'kasaita yace"haba mum kada kisa wannan ta'kwalar ta rainani mana."
[9/23, 10:00 PM] mum meenat: Yanuna hanan wadda ta zubama yayan nata idanu tana kallonshi,
Dasauri ta tashi ta la'be bayan mum dafad'in "mum zakije dani".
Doctor ru'kayya tamurmusa tace"kibari dai watarana saikije lokacin kinsamu hutun makaranta,yanzu kam ai zaki takuratane."
(tazata zahra babbace )
Isha'q kam fakaitarta yayi yasaki dariya dafad'in"sai mumcy",
Tana zaune tana kallon wani series yafito cikin hadadd'en yadinshi filtex mai yal'ki ruwan madara,
Kanshi yasha hular zanna bukar baqa,
Kafarshi cikin bakin takalmin daya matu'kar dacewa da shigar tashi.
Handsome and giant,
(abinda na raya kenan.)
Hadadd'en 'kamshin turaren American crew yakasa barin jikinshi,
Still akwai farin glass a idanunshi,
Ita kanta doctor ru'kayya tana alfahari da isha'q matsayin d'anta very handsome guy.
Yanada dukan qualities daya kamata mace taso a tattare dashi,
Dogone irin tsayin hadaddun maza d'innan,yanada fasalin 'karfi da jarumta a tattare dashi don 'kwarae mayen exercise ne.
Yana rud'a makwad'aitan mata da kamfacecen 'kirjinshi dakuma murdadden jikinshi.
Wankan tarwad'ane wato ya d'auko kalar doctor ru'kayya ne,
Sa'banin yayanshi aliyu dayake fari tar yad'auko kalar mahaifinsu.
Isha'q gogaggen matashine wayayye daya samu shedar kammala karatunshi na degree mataki na biyu akan mass communication ma'aikacine da gidan talabijin ta 'kasa wato NTA sosai yake samun sa'konnin yammatan dasuke mutuwar 'kaunarshi musamman don fara'arshi,
Dakuma iya zama da mutane don isha'q bdai iya kyautatawa ba.
'karasowa yayi jikinta ya tallafi fuskarta da hannayenta"am readay my mum"
Yafad'a da shagwa'barshi,memasa kyau.
Tace "i see"
Tami'ke tana gyara zama mayafinta dasaka glass d'inta,
Isha'q ya tsuramata idanu"am proud of you be my mother mumma."
Tashafi fuskarshi itama da murmushi,aranta tana jin zallah farin ciki saboda dawowar walwalar d'anta daya rasa tsawon lokaci.
Tare suka jera gwanin sha'awa suka shige cikin d'aya daga cikin motocin gidan,
Tazauna a mazaunin kusa da driver yayinda isha'q yake driving suka lula gidansu zahra.
Umma tagama gyara d'an matsakaicin gidansu,tana saka turaren wuta tajiyo sallamar doctor ru'kayya,
Taleko da fara'arta tana fad'in "lale marhaba da ba'kin yamma."
Doctor ru'kayya ta murmusa aranta tana yaba wayewar umma.
Ruwan randa mai sanyi umma ta'ajiye gaban doctor ru'kayya,bayan ta shimfid'a mata tabarma.
Dr.rukayya tazauna tana cire gilashin idanunta,likaci guda tana kai ruwan da umma ta'ajiye mata a baki.
Takur'ba kana tace da umma"nasan baki sanniba ko?."
Umma ta gyad'a kai"kwarai kuwa."
Dr. Ru'kayya tasake murmusawa tace a ta'kaice"sunana ru'kayya anas kado malumfashi,ni haifaffiyar malumfashi ce,iyaye da dangi mahaifina y'an canne,sai dai dangin mamana sune mutanen funtu'a, nayi karatun likitana anan Nigeria sai dai nasamu sakamakon zama babbar medical doctor ne a India,inda acanne na'karasa karatun nawa.
Nayi aure anan kaduna da mijina babban d'an kasuwane anan abubakar gumi,awancen lokacin ayanzu yanada manyan kamfanoni a ciki da wajen 'kasar nan.
Inada y'ay'a uku maza biyu sai autata hanan,
Babban sunanshi aliyu yayinda mai binsa shine isha'q,
Daganan haihuwa ta d'aukemun sai daga baya Allah yabani hanan,Aliyu yanzu haka yana 'kasar turkey yana kula da kamfanin mahaifinshi dake jigilar rid'i."
Muje zuwa
September 23, 2017at 10:27pm ·






*by anty y'ar charas*����‍♀
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀




NEW WORLD NOVELS




BY MAMAN MEENAT


EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR)


Wannan shafin naku ne yn (Madarasatul Tahafeezul Qur' an Funtua, Allah ka qaramana fahimta a
iliminmu)




Chapter 6.




Doctor ru'kayya tad'an tsagaita jin ana kwad'a sallama,duka itada umma sukakai dubansu ga hanyar shigowar,abbane yashigo da ledar yalo a hannunshi,umma tami'ke da sauri tana mashi sannu dazuwa ta'amshi ledar dake hannunshi tawuce d'aki da'ita.
Abba yadubi hajiya ru'kayya kallon rashin sani,
Itakuwa 'kasa tayi dakai tace"malam ina wuni ya hidindimu."
Abba ya'amsa da "Alhmdlh"yawuce ciki bakinshi fal da tambayoyi.
Daki yasamu umma tsaye da alama zaman jiranshi takeyi,yamata kallon tsaf kafin yace"wace hajiyace nagani anan tsakar gida,kuma hada wani d'an saurayi nagani a 'kofar gida dawata kwatsetsiyar mota,wasuke nema kuma?."
Umma tad'anyi jim kafin tace"to malam nikam bazan iyacewa komai ba,nadaiga tazo batace ga abinda yakawota ba,amma naji tad'auko tarihin yaruwarta tana bani,bansan da wacce tazo ba."
Abba yace "shige muje,aiyanzu zamani ya canja bana barki ked'ayaba.ina zahra ne,ko bata dawo daga islamiyyar ba.?
Umma tace"kaima kasan nanda isha'i yayima zahra kad'an kaganta anan gidan,watakil sai takwas na dare idan tagama yawon tsokanar jama'a.
Abba yayi 'kwafa yace"gab nake da kawo 'karshen iskancin yarinyar nan ai.
Umma tafito har tsakar gidan tana mitar"ai indai zahra ce,bazance bazaka iyaba amma abune mai wahalar gaske."
Dr.ru'kayya ta kafe umma da idanu tanason nazarin maganar datake jiyowa tana tashi daga bakin umman.
Gefe baba yazauna bisa kujerar roba,yayinda umma tazauna akan y'ar tsugunno.
Abba yasake gyaran murya yace da dr.rukayya"baiwar Allah lafiya dai,bamusanki ba,maid'akina tace kinzo kinata bata tarihinki kodai kinyi 'batan kaine.?"
Dr.ru'kayya murmushi tasaki dacewa "ko d'aya malam.kamar yanda nabawa matar ka labarina hakane,inada yaro isha'q wata'kila kaganshi anan waje,hakane?"
Tayi tambayar gami da tsatsare abba da fararen idanunta masu cike da zallah wayewa.
Haka kawai abba yaji tayi mashi kwarjini idanu,tanada tarin baiwar cika ido.
Ya'amsa dacewa"kwarai kuwa."
Tace "gud"
"Yarona isha'q yarone nagari,yanada kyakyawan hali abin ayaba,bawai don yana d'anaba a'a,halin isha'q yasha banban dana sauran maza donshi mutum ne dayasan hakkin wanda yake tare dashi,bayada girman kai bayada miskilanci,yataso tun yana yaro tare da zahra,d'iyar kanwatace wadda Allah yayima rasuwa tun ranar data haifeta batako kalli fuskarta ba.zahra tatashi cikin maraicin uwa hakan yasaka nad'auke duk da mahaifinta baiso hakanba, nareni zahra cikin 'kauna da aminci.
Zahra tasha'ku da isha'q saboda idan bani ko isha'q ba zahra bata yarda dakowa acikin gidanmu.
Lokacin da isha'q yashiga secondary zahra anyayeta,komai nata isha'q ne yakemata shine ya canja mata sunanta daga zahra adam yamayar mata *zahra adam isha'q*,tunda nake a rayuwa banta'ba ganin soyayya da sha'kuwa irinta zahra da isha'q ba.
Kai intakaice maku labari,lokacin da isha'q zaitafi Germany karatu gaba d'aya dashi da zahra saida suka kwanta asibiti.
Alokacin munzata sha'kuwace,sai dai abin mamaki sam zahra bata kula samari duk da takammala karatunta na secondry ko saurayi zuwa yayi wajenta saitace yaje yatambayi isha'q idan yayimashi to itama yamata.
Isha'q kam kullum cikin kushe samarin zahra yake,kullum cewarshi hadadd'en gaye zahranshi zata aura."
Doctor ru'kayya ta numfasa tacigaba,
"zahra yarinyace mai tarbiyya da tsoron Allah,tanada matukar natsuwa da kamala,mahaddaciyar Alqur'ani ce.zahra wankan tarwad'ace tanada yanayin girman jiki,don duka sa'anninta zaka zata tagirme masu saboda jikinta mai saurin tofone,
Sam magana bata dami zahra ba,gwanar kwalliya da tsafta,gwanar iya kalailaye mutane da tattausan lafazi ce.
Lokacin dana lura cewar zahra da isha'q sunkamu dason junansu sainafi kowa murna,don inaganin isha'q yayi matarvda har duniya tanad'e bazaiyi kaico da itaba.
Sa'banin yayanshi dabai dace damacen kirkiba.
Isha'q baitafi karatuba saida baikonshi da zahra,
Koda yaushe suna manne a waya suna firar soyayya,
Alokacin itama takoma makaranta tana karantar likita cewarta zata gajenine.
Isha'q yagama karatunshi da sakamako mai kyau yadawo gida,alokacin aka tsaida maganar aurenshi da zahra dangi kowa yayi murna."
Tashare hawaye taci gaba,
"sai dai kash ana saura kwana uku bikinshi zahra tatashi da matsanancin ciwon mara cikin dare wanda yayi sanadiyyar d'aukewar numfashinta duk da kokarin ceton ranta damukayi Allah ya amshi abarshi.
Alokacin isha'q haukane kawai baiyiba saboda zautuwa saida yakwashe sati guda baisan inda kanshi yakeba,daga baya zama tamkar wanda yarasa memory nashi.dataimakon Allah da addu'u a isha'q yazama normal sai dai duk barkwancin isha'q yatafi yazama tsakaninshi damu gaisuwa kawai,yaci alwashin bazai taba aureba.har yakoma ga mahaliccin shi muddin baisamu kwatankwacin zahra ba,
Tad'ora dafad'in "babu tallar yammatan daba ayiwa isha'q ba amma yace ina.shifa angon xahra ne,tausayinshi yasaka naxura mashi idanuwa,har tsawon watanni shidda.
Dayake Allah gafurune kuma rahimu saiya maido mana abinda muka rasa tsawon lokaci muke kwana muke tashi da kukan rashinta."
Tadakata tana nazarin fuskokin dattijan biyu,
Sai dai cikinsu babu wanda yasan inda zancenta yadosa,hasalima anasu ganin wannan matsalace data dace tasanarma wad'anda suka santa bawai basuba.
Indai ba'itama tarasa nata hankalinba,su menene nasu illah iyaka suce Allah yajikan rai.
(anasu ganin ba.)
Abba yad'an numfasa yace"to dafarko muna maki ta'aziyya dakuma bakin cikin rasa y'a tamkar zahra.saimuce Allah yajikan rai,abu nabiyu daya tsayamun araina shine mudai bamusan menene ainahin dalilinki na za'barmu a matsayin wadanda zaki sanarma damuwarki ba.
Idan har kina son sanarda wani damuwarkine babu mafi cancanta kamar yan'uwanki da danginki bawai muba,da bamuda maganin dazamu iya baki domin warkewar damuwarku.
Ummata jinjina kai"wannan gaskiyane."
Murmushi doctor ru'kayya tayi tace"malam aikune maganin matsalata,nazone da 'kokon barata dakuma nan arziki akan ku taimakeni,kamar yanda Allah ya taimakeku idan baku za'bama d'iyarku zahra mijiba kubama d'ana isha'q aurenta."
Daga umma har abba had'a idanu sukayi,lokaci guda suka sakarma juna murmushi,abba yace"toga dai dukkan alamu acikin abu biyi dole asamu d'aya,imma dai makuwa kikayi kokuma kema bakida hankalin.idan bayaga haka yaushe zakice inbama d'anki auren zahra.? Tukunnama haka kawai siyaa bagatatan sai ind'auki y'a inbaki saikace banida hankali."
Dr. Rukayya taji zafin maganar abba,amma dayake ance mai nema baya fushi,saita sake numfasawa tace"kayi ha'kuri abban zahra nafahimci baka gane zancena ba sabo......"
Sauran maganar ta ma'kale a fatar bakinta lokacin da zahra ta kunno kai gidan, tana fad'in"Allah ya isa banyafe ba,muguwa azzaluma kinbugi wuta balbal har kabarinki na balbala da wuta,kuma wlh yaro ya'kara cemun zahra'u mala'ikar yara sainaci kutmar babbar saibitin babakeren buuuuu........."
Bata 'karasaba umma takaima bakin naushi,tace "to jarababbiya ko'ina saikin nuna halin naki."
Zahra cikin hawaye tace"to umma sai takamani tayita dukana wai don nabugi d'anta aishi yafara jana."
Umma ta zuba mata harara"gara dayajaki aike karyace ko.dakowa zaidinga tsokana,kinzama sakarya a layi kowanne datti badole a sauke a kankiba."
Zahra tace "wlh anjima sainayima gidansu ruwan duwatsu."
Umma tayi tsoki"aikin da kika iya kenan fitinanniya."
Dr.ru'kayya datayi mutuwar zaune,tasaki baki aranta tana tasbihi ga Allah wanda ya'kagi kamanni yakuma banbanta halayya."
Nima sai naga comments xan cigaba don naga kamar buk din beyi muku dadi ba


Kuna tare da maman meenat, Aisha t. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀




By maman meenat


EDITED BY AISHA ABDULLAHI(UMMUN FAROUQ)


CHAPTER 7.




Umma taja tsoki takoma tazauna abinta,
Yayinda zahra ta cillar da jakar islamiyyar dakuma hijabi tafad'a band'aki.
Dr.ru'kayya tasauke numfashi tana kallon su umma kafin tace"wannan kuma 'kanuwar Zahran ce kokuwa.?
Umma ta kalleta da mamaki tace"a'a itace zahran ai."
Wani shegen gumine ya karyoma dr.ru'kayya lokaci guda tafara tsane zufa da handkerchief dake hannunta aranta tana addu'ar tafarka daga rud'adden mafarkin dayayi hajijiya da tunaninta dama kwakwalwarta.
Tad'an saita kanta kad'an kafin tad'ora dafad'in"to agaskiya dolene ku kalleni a matsayin wacce kanta ya zautu,kokuma 'batan kai inba hakaba babu mahaluki mai hankalin dazai dubi karancin shekaru irinna zahra a gari ba 'kauyeba yace ayimata zancen aure."
Tad'an tsagaita tana sauke numfashi kafin tad'ora dafad'in."adukkan zatona dakuma tunanina nayi zaton zahran babbar budurwa ce,amma don kamanni da tawa zahran tabbas suna kamanni nagasken gaske,sai dai kash wannan zahran tayi kankantar dabe kamata ace anyimata aure yanzuba."
Sai lokacin su abba suka fahimci inda tasa gaba,
Abba yami'ke yana cewa"inace dai yaron dakeson zahran shine awaje tsaye ko.?"
Doctor ru'kayya ta'amsa dacewar"shine malam",
Abba yafita kofar gidan,isha'q har lokacin yakafe kofar gidannasu zahra da manyan idanunshi yanason ganin ta'inda kyakyawar fuskar zahra mai kama data black Americans zata 'bullo,sai dai sa'banin zahra saiyaga abba yafito yana sa'ba babbar riga.
Isha'q yayi saurin du'kawa yana gaida abba,
Abba ya'amsa kanshi tsaye yace"kaine isiyaku."?
Isha'q yawaro idanuwansa masu kwarjini da haiba,yace"abba isha'q nake."
Abba yace "afto ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login