Showing 21001 words to 24000 words out of 25328 words

Chapter 8 - MIJIN KWAILA Book Complete .txt

auta agabane wai eye."


sahura tana dariya tace"allah umman zahra kibani ita insakata daki
inmata yar nasihar nan tamu ta manya watakila ashawo kanta.


umma gaba tayi"kyaji dashi dai."


su anty hafsa ne suka shigarma zahra akayita caccakar juna.


hakan yabama zahra damar sulalewa tafita babu wanda yasani.


akofar gida tayi kacibis dasu ummilolo anrasa gwanin dazai ahiga gidansu zahra kowa yana tsoron unma.


dasauri zahra takarasa ta basu hannu suka kashe tadubi uwande datasaki baki tana kallonta tace"dalla lafiya kike kallona,konaci ban biya ba."


uwande ta washe hakora tace"uhm ganinai kinzama yar gayu wlh."


dariya zahra tasaka kafin tace"yara kuma bakuda wayo kuce aimuku aure irinnawa,yara gidan bene zankoma inta kwana acan."


ummilolo tadanyi sakale,saikuma tasaki dariya"su zahra yan gayu za'asha dadin bene."


zahra ta kyalkyale da dariyar jin dadi,


ummilolo tace"dama ace nice zahra yaseen indinga hayewa kan bene inayin sululu.indinga shan dadina."


sauran yaran suka dinga dariya dafadin"ahegiya zahra za'asha dadi🤣.


zahra jin ana zugata hadacewa"aidama d'arewa zanyi har abinci akan bene zandinga ci,idan yara sukaje shan dadi inkorosu yanda akeyi gidan alhaji canji."


duk yaran suka goya mata baya akan haka zatayi.


yar purse din hannunta tabude tafiddo dari biyar din da abba yabata da safe kafin yafita yace yaudai tasha shagalinta.


nunama su ummilolo tayi,nanfa uwande uwar shawara tace"taf danice zahra kasuwa zanje insiyo magarya da aduwa da kukar yin kwarbebe indingayi inashan abuna wlh."


aiko zahra tace efaaa.azo aje kasuwa asiyo hada farama."


hakan kuwace ta kasance,duk tarkacen dasuka lissafa seda suka siyo hada goruba,zahra jinta take kamar yau take sallah don yau tana watayawa son ranta.


gidan su uwande suka shige,gidan bakowa sunacan gidansu zahra.


dayake gidan ginin kasane katangar duk ta gwanbale hakan yasaka zahra d'arewa akan katangar tana gwaguyar goruba hankalinta kwance.


sauran kawayen suma suna tsaitsaye gefenta,tadaiyi abin kirki tabama duk mutum biyu daya su raba.


itakuma uwar gayya tadumtse ledar a hannunta.


acan gidansu umma kam hankali yatafi bawanda yafarga da zahra tafice daga gidan.


***"***bangaren ango ishaq kam yau farin ciki bqya misaltuwa kallo daya zakamashi ka tabbatar da hakan.


duk da ayyuka sun sakashi gaba yau yaso ace shine dakanshi zai dauko little zahranshi,amma bayanda ya iya dole yayi handling komai awajen sadiq dasauran friends dinshi.


Dr.rukayya ma gida yagama cika da baki,su aysher ne kan gaba wajen hidima.


gwaggo rabima kakar ishaq ta'iso tun jiya hakan ba karamin dadi yama dr.ayaher ba.
[8:18PM, 11/27/2017] maman meenat😍: wadda keta kaiwa da kawowa,


gwaggo rabi ancakare da wani leshi me dankaren kauri,


gwaggoro tayi da kallabin tadauko kujera tadasa kofar dazata sadaka da sashin da zahra zata zauna tahana koda yara su gifta.


duk wanda zaishiga zata soma sababi"kaga munafurci wato anga isiya zaiyi amarya shine akeso a'bata mashi dakin amarya to naga me wucewa nan."


yanda ta kwama gilas afuska kamar aku kuturu shine zaibaka dariya🤶🏼.


ganin hakan yasaka dr.aysher neman kujera tazauna gefenta dafadin"bari intayaki gadi gwaggo naga yara sunason bata dakin amaryar."


gwaggo rabi tace"kemadai kya fada yannan,ita waccan(tana nufin rukayya)dayake bata kishin danta aikinga tazuba masu ido,salon akawo amaryar tace dakin yayi dauda."


dr.aysherh tace "nimadai haka nagani gwaggo".


gwaggo rabi tawangale hakoran dawasu sunfara zubewa tace"ainakosa inga wannan amaryar nasam saitafi ta dan'uwanshi,dayaje yakwaso kafura gashinan jikokina sunzama kamar basu sanniba da anyi magana su turanci,ke ko sallah basayi fa.kinga yanzu ita wannan datazo ta haifomun nawa nasu ko kallo basu isheni ba."


dariya takama dr.aysher taguntse baki.


nima dai dariyar nayi nace " ​mata ku qame qam​🤣


​mum meenat​🌹


[12/12, 4:31 PM] ‪+234 814 483 2069‬: *MIJIN 'KWAILA*🤦🏼‍♀










Chapter 24.










*written by maman meenat*😍














*edited by Aysha abdullahi (umman faruq*😘










*Inasake jaddada godiya gareku masoyana masu kaunar rubutuna hakika kunada gurbi na musamman acikin zuciyata.*


*inasonku fiye da ynda kuke sona,naga sakonninku masu tarin yawa akan tambayar maman meenat lafiya.masu kirana masu text messages damasu taboni ta watssapp hakika ina jindadin haka tare da dinbin godiya,Alhamdulillah meenat tasamu lafiya jazakumullah for the special prayers*😘
















Wuraren 5:pm yan daukar amarya suka iso,zahra dakecan tana wasanta dasu ummilolo tahango anty lubnah ta nufosu a fusace.hakan yasakata dira daga kan guntuwar katamgar dasauri,karasawa tayi kusa da anty lubnah kafin tayi wata mgna anty ta tareta dacewa"da iznin wa kika fito daga gida?"


Idanun zahra dasukayi narai-narai tasoma kwabe baki danufin kuka,anty lubnah tamaka mata harara tace"kika yimun kuka a swear saina baki mari stupid din yarinya kawai."


Zahra ta kauda kai taji haushi anty taamata fada agaban kawayenta.


Tasa keyarta antin tayi,uwande tabiyota da sauran tarkacen data siyo tana cewa"zahra ga magaryarki".


Anti lubnah tace"ku'ajiyemata kwa taho dashi,aizakuzo ko?".


Dadi ya ishesu suka amsa da eh.


Zahra namasu kashedin kada suci mata ko guda dayane.


Asirrance anty lubnah tashiga da zahra gidan wanda yake makil da jama'a don ko zuga yan unguwa sukayo suma zasuje gidan zahra ganin kwaf.


Saida suka sake cudata tasille jikinta da wanka,wannan karon shigar tattausan voyal lace tayi,dinkin buba da single wrapper, tayi matukar kyau babu wani tarkacen make up dasuka bata damar tayi.


Sosai umma tayimata nasiha wanda duk rashin jinta saida jikinta yayi sanyi kalau.


Inna maryama ce yayar umma ta lillubo amarya da katon abaya anrufe fuskarta ruf dashi,


Sauran mata suka soma guda.


Dakin Abba akashiga da'ita da hikima da dabara iron tasu ta manya yayima zahran nasiha mai tsayawa arai.


Daganan yabama innan umarnin tafiya da zahra.


Sai alokacin hawaye masu zafi suka soma bin kuncin umma,bata taba tsammanin rabuwa da zahra a irin wannan lokacin ba.


Tanaji tana gani aka fice da autarta zahra zuwa gidan aure.


Da addu'ar dawwamammen zaman lafiya tabisu .


Shima Abba kewa ba kadan ba yakeji,bayan cijewa da auriya shima zai iya saka kuk Zahra dai ko'ajikinta wai an tsikari kakkaus.


Amotama wara idanunta tayi fes tana kallon hanya,aranta tanajin nishadi mara misaltuwa.


Tafiya menisa ta sadasu da malali quarters inda gidan dr.rukayya yake,kato n gida daya gji da haduwa.


Horn sukai me gadi ya bude masu get,daganan motocin suka fara sunna hancinsu cikin gidan.


Sashen mummy suka wuce da ita mum din dakanta takama hannun zahran tawuce da ita part dinta don batason jin kananun maganganun dake tashi nacewar ishaq ya auri *kwaila*.


Su anty hafsa sune suka tsaya da zahra suka hanata duk wani rawar gaban hantsi don kuwa burinta tana zuwa ta dare bene😝.


Sukam su ummilolo ai duniya sabuwa ankashe tsufa an daure mutuwa.
Baki suka saki suna mamakin gidan zahra aransu suna raya zahra anzama yan gayu.


Basu anty lubnah sukabar gidan ba sai wajajen karfe Tara na dare,sosai suka sake kimtsa dakin zahran dakuma sake jaddada mata kada tasake tayi wani abu dazaisa kowa ya tsaneta,takame takuma zama mai hakuri tarage rashin kunya da saurin fada.


Itadai da to kaewai take binsu.


Ba karamin kokari Abba yayi
Adakin zahra ba kam


Donkuwa komai yaji masha Allah.


Uwande saida xasu tafi tabama zahra tarkacenta dayimata saida safe.


Sai a lokacinne idanun zahra suka fara raina fata,bata zata haka abin yakeba saida su anty lubnah zasu tafi.


Kuka sosai tasaka tarikesu gam tana cewa ita su maidata wajen umma,


Bakaramin tausyi tabasu ba,amma kuma babu yanda suka iya.


Mummy dakanta tashiga dakin tana rarrashin zahra,


Takuma turamata hanan suyi wasa,amma ayake akwai rashin sabo itada hanan din kallon-kallo sukayita ma juna.


Gwaggo rabi dai ciwon kafarta ya matsamata shine yahanata zuwa ganin amarya tayi kwanciyarta tace saida sfe taganta .




Goma da mintuna ashirin ango ishaq yafaka motarshi a farfajiyar gidan,fitowa yayi cikin shigarshi ta manyan kaya dasuka dace da siffarshi ta hadadden namiji.


Kamshin turarenshi kadai ya isa ya tabbatar maka cewa angone.


Hannunshi yana rike da ledar kaza da yoghurt daya siyoma amarya zahra,kai harma da chocolate.


Da kuzarinshi yake tunkarar gidan kada kaso ka tona zallar farin ciki awajenshi.


Wai yau shine Allah ya mallakama zahra amatsyin mata,tabbas bayada abinyi sai godiy.....












Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe zamu juna ida. Allah mai kowa da komai ya aramana lokaci.




*for any correction, comments or complaint about this book u should contact me at 07014709470*...




*mum meenat*✍🏼
[12/12, 4:31 PM] ‪+234 814 483 2069‬: [06/12 12:40 pm] Maman Meenat: *MIJIN 'KWAILA*🤦🏼‍♀












Chapter 25.














*Written by maman meenat*😍












*Edited by Aysha Abdullahi T.Fulani(umman faruq)*😘










*SAKON MASOYA*😘




*Salam er uwa.... Sunana Maryam Muhammad* *Alameen... Amma ana kira na first lady... Asalina er* *garin Maiduguri ce... Amma yanzu ina aure a zaria*
*Wato hakika ina karanta novel dinki ne na MIJIN KWAILA* *gasky na dade banyi dariar da nasha da nake* *karanta novel din ba🤣🤣🤣*
*Allah ya kara baseera da zakin hannu*
*Daga masoyiyar ki MARYAM FIRST LADY (maman deena)*.




*mum meenat*😍


Wa'alaikissalam




Nagode sosai da kulawa Maryam




Dafatan zakici gaba da bibiyar labarin mijin kwaila..😘










Da wannan tunanin ango ishaq yashiga cikin gidan nasu,


Tsayawa lissafa farin cikinshi awannan rana ganina bata bakine.


Sashen mummy yafara zuwa bai sameta ba tana bangaren Daddy saidai gwaggo rabi databi kujera ta bararraje kafafu tana matsasu don jitake kamar ana mata sukuwar dawakai acikinsu.


Dasallama ishaq tashiga falon,gwaggo rabi ta'amsa lokaci guda tana wangale hakora dafadin"Ango kasha kamshi,"


Ishaq ya sadda kai yana dariya kasa-kasa yace"kewai tsohuwarnan kardai har yanzu baki kwanta ba."


Gwaggo rabi ta tale baki,kafin tace"inanaga ta kwanciya,ai inanan nakasa natsare dama jiran dawowarka nake ai,Donna kafafu sun matsamun aida acan bangarenku zan kwana".


Ishaq ya bude ido sosai yace"kwana kuma gwaggo? "


Gwaggo rabi tace "kwarae kuwa,saboda banason amarya tabukaci wani taimako ba babba akusa,tunda aikai da ita suka sabon shigane,jirani dai ina zuwa."


Tamike tana dafa cinya tana tafiya a gwagwale,


Ishaq bin bayanta yayi da kallo harta shige dakin datake zama aduk lokacin datazo.


Azuciyarshi yana mai-maita kalmar sabon shiga'to mekenan?"


Juyawo da kallonshi yayi gareta jin tana tahowa.


Takaraso dakyar tana mayar da numfashi tazauna jagwab,tadora dafadin"tunda aka saka ranar aurenku nasiyo wadannan kayan na'ajiye inajiran lokaci."


Amma kafar nan bata tashi yimun rashin mutum ciba sai yau."


"Karbi nan".


Tafada tana mikama ishaq bakar ledar dake hannunta.


Amsa yayi fuskarshi cike fal da tarin tambayoyi,


" bude mana kagani"


Muryar gwaggo rabi ta katse tunaninshi.


Ahankali yasoma warware ledar,wani farin kyalle yafiddo saikuma wani sassake aciki.


Yatsura mata idanu,kafin yace"kyalle nagani dakuma icce namiye wannan?"


Gwaggo rabi da tuntsuro kallabi gaban goshi kana tace"kyalle ai shine zaka shimfada kafin kataki amaryar taka,shikuma wannan iccen ai sassaken kukane,kayi kokarin dafashi da jar kanwa yanzunnan kashashi.To inamai tabbatar maka duk taurin matarka saika hudata,don zaka kara karfi dakuma kuzari,
Aimu zamanin my maza basa shigar mace haka bawani dan tanadi yo ai rainaka zatayi."


Takare tana washe hakora,ganin ishaq ya kasa magana yasa race"kada kawani damu,wannan maganin kasadinne ai,karyar mace taga gazawarka.


Ko cikin darene kuka gama ka dawon da kyallenan anunama dangi,matarka takawo matancinta gidanka kajiko,jeka ango Allah yabada lafiyar jiki."


Tafada lokacin datake kama hannunshi da turashi zuwa waje.


Mamaki ya ishi ishaq, yace"yanzu gwaggo rabi don Allah kina nufin bakubar wannan banzar Al'adar ba har yanzu,"


Towaima cemaki nayi abinda yasakani yin auren kenan,haba gwaggo don Allah kima daina wannan kadasu mummy sujiki."


Kallaon banza tamashi tace"eh aifa.to saurareni dakyau,ko ita uwar taka saida naga shedar jinin matancinta bare matarka,kuma a al'ada ai yau dai daka shiga daki yaune zaka taki amaryarka,don haka inkasa iyashege wallahi dakaina zan shiga in shimfada kyallen."


Taci gaba da sababi"yo harni za'anunama boko,ba boko ba walla koma menene ayau dai saika taki yarinyar nan,don nakosa inga jikokina ehe."
[06/12 1:11 pm] Maman Meenat: Ishaq kasa magana yayi don tsananin mamaki,amma daya tuna jaraba irinta gwaggo rabi saiya saki murmushi yace"shikenan matar,ai duk abinda kikace shi za'ayi,
Bari inje kada amarya tagaji da jirana ko?"


Yakare maganar yana haramar wucewa.


Gwaggo rabi data rangada guda tace"jeka sabon ango Allah yabada sa'a,bance ka sasdauta mataba.
Don banson ta rainamun kai.
Bayanma bikin yazo ina umara ai naso ace dakaina namka hadin uban maza,".


Dariya kawai ishaq yayi yashige abinshi.


Gwaggo rabi ta bi bayanshi da addu'a harya bacema ganinta.


Komawa ciki tayi ranta fes,addu'arta daya daren yau tasamu jikoki.🤣


Zahra amarya tuni tasoma baccinta da kayan dake jikinta, ta takure akan kujerar datake zaune.


Hanan dama tana ganin zahra tfara bacci itama tayi dakinta abinta,don dama atakure take.


Da sallama yashiga dakin,
Ba'a amsaba,sai kamshin turaren wuta kawai dake tashi.


Yakarasa ciki ahankali,
Idanunshi sukayi tozali da zahra dake kudundune tana kwasar bacci abinta.


Ajiye ledar hannunshi yayi,ahankali yasaka yatsanshi ya zagaye round face dinta dake kara kyau intana bacci.


Tsuramata idanuwa kawai yayi,ahankali tunanin late zahra yasoma ziyrtar zuciyrshi,


Ya numshe idanunshi dasuka ciko da hawaye,


Baitaba ganin kamanni zallar kammani kalar na zahra da zahra ba.


Yanada tabbas dakuma yakinin Allah ne ya canja mashi little zahra da waccen late zahra din.


Wani mugun sontane yake ratsa dukkan sasan jikinshi,


Kama hannunta yayi ahankali yasaka cikin nashi yana murzawa ahankali.


Hakanne ya farkar da zahra dake bacci tabude idanunta tar akanshi.


Donma sa'arta daya batada magagin bacci.


Idanunta ya gauraya dana ishaq, tamike dasauri tana murmushi,tace"lah kadawo?.


Shima smile ya sakar mata yace"nadawo zahra,haka kike bacci da wuri dama".


Dariya tasaki kawai.


Kamo hannunta yayi yace "zokici abinci ko?"


Tadan langwabe tace "aina koshi."


Namaci wanda mummy takawo.


Kallonta yake cikin ido yace"nawa special one ne ai.oya zokici".


Bamusu tamike,dakanshi yakama hannu ta har toilet saida tawanke baki,


Shine ya yanka mata kazar,zahra wadda tasaki baki tana kallonshi sam bata tankaba.


Ganin ya nufi bakinta da naman yasa tace"tab!nidai kabani inci dakaina,saikace banda lafiyane zaka bani abaki."


Dariya kawai yayi yamika mata plate din,datake batajin yunwa bataci wani me yawaba ta ture.


Dakanshi ya hada mata ruwan wanka tawatsa tana korafin"nidai ummana batacewa sainayi wanka idan ina bacci."


Kayan baccinta yafito mata dasu,nanma bata musaba tatube riga agabanshi tasaka ta baccin.


Kirjin Kama's kamar siminti🙈 .


Bai damuba,shidai kallonta kawai yake.


Saida tagama tahaye gado takwanta abinta.


Shima wankan yayo yagama shirinshi dayake na al'ada,


Ahankali yahawo kan gadon,yajawo zahra jikinshi.babu komai aranshi kawai yanason jinta kusa dashi.


Zahra kam bigit tamike idanu waje tace"anan zata kwanta,"


Bai tankataba,illa smile daya sakarmata.


Mikewa tayi,tana yayimar batgo tace"tab!nidai wallahi bazan kwanta kusa dakai ba,niba 'yar iska bace."


Ishaq yarike wuya yana kallon zahra dake murguda baki.












*mum meenat✍🏼*














*for any correction,comments or complain you should contact me at 07014709470*😘


*MIJIN 'KWAILA*🤦🏼‍♀








*written by Maman meenat*😍








Chapter 26.










*Ina baku hakuri masoya akan jina dakukai shiru jiya,nayi typing har nayi post abun haushi WhatsApp din yasamu matsala wannan yasaka gaba daya nayi missing komai nawa saida nasake installing kuyi hakuri pls*.


*Wasu zasuga sunman magana banyi responds ba,tokuma kuyi hakuri matsalar tashafeku kuma,don gaba daya chats dina suka 'bace.I luv you guys'😘*.












Ishaq wanda yasake hannayenshi ya tallafo wuyanshi kallon zahra kawai yake yana smiling, wai ita ba yar iska bace.Chaii,shikam inbanda soyayyama mezai tsinta ajikin zahra wadda ko irin yar kirgan danginnan nayara ma bata fara ba.


Sakkowa yayi ahankali yatako zuwa inda zahran take kwance,gaba daya ta takure jikinta tasaka kafa duk ta tattake bargon datake ciki lullube aganinta babu tayanda ishaq zai iya budewa.


Acikin ranta kuwa tana ayyana ishaq amatsayin dan iska,to dan iska mana inba iskanci ba nameye zaice wai zai kwanta kusa da ita?"


Tai kwafa daga kwancen datake aranta taraya tadena sakar mashi fuska tunda d'an iskane dama,kai gobema zatayi tafiyarta gida tafasa shan dad'in bene.


Da tulin tunane tunane babban barawo bacci ya sureta,batayi aune ba.


Ishaq dake tsugune gabanta yanajin alamun tafara bacci yasauke ajiyar zuciya,aranshi yaraya "zahra hukumace saida lallashi.


Kacokam yadauketa itada bargon ya shimfide bisa gado,yagyara mata kwanciya yaja pillow yadora kanta akai,gashinta yasauka bisa pillon.


Yadan jima yana kallon fuskarta kafin yashafi tattausan gashintan yayi addu'a ya shafa mata gami da sumbatar goshinta.


Yajuya ahankali yarage hasken dakin daga full light zuwa dim light yafice daga dakin bayan yaja mata kofar.


Kai tsaye dakinshi ya nufa,yagama shirinshi yakwanta abinshi aranshi yana karajin kaunar zahranshi jini da tsoka.


Yadau tsayin lokaci kafin bacci yayi gaba dashi.


Washe gari karfe 4:30am yatashi kamar yanda yasaba koda yaushe,a'aldarshi yakan tashi ya gabatar da nafiloli yayi karatun Alqur'ani kafin kuma yayi sallar asubahi.


Hakance ta kasance kuwa don saida ya kamalla komai yayi shirin masallaci,dakin zahra yanufa danufin tayar da'ita tayi sallah.amma ga mamakinshi ya'isketa tana sallar.


Wucewa masallaci yayi abinshi aranshi yana raya uhm lallai zahra anfara hankali koda yake gaduk wanda yasan Abba dakuma tarbiyar gidanshi yasan wasa da ibada baya daya daga cikin dabi'unsu.
Abba mutum ne jajurtacce daka tsaya tsayin daka wajen gina rayuwar iyalinshi abisa koyarwar kitabu wassunah donma Allah yabashi zahra datake neman gagararsu.


Ishaq bud'e kofar part din nasu yayi danufin wucewa masallaci, amma kuma saime?


Gwaggo rabi yagani rakabe jikin glass din window takasa kunne bagalo,ko motsin kirki batayi gaba daya hankalinta yana kan abinda takeyi.


Gaban ishaq yafad'i,aranshi ya ayyana gwaggo rabi amatsayin jarababiyar tsohuwa,to jaraba mana,inba jaraba ba mezai kawota kofar taga da asalatun fari.?


Wato tana labene taji abinda yake wakana tsakaninshi da zahra.


Kwafa yayi kafin yakarasa inda take gami da dafa kafadarta.


Azabure tajuya tana cewa"wa'innahu min sulaimana....."


Sauran maganar tamakale afatar bakinta ganin ishaq ne,tasauke ajiyar zuciya cike da borin kunya tace"Amm,af...dama cewa nayi bari inzo inji ko kuna bukatar wani taimako,kasan yaran yanzu badai raki ba.daga sun kwana da namiji saikaji sun langwabe wai basu da lafiya."


Takare maganar tana gyara daurin zanenta dayake kokarin kwancewa gami dajan majina sharab,tawaige gefe ta fyace feeet.ta durje hancinnata da tafin hannu,bayan tahad'e hannun na dama da hagu ta mutsuke kamar wacce ke shafa versiline.


Ishaq ya watsa mata harara cike da kallon yanda take kazanta yace"to ai saiki koma inda kika fito,dondai bawani taimako naki damuke bukata."


Wangale baki tayi tace"to ai shikenan ma,fitomun da kyallen ko."


Juyawa yayi yana tafiya jin anfara tada sallah yace"kije kiyi sallah abinda zan dawo ne."


Aiko bamusu tajuya itama tana sambatu dafadin"to Allah dai yasa Anfara asa'a ai haka muke bukata,kafi yayanka hankali me auren kafura.kaga da'ace yanajin maganata Aida tuni yasaki kafurar nan yazo nan gida yayi aurenshi abinshi.


Shidai ishaq gaba yayi baisake tanka taba,sai dai harga Allah bayason wannan sakarcin da tsohuwar takeyi,aganinshi ragema kanta daraja take.
Yo danma zahra yarinyace,da'ace babbace taleko taga abinda Rabin takeyi aitsaf zata wanketa soso da sabulu.


Yaja tsaki shidaya yana takaicin halin kakar tashi.
















*real mum meenat*


Maman muhamman Naseer ba😘


*MIJIN 'KWAILA*🤦🏼‍♀












Chapter 27.










*writing by Maman meenat*😍










Sai wajajen karfe bakwai yashigo gidan,bangaren amarya zahra yafara lekawa,kwance ya isketa ta kudundune cikin bargo.hakan yabashi tabbacin bacci takeyi,yaja mata kofar yanufi bangaren iyayen nashi.


Gwaggo rabi itace uwar zaman falo to yaudai bata falon don haka kanshi tsaye yanufi dakin mum din,tana gaban dressing mirror tana gyara zaman kallabin kanta lokacin dayayi sallama hadi da sawo kai cikin ni'imtaccen dakin nata dabai rabo da kamshi.


Murmushi tasaki tana amsa sallamar tashi, karasawa yayi inda take yadafa kafadunta hadi da d'an kwantar dakai bisa bayanta yace"morning momma."


Tasaki karamar dariya dacewa"haba ishaq kaiwai meyasa har yanzu sam kaki ka girmane,yanzufa kazama babba kafara aje zuri'a saika rage wannan shagwabar taka.haka yayanka zasu taso suganka gotai-gotai kana yimun shagwaba ko?.


Dariya yayi sosai yace"mummy niko yara d'ari na ajiye ai bazan dena yimaki shagwaba ba,kefa mumma dina ce.kuma wacce akoda yaushe Idan nakalleta nakanji dadi mara misaltuwa so why zandena langwabe wa momma alhalin har yanzu am still young. "


Gyada kai tayi tana dariya tace"to aikaga saika bada himma,ina d'iyata zahra baku shigo tare ba mu gaisa."


"Naleka na'iske tana bacci,inaga bayan tayi sallah ta kwanta."


Yabata amsa lokacin dayake goge mata takalmin data fiddo zata saka.


Mikewa tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login