Showing 12001 words to 15000 words out of 25328 words

Chapter 5 - MIJIN KWAILA Book Complete .txt

haka dasauri tashige gida tanacema zahra "jirani yanzu zan fito,"
Mintuna kadan kuwa saigata tasha tsaka tsami fuskarnan har shining take saboda Vaseline data sha,
Jerawa sukayi da zahra suna tafe sun labarin boko.zahra nagayamata yanda taci uban wata prefect dinsu jiya sunata kyalkyala dariya,
Sanda suka isa gidan anty hafsa tagama gyara gidan tsaf,tashirya zaman jiransu zahra kawai takeyi.
Da sallama suka shiga,zahra tuni tafara bude-buden fridge wai zatasha exotic saida anty hafsat ta wona zahra sannan tabar gidan tana sake jadadda masu akan kada suyi mata 'barna.
Sundad'e zaune afalo suna kallo,kafin ummilolo tad'an yamutsa fuska dacewa"ni yunwama nakeji,dama banci abinci ba nataho",
Zahra tami'ke tana binciken kitchen din anty hafsa amma bata samu abinci ba,coz ta'boye duka abincinta saboda tasan halin zahra.
Ganin babu yasaka zahra cewa"kawai kizo mu girka da kanmu,"
Ummilolo tad'an zaro idanuwa,saikuma tace"to".
Fridge zahra tafara budewa dan'kare yake da nama dakuma kifi,hakan yasaka zahra kwaso uban nama tabama ummilolo wai ta soya masu ita bari ta d'ora shinkafa.
Haka kuwa akayi,
Zahra dake kokarin kunna gas tace da ummilolo"yarinya ki wanke namannan yafita tas naji ummana tanacewa nama 'karnine dashi."
Ba gardama ummilolo ta zuba uban ruwa acikin nama tasoma durza kamar tana wanke kayan sawa,saida ta tabbatar naman yacanja kala daga jaa zuwa fari 'kal sannan tanunama zahra wadda tazuba mai yakusa kwalba acikin tukunya tanata banka mashi wuta,
Saida zahra ta sunsuna naman kafin tace"yawanku amma kid'an kara durzashi naji yana 'karni ,
Ummilolo takuwa dage iyakar karfinta taci gaba da wankin nama.
Zahra bayan soyuwar man shinkafa ta dumbuzo batako wankeba ta afka cikin man...




Kuyi hqr nagaji yau




Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah ��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*����‍♀


*by maman meenat*


edited by Aisha T.fulani (umman faruq)


*wannan shafin cigiyane*
*inakuke my dada.aisha tasi'u yamel.kuna ina maman meenat na gaisheku.bilkisu gudaje ur page is here*��




Chapter 13.




Ummilolo takuwa dage taci gaba da wankin nama saida naman yafara zaganyewa tsabar azabar dayasha,
Tajuyo da robar da naman yake ciki tana tambayar zahra "yayi haka?"
Zahra tagyad'a kai"yauwa ummilolo shiyasa kike burgeni wayo gareki kinfi uwande wayo."
Ummilolo tahau washe baki zahra ta yabeta,
Tace"tome zanyi yanzu",
Zahra dake juya shinkafa cikin mai tabata amsa"kitsiyayi mai kawai kici gaba da soyawa".
Hakan ce kuwa takasance,ummilolo ta antaya uban mai a cikin kaskon tuya tawatsa naman ciki man baikoyi zafi ba,hakanan bata tafasa naman ba bare zancen su gishiri da magi da sauran tarkacen kamshi.
Zahra dake juya shinkafa saida ta tabbatar shinkafar tacanja kala daga light brown zuwa dark brown sannan tadebo tulin kayan miyan data jajjaga tawatsa ciki,taci gaba da soyawa tana bama ummilolo labarin "ina kallon yanda anty murja take soya shinkafa wai sunanshi ko frad race ne komenene oho mata,(fride rice)amma yanada dad'i irinshi zanmana. "
Ummilolo tagyd'a kai idanunta jajawur saboda yanda mai yake fantsalomata yana 'konata amma takasa sanarma zahra saboda tsoron masifar zahran.
Saida kayan miyan da zahra take soyawa yafara sarqesu sannan ta antaya ruwa yashanye kan shinkafar gaba d'aya,
Takuma dunbuzo maggi star da already anty hafsa tadakeshi ta ajiye a mazubi mai kyau,xahra tazuba yafi cokali biyar wai yanda zasu sha dad'i.
Takoma akan gishiri shima batayi zubawar wasaba,hakanan curry tace dole ta zuba mai yawa yanda abincin zaiyi dadi na hakika.
Saida ta kammala tajuyo wajen ummilolo tana bata labarin"yarinya idan yayi dad'i har ummanmu zan d'iba nakaimawa,ance babu kyau kaci abu mai dad'i baka kaima mamanka ba."
Ta tsaya cik da maganar sakamakon hango naman da ummilolo ke soyawa yakusa zama gawayi saboda tsabar baqin dayayi,
Wani wawan naushi ta sakarma ummilolo a baki,cikin rashin sa'a bakib ummilolo ya fashe sai jini.
Duk da haka zahra saida tarufeta da masifar"dalla can dubeki wawuya baki iya komaiba,kalli yanda kika qona naman,donkinga ba gidan y'an uwanku bane."
Idanun ummilolo suna fitar da hawaye tace"tokuma saiki kama dukana"?
Zahra dayake tana 'kaunar ummilolo saita rage murya"tokiyi hakuri nadena,mushirya."
Tami'kama ummilolo yatsa suka sar'ke cikin na juna,
Saida suka gama girki zahra tazuba masu a plate,
Sai daifa loma guda ummilolo takai bakinta lokacin zahra taje d'ebo masu ruwa.
Da'kyar ta iya had'iyeta tsabar mai acikin mai take tsamo shinkafar gawani minahikin gishiri da masifaffen yaji,
Naman kuwa aiko dutse ya shafa mashi lafiya.
Zahra ta 'karaso da sauri tana masifar"ummilolo kefa munafika ce,shine kika faraci tun kafin inzo ko?"
Ummilolo cewa tayi"Allah yabaki ha'kuri",
Zahra tazauna tana hararta,
Lokaci guda takai yankan nama bakinta saidai duk iyakar hikimarta da kokarinta nama yace baisan zancen taunuwa ba.
Hakan yasakata furzar dashi babu shiri,lokaci guda tarufe ummilolo da ruwan masifa wai itace bata iya soya nama ba,
Itadai ummilolo tundaga lomar farko tatsame hannayenta tace ta koshi.
Zahra takai cokalin shinkafa a baki,cikin abinda baifi daqiqa gudaba ta furzar dashi a'kasa lokaci guda tana guntsar ruwa abakinta don jitayi yaji yana neman daskare mata halshe,
Idanu tawatsama ummilolo wadda dariya ke kokarin kwacemata tace"hegiya kece zaki cinyeshi aike kika saka na girka."
Idanun ummilolo tuni sun kawo ruwa,tafara rokon zahra dakyar zahra tace "jeki samo almajirai kice suzo suda yawa."
Ummilolo baki har kunne ta falla waje tana kiran almajirai,saikuwa gasu sun tasarma goma har suna turereniya,
Cikinsu babu wanda robarshi bata cika da abincin ba ga tulin nama kamar hauka.
Amma koda kyalla idanu sukaga mugun man dake yawo cikin shinkafar saida jikinsu yayi sanyi,
'karshe a zaure suka zubar da abincin don tundaga lomar farko suka tabbatar masu girkin basuda lafiyar kwakwalwa.
Tiles din anty hafsa yasha mopping amma haka sukayi mata dama-dama dashi bacikin gidan ba hatta zauren saida suka la'anta karshe sukayita jifar su zahra.
.......................................
Ankawo lefen zahra abin yabama kowa mamaki,amma kuma ba'abun mamaki bane duba da irin dukiyar da mahaifan isha'q suka tara dama shi kanshi isha'q din.
Saitin akwati shidda ne,sha'kare da kaya na burgewa duka mfi yawan kayan English wears ne,hadaddun tops gasunan lesuna da atamfofi dayawa duk an dinkasu,
Kai hatta da takalma size dinta aka kwaso,musamman mummy taje dubai tayoma zahra siyayyar,
Mutanen unguwafa sai mamaki suke da kayan lefen zahra,ahaka taro ya watse dangin mummy suna ganin ankwaso zahra diyar talakawa kuma karama sosai,saidai sun yaba da irin tarbar mutuncin da akayimasu.
Yan unguwa kuwa zuga guda sukayita zuwa kallon lefen zahra balbali zahra bala'i.
Zahra kam koda suka dawo gida taga kayan kasa dena kallonsu tayi,babu abinda yafi bata mamaki da umma tace mata wai duk natane.........




real mum meenat.
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀




BY MAMAN MEENAT






EDITED:AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)


Muna tare daku masoyanmu, Allah yabar so sa qauna ��




Chapter 14.








Zahra ta gwada wasu daga cikin kayan yafi a 'kirga musamman takalman sunyi mata kyau a idanunta harwani canja salon tafiya takeyi wai yanda zata dinga yimasu uwande yanga take gwadawa,
Tun umma na korarta harta gaji ta zura mata idanu.
Mata kuwa har dare basu dena sintiri gidan umma kallon lefe ba.
Kwanci tashi bawuya gamai tsawancin kwana,cikin juyawar lokaci dare yakan wanzu yabada safiya safiya tazama maraice maraice yakoma dare,
Acikin wannan juyin na lokaci Allah yakawo mu ranar da take d'aurin auren zahra.
Abun kamar yaune akafara zancen amma dayake komai baida wuya awajen Allah saigashi lokaci yayi,shiyasa bahaushe yake cewa komai akasama rana tozaizo,hakanne kuwa tabbas!.
Ango isha'q cikin d'anyar shaddar githzener dinkin boda wanda ya masifar fito da tarin baiwar kyau da kwarjinin da Allah yabashi,gefe guda yakwafa hula kalar shaddar jikinshi mayen turarenshi yana aikin fitar da 'kamshin da'akoda yaushe yake manne jikinshi,
Akwai bakin takalmin Gucci akafarshi sai siririn glass dake kuma 'kayatar da kyakyawar fuskar tashi,
Lokacin daya fito cikin gidan ta'ke yake da mata y'an uwa da abokan arziki,gefe guda mummy da tarin 'kawayenta anata hada-hada da abincicika.
Ratsa mutanen yajeyi har yakai inda mummy take,yana zuwa ta bayanta ya rungumeta,turarenshi kadai ya shaidamata isha'q d'inta ne.
Juyo dashi tayi a hankali lokaci guda wasu siraran hawaye suka sauka akan fuskar isha'q dr.ru'kayya tasan me hakan yake nufi don haka tafara shafar sumar kanshi tana zuba mashi addu'ar fatan nasara dakuma dacewa akan auren nashi dayasa gaba.
Taron abokananshi duka suna waje suna jiran fitowar ango fuska kamar wanda akayima kyautar gonar auduga haka bakin isha'q yaki rufuwa,dayawa mutane suna mamakin yanda isha'q ya 'kallafa rai akan mace haka soyayya mai zaifi yakeyima zahra so bana wasaba.
Dady ma yana tare da manyan abokananshi wanda sune zasu amshi auren isha'q,sai dai ya aliyu dabai samu zuwa ba,saboda yanayin aiki dayasha karfinshi.
Gidansu zahra kam shina cike yake da mutane anata girke-girke,zahra kam musamman anty lubnah ta gyareta cikin wata atamfa super atamfar jace mai manyan fulawowi dinki doguwar riga bubu tamatukar daukar zahra, musamman jan abu ga ba'ki.
Basu saka mata relaxer aka ba,saidai sun gyare mata gashinta ya kwanta luf yasauka har akan gadon bayanta,duk yanda taso subarta tayi kwalliyarta sun hanata kwalliya maikyau suka tsara mata wanda tayi matu'kar fito da kyan zahran.
Gidan anty hauwa nan kusa da gidan su zahran nan zahra ta tara 'kawayenta sunfi goma sha biyar..
Umma ce ta'aiko masu da abinci,zokaga yanda su ummilolo aka cakare da kayan sallah bikin babbar aminiya sukutum da guda.
Farko abun kamar abin arzi'ki zahra bata tokali kowa fad'a ba,
Saida lami tazo gidan ana cin abinci ana fira uwande ce tafara cewa"yauwa natuna ke lami bayan gulma da munafurci maiya kawoki gidanaanan bayan kince mun wai mamanku tace ko anyi auren zahra babu inda auren zaije tunda zahra batada hankali"?
Lami datakai lomar shinkafa abaki batasan sanda ta 'kware ba,ta fiddo idanu waje dacewa"kai uwande Allah yatsine uwar mai 'karya yaushe nace maki haka?"
Uwande wadda taci d'ammara tace"kada kimaida karuwa y'ar iska,ranar nan da aka aikeki shagon habu cheese zaki siyo maganin sauro da daddare konayi 'karya"?
Ta'tambayi lami tana fiddo idanuwanta waje,
Lami takasa motsi duka jikinta yad'au rawa.
Zahra kam aituni tacire d'an kwali tayi d'ammara tafara turza 'kafafu 'kasa dacewa"aidama nasan babbar munafukace lami,kuma saikin gayamun gidan ubanda nazama mahaukaciya".
Lami idanu suka kawo ruwa,amma dayake itama badaga bayaba wajen iya masifa tayi tamaza wajen cema zahra"gidan ubanki,kika zama mahaukaciyar kodan kinga nayi shiru,shiru shiru ba tsoro bane gudun maganane."
Aitun kafin takai aya su ummilolo sunfara zuga zahra da ri'ke baki"yanzu ke lami zahran kike zagi?wlh zahra kici ubanta rigima uban wata kashe?"
Aiko zahra jiki har tsuma yakeyi ta bugi 'kirjin lami,itama lamin takuwa dage iyakar karfinta ta mangaje zahra har saida kan zahra yabugi bango tafad'i 'kasa.
D'agowar da zahra zatayi idanunta yasauka akan jamila tana mata dariya,
Aiko koda zahra ta d'auki lami saita sunkuta da 'kasa,tahaye tana bugu iyakar karfinta.
Yara suna sake tura zahra,azabar duka yasaka lami cizon zahra a yatsa,aiko zahra kamar jira takeyi tafara naushin bakin lami iyakar karfinta cikin rashin sa'a hakorin lami ya fita baki yayita jini.
Koda zahra taga lami tari'kr baki tana 'buratin kuka,sapita d'aga lami tace dawa Allah ya had'ata bada jamila ba?.
Kama jamila tayi da kokawa,rigima kica-kica aka yaga rigar zahra,abinda ya'kara fusatata ta ri'ke kitson jamila d'aya iyakar karfinta su ummilolo suna jan jamilan amma saida zahra ta fincikeshi fitt kitson ya fita.
Hakan yasaka jamila fashewa da kuka,ta kwashi kitso tayi gida tana kuka itada lami,
Gidansu jamila gidan yawane gasu masifaffu hakan yasaka sukayo zangi guda saigasu sunyo gidan anty hauwa,zasu bugi zahra.
Ganin hakan yasaka zahra ware iyakar karfinta ta angije jamila wadda ke maida ba'asin yanda akayi,waje tayi aguje yayinda sauran yara suka rufa mata baya...
Dai-dai lokacin da motar su isha'q ta iso kofar gidan,tare da manyan abokananshi,
Gefe guda waliyyan isha'q ne cikin fara qal ta shadda.
Zahra nazuwa batare datasan waye gabanta ba,tasaka iyakar karfinta danufin angije kowaye ya tare mata hanyar shigewa gida.
Idanun isha'q ya sauka akan nata idanun,cik tatsaya takasa motsawa bayan hakin datake ajiyewa.
Sauran yaran harsun iso wajen,sadi'q ya kalli isha'q yana tambayar wacece wannan kuma?"
Baikai ga tankawa ba,zahra tasake kwasa aguje tajuya don ganin hanyar gidan nasu a cunkushe.
Gudu sosai takeyi yayun jamila suna biye da'ita dai-dai zata tsallake titin mandawari cikin tsautsayi da baya wuce ranarshi wata 'katuwar prado ce taxo wucewa sam idanun zahra a rufe suke,jikake 'kuuuuu karar buge mutum da motar tayi kasantuwar itama motar a guje take....
Yayun jamila na ganin haka suka juya aguhe waidon kada ace sune,
Zahra kam babu alamar rai a tattare da ita,
Sai jini dake kwaranya akanta harzuwa bakinta da hancinta,akid'imen matashin dake driving motar yafito cikin tsananin tashin hankali ya sunkucin zahra.....


Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀BY MAMAN MEENAT




EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)


Wannan shafin naku ne yara manyan gobe Allah ya shirya mana ku baki daya meenat, saleem �� ismaeel, nasir, aliyu hydr zakin fama, my little haneef, umar farauq adon gari, fysal, little angel aisha






Chapter15.








Tsananin tashin hankalin ganin halin da zahran take ciki yasaka saurayin turata kujerar baya yabama motar wuta sosai yana gudu,addu'arshi d'aya kada yarinyar ta mace a hannunshi.
Wata tsadaddiyar private hospital yakaita,wanda anan suka yanki kati,nan likitansu yake muddin sukazo kasar shine yake kula dasu.
Dr.haisam siririn likita fari 'kal dashi yanada sanqo akanshi,
Shine yafito da sauri don already saurayin daya kad'e zahra yakirashi awaya.
Da nosing guda biyu suka taho suna turo gadon da zai d'au zahra,
Yanda jini ke zuba yafi sake d'aga hankalin matashin.
Kasa natsuwa yayi musamman lokacin dayaga anshige da zahra emergency room saiyake ganin kamar bazata tashi ba,
Zagaye asibitin kawai yakeyi yana naushin iska,gami da furzo da zazzafar iska daga bakinshi yatambayi kanshi fiye da sau d'ari how coms hakan ta faru shikam ko kaza baita'ba kadewa ba barantana dan mutum.
Kusan 2hours yakasa natsuwa,saiyake danasanin zuwanshi kasar Nigeria yazo a rashin sa'a lallai.
Ganin dr.haisam yafito da sauri yasaka saurayin nufarshi idanu jajur yake tambayar "doctor yajikinta bana fatan tamutu sanadiyya ta doctor pls"...
Likitan yayi gaba yana bashi amsa"biyoni muje office dina ko?"
Bamusu yabi bayan likitan jikinshi duka a sabule yake,
Akujera mai fuskantar ta likitan ya zauna yana matsar yatsun hannayenshi d'aya bayan d'aya.
Yan rubuce-rubuce likitan yayi kafin yakai dubanshi akan sauran yakira sunanshi a tausashe" Aliyu ahmad(A.A).
Aliyu ya kafeshi da jajayen idanunshi da babu d'igon walwala acikinsu yabama likitan amsa"sunana kenan,likita sanar dani halinda patient dinnan take ciki kasani sarai banason jan time inabama lokacina muhimmanci fiye da komai".
Gyad'a kai likitan yayi dacewa"hakane".
Yasake numfasawa akaro na biyu"A.A bazan 'boye maka halinda yarinyar nan take ciki ba,hakika tana cikin hali na tsaka mai wuya,babbar matsalar kantane yasamu matsala akwai yuwuwar kozata samu kanta lallai zatayi loosing memory nata."
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,abinda A'A yake maimaitawa kenan,
Saikuma ya marairaice fuska kamar ba A'A da dr.haisam yasani ba,A'a da magana ma ta fatar baki wahala take bashi amma yau shine yake zuba surutu yaga wahala na tunkaro shi.
Cigaba da magana A'a yayi"doctor pls babu wata hanya da yarinyar nan zata zama normal,banason wani abu ya faru da ita ta sanadiyyata.
Natureta da mota kuma ace tayi losing memory what's wrong with me doctor"?
Dafashi dr.yayi dacewa"calm down my friend,wannan matsalar zamu iya solving nata ta hanya mafi sau'ki ammafa sai kabada hadin kai".
Cikin za'kuwa A'a yace"komenene doctor zanyi kokari nidai kada yarinyar mutane ta salwanta dalilina ".
Likitan ya gyad'a kai"d only thing shine a fitar da yarinyar nan waje shine kawai hanyar da nake ganin zamu iya controlin din matsalar tun kafin ta mamaye kwakwalwarta,jinin dake zuba a kanta shine bamaso ya ta'ba kwakwalwa da yawa hakan zai'iya zama sanadiyyarta korasa hankalinta gaba d'aya,
So kadaisan yanayin kasar tamu bawai bamuda kwararrun likitoci bane saidai likitocin dayawansu basuda lokacin patient dinsu."
Aliyu yasauke numfashi,lokaci guda yana cewa"matsalar bazata wuce yanda zan gano ainahin iyayen yarinyar ba,amma zanyi kokarin bada cigiya duk inda ya kamata inyaso sai ayi komai akan idanunsu."
Kallon mamaki dr.haisam yakema A'a kafin yace"abokina wannan matsalar fa bawai matsalace da zamu iya jan time akanta ba,matukar munason rayuqar yarinyar tofa dolene aga yau zuwa gobe ya kasance tana 'kasar cairo don ganawa da kwararruwuce wannan lokacin tamkar rasa yarinyar ne.so d only way inaga kafara processing yanda zakabar kasar da'ita nikuma zanmaka dukkan wani shige da fice daya dace don ganin kasamu manyan likitocin in time."
Mikewa A'a yayi jiki babu lakka,
Aranshi yana raya"kai tsautsayi baya wuce ranarshi,
Dakin da zahra take yashiga tana kwance tayi plat bazaka ta'ba gane kamaninta ba,matukar bakasan taba.
Kanta gaba d'aya ya kumbura fuskarta tayi suntum idanunta duka sunzama kananu saboda kumburin fuskarta impact dai kamaninta gaba daya bakace zahra bace.
A'a jiyayi wani mugun tausayin yarinyar yashigeshi,idan banda taimakon oxygen aibazaka taba yarda zahra tanada raiba,
To ba motsi ba motsawa gatananan kamar gawa haka take.
Dasauri yajuya yafice yabar dakin hankalinshi yakai kololuwar tashi,number mum dinshi yaketa try amma bata shiga sam.
....................................
Isha'q ango anata fama da jama'a amma sam hankalinshi baya tare dashi,saiyake ganin kamar akwai wani abu personal dazai faru.
Yanadai cijewa ne kawai bayason yanunama fans nashi cewar yarinyar data kwasa a guje itace amaryarshi amma a time din jiyake kamar ya bita ya rungume kayanshi yahana koda quda sauka ajikinta.
Duk jama'a sungama hallara liman yafara haramar d'aura aure,lokacin da su ummilolo suka 'karaso wajen a gujesuna kuka da majina sha'be-sha'be,isha'q yafara lura da hakan dasauri yayi wajensu yana tambayar abinda yake faruwa saboda yanda jikinshi yabashi akwai wani mummunan labari dazai riskeshi.
Cikin kuka ummilolo take sanar mashi"wani mai motane ya banke zahra kuma yatafi da i.."
Bata 'karasa ba,isha'q yajuya da saurin gaske ya fad'a motar dasukazo da abokanshi yajata aguje zuciyarshi tana wasiwasin anya zahranshi ce"?
Ganin yanda yafice cikin taron jama'a a kidime shine dalilin dayasaka mutane farga suka fara tambayar abinda ke faruwa.
Itakuwa ummilolo tana mayar da martani cewa zahra ce mai mota yabuge yakuma saceta,
Lokacin da ummilolo take maganar abba yafito daga cikin gida yana sa'ba babbar riga tsayawa yayi cik kamar wanda aka dasa.
Gaba d'aya ma'aikatun kwakwalwarshi sun dakata da aiki na wucin gadi...
Juyawa yayi cikin gida hankali tashe,yana sanarma liman adakata da d'aura aurennan tukunna...
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha ��
4 comments, 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀




BY MAMAN MEENAT


EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ) ��








Kuna raina mmn Fysal, mmn Amna ina alfahari daku yn uwana








Chapter16.






Yanayin yanda mutane sukaga abba yashiga gidanne ya d'aga hankalin kowa,umma tana bakin gado a zaune abba ya aika kiranta.
Da sallama tashiga d'akin cikin abinda baishige minti gudaba tagano damuwar dake kan fuskar mijin nata,
Tambayarshi take cikin taushin murya:"abban zahra lafiya kuwa,meyake damunka"?
"bani ruwa tukun"
Cewar abba wanda yake kokarin tu'be malunmalun d'in dake jikinshi,
Ruwan randar abba umman ta mi'kamashi,ya kafa kai sosai yasha ruwan sida yafara karantama umma yarda daduk wata kaddara ta alkairi kota sharri kafin sanar da ita abinda ya faru da zahran.
Umma kam zuface tagama rufeta,tami'ke da sauri tana kai kawo atsakiyar d'akin sai alokacin ta'iya watsama abba tambayar"yanzu zahran tana inane"?
Shima mikewa yayi yana tafiya yana amsa mata"takamaimai banace ga inda take ba,amma zamu bincika asibitoci muga halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login