Showing 24001 words to 25328 words out of 25328 words
Chapter 9 - MIJIN KWAILA Book Complete .txt
tace"to aibari intasaka gaba muje kugaisa da dady,saimuje mugaisheda gwaggo rabi,mumata bangajiyar biki ko?.
Ishaq kai yasoma sosawa yace'am haba,gwaggo ai tuni mun gaisa,sai dai ko dady din."
Itadai mummy gaba tayi,tana cewa"to aisaika bada himma,dafatan baka mance yau Saturday ba.kace kunada meeting appointed da shugaban NTA akan tafiyar ka ko.?"
Narke idanu yayi yakoma kalar tausayi,yace"ina sane mum but ina tunanin yanda zantafi inbar zahra banmasan iya adadin tym dazanyi a can kasar ba."
Kallonshi mum din tayi tace"wannan aiba abun damuwa bane ishaq, anawa ganin wannan riba biyu ce.natabbatar kafin kadawo zahra takara girma takumayi hankali,da ikon Allah.kaima zakafi son hakan ai."
Sadda kai kasa yayi kawai.
Har akasan zuciyarshi bayason tafiya yabar zahra,haba toma menene amfanin auren matukar baya tare da ita."?
Kai tsaye bangaren dady suka nufa,yana zaune bisa sallaya yana karatun Alqur'ani sukayi sallama.
Saida yakai karshen ayar dayake karantawa yadago kai yana kallonsu hadi da sakar masu mutmushi,
Suma murmushin sukeyi mai,musamman ishaq dayakejin tamkar an nunkamai farin cikin shine.
Mum tafara gaidashi,sannan ishaq shima yabada tashi gaisuwar.
Dady dake shafa kan ishaq yace"babana angirma,naga kwana guda harka kara kiba,me zahra y'ata dafa makane haka".
Mummy data kyalkyale da dariya tace"ah to tambayarshi dai."
Shidai ishaq dukar dakai yayi kawai yana smiling,
Kamar daga sama suka jiyo muryar gwaggo rabi,tana fadin ina mesunan malam din yakene.
Wato nizaka mayar shashasha ko,inzauna tsayin lokaci ina jiranka ashe kainan kataho wajen uwayenka kabarni baki sake,tunda ni ba uwarka bace ko?"
Takare maganar tana shigowa dakin,
Ishaq aranshi banda Innalillahi babu abinda yake mai-maitawa.shikenan yau tsohuwar nan zata mashi fallasa kuwa iri-iri.
Gwaggo rabi data nemi waje tazauna tace"dakai nake,kayimun kasake,nace ina kyallena ko uwayen naka kafara kawomawa sugani.tunda naga ai kabanbanta tskanina dasu,todai kasani tushiya itace mafarin dawa.daban haifi ubannakmeida kaima bai haifeka ba.tomezaku boyemun,inma yarinya bata kawo matancinta gidan miji ba aigwara kufada tunda wuri tagane inda dare yayi mata."
Zufa sharkaf tagama rufe ishaq yace"haba iya,waike meyasa kike hakane don Allah? Nace ai kijirani ina zuwa ko?".
"Injiraka ina?.
Cewar gwaggo rabi dake runtse idanu saboda tsabagen masifa.
Taci gaba" kaga daka ganni nan,duk da banyi boko ba tofa bawata bariki dadan boko zaiyi inkasa ganewa.inma zaka fito da sheda kafito da'ita kowa yagani.nan dai dagani saiko iyayenka gasu,bawani bare acikinmu."
Dady daya kasa gane kan inda zancen yanufa yace"shin tsaya gwaggo, waidon Allah duka wannan tada jijiyar wuyan dakukeyi ta mecece,meke faruwa ne.?
"Ka tambayeshi,"
Cewar gwaggo rabi dake nuna ishaq da yatsa.
Dady yajuyo wajen ishaq dya dukar dakai kasa yace"babana ya'akayine,meke faruwa tsakaninka da mutiniyar taka kuma."
Ishaq ya sauke ajiyar zuciya yace"no dady,bawani Abu bane kawai dai...."
"Kawai dai me?.."
Gwaggo rabi ta katseshi,
Taci gaba"inma zaka fito fili ka sanar dasu gaskiyar zance kafito,donni ba'a munafurci dani kasani."
Dr.rukayya da tunda ake maganar sai yanzu tasa baki tace"gwaggo inaga idan yaki fadi kawai kirabu dashi kisanar damu abinda ke faruwa."
Zumbur ishaq yace"but Mumm."
Da hannu ta dakatar dashi,tace munajinki gwaggo.
Aiko gwaggo rabi kamar dama jira take,tasoma wassafa labarin yanda komai ya wakana AtoZ.ba dady da ishaq ba hatta mummy saida abin yabata kunya.
Tace"gwaggo inaga don-dai bakisan wacece amaryar ba yasa kike wannan maganar,amma duk meenat*a anawa ganin yanzu andena wannan al'adar ai tuni. "
"To gwanar na'iya."
Cewar gwaggon,"aiduk abinda yaronnan yakeyi da daurin gindinki yakeyinshi.amma bari inje wajen amarysr dakaina".
Tamike tana dafa kafa tayi gaba,bata saurari kiran dasukeyima taba.
Ishaq yamike zai bita,dady yace"barta taganota watakila idan tagantan zata dena maganar datakeyi."
Dole yakoma yazauna hadi da dafe kai kawai,yana tunanin rikici irinna wannan tsohuwar.
Da sababi tashiga sashen amma jin anyi tsit yasakata cewa"to lallai y'ar mai,kyaci ubanki kuwa.wato agidan jikana zaki kawomana lalata,to munfi karfinki munrigaki munce Allah kina ina fito algunguma."
Still dai shiru taji,don haka ta nufi dakin datake ktautata zaton na amaryar ne ,tana tijara.
Wayam dakin ba kowa,
Hakan yasakata rike baki dace"ah lallaifa,amaryar kinsamu sake ."
Bata karasa maganar ta ba,tajiyo abu saman kanta racacau...
Tazabura dasauri tace"mun shiga uku,ruwa kuma adaki me rufi?.."
Sauran maganar ta makale afatar bakinta hango zahra datayi can koli bisa wardrobe tana tsotsar magarya.
Fuskarnan tasha shegiyar kwalliyar nan tata mekama data aljanu.
Goruba tadauko tafara gwaguya,bayan tafesoma gwaggo rabi yayan magaryar data tara abakinta.
Tanaci tana gwalo idanu,dayake barakumullah akwai manyan idanu saita kara tsorata gwaggo rabin.
Aiko aguje ta ufa,tana fadin wayyo ku agajeni, jama'a aljana a dakin amarya....
Zahra jin an ambaci aljana yasata durowa Dirk, kamar wacce aka jeho ta rufama gwaggo rabi baya....
*mum meenat*😍
Maman Nasirudden dinku💃🏼
*
*mum meenat
*MIJIN 'KWAILA🤦🏼♀*
Chapter 28.
*Writing by Maman meenat😍*
*Edited by Aisha Abdullahi T.Fulani (Umman farouq)*
*Wannan shafin d'ungurunhun na sadaukar dashi gareki Ameena Muhammad'meenat faxy novel😘.*
*Dakuma Ameenat shamsu,my meenat Ameena Abdullahi kai dama dukkan wata mesuna Amina,hakika mum meenat tana kaunarku sosai*.
*Khairat baffa,da Amshat Kuma ban mance daku ba,Nace kuji dadinku.😉*
Zahra jin an ambaci aljana yasakata wantsalowa tarufama gwaggo rabi baya,
Wasan tsere suka soma,gudun inbakayi bani wuri.
Gwaggo rabi banda ihu babu abinda take zabgawa.
Jin taku abayanta yasakata waigowa,wayyo na Allah na ai qamewa tayi qam.
Bakinta yana karkawar fad'in"qulu,hiya ilaiya,,kuke ganinmu bamu ke ganinku.
Kirufaman asiri natuba,wa'innahu min sulaimana."
Sai alokacin zahra ta fahimci abinda gwaggo rabin take nufi,wato tana zaton itace aljanar🤔.
Dayake abu yazo game nema,dama hausawa sunce wai meneman kuka bare anjefeshi da kashin awaki,don hka zahra ta takarkare tasoma gwagwaloma gwaggo rabi idanu tana tsomalo baki tana kanannade hannuwa.
Gwaggo rabi dai a'inda tayanke jiki tafadi saiga fitsari,sirrrrrrrr yana bin kafafunta yana gangarowa bisa tile's.
Zahra wacce dariya taso kwacemawa tadaure takama kafafun gwaggo rabi tanaja qiiiiii,har takaita bakin kofar falon.
Itadai gwaggo rabi idanu suna rufe,addu'a babu kalar wacce batayi,kai hatta addu,'ar saka tufafi saida gwaggo rabi ta karantota awannan lokaci duk da bama dai-dai take karantawa ba.
Ai zahra nakaita bakin kofa,takoma ciki aguje tana sheka dariya dacewa"y'ar tsohuwa me shegen tsoro,gobema kisake xagin abbana saina jefa maki qadangare ta windon daki.",
Tayi kwafa,tashige bayi tadau soso da sabili tawanke fuskarta fes,tamutsuka mai da powder kawai,tacanja kayanta daga bakar jalabiya zuwa Riga da wando yan Pakistan.
Hayewa gado tayi abinta tana kyalkyala dariya hada rike ciki,aranta ta'ayyana aiko gwaggo rabi tabani tunda haka take da shegen tsoro .
Gwaggo rabi dai tana zaune jagwab kofar daki,idanuwa arufe don duk zatonta Jan dataji anayimata aljanune suka saceta.
Tsoronta d'aya tabude idanuwa taganta fadar sarkin Aljanu.
Dr.aysherh daketa kwad'a sallama itada yar lelenta aneesa wadda takile cikin matsiyacin swiss,jikinta na aman kamshin turare,
Baki tasaki sororo tace"wanake gani haka kamar gwaggo rabi? ".
" Nice y'ar nan,don Allah wacce duniya nake,tamutane kota aljanu?"
Gwaggo rabi ta tambaya cikin rawar murya.
Dr.aysherh tajuya takalli anee wadda kema gwaggo rabin kallon raini,suka sakarma juna murmushi.
Dr.aysherh tace"bude idanunki gwaggo hajiya Aisha ce,nice bude,.ahankali tabude idanun aiko saita kankame hannun aysherh tanacewa wlh aljana nagani adakin amaryar isiyaku,
Har rywan sama tayomun.
Gara mugaggauta barin wurinnan tunkafin takaimu fadarsu."
Dan bubbuga kafarta aysherhn tayi ganin atsorace take tace"aljana kamar ya,ke a'ina kikaga aljanar,?"
Gwaggo rabi baki na rawa tace,",a dakin amarya mana.Nan dai takwashe komai tasanar ma aysha ."
Wani killer smile ayshan tasaki tana kallon aneesa dake smiling din itama.don sunsani babu wanda zai aikata wannan aikin sai zahra.
kama hannunta ayshan tayi tace"saurareni gwaggo, aiwato ita wannan aljanar dakika gani tofa amaryar ishaq ce take rikida tazama aljana.don haka kada kiyarda koda wasa yau ace wani yaji wannan labarin tofa zata biyo dare ta kasheki.
Shawarar dazan baki kija bakinki kiyi shiru karki sanarma kowa abinda kika gani."
Gwaggo rabi tace"aini yauma zanbar wannan jarababben gidan tunda abu yahada hadasu aljanu aikuma bani basake shigowa gidannan har abada."
Aysha ta guntse dariyarta tace"lahh,karki soma,aimaganinta d'aya dazamuyi shine mutursasa ishaq yaqara aure,tanuna anee dayatsa.Kinga yarinyata nan,tanada maganin iskokai,tokawai kiruntse idanuwa lalli idan ishaq bai aureta ba,tofa ko tsinuwace ki gifta akan mahaifinshi.
Tahakane kawai zamuyi maganin wannan bakar aljanar kuma shima jikanki ishaq yasamu magada tunda kindaisan su aljanu bakamar bil'adama Duke ba basa haihuwa."
Gwaggo rabi tayi tsuru,tana ayyana ishaq amatsayin mara hankali,to Mara hankali mana,tayaya zaka hada jini da mutanen 'boye.oh itadai taga takanta jikoki daga me auren kafura same auren aljanu.?"
Tamatse hawaye tana shima aysha albatka tace"wlh ko'ubanwa yatsaya mar agarinnan saiya auri wannan kyakywar yarinyar yarabu da waccen aljanar muje.
Takama hannun aysherh, sukayi gaba aishan nakara zugata dayimata famfo.
Zahra dake labe tanajin duk abinda sukeyi tayi kwafa,dacewa dukanku zakuci ubanku yara.....
*real mum meenat*😍
*pls kuyi manage da wannan,yarona Nasser babu lafiya,shima kyanda takama munshi,kusashi a addu'a da bakunanku masu albarka.Allah yasa yagamata lafiya.*Ameen😭.